Showing 6001 words to 9000 words out of 33160 words
Chapter 3 - MIJIN TACE 4 COMPLETE HAUSA NOVEL BY SODANGI.txt
na sani da wuya kwarai in ga
Mama cikin wani hali da zai bani tausayi cikin sauri,
halin da ya'yanta ke ciki na kasa zaman 'aure da
yanda suka lalace suka zama tanfar ba su ne
wadannan yan gatan ba-da suke sha'aninsu irin
yanda suka ga dama.
Su daura zani irin wanda suke so komai suka yi
shi ne daidai, ra'ayinsu kua shi ne abin dauka, a bar
nà kowa ya bani tausayi bana kuma jin dadin irin
tsana da tsangwàmar da Babanmu ke nuna musu a
zahir nafi sha'awar da sai ya bar abin tsakaninshi da
uwarsu, tunda ita ce tayi sanadin komai.
Wanda duk yasan Mama, ya santa yasan halinta,
33
yagar hain da ita da 'ya'yanta suke ciki a yau, kalma
guda daya da zai iya furtawa cikir sauri ita ce, laifin
uwarsu ne.
Watsewar da aka yi aka bar mu dagani sai Baba
atsakar gida, yasa shi kallons cikii tnuroushi ya ce
min ba za ki sa a kwashe kayan da ki ka zo da su a
kaiwa innarku ta raba ba?
Nayi murmushi na ce ai sai ta.raberwa danginta
Babe namu dangin basu samu bą. Babana yayi
dariyar jin dądi a dalilin jin da yayi na tsame kaina
daga cikin dangin Innata.
Na ce, ai kai ne za ka raba sai kowa ya samu
tunda kowa naka ne. Wani dadin ya sake kama shi,
na ce amma kar ka manta da mutanen giyade, yayi
dariya mai karfi.
To in yi rabo kuma in manta da mutanen giyade
Humaira? Rabo na gaskiya Babana ya yi yanayi ina
tuna mishi wadanda ya manta da śsu.
Makwabta yan uwa, abokan tare ta kowane
bangare ya bayar, don ko ta bangaren Zubaida ya
bata turmi biyu ya ce na mahaifiyarta da kanwarta,
sabulai da omo na mutanen gidansu.
Mama kuwa kaya masu yawa ita da duk wanda
tasa zata ba har ma nata kason yafi na lnnarta yawa,
yana kallona ya ce bamu yi wa Gabo kwauron nata
ba ko? Nayi murmushi na ce, in bai ishe ta ba sai ta
sayà da kudinta ta kara, ya ce to haka.
34
Mun kammala komai ne muka shiga falon
Babana ni da shi muka sake. gaisawae na isar da
gaisuwar Ado a gare shi. Wai shi har yanzu yana
fushi dani ne ko?
Nayi maza na ce mishi a'a Baba, ya zubo min ido
yana kallona, nan take kuma ya zubo min
hannayenshi alamar dakwa.
"Kul ki ka kawo min iya shege, in ba fushi yake
yi dani ba don me tunda ya tafi bai sake waiwayowa
ba, ko a waya bai taða nemana ba'?"
Cikin natsuwa da nuna ladabi na ce, ba zai yi
fushi da kai ba Baba, to shi a wa ma da zai ce zai yi
fushi da kai? Shi din kullum a cikin fadar alherinka
yake.
Yana kuma gaya nin cewar ya karu da ilimi iri-
iri a wurinka na darasin rayuwa, yasha gaya min
cewar kai ne mafi alherin mutuIIn da yasa ni wanda
bai taba kyashin na kasa dashi ya samu alheri a tare
dashi ba.
"Bai yi fushi da kai ba Baba, sai dai kuma zai ji
nauyin kiranka a waya,. watakila so yake ya samu
damar da zai zo gabanka ya roke ka gafara kan
kuskuren da ya aikata maka."
To wane kuskure ya aikata min Humaira? Da ya
rike min ke? Shi mijinki tun kafin ya aure ki ai ni da
na dauke shi to balle kuma da yake aurenki yake
kuma rike min da ke cikin rufin asiri a yanzu."
35
Dadi ya kämä ni na ce to zan gaya mishi ya daina
tsoron kiranka Baba zai. kuma kira ka, to to to gaya
mishi.
Bayan wannan hirar nabi sai na isar da sakon
Ado gare shi na ce, amma ya ce kar in gaya mata sai
in kai din ka yarda ka aminoe, don haka sai in ka
yarda ne zata ji Baba.
Yarda? Yarda kai Humaira in da ina da hali
kamar da da bara ban biya mata ba? To bani da hali,
komai da ki ka sani babu shi, babu shi Baba? Nayi
mishi tambayar a firgice, ya ce ai babu ba I gani ba?
Ina ki ka ga ina zuwa? Nayi salati na ce yaya aka yi
Baba? Na shiga hankaling sosai don jin äbin da ya
same shi.
Sai kawai. naji ya ce min Baba da lorahi, hannu
biyu na saka na dafe kai3a, cikin tsananin kaduwa.
Bayan tafiyar mijinki sai wannan ja'irar matar
muguwa ta tasa i a gaba akan in maida su makwafin
mijinki a kasuwa.
Ta tasa ni a gaba da fitintinu iri-iri sai da na kái
su kasuwar, ba aje ko ina ba sai na gane kasuwar
tawa ba za ta juri ta'adin da ako yi mata ba don haka
sai na rufe ido nayi ta maza na kore su na kuma
haramta musu zuwa kasuwa.
Ni da uwarsu muka shiga wani Irali na babu dadi,
ga can kasuwar ma babu dadi, tunda na riga na samu
matsala, abokaina duk sun yi gaba sun bar ni, don
36
haka sai na ce to wadannan gidaje da mijinki ya
dawo min dasu tunda dama ban san da su ba, bari in
sanya su a kasuwa in karbi kudinsu in kara jari don
in koma harkar sosai.
An kawo min kudin gidajennan da kwana biyu
don mutum daya ne ya saye su, barayi suka zo min
gidan nan da daddare suka shigo min nan.
Kin ga kin gani ya nuna min wani shafcecen tabo
a keyarshi wanda na tabbatar ban san shi dashi ba ya
ce su suka buga in karfen da suka zo dashi suka
bincike min daki suka dauki kudi suka bar ni nan a
kwance a sume.
Sai daga baya sai da asiri ya tonu aka samu aka
kama guda daya, sai ya ce wai su Ibrahim da Baba ne
suka turo su zo suyi min satar.
Ni kam kuka sosai na kama yi saboda bakin ciki
da tausayin Babana, tabbas Mama ta cuci Baba na,
don kuwa ita tayi mishi sanadin lalacewar 'ya' yanshi.
yayan da kowa yasan babu abinda bai yi akan su ba,
don su zama mutanen kirki.
Bata aike shi ba, bata kuma bar shi yayi shi
kadai ba, kullum gini yake yi tana rusawa share
hawayenki kiyi shiru, Humairah ai ya wuce.
Ya wuce, kana zaune baka komai Baba? Yayi
murmushi ya ce to ba gani a raye ba? Da sun yi
nasarar kashe ni ko nakasa ni a wani wuri fa? Na
sake fashewa da wani sabon kukan.
37
Baba Yahya ne ya iso saboda kiran da Babana
yayi mishi, matar Sarkin Noma ne ta iso, nayi
murmushi na soa gaishe shi ai tunda naga tsaraba na
ce to ta Dabai ta iso kenan?
Babana ya kyalkyale dadariya, ya ce ai sunan da
ka sanya mata kenan? Baba Yahya ai ni sunanta
kenan a wurina tunda dai ta ki zama cikin mu ta
koma cikin danginta, to ba zan kirata da wani suna
ba, sai wannan ina ta ke?
Babana ya daga murya ya kira Zubaida da ke
goye da ita ta kawowa Baba Yahya ita ya karbe ta
cikin farin ciki yana fadin ka gani ba, wannan da
ganinta ai kasan gidan noma ta fito, taci hatsi ta
koshi.
Baba ashe abinda ya faru kenan mu ba mu sani
ba? Na tanbayi Baba Yahya cikin natsuwa don in yi
mishi jaje, sai ya ce min kece ba ki sani ba Aisham,
amma ko sanda muka je wurinku, ni da Mallam ai
mijinki ya yi mana jajen al'amarin ya ce min Innarku
ce ta gaya mishi.
Mamakin Ado yayi matukar kama ni, me yake
nufi da wannan abin da yayi bai gaya min ba, bai
kuma yi wa Babana jaje ko a waya ba?
Maganar tafiyar Inna da ya soma yi wa Baba ya
katse tunanin nawa, ni kam in ban da alheri Ado ya
yi wa Innata ai da na karbe kudin na mayar mishi
dasu, ban ji dadin yanda yayi ko in kula da abin da ya
38
samu Babana ba.
Baba Yahya ya yi matukar murna, ya yi ta
addu'a yana sanya albarka, ya rungumi kudi ya tafi
dasu, wai zai je yayi duk wani abin da ya dace a
gama komai sai bayan tafiyar tashi ne ma maganar ta
watsu a cikin gida.
Mama tayi matukar kidimewa, hankalinta ya
tashi ta shiga rusa kuka tana zage-zage, Zubaida
kuwa sai faman tsalle take yi tana murna tana fadin
yau fa ga inda haihuwar 'ya mace tayi rana.
An mallake ta ita kuma ta mallako wa uwarta
mijinta, Inna kam ba zan iya kwatanta farin cikinta
ba, kan ka ce meye wannan yan uwanta har sun cika
gida da kuma makwabta, har lokacin Mama ba ta
daina kuka da zage-zagen da take yi ba.
Babana yaje ya daga labulenta ya ce mata, ji
mana Majadan, kin san dai dama na gaya miki
sharadin zamanki a gidan nan yanzu shi ne ki zauna
da kowa lafiya, don ba. zan iya lamuntar hayaniya ko
tashin hankali a cikin iyalina ba.
Don haka in kin ga kina da matsala ko za kije
gidan ku ne? tayi maza ta suro gyalenta ta yafa ko
gama rufe jiki bai yi ba saboda nadewan da yayi tana
fadin ebh, ai gara min hakan yafi min wannan zaman
da nake yi cikin bakin ciki, wulakanci da kuma
zalunci.
Ni kam ai ba zan taba yafe aka ba, sai kaga
39
8akamakon...Babana ya bi ta da kallo yace, ke
Majadan ki taimake ni in kin je gidan naku kar ki
dawo."
Cak! Marma ta tsaya, ban san tunanin me tayi ba,
sai kuma naga ta juyo ta shige dakin nata tayi shiru.
Kwanana biyu a gida na soma zaga dangi yan
uwa da kuma abokan arziki, har giyade na tafi da
zani kuwa mun tafi ne da su Atika da Aliya da
Sa'adatu.
Kan hanyarmu ta dawowa daga Giyade na yi wa
yan uwana magana kan halin da Babanu yake ciki na
zaman rashin abin yi, bai kamata mu bar shi a haka
ba.
Aliya ta kalle ni cikin natsuwa ta ce, ni kam Anti
ban ga abin da ya shigar damu cikin wannan maganar
ba, musamman ke matsalarsu shi da matarshi da
'ya'yansu, mu kam ai ko da yake harkar ma anyi
lokacin da abinci ma aka hana shi.
Ba mu koshi da abin da ya faru nayi ta kawo
mishi kaji yana ci har ya murmure, ba shi kenan ba?
Innarmu bata cikin matsala, ba kua zata sake shiga ba
da yardar Ubangii, to su karata mana ko kuwa Anti?
Ta zubawa Atika ido, Atika ta tabe baki ta ce,
uhn, kyale Anti kawai in kudin sunyi miki yawa ne
ki kawo a rinka juya miki su zasu yi amfani a gaba.
Na zuba musu ido ina mnamakin yanda ko kadan
basa tausayin wahalar da Babanmu ya shiga kan in yi
40
musu wata magana sai Atika ta ce min ni ina ce shi
ya kore ki ke da mijinki don taji dadi.
Kuje ku kuma ku wulakanta sannan bayan tafiyar
taku kin san abin da ya faru? Nayi maza na ce mata
a'a, ta ce ina ce sakin Inna yayi?
Da karfi na kurma wa Atika ihu tare da fadin kar
kiyi min haka Atika, ta ce to tabar maganar. Ta ci
gaba da baiwa Baba nono wanda ni na mika mata shi
ta sake waiwayowa tana kallona cikin natsuwa ta ce
min.
Ina ce sai da suka yi mishi abin da suka yi mishin
ne da ya kori uwarsu a gidan shi ne yazo wai inna ta
koma, su Baba Yahya suka ki da Alhaji Babba, shi ne
mai babban allo ya ce a'a ta koma dakinta ta zauna
saboda in muka je gidan mu samu dakin da muka
shiga, muka zauna.
Amma ba za ta koa ba sai yaje ya daidaita da
matarshi ya dawo da ita tukuna, ya hada su dukansu
yayi hakuri ya zauna dasu don sun riga sun zama
bangaren rayuwarshi.
Inna tana da matsala ne? bata da ita, kullum Yaya
Ado yana yi mata aike tana gaya mana ni ta bangare
na mijina ba mai sakin kudi ba ne, saboda yana taka
tsan-tsan dukiyar ba tashi ba ne ta Baba ce.
Ama ya samar min da wata hanya da ake juya
min kudi, ina armfana ina yi mata abin da nake iyawa,
Aliya ma tana yi mijin tama yana yi darna kuma
41
danta ne tana kuma da 'yan uwanta ga shagonta na
dinki.
Kin ganta da matsala ne? na girgiza kai a hankali
cikin sanyin jiki, can' cikin zuciyata kuma na gane
abinda yasa Ado bai taba furta min abinda ya farun
ba, tunda na Innan ma bai gaya min ba.
Mun dawo gida da yamma gaba daya nuka dawo
sai dare mazansu zasu zò su dauke su. Sa'adatu tana
goye da Umahmnah, ni kuma in rungume da Babaa
akan kafadata, yayin da Atika da Aliya suke rike
mana da kayan tsarabar kauye da muka dawo dashi.
A tsakar gida muka samu Babana ya kwance
buhun shinkafa yana aunawa can gefe kuma ga doya
ya kasata kashi uku, Mama tana tsaye tana kallon
abin da yake yi.
Karo na farko da na ganta a tsakar gida tun da
nazo, da sauri naje na kwantar da Baban Atika a daki
na dawo na karbi mudun a hannunshi ina aunawa
yana nuna min in da zan saka.
Kin ganni ina awo ba Humairah? Na ce mishi eh
Baba. Ya ce to daurowa yake yi a daure, Alkali kin
gane? Na ce mishi eh, Baba. Ya ce to kin ga wannan
buhun shinkafar da wannan doyar kawo min su aka
yi kyauta
Na yi wa wanda ya kawo din addu'a, Babana ya
amsa da amin. Kafin ya ci gaba da yi min bayani.
Yanzu komai raba shi nake yi a gidan nan in kasa
42
kashi uku in baiwa kowa nashi ya adana a wurinshi
saboda Inna ce zan ajiye ayi amfani da shi gaba daya.
To sai a biyo dare a kwashe aje a Boye ana baiwa
kattin banza kin ga haka zai yiwu? Duk da Mama
tana wurin bai hana ni cewa a'a ba, a zuciyata na ce
ke ki ka koya mishi cewa ana kwashe mishi hatsi ana
6oyewa.
Shi yasa nake rabona daidai da daidai rabo na
adalci in kasa kashí uku kowa ya dauka, ko kuwa?
Na ce haka ne, nayi kamar in ce amma da an dan yi
wa adalcin kwaskwarima, don ya kara tafiya daidai.
Tunda ita Zubaida babu da ko daya a dakinta, ita
ita kadaice sai kuma ake yi mata rabo na daidai
tsakaninta da Innata mai ya'ya uku da kuma Mama
mai 'ya'ya uku manyan mutane duk da ita hudu ga
kuma jikoki guda bakwai.
Da nayi wani tunanin sai naga to menene nawa a
ciki in ja bakina kawai in yi shiru mana, mai ya kare
musu a tsakaninsu.
Na daga ido na kalli Mama da tun sanda Babana
ya ce mata dauki take kallon kason ta rasa wanda
zata zaba. Furfura na gani a girarta da kuma gashin
idonta.
Gabana ya fadi na ce ashe a kan yi furfura har a
gashin ido? Lemon da nayi mata a tsakar gida yau ya
Kara bayyanar min da sirrin al'amarinta gaba daya.
Gaba daya ta canza, gaba daya tsufa ya yanko ya
43
afka mata, sai ka ce wacce tayi tamanin alhalin
kwata-kwata shckarun Mama in tayi da yawa ne zata
yi hamsin koda biyu, shekaru biyu kawai da suka
wuce ai gamu dinta take a cike ga kyau ga zati ga
kwalliya, ga iya isa da nuna gadara.
A zuciyata na Kara tabbatarwa kaina da cewar
babu abin da yaff bakin ciki nukurkusa dan Adam,
musamman ma amce ace tana fuskantar bakin ciki
kan haihuwarta da kuma aurenta wanda abin da ya
samu Miama kenan a lokaci daya.
Tunda yanzu dai a zahiri yake a bayyane in
akwai abin da Babana yake zaune dashi akan lalura
to Mama ce de 'ya' yanta wadanda a baya kuma su ya
ray tsawon rayuwar shi yana so yana fifitawa yana
yiwa hidina da dawainiyar ba tare da yana tunanin
akwai wasu masu hakki a bayan nasu ba.
Babana yaja tsaki saboda kallon kashin da Mama
ke ta yi, ki dauka mana. Yayi maganar cikin tsawa,
idonta yana kan na gabanshi, ta nuna da hannunta ga
wanda nake so.
Haushinta ya kama shi an ki a baki wannan din
na gabanki za ki dauka.
Na ce yi hakuri Baba, bari a kwashe mata
wannan din, nasa hannu na soma diban doyar ina kai
mata kofar dakinta su Buhari suna karasa mata dashi
cikin daki. A zuciyata tunani nake yi a irin iyalin da
ke dakain Mama,
44
Wannan kason da aka bata kwana nawa zai yi
mata? Da na dan yi wani tunani kuma sai naga to
Mama ma dai ba abin tausayi ba coe, sai dai kawai
mutum ya tausayawa wanda yake tare da ita saboda
shi din dan uwanshi ne.
Amma in ba haka ba ai tukunyar gidanmu tana
hade ana girki gaba daya na wajo ma in ya shigo
gidan mu zai ci ya koshi, Babana yana cikin
harkarshi bai da wata matsalar babu.
A wannan lokacin tasa iko ta raka tukunyar ta ce
kowa yayi girkin shi don kawai ta ganawa Inna
azaba, ga bakin cikin kishiayr da tasa aka yi mata, ga
hakkokinta na aure duk ta danne sai wanda tsananin
rabo yasa aka bata.
Amma bai isheta taga bari ta ganawa 'ya'yanta
azabar yunwa.watakia tana ganin ta hakanne kawai
zata iya korarta, to wahala kam mun sha daidai
wargwado, amma bata yi nisa mai yawa ba sai ta
wuce maha ta kuma wucewa uwarmu ta kuma juyo ta
dawo mata ta inda bata taba zato ba.
Wai ace mutum bai san yayi adalci ba? An ce a
karkace za'a tashi amma shi kullum aikinshi kenan
zalunci, cuta, a raina na ce yau kenan ki ka san
wannan.
Zai yi magana nayi maza na ce mishi, kayi
hakuri Baba. Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce, in yi
hakuri ta zage ni? Na ce eh ai babu komai, ya ce to
45
shi kenan. Nasa hannu na sake kwashe kashin da yafi
dama-dama bna kaiwa Zubaida.
Na kirą, Sa'a ta kwashéwa nnarmu na karshen
tunda dama kason nashi hawa-hawa ne, wani yafi
wam na' kuma sân Zubaida yaso ya baiwa babba, ita
Mama dan Rararain Innarmu ta dauki na tsakiya sai
Mama taki.
Shi wansan rabo da ki ka ga ina yi, na ce eh
Baba, ya kale ni yà cc shi ne kaso na gaskiya, da
sauri na ce mishi haka ne Baba.
Ba tare da na tambayi dailin shi na fadin hakan
ba, sai naji yace min ita wannan yarinyar ya nuna
min dakinta, nayi murmushi na ce anti? Yayi maza
ya ce min eh, na ce eh, ya ce shi yaroh yasan babu ne?
Nayi maza nå ce mishi a'a Baba bai sani ba, ya
ce to kin ga dole a bata da yawa, na ce haka ne. Ya
sake nuna min dakin Marma da dan yatsanshi, na ce
eh, alamar na gane. Ya rage inuryà ye ce ni ne zan
zauna ina ciyar ta ya'yan gidan wasu da kuma
zäurawa?
Nayi maza na ce, a'a Baba, ba zai yiwu ba.
Amma itama Habiba auren ya mutu ge? ya girgiza
kai nuna alamar bai mutu ba, ya ce amma an samu ta
koma da kyar ta haihu a can taje tayi fada da uwar
miji akan naman suna.
Daga cikin dakinta Zubaida ta daga murya ta ce
fada ko duka? Dukan uwar mijin tayi, nayi kamar
.
46
ban ji ba, don bana son hirar tamu ta zama sanadin
fitina.
To ita Innarkı ko ban bata ba tana da shi, wani
lokaci ma in naga zata kure min Zubaidan ta rasá,
shiga wurinta nake yi in debo mata na ce haka né
Baba.
Da iyakacin gaskiyata :sai naga hikiar rabon
nashi, don haka ko babu adalci a ciki to daj akwai
dabara tunda shi ka adalci ai bai wuce baiwa mai
hakki hakkinshi ba.
Rannan muna kwance ni da Inna alkan gadonta
bayan su Atika, sun tafi gidajen su sun bar mu, hirą
muke