Showing 33001 words to 33160 words out of 33160 words
Chapter 12 - MIJIN TACE 4 COMPLETE HAUSA NOVEL BY SODANGI.txt
ganin tanfar da dai
ace shi din shi kadai halinshi kan gamsar har ya iya
wanke laifuffukan da sauran yan uwanshi kan yi wa
sauran mata, to da sai in ce wa 'yan uwan nawa mata
cewar ai babu wani goyo mai dadi irin goya
NAMIJI.
Don kuwa shi namijin ba kowa ba ne face wani
cikakken mutum kammalalle, jarumi mai fuskantar
kowane irin al'amari da karfin zuciyarshi, mai iya
Juyawa daga wani mataki ya koma wani ba tare daa
yana waiwaye ba.
Mai tarar kowane irin wahala da jaruntakarshi
don ya zamo kariya ga na kasa da shi mai sanin ya
kamata wanda kuma yake iya saka alheri da alheri.
Ni kam a wurina wannan shi ne namiji.
Na gode.
159
Mu sake gamuwa dàku cikin wani sabon littafin
nawa IN KUNNE YA JI...' Hausawa suka ce wai
jiki ya tsira, da ikon Allah zamu sake haduwa daku
nan ba da dadewa ba, cikin yardar Ubangijinmu.
Kafin nan ina yi muku sallama tare da cewa;
(Wassalau alaikum)
Allahumma iah sahala illa maja'altahu sahalan,
wa'anta taj'alul hazana izah shi 'ita sahalan."
Na gode.
Hafsat Chindo Sodangi.
17/1/2013
160