Showing 24001 words to 27000 words out of 33160 words

Chapter 9 - MIJIN TACE 4 COMPLETE HAUSA NOVEL BY SODANGI.txt

an riga an yi ta ba, Mallam
Umar sai yasa a fasa abin da aka sa a gaba? Ya ce
a'a Inna a dai bar shi a hakan kawai na juya na fita
na basu wuri cikin zuciyata dai ina mamakin abinda
aka sanya a gabad a ya sanya Inna fadin mutuwar
Mallam ba za ta bana ayi ba.
Nasan lalle yana da muhimmancia wurinta.
Kwananu biyu a gida na kwashe iyalina muka
koma gida muka je muka samu Mama wacce ba sai
na tsaya fadin mutuwar Mallam tayi matukar
faranta mata rai ba, a zuciyata na ce uhun murnar
mutuwa kam ma ai murnar banza ce, tunda kai ma
mai murnar ba ka tsira ba, wani naka ma bai tsira
ba.
Kwananmu biyu da komawa, Ado yayi
tafiyarshi wacce dama zai yi rasuwar Mallam tasa

117
ya daga, ni kam ina gida tare da iyalina tunda
Mallam ya rasu na kara maida komai ba komai ba.
Kullum sai na tuna shi, na tuna kalamanshi
musamman nasihohinshi da mafi yawancin lokaci
yake yawan nanatawa, wannan duniyar ai ba komai
ba ne, dan dadinta kuma takaitacce ne.
sAl' amuran cikinta kuwa in har kana da hankali
to na tsoratarwa ne, ina iyayenmu suke? Ai muna
kallonsu suka kare ba mu yi komai ba don ba mu
da ikon yin to haka randa tazo kanmu to gashi
kuwa tazo din yau baya nan.
Duk yawan iyalinshi kuma taruwa kawai muka
yi muka yi kuka muka tashi wannan kadai ya ishi
bawa tsoro.
Sati biyu da tafiyar Ado ya dawo ya kwana a
gida gari ya waye daga ni har shi ga dukkan alamu
muna cikin jimami don 'yan abubuwan da suka
gudana a tsakaninmu duka babu wani matsanancin
nishadi a ciki.
Tun kwanaki fa naso muyi wata yar magana
da ke rasuwar da aka yi ne yasa na dakatar da
al'amuran zuwa wannan lokacin.
Na zuba mishi ido ina kallonshi cikin natsuwa
da sauraro. Sai naji ya ce min kin san abokina na
ruwan bungo da matanshi da iyalinshi duka na ce
mishi eh, ya ce ke da kanki ne kike gaya min cewar

118

suna da kokari wajen kula da tarbiyar 'ya'yansu, na
ce haka ne.
Ya sake kallona cikin natsuwa ya ce min, to tun
kwanakin baya kamar sati shida da suka wuce nayi
mishi waya na ce mishi in akwai yarinya budurwa a
gidanshi ina so.
Abinda naji a zuciyata yafi karfin a kira shi
faduwar gaba, na dai daure kawai na zuba mishi
ido ina kallonshi cikin wani yanayi da ban tabbatar
ba a-farke nake ko a mafarki nake oho?
Ni da ke muna da fahintar juna, kanmu a hade
yake bamu da wata matsala a tsakaninmu, yarinyar
da zan kawo ba wata yarinya ba ce da ba ki san
tarbiyarta ba, kin san iyayenta kin san komai dinsu.
Har ma kuna mutunci ke da su.
Yar wajen Hannatu ce, bana so ki dauki wani
abu da tsanani ko kiyi tunanin saboda wani zan yi
musamman da yake na sha gaya miki cewar ina son
mata biyu amma ba zan yi ba, sai adaidai lokacin
da ke da kanki za ki shaida cewar nayi miki adalci.
Ban san yanda aka yi ba, sai kawai na tambayi
Ado to adalcin me kayi min a yau da zaka kawo
min ita? Ban san shi ba in kuma akwai shi nuna
min shi.
Shiru yayi yana kallona, bai tanka ba, tuni naji,
wani abu yana motsi cikin Jikina daya sani

119

shure mishi abin karyawan nashi da kafata na mike
tsaye ina fadin, ai tuni nasan abutarka da Mallam
Haruna in ba sa'a nayi ba tsiya zata zame min.
Baka da hira sai ta ya yanshi ni ina nasan su
balle in san wata tarbiyar su da ka ke cewa na gaya
maka? Ina ruwana da su, Mama ce ta saka kayi
aure don burinta ya cika ba kuma zai cikan ba a
haka zata mutu.
Kar ki zagi Mama Humairah, saboda bana so
kiyi sanadin da maganar zata lalace a tsakaninmu,
kar ki neme ni da fitina tunda ni ba ita nake nema
da ke ba.
Ki bari mu tafiyar da al'amuranmu yanda muka
saba yi saboda yaran nan sun riga sun fara wayo
bana so su shaida wani sabani a tsakaninmu.
Na mulmulo wani irin mahaukacin ashar irin
wanda ban taba ba na antakawa yaran na ce su
sheda komai, saboda ka shirya cutata wannan
mutuwar tsohuwar tasa ka kayi aure mugu...caraf
yayi ya kama min baki ya rike, yana sakin bakin
kuma ya faska mishi mari.
Kafin ta sa ni auren wata ai ta sani aurenki,.
kenan ba yau na fara yi mata biyayya akan aure ba.
Hannu biyu na saka na kama rigar Ado na rike
na ce to a saken kawai tunda ai bayan umarnin
aurena ta baka umarnin sakina sake ni kawai a yau

120
kowa ya huta.
Kama hannayená nayi yá tattara su wuri daya
ya hada su a jikina, ya hankada ni nayi tsalle na
kife can gefe. Ya kama hanya yayi tafiyarshi
Ana cikin haka sai ga su Ruwailah sun iso da
su Furerah, Jama'ar cikin gida gaba daya sai 'yan
kadanne ba su zo ba, gaba daya labarin auren Ado
ya bazu ko'ina.
Don haka suka zo su jajanta min al'amarin
tunda su din a yau nawa ne a bangarena suke.
Muna zazzaune jungum-jungum gaba daya mun
buga uban tagumi, kowa da lissafin da zuciyarshi
take yi, na hanyoyin da zamu bi auren ya wargaje
kafin ranar daura shi.
Sai da Sa'adatu ta iso tana rike da hannun
danta sun sha kwalliya sai walkiya suke yi. Hajiya
sannu da zuwa, suka soma gaishe ta tana amsawa a
lalace, a wulakance na zuba mata ido ina kallonta.
A zuciyata ina tambayar kaina dama yarinyar
nan ta iya yi wa mutane irin wannan wulakancin r
ni ban sani ba? Wai ita matar me kudi ko? To bari
Ana gama gaisuwar ta mike ta nufî can cikin
daki ta bar mu, don haka muka ci gaba da tattauna
al'amuranmu irin masoya sai gata ta sake fitowva
fuskarta a murtuke kai duk ku watse ku bar gidan
nan ko kuma in kira Yaya Ado in gaya mishi

121
abinda naji kuna tattaunawa a kai.
A fusace na ce mata, ke Sa'a za ki ci mutuncin
mutanena ne a gabana? Kina hauka ne? za ki kawo
min iskanci ne da rashin kunya? Nan da nan ta
kama kuka haba Anti, kishiya musiba ce? Da in
za' ayi miki ita sai ki birkice ki fita hankalinki ki
tara mutanen da zasu yi miki karya?
Su wacece bata da kishiya a cikinsu? In kura
tana maganin zawo tayi wa kanta mana, kin san ki
ga yawa wani gaskiya ya ji amma in gaskiyar tazo
kanki ba za ki iya aiki da ita ba?
Na wanke Sa'a da mari mai kyau saboda
maganganun nata sun zama rashin kunya a wurina.
A'a-a'a to mu kam barî mu tafi, su Ruwailah
suka soma zare jiki suna shiga suna gaida Mama
daga can kuma sai su wuce, ta sake kallona cikin
natsuwa ta ce min.
Sai dai kiyi hakuri Anti, ko kuma ki mike kiyi
ta dukana amma zan gaya miki cewar wannan
kishin naki bai dace da ke ba, don kuwa yafi kama
da kishi irin na jahilan mata, ba matan da suka
karanta addini suka san shi ba.
Ita kaddara yarda da ita ai sharadi ne na cikar
Imani, kaddarar kuma wacce ka ke so ne da wacce
ba ka so, kan ayi miki kishiya ai Anti Aliya aka
fara yi wa ba kya nan ne lokacin yasa baki ga bukin

122

da muka yi ba ita irin kishin Innarmu take ji ke kua
kina yin irin na Mama.
Na kalli Sa'a cikin tsananin fushi na ce, ranki
zai 6aci fa, ta ce kiyi hakuri.
Ado ya shigo, Sa'a tana ganin shi ta soma
murmushi, Yaya ashe kana gida? Ya ce, mata eh,
yasa hannu ya dauki danta ya rungume a jikin shi,
me yaron nan yake ci ne haka?
Ta taya shi murmushin da yake yi ta ce ai
shekaran jiya naji Barisster yana cewa wai wannan
yaron irin Baba Yahya zai yi. Ado ya kyalkyale da
dariya ya ce, ina ruwan Super D.
Ta gaishe shi cikin ladabi tana tambayarshi
yaya ashe hidima tazo? Bai amsa ba ya dan kalle ni
kun tattauna ne da yayar taki? Ta ce uh uhn ai ni ba
wurinta nazo ba, ba ita nazo wa bukin ba.
Ni ki ka zowa kenan? Tayi maza ta ce mishi eh,
ai shi yasa nazo da wuri don in akwai wani abin da
za'a shirya mishi sai a shirya. Dadi ya kama Ado
ya ce to muje wurina mana ki sauka a can ai akwai
daki, kya so ki zauna a nan?
Ya mike ya daukan mata danta ita kuma taja
jakarta suka tafi, ina kallonta sai da ta shiga wurin
Mama ta dade kafin ta fito ta shiga wurin nashi, a
zuciyata nace lallai Sa'a ba karamar mara mutunci
ba ce, amma barta ni da ita ne.

123

Daga can nesa ne kawai nake hangen Sa'adatu
da irin kaiwa-da-komowan da take yi tsakanin
wurin Ado, wurin yara, da kuma na Mama da ma
kuma ita din aminiyar yara ce.
Amma ni ko kallon wurina bata yi, sai
mamakinta nake ji wato ita wannan saboda Ado
abokin mijinta ne shi kenan ta koma bangarenshi
kenan?
Wajen karfe hudun yamma sai ga Hajiya Aliya
da 'ya'yanta guda biyar maza biyu mata uku da
kannen mijinta biyu yan mata ya'yan amaren
Hajiya Kubrah.
Tana ganina ta kalle ni ta ce yaya haka Anti?
Nayi murmushi na ce babu komai Aliya, me ki ka
gani? Ta kalli 'yanmatan da tazo dasu har da
ya'yan nata ta ce wa Umahmah da tazo gaisheta
kuje tare ki kuma maida su yan gida tayi
murmushi ta ce Inna ai ba baki ba ne ta ce eh amma
ki kara, suka tafi.
Sa'adatu ta hauro saboda ganin zuwan Aliyan,
na gaya mata abinda Sa'an tayi tun kan Sa'a tayi
magana Aliya ta kalle ni ta ce haba Anti, in ki ka ce
haka za ki yi ai mu da uwarmu ki ka tozarta babu
irin mutanen da ba mu tarawa yaya Ado a gidan
nan ba sanda yayi hidimar Sa'a ya kuma yi. mana
goma shatara ko ma ashirin da tara ta arziki.

124
Sai kuma yanzu hidima tazo kan shi zai yi kice
za ki tsuke fuska ko ayi tashin hankali da ke?2
Gaskiya ba ma ciki, shi kishin mafi ba yanda ki ka
ga na gidanmu yake ba, ki kama mijinki kawai ki
rike gam a hannunki, ba wai ki rike shi a jiki ki
hana shi zuwa wajen wata matar ba.
Ki hanata hadakinta a'a ki bar mishi jikinshi
yayi ta yawo yaje wurinta ya ji dadi yayi abinda
yake so ya more, Ubangiji ne ya halatta mishi ita,
amma ke kina rike da zuciyarshi in da duk yaje
yana tunawa da ke in zai yi magana sunanki zai
ambata, in zai fadi alheri naki ya sani.
Sannan ko mu yanzu a gidan namu ba ki ga
yanda Inna ta maida gidan ba, Zubaida da 'ya'yanta
ai basa gabanta, tuni ta sake hada girkin gidan
tunda Mama ta fita ta bar musu gidansu ke. baki ga
yanda Baba ya yi gwanin kyau ba?
Sa'a ta ce a to, shi Yaya Ado ma ba zai takuru
ba tunda ba ki ga abinda ke cikin wurin nashi ba
wal kawai in kin ganshi sai kin yi mamaki, gashi
kuma naji yana maganar kayan daki ina jin shi ne
mai yi.
Na ce to ba gashi ba tun ba a yi auren ba zai
fara zalunci. Aliya tayi maza ta ce zalunci anti?
Yanzu ke akwai wani abinda Yaya Ado zai yi waa
wata mata ki ce ya zalunce ki?

125

Sunkuyawa fa yayi ya yi noma yana yarfe gumi
ya tara kudin ya biyawa umarmu kujera taje ta sauke
faralinta, bayan nan ki ka biya mata da kudin aikinki,
yazo ya mallaka miki gonar da a yanzu duk shekara
ki ke kaita Ummura da watan Azumi kin kai Baba
kin kai mai babban allo.
Ba daga gidanmu ki ka zo da gonar ba sannan in
kin manta in tuna miki ba ki zo gidan shi da kayan
daki ba, kuma in ba ki sani ba in gaya miki ba fa
tsoronki yake ji ba.
Yana jin kunyar ki ne saboda kin yi sa'a yana
sonki yana kuma ganin darajar iyayenmu, to taimake
mu ki bar shi a haka kar ki kure hakurinshi don ko su
Ahmad da suke 'yan uwanmu ne in suka balle hancin
tsiya ba dadinsu ake ji ba.
Sa'a tayi mazá ta ce, na dai gode.
Ado ya shigo daga waje da sauri da alamar yaga
zuwan nata, Hajiya Aliya ashe kema kina tafe tun
yau? Ta ce eb, Inna ce ta roke shi ya bar ni in zo da
wuri don in kawo maka wannan sakon.
Sako? Yayi tambayar cikin tunani, ta ce eh, tayi
maza ta jawo katon akwatin da ta zo dashi wanda
nayi zaton kayanta ne da na ya'yanta a ciki, tana
bude shi ta soma zaro atamfofi tsala-tsala duka super
guda shida, manyan lesuna hudu da kuma shaddoji
masu tasa guda biyu.
Tana gama zaro su ta ce wai in ji ta a kawo maka

126
ka zuba akan na lefe.
Wani irin matsanancin dadi ne ya kama Ado, a
hankali ya nemi wuri ya zauna a bakin kujcra cikin
natsuwa ya ce, Aliya, tayi maza ta amsa na'am Yayya,
ya ce mahaifiyarku tana da girnma a wurina, saboda
ita din wata irin mata ce da samun irinta yake da
wahala.
Ina matukar girmamata sbaoda halayenta na
girma da mutunci ga ta da adalci ga na kasa da ita,
amma Humairat bata gane abin da nake nufi ba. Naje
na same ta ita da mai babban allo nayi musu maganar
zan yi aure amma ina so suyi wa Humaira magana
don bana son matsala a cikin iyalina.
To kan akai ga hakan ga Mallam babu shi, ni
kuma a yanzu ba zan je in kai kararta wurin Inna ba,
zan bar Inna kawai tunda nasan ita bata manta
mahaifinta ya rasu ba, kamar yanda ita Humaira ta
manta.
Aliya tayi maza ta ce, itama bata manta ba Yaya,
ya ce ta manta tunda ta bude baki ta zage ni ta ce in
tuna mata da adalcin da na taba yi mata don ita bata
san shi ba.
Aliya tayi salati ta ce, in ita ta mantra su mu ba
mu mance ba, ba kuma zamu mance ba. Amma
maganar zagi kar ka rinka fada yaya, ya ce kar in ce
ta zagen Aliya! Ta zagi Mama a gabana ta kuma
durawa ya' yana ashar a gabana?

127
In haka ake karatu zan barta tayi ta zaryar
makarantar addini? Aliya ta ce ai matsalarmu kenan
yin aiki da abin da muka sanin gashi kuma kullum
ana gaya mana cewar mu mata babu abin da yake
saurin kai mu wuta irin kafurcewa ni' ima.
Amma kayi hakuri ya ce to yaya zan yi? Alamar
dai ranshi ya baci sosai da abinda nayi mishin.
Gaba daya 'yan uwana har Atika da ta iso bata
goyi bayan yanda naso mu yiwa bukin ba, itama
cewa tayi mutuncinmu zamu zubar, don haka
rungumar hidimar suka yi da hannu bibiyu suka
kankane komai, wanda ba haka Mama taso ayi ba.
lta taso ne a warc ga 'yan uwan Ado da nawa sia
ita ta jagoranci hidimar Ado sai taga ba haka ba ne.
Dangin Inna da na Babana da suka zo min bukin
ba za su lissafu ba, su Habiba da Anti Kaltume ma
muna hade dasu, Sha'awa da Suwaiba ne suka koma
wai su suná dangin miji.
Ga kawaye na zamani, kawayen da aka yi bayan
daula ta sau, don haka hidima sosai aka yi.
Kane-kanen da Sa'a tayi kan hidimar Ado ba
karamin taimako ko amfani yayi min ba, ba don ina
ganin kO za a zarce ni da wani abu ma to ba wani mai
yawa ba ne sai dai duk da haka zafin yana nan a can
ciki zuciyata tafasa take yi.
Wani lokaci ni da kaina ma mamakin kaina nake
ji, saboda a farkon rasuwar mai babban allo na dauka

128

babu wani abin'da zai sake samuna in ji zafinshi, sai
gashi maganar auren Ado yayi min wani irin dukan
da ya kidimar dani.
Ya mantar dani wast abubuwa masu yawan
gaske, kai kishi al'annsrin shi yana da girma, sai dai
kawai hakuri. Tsananin batin rai ne yayi min yawa,
bakin ciki ya addabi 2mciyata. yayi dalilin da ya sa na
kame bakina na kulie shi nayi shiru na daina fadin
komai in ban da 'la'haula wala kuwata."
Hidima irin wacce Ado yayi tana da yawa, wane
ta bukin Sa'adatu, da nake ta bada labari, iyaka dai
kawai na sani ko da nake wurina a kammale 'yan
uwana su Habibah su Aliya, Atika, Anti Kaltume,
Sa'a sune suke tsarc da komai.
Anyi daurir aure an kuma ce min har sü Babana
da su Baba Yahya da su Alhaji Maikudi duk sun zo
wa Ado daurin auren.
Da daddare kúwa ana idar da Sallar Magariba
amarya ta iso, duk wacce taga amaryar sai naji tazo
tana fadin kai mazan nan sai fa a bar su kawai, ban
dai san me suka gam ba.
Sannan koda nasan gidan Mallam Haruna da
iyalinshi na kasa gane ita wannan yarinyar da aka ce
wai sunanta Balkisu, saboda ni nafi sanin uwargidan
gidan Hannatu da 'ya'yan dakinta.
Wannan kuwa an ce yar amaryar gidan co Mamya
wacce ko gaisuwa da ita ban cika yi ba, don ba

129
kasafai ka ke ganinta a waje ba.
Taro ya tashi, Jama'a sai iatiya suke tayi saura
wadanda suka rage saura kadan Hajiya Kubra ta
shigo wurina tana murmushi, yau uwarki har da
goggoro ta daura.
Nayi maza na tambaye ta wacce a cikin iyayen
nawa? Ta ce wacce uwa ke gare ki da ta wuce
Mama? Na tsuke fuska na ce Mama kuma Hajiya?
Tayi maza ta ce eh, ita uwarki ce kar kuma ki yarda
ki biye mata akan komai.
Kiyi hidimarki kawai, wannan yarinyar kuma kar
ki yarda kuruciyarta tasa ki zalunceta, shi kuma
mijinki ki kara mutunta shi don ki karawa kanki
girma da daraja albarkar 'ya'yanku ma ta karu, na ce
to Hajiya na gode.
Dare yayi babu kowa a gidan, ina kivance kan
gadona tun bayan fitar Ado daga dakin da yazo yayi
min sai da safe, ban iya motsawa na tashi naje na
kulle kofar tawa ba, sai kallon agogo kawai nake yi
ina lissafin cikin zuciyata a sanin halin Ado da nayi
yanzu ya gama kaya ne yana yin kaza.
Ina cikin haka ne kawai naga yarinya ta fado min
daki da gudu a firgice kwarai take, tayi matukar
tsorata da abinda ta gani, tsallake ni tayi ta wuce can
bayana ta makure wuri daya.
Na waiwaya na kalle ta, 6ari take yi kar-kar-kar
daga ita sai yar wata lalatacciyar shimi ne a jikinta,

130
ga nonuwanta nan ba suma karasa fitowa sosai ba,
Yarinya ce 'yar karama da ba ta wuce shekara sha
hudu zuwa biyar ba.
Kamar dai ace sa'ar Umahmah, kyakkyawar
yarinye don kuwa zafin kishinta bai iya rufe min ido
ya hana'ni ganin kyan nata ba. Na tuna sanda dima.
nawa nonuwan suke kamar nata..
Cikin zuciyata na co, kai lalle Ado! Ado nabaiji
ne, yau ne na gane me yake nufi da yawan ambaton
kanshi namiji da yake yi, sai gashi ya shigo yana
daure da rigar baccin da ke jikinshi da belt
Muna hada ido dashi ya sakar min wani lallausan
murmush, a zuciyata na ce shi ma yasan ya cuce ni,
ya gama de ni.
To zomarna Humaira, ya juya ya fita ban yi
jayayya da shi ba na bi bayanshi zuwa tsakar gida
dan fito min da yarinyar nan sai ki auro kofarki, ki
kulle, ai dare yayi me ki ke yi har yezu idenki biyú?
Na harare shi na çe, kai vie ka,ke yi? Yayi.
murmushi ya ce to naji fito mii da ita don kin ga na
riga nayi niyya zan shiga dakinta. Na ce toai bani na
kawo ta ba, ka shiga ka dauke ta mana.
Cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login