Showing 9001 words to 12000 words out of 33160 words
Chapter 4 - MIJIN TACE 4 COMPLETE HAUSA NOVEL BY SODANGI.txt
yi kan al'amuran da yanda rayuwa ke tatiya,
Inna ta kalle ni tayi murmushi ta ce "Sanda ku ke
yara yan kanana a lokacin da nake ganin tanfar
abinda ke faruwa a, kaiga ba zai taba wucewa ba.
Kullum 'naje gaban Mallam mai, babban allo ina
kuka zaunar da ni yake yi ya yi ta bani hakuri, sai ya
ga natsawata ta dawo jikina.sai ya ce min, wadannan
yaran da ki ke haifa Binta ai kawayenki ne.
Kwana nawa ne, in Ubangiji ya amfana miki su
za ki ga sun girma sun zama abokan mu'amalar
rayuwarki? To amma fa sai kin yi hakuri, sai kin
zauna kin yi tarbiyarsu ta yanda Ubangiji zai taimake
ki su zama mutanen kirki.
To amma fa sai kin yi hakuri, ki zama ke din
bata kanki ki ke yi ba, don kuwa in ki ka yi kuskuren
47
da suka lalace, sai ya girgiza kai nuna alamar abinda
zai biyo bayan hakan ba karami ba ne.
To gashi nan a yau, ta sake wani murmushin
kafin ta ce na godewa Ubangiji da ya sanya ni na
zamo mai bin umarnin iyaye, na ce ban taba sabawa
umarnin nasu ba komai zafinshi a kaina.
Ta kalle ni ta ce na kira mijinki dazu don in yi
mishi godiya, bai bari mun yi tmaganar ba, na roke ki
kiyi mishi biyayya iya iyawarki, ki kuma zauna da
kowa nashi bisa gaskiya da adalci.
In hali yasa shi kawo miki abokiyar zama, to duk
yanda ki ka kai da kinta kar ki zalunceta, kar ki
danne mata hakkinta, na ce mata to Inna.
Washegari da safe ina tashe da kwanonon
dafafiyar kaza mai nonon Rakui da Innan ta dafa
min, wai da ita zan karya. na rike da wayar Inna ina
kokarin kiran Ado, don mu gaisa.
Na kai wayar kunnena ina sauraror ya dauka, na
kalli Inna cikin natsuwa na ce, ni wannän na menene
ne Inna? Ban fa ga alamar za ta yi wani dadi ba.
Inna ta ce, a to ko babu.dadi dai cinyeta aka ce
kiyi ki sha romon, na saké kalionta in ji waye Inna?
Ta ce Aliya, ita ta kawo ta ce in dafa miki wai ba za
ta iya ba ki da hannunta tana jin kunya.
Ado ya dauki wayar yana jin ni ce ya rage fara'a,
na gaishe shi yaya su Bala dai suna lafiya? Ya ce yau
ne ya kamata kiyi waya ki tambaye shi? Ai na kuma
48
gane ki wato ke in ki ka samu 'yan uwanki to zance
kuma ya Rare, kowa ma za ki iya mantawa da shi.
Na rasa abinda zan yi in wankc kaina, sai na tuna
na ce, to kawu ka ki ka sai min waya, zan yi ta bin
wayoyin mutane ne ina kiranka, ni kunyar hakan
nake ji.
Ya dan ii sanyi, ina Umahrnah? Ko tana wurin
uwarta? Na ce mishi eh, ba ki sani ba Humairah, sai
bayan da ki ka taho naje gida kan wani abin da ya kai
ni, sai na gane nayi kuskure.
Da sauri na tambaye shi, kuskuren me kayi? Inna
ma ta kallo ni don jin yarda na ambaci kuskuren, ya
ce kwanakin da na baki sunyi min yawa, zan koma
Dabai wannan satin saboda aikin gonata ki dawo gida
kawai.
Gabana yayi matukar faduwa, na ce haba Kawu,
yau ne ma fa nake da kwanaki shida a garin ran. Ba
za ki dawo. din ba kenan? Na ce a'a ba wai ba zan
dawo ba ne, amma ni gaskiya...bai jira jin gaskiyar
tawa ba ya kashe wayar.
Inna ta kalle ni so yake ki koma gobe? Na bata
rai saboda ran nawa ya baci, na ce ban sani ba tunda
ya kashe, to kira shi mana kiji, ya baro ki kin zo
lafiya cikin farin ciki da alhairori iri-iri ai ba za ayi
sanadin bacin ranshi ba.
Na sake kiranshi, nayi zaton ba zai dauka ba, sai
naga ya dauka. A hankali na ce mishi kayi hakuri in
49
ranka ne ya 6aci, ko da bana kusa dashi nasan
murmushi yayi.
Inna tana nan kenan? Na ce mishi eh, ya ce nasan
ita ce zata ce ki bani. hakuri tunda ke ba dabi'arki ba
ce, Ban.yi magapa ba shiru nayi ina sauraronshi.
Ki dawo gida awai Humairah, kin san tunda
muka yi aure bamu taba yin nesa da juna haka ba,
abin yayi min tsanani da yawa, nafi sabawa da pi in
tafi in barki a gida ina jin.marmarinki sai in juya,
amma ba ke ki tafi ki bar ni ba.
Da kyar Ado ya yarda ya janye maganar tafiyar
daga kwana bakwai, ya maida ita kwana tara.
Shi kenan sai kawai na soma shiry-shiryen
komawa gida, ciki har da karasa zuwa wuraren 'yan
uwan da, ban je ba. Inna kuma a gida tana tashi zan
koma dakina.
Duk da naje gidan mai babban alo, tun washe
garin zuwana gida na sake komawa wajen shi don ba
zai yiwu in zo in tafi ban gaya mishi halin da na baro
gidan mijina dà 'yan uwanshi ba, don ya bani
shawara ko kuma ąaddu'a.
A gidan mai babban allo ina zaune gabanshi shi
da uwargidanshi Hajiya 'Yar Dubu, matarshi ta
sakun lalle, matar da ya yi sa'a ta. zame mishi
uwargida ta gaskiya, wacce ta danne al'amarin kishi
tsakaninta da kowa ta tsaida adalcin da yayi sanadin
da gidan ya zama dunkulallen gidan da babu
50
bambanci tsakanin ya'yan nan da na can.
Ta sauko da Umahmah daga bayanta ta kar6i
uwa zam-zam wurin mai babban allo, ta
kwankwada mata kafin ta mika mishi ita, ta sake
neman wuri ta zauna cikin natsuwa ta ce min aure
suke so yayi ba kuma zasu barku ku zauna lafiya ba,
sai sun ga sun sa shi yayi.
Ba su kadai ba ne mafi yawancin 'yan uwan miji
ai zuwa suke in dai zasu ji ka shiru da dan uwansu sai
suce fin Karfinshi aka yi ko da kuwa hakuri ka ke yi.
Nayi maza na ce mata, haka ne Hajiya, ta ce to
ke ni ganau ce ba jiyau ba, kar ki yarda ki shiga
layinda ba na gaskiya ba ne, don ka mallake miji ka
hanashi tsaida adalci tsakanin iyalinshi, ka hana shi
yiwa kowa adalci.
In dai ba ka mallaki 'ya'yanka ka hana su
lalacewa ba, baka kuma mallaki hikima da dabarar
hana alhaki kama ka ba, ai kayi shirme.
Na ce haka ne Hajiya, ta ce to ladabi da biyayya
tsakaninki da mijinki, yi nayi bari na bari, in yana
fada a bashi hakuri ba yana fada ana fada ba.
Su kuwa 'yan uwan miji nan da ki ke kallon su
fita harkarsu kawai za ki yi, da wuya kwarai ki ga
wata mata da zata ce miki bata da tabonsu, sai dai
aniyarsu kawai ta bisu.
Mai babban allo ya yi murmushi alamar yasan
wani abu ko in da addu'ar ta Hajiya ta dosa, bai ce
51
komai ba sai da ya ji hirar tamu tazo karshe sai ya ce
min ke Aishatu.
Nayi maza na ce mishi na'am Mallam, ya ce to
gyara zama da kyau sai kiji abin da zan gaya miki, na
sake cewa to tare da yin abin da ya ce min din.
Cikin natsuwa ya soma yi min magana, kin ga
wadannan mutane da ki ke tare da su? Na ce mnishi
eb, ya ce to je ki maza ki gyara abinda ke tsakaninku
Ba mijinki ne zai gyara miki ba, ba kuma shi ne
zai rinka tare miki fada tsakaninki da su ba, in dai ba
shima nema ki ke ki maida shi ya zama abin da ya
zama ba.
Ai ke mace ce suma mata ne, halinku daya,
dabi'arku daya, rashin kirkinku daya. Dangin miji ba
mutanen kirki ba ne, amna wuria matar da bata yi
wa kanta adalci ba. Ama in zata yi wa kanta adalci to
zata gane su din "yan uwane na gaskiya, abokan
zama na amana.
Tasan yanda ta tyi ta zäuna da su lafiya bisa
girmamawa da mutuntawa da adalci, ba don komai
ba sai don tasan ita din atà wani Bangaren wata rana
dangin mijin wata ne ko kuma üwar mijin wata, to
me zai hana ka yi wa wasu adalci don kai ma naka in
sun zo suyi maka?
Yanzu dan karamin misali zan yi miki, Hadiza ni
na haife ta? Na daga ido na kalle shi don jin ya kira
Hajiya Kubra Hadiza, ya ce ba sunanta kenan ba?
52
Nayi maza na ce sunanta ne, ya sake tambayata
ni ne na haife ta? Na ce a'a, ya gyada kai ya ce ai kin
san gidan ubanta, kin san iyayenta, tunda kuna zuwa.
Na ce mishi eh, ya zuba min ido yana kallona,
kafin ya ce min to da wata yar da ta fi ta a nan
gidan? Nayi maza na ce mishi a'a, ya ce to da ta
dauke mu a yanda mafi yawancinku ku ke daukan
dangin miji zamu zama bhaka mu da ita? wo en
Na ce a'a, ya ce to dubi tsakaninta da uwarki ita
tafi kowa kusa da ita, ba haihuwa uwarki tayi ba, ba
daga gidansu tazo da ita ba, kanwar mijinta ne ta
maida ita yarta, ta hada damu duka ta rike mu da
gaskiya don ta yarda mu ne 'yan uwan da tafi bukatar
zaman lafiya da su.
Ranta ba ya baci ne? Yana baci, tunda mijinta
shima shi ne amma bata taba tsallake ni taje takai
kararshi wurin mahaifinta ba, duk da ni ban taba
zaunar da shi a gabanta nayi mishi fada kan laifinshi
da ta kawo in ba.
Sai in ta tafi in yi mishi nasiha, in gaya mishi ya
yi hankali da gidanshi, kuma ko da mijinta ya soma
yi mata kishiyoyi bata canza ba, ta kuma san daga
nan gidan ne aka sa shi ya yi mata amaryarta ta farko.
To yau me gari ya waya? Da tayi hakuri ta yi wa
kowa adalci ta zauna da kowa da amana har
kishiyoyinta yau waye gidan?
Shiru nayi ina kallonshi, da kanshi ya ce, ita ce
53
don kuwa ita ce wuar Alhaji Abba, ko shi kadai ta
haifa kuwa kin san tayi haihuwa mai albarka, balle ga
su Ahmad ga su nan da yawa don ita kadai mutun
takwas yanzu take da su.
Ko ba ka sónta zaka je gaishe ta don tasa baki
danta ya yi maka alfarmar da ka ke nema a wurinshi,
tunda babu abin da ya ke so da girmamawa irinta.
Don haka je ki ki gyara tsakaninki da kowa ki
zauna da kowa lafiya kiyiwa kowa adalci.
Na ce to, ai ba na gane abinda zan yi usu ne
Mallam, ni a ganina muna iyakacin kokarinmu ni da
mijina a kansu, tsanata kawai suka yi.
Wani murmushin ya sake kafin ya ce, to bari dai
in dan sa ki a hanya, kin ga dan uwa na Musulunci
kawai? Ina nufin ba dan uwan da hakki biyu ya hada
ku ba, hak kin Musulunci da hakkin makwabtaka.
Na ce mishi eh, ya ce to yana da wasu
hakkukuwa guda biyar da suka zama wajibi akan ka
kai Musulmi. Hakkukuwan kuwa su ne, na farko in
ya yi sallama ka amsa, idan yayi atishawa ya yi
hamdala kayi mishi addu'a ta nemar mishi gafarar
Ubangiji, in ya yi rashin lafiya kaje har in da yake
kwance ka gaishe shi.
In ya rasu ka halarci zana'idarshi, in ya gayyace
ka cin abincinshi kar ka ki uwa, kin ji su su biyar?
Na ce eh Mallam, ya ce to yan uwantakan
Musulunci ne yake da wadanran hakkokin.
54
To ina ga 'yan uwantakar da ta zama bayan na
Musulunci akwai na makwabtaka? Kin taba sanin
hakkin makwabci akan makwabci? Ban kai ga ba shi
amsa ba sai ya ci gaba.
Ya ce, to ga kuma uwa uba na zumunci, babu
abin da ke ruguza bawa irin shi, akwai kuma alhairori
da yawa ga wanda yayi hakuri ya yi shi ya bada
hakkin shi.
Wasu Malaman sai suka ce tun a duniya ake
amfana da tukucin shi, ayi ta jan kwanakin mai yin
shi don ya dade yana yi, wasu suka ce a'a ba kara
mishi kwanaki ake yi ba ayukanshi na lada ake
nunnunka mishi.
Wasu kuma suka ce zuriyarshi ce bata tabewa,
sai ayi tayi mata albarka, to wanne ne a ciki in anyi
mana ba a so? Na ce babu, ya ce to kiyi hankali da
su, don hakki uku suke da shi a kanku.
Hakkin Musulunci, hakkin makwabtaka da
kuma hakkin zumunci, na ce mishi to Mallam.
Na sake kallonshi cikin natsuwa na ce mishi, to
ba ni addu'a Mallam. Ya yi murmushi ya ce
wadancan da na baki kin raina su?
Shiru nayi ban ba shi amsa ba, sai na ji ya ce je
ki ki rike su sun ishe ki istigafari. Hailala, Salatin
Manzon Rahama, kiyi tayin su gwargwadon iko sa
ki cikata da la'hau'la 100.
Nasha gatya miki ita kadai in ki ka rike ta ta isa,
55
magani dari babu daya take yi wa mai karantata
karami daga cikin maganin nata kuma shi ne bakin
ciki.
Nayi wa Mallam godiya nayi mishi fatan alheri,
nayi sallama da shi da iyalanshi na fito daga gidanshi
cikin zuciyata ina tunanin babu abin da ya dace damu
illa mu tashi kawai mu bar gidannan muyi nesa da
kowa balle hakkin wani yaje yana hawa kan mu,
kuma wai komai mugun halin mutum sai ace wai sai
ka ba shi hakkinshi.
To in kayi nesa da shi ba ka huta ba? Sai da na
biyo gidan Anti Ramlah na shaida mata tafiyar tawa
kafin na isa gida.
A gida Inna sai shiri take yi gaba daya 'ya'yan da
aka haifa da Umahmah mata biyu Nusaiba da Hindu
ya'yan Ruwaila da Ade da kuma da namiji daya na
amaryar gidan Usman.
Sayayya mai kyau Inna tayi musu iri kuma daya,
tsofaffin gida kuma duka atamfofi dattawan gidan
shaddodi yadi biyar-biyar matan gidan da a hira ne
kawai na gaya wa inna yawan su na kuma ce mata
cikinsu mata biyu ne kawai ba su haihu ba.
Tayi dariya ta ce, lalle gidan naku gidan yawa ne,
gaba daya dakunan sai da ta baiwa yaro daya riga ai
kyau na kalli irin lodin tsarabar da ta tara wai duka na
mutanen gida ne, na ce mata aa Inna, to ni da zan zo
me suka ba ni suka ce in kawo miki?
56
Nan da nan fuskarta ta yamutsse alamar
maganarta bata yi mata dadi ba, nayi maza na ce
mata to kiyi hakuri.
Ana gobe zan tafi gidanmu ya cika makil da 'yan
uwa wai an zo min wunin sallama wasu kua sun zo
ne yi wa Inna taimakon aikin abin tsarabar da zan tafi
da shi.
Muna gefe ni dà Anti Ramlah wacce tazo min da
mai kitso,da kuma lalle su suna ta aikinsu mu kuma
hirarmu muke yi. Ai naso in zo miki da kaza mai
nonon rakumi ban samu nonon ba ne.
Na ce ar na ci, da sauri ta ce min a ina ki ka
samu? Na ce, Aliya ce ta kawo, Anti Ramlah ta ce,
kai Hajiya Aliya fa ta kile ko da yake dai ai sirikar
Hajiya Kubra ce.
Gyaran jiki sosai aka yi min kafin aka yi min
adon lallen dan daidai mai kyan gani da sha'awa,
sannan aka yarfa min kitso.
Azahar bata yi.ba sai ga Bala da direban da ya
kawo ni sun iso, Inna tana ta dariya kai Bala har kun
iso? Bala yana fara'a don sun riga sun saba da inna
saboda jan shi a jiki da take yi.
Nan da nan ta shiga ina aka saka dashi da direban
kafin yamma komai ya kammala, dubulan, nakiya,
alkaki, tayota, tuwon madara, kwakumeti, babu abina
da Inna da masu taimakonta basu yi ba.
Da yamma kuma sai ga Hajiya Kubra an kawo ta
57
a sabuwar motar da Alhaji Abba ya saya mata, sai da
ta shiga suka gaisa da Mama kamar yanda ta saba
sannan ta shigo wurin Inna.
Kwalla guda tazo dashi shake da soyayyan
naman rago, ga kuma danbun naman abokitin
kwallan ga kuma man. shanu da yaji ki kaiwa mijinki.
Wannan nashi ne, ki kuma gaya mishi na gode,
Ubangiji ya yi wa zuriyarshi albarka, zan kuma zo da
kaina in yi mishi godiya, na ce mata to.
Washegari tun safe aka gama shiri' na shiga wurin
Babana muka dan yi hira na bashi hakuri akan
al amura na kawo abin da zan iya bashi na bashi duk
da dai nasan ba komai zai yi mishi ba sái dai kuma ya
ji dadi yayi tasa min albarka.
Itama Mama na shiga nayi mata sallama na ce
mata ni zan tafi, kallona kawai take yi watakila
kalmar da zata yi amfani da ita ne a kaina ta rasa, na
mike muka yi sallama da su Habiba na mika wa
'ya'yan Sha'awa dubu biyu na ce su raba.
Habiba ta biyo ni tana yi min rakiya zuwa ko far
gida, in da 'yan uwa duk suke tsaye suna jiran
fitowata.
A cikin zaure na tsaya don yin magana da ita,
saboda ta hakura ta sauke girmen kai ta sassauto har
dakin Inna ta biyo ni tana yi min sannu da zuwa, har
ina jin Mama tana tambayar ta kema kin bi ne saboda
yar wainar da take baki?
58
Na kalle ta cikin natsuwa na ce mata, in hali yayi
kin koma dakinki kiyi hakuri, Habiba saboda kema
kin san wannan zaman naku ba tsari ba ne, tayi maza
ta ce min haka ne Humairah, na gode.
Na ciro dubu hudu na milka mata na ce kiyi
hakuri godiya tayi tayi min, na juya zan tafi tana bina
kice ina gaida Kawu, na ce zai ji. ln kin samu mai
zUwa ki aiko min da zani don zannuwan nawa sun
fara yin sanyi.
Na ce to, ai kwauron baki ki ka yi Habiba da kin
gaya min da wuri duba miki, to amma yanzu kinga
kayana har an riga an daure su.
Adam da Baba Karami suna tsatsaye ga Sa' adatu
tana rungume da Umahmah 'ya'yan makwabta ma
duk suna tsaitsaye, na sake yin sallama da Baba na
shiga mota muka kama hanya daidai karfe bakwai da
rabi na safe.
A gida rannan muka yi sallar azahar a gidan
kuma na samu Ado shima kuma a safiyar ya iso don
haka tsaf na samu dakin yayi matukar farin cikin
dawowan namu, ya kuma yi magana mai yawa kan
irin hidimar da Inna da 'yan uwanta suka yi.
Nan da nan na shiga rabon tsaraba nan da nan
aka shiga zirga-zirgan zuwa yi min sannu da zuwa,
sai ka ce ba ni ce na tafi ana amsa salamar tawa da
kyar ba, na ce kai akwai hikima mai yawa a cikin
al'adar bahaushe ta yin tsaraba.
59
Ni kuwa duk wanda yazo sai na mika mishi wani
abu yara in sun shigo in debo tuwon madara ko
kwakumeti in danka musu.
Dare nayi Ado ya tasa ni a gaba ya soma bari
yana rawar jiki yana marairaita, tanfar dai wani
lokaci mai tsawo muka yi ba mu hadu ba.
Na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi ni fa ji
nake ma kamar abinnan yazo min da sauri, ya tsuke
fuska yana fadin wasa kenan, ki ce min duk wannan
kwalliyar da kyale-kyalen a haka nan za su tashi?
Rannan sa ar da muka yi ni da Ado shi ne na
samu ya saiwa Umahmah dan gadon jarirai a ciki tun
farko ya sanyata ban da haka kuma dakin namu can
gefe yake babu ai jin abiri da muke ciki.
nna ce ta kara gyara min ke, shiru nayi ban
tanka mishi ba. nna tana sona Humairah, ya gama
maganganun shi, ban yarda na ce mishi komai ba.
Washegari da wuri na fita na gaida kowa na
kaiwa Goggo Ayalle Umahmah na kai mata ita tare
da danbun nama da man shanu har da yaji, na kuma
ce mata 6oye Goggo don ku kadai na baiwa daga ke
sai baba, ya kamata to wannan tsaraba dama ai ba na
kowa da kowa ba ne.
Tun daga ranar ban sake ganin wani yaro ya
shigo wurina