Showing 1 words to 3000 words out of 53693 words

Chapter 1 - LABARINA Series Complete by Mimi queen.txt

ο»ΏLABARINA
New Series Book


Alkalamin. ✍️

Mimi.πŸ‘Έ*
Haleemart Iserh
(ummu ramlat)


MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION


Bismillahir Rahmanir Raheem

Ya Allah kayimin gafara ka tsaremu daga sharrin zamani don Alfarmar Annabi da Al kur'ani, komai na rubuta kan kuskure Allah ka gafartamin ina tuba a gareka.


Wannan labarin ba true life story bane, kirkirarrene amma ya banbanta da sauran labaran da aka saba ji....




























































Ina fatan wannan labari me taken *LABARINA* Zai kayatar, nishadantar da wa'azantar da Alumma baki daya, dafatan Allah yasadamu da mafificin Alkhairin dake cikin wannan littafin ina tuba a gareka ya Allah karabamu da sharrin dake ciki.


*Masoyana kubiyoni cikin wannan kayataccen littafin mai taken LABARINA*
*Muje zuwa masoya fatan Alkhairy Inayinku πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹*..........



*Dedicated to yhu my Amjad I love yhu πŸ’–πŸ’–*




1&2














































































Labarina labarine me cikeda kunci, cikin kunci na taso tun tasowata bantaba tunanin zanji dadin rayuwaba, da wuya rana tafito tafadi ban zubda hawayeba, kuka ya kasance sana'ata ako wani lokaci in banyiba banajin dadi bahaushe nacewa ba'a sabo da wahala amma ni inda sabo nasaba.
Sai yaushene zanyi dariya nabar kuka sai yaushene zan samu yanci a rayuwata?? πŸ€”πŸ€”πŸ€”
Hummmm me karatu ku biyoni danjin labarina.










































































*Nasarawa G. R. A.*


Kayataccen gidane wanda yafi karfin gida sedai na kirashi da mansion Alh. Aliyu bello khaliyal shine mamallakin gidan, soldier ne daya taka rawar gani a kasarnan ya rike mikamai da dama kafin yayi ritaya, cikakke kuma haifaffan garin khaliyal ne dake jahar kebbi kuma cikakken fulanin khaliyal aikine ya dawo dashi garin kano.


Daga can baya boys quaters inda masu aiki suke rayuwa.
Shashshekar kuka na dingi jiyowa na kutsa kai inda nakejin kukan na fitowa.
Wata yarinyace da bazata wuce 15 to 16 years ba zaune ta rakube gefe guda dukda kayan dake jikinta sun kode Sunyi duhu be hana hasken yarinyar bayyanaba kuma kallo guda zaka mata kagane ba karamar kyakykyawa bace cikakkiyar shuwa Arab kuma bafullatana.
Hawayene ke fareti bisa dakalin fuskarta duk da kuka take hakan be hana bayyanuwar cute dimple dinta dake lotsawa a lallausan kumatuntaba a hankali eyelashes dinta daya jike sharkaf da hawaye yake sama da kasa alamun tana lumlumshe idanta da suke manya manya kuma cikinsu brown ne, har lokacin hawayene ke zuba daga eyes dinta tana shashshekar kuka.
Daidai lokacin aka turo dakin daga kanta tayi tana kallon wacce ta shigo
Cikin tausayawa Mairo ta kariso tana mejin tausayin yarinyar a cikin zuciyarta kanta ta dafa cikin tausayawa tace. "Kiyi hakuri komai yai farko zeyi karshe Kinji *UMMU RUMANA* siririn hannunta tasa ta share hawayen dake zubo mata har lokacin hawayen sake zubowa suke, Mairo tace. "Ko kefa yar Albarka tashi kije gatacan naji tana nemanki" a sanyaye ta mike Seda ta mike na kara yaba kyan Rumana ainun.
Doguwace siririya batada wani kiba sosai amma a cike tak fam komai available, kirjinta cike yake ba laifi haka tanada hips tanada jikin hutu gashin kanta har gadon baya se lilo yakeyi a gadon bayanta saboda ta daureshi da kyalle.
Mairo tabita da kallo harta fice sannan ta saki ijiyar zuciya."Ya Allah kadubi marainiyarka katausaya mata".
Seda ta wanke fuskarta a famfoo sannan ta nufi cikin gidan a sanyaye ta kutsa kai cikin falon
Yaran hajiya Umaima, Raudah se babban wansu Faheed suna zaune a falo. Faheed nasha shusha sukuma kowa yana danna wayane hajiya dake saukowa. Daga upstairsta dakawa Rumana tsawa da fadin. "Kee...!! " wanda Seda jikinta yafara rawa a firgice ta juyo jiki na rawa cikin cool voice dinta me tsananin dadi tace a firgice. "Na'am na........ " harara ta dada watsa mata "ke. dan uwarki se yanzu kikaga daman zuwa. " shiru tayi hajiya ta sauko tana binta da wani mugun kallo.






































































Kan Rumana na Kasa ta Kasa ko kwakwkwaran motsi, Haj. tace cikin isa da nuna gadara. "Ki wuce akwai aiki a kitchen inkin gama kije ga kayansu raudah can ki wanke musushi da kyau kafin magrib tayi kuma ki goge. " gyada kai tayi kafin tasoma takawa zuwa kitchen,
Tsawan da fahid yadaka matane yasata juyowa a firgice. "zonan" yafadi a sanyaye ta karisa shishan yasaki tareda sa hannu ya riko wuyanta. "Ke shegiya baki ganni bane zaki wuce batareda kin gaidaniba??. "
Haj. Hayewa sama tayi ko kallonsu bata yiba. Raudah cikin zolaya tace. "Amma kai bro mugune wannan shaka haka aiseka kasheta. " umaima dake latsa waya taja dogon tsaki. "Mtsssww ina ruwanmu ya kashe shegiya ya dame mune. " dukkansu aukasa daria hararanta fahid yayi tareda sakinta ta zube a Kasa yana fadin. "Jeki gama aikin da mommy tasaki kidawo yau se naci uwarki shegiya Mtsssww. " ya kai mata hauri kaman wata dabba
Tana sharan hawaye ta wuce kitchen domin taji shakan sosai,
Aikine sosai a kitchen din batareda bata lokaciba tasoma cikin abunda befi minti arba inba ta gama komai,
Ta fito haraban gidan ta nufa inda ake wanki kayane jibge dan sunkai kulli shida. Nan ta dauki botiki taje ta debo ruwa a famfoo ta dawo nan tafara wankin.


Duk saurinta na kada magrib ya risketa tana wankin Seda magriba tayi dan wankin dayawa a wahalce ta gama dan wani bala'en yunwa da takeji, Alwala ta daura ta nufi sashinsu inda suke itada masu aikin gidan. Tana shiga tagabatar da magriba dinta tana zaune aka kira isha'i ta tashi ta gabatar,
Gefe takoma ta rakube jikinta serawa yake Gashi yadau zafi, mairoce ta shigo dafa Rumana tayi. "Ummu Rumana ya jikin. "? Cikin dauriya tace. "da sauki. " tace. "Allah kara sauki." tace. "Amin. " mairo tace. "Tashi ga wannan na dauko miki a boye maza tashi kici." Rumana ta dago da sauri tareda amsan roban shinkafan dake hannun mairo nan da sauri da sauri tayi bismilla tafaraci domin ji take kaman Zata mutu Sbd yunwa. πŸ₯±














































Mairo ta bitada kallon tausayi fita tayi taje ta debo mata ruwa a famfoo ta dawo ta dawo mata.
Bayan ta gamaci tasha ruwa kan yar figigiyar tabarmarta ta kishingida ta lumshe ido kaman me bacci amma nan tunanin rayuwarta takeyi a yan shekaru irinna Rumana hartasan meye kuncin rayuwa,


Hawayen daya zubo mata tashare tareda tashi tazauna wani ragaggiyar Ghana most go naga tajawo daba
Kayan kirki a cikinta ta bude wani text book naga taciro ta koma kan tabarmarta ta bude tana karantawa.
Har Seda nayi mamaki dama Rumana ta iya karatu a ido zakace jahilace hummm amma abun ba haka yakeba tadade tana duba text book πŸ“š din kafin tasamu da kyar tayi bacci.




















































*Yanzu aka fara πŸ₯°*


*shares*
*Comments*
*and vote*




*Mimi ✍️*
8/20/21, 8:14 AM - Mimi: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*LABARINA*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Alkalamin. ✍️

*Mimi.πŸ‘Έ*


Haleemart Iserh
*(ummu ramlat)*


*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*
*M. W. A*


*Bismillahir Rahmanir Raheem*


3&4


Wanshe kare.


Kaman yanda tasaba bayan tayi sallah ta nufi cikin gidan dan tayi aikinta, bayan ta gaida Haj. duk da bata amsaba bata damuba ta tashi ta soma aikace aikace. Tana cikin mopping Abbanta ya sauko durkusawa tayi. "Ina kwana Abba. " ko kallon inda take beyiba Haj. Ko ta watsa mata wani mugun harara da sauri tayi kasa da kanta. Raudah ce ta sauko tana miji a yatsine tace. "Sannu daddy. " Murmurshi yayi. "Yar daddy an tashi. "? Tace. "Eh daddy. " harta juya se kuma ta juyo. "Yawwa daddy maganan da mukayi na siyamin sabuwar mota da kace zakayi karshen month. " yace "Inasane gobennan zaa kawo guda uku daga Italy daya naki daya na Faheed dayan kuma na umaimace. " dariyar mugunta tayi tana hararan rumana da ta daina mopping din tana kallonsu.


















































Harara raudah ta zabga mata. "Lafiya kike kallonmu. " Abba yadan juyo ya kalleta ta gefen ido tareda zabga mata harara.
Nan suka karisa dinning dubanta Abba yayi. "Ke jeki kira umaima da Faheed su kadai muke jira. " da farin cikinta ta juya dan kiransu tanajin dadi yau Abba yasata aiki, kafin tahau upstairs suka sauko a tare dukkansu harara suka watsa mata ta durkusa tana gaidasu suka bigeta suka wuce.
Tashi tayi taje taci gaba da aikinta. Tana kallo suka gama break din nan Abba yatashi ze wuce office, yazo fita tace. "Adawo lpy Abbah. " ko kallonta beyiba balle ya amsa ya wuce, yana fita haj. ta tashi ta cafkota ta zabga mata rankwashi. "Ke dan uwarki bance kada ki karama Alh. Maganaba. "? Shiru tayi fahid ya dago. "Mummy barmu da ita yau zamuci uwarta. " haj. tace. "Yawwa kuci uwar shegiya. " ta saki rumana akan tyles ta wuce,


































































Faheed yace. "Zo nan. " jiki na rawa ta karisa yace. "Ke Jiya banace dan ubanki inkin gama kizoba shine kikaki ko. "? a sanyaye tace. "Kayi hakuri ya Faheed ban gamaba se bayan magrib kuma banyi sallahba shiyasa naje nayi.... " umaima ta zabga mata harara. "Shegiya to waye baya sallah seke masallaci ko.? bro kabarni da ita yau naci ubanta munafukan mtssttww. " Rumana cikin murya me zaki tace. "Dan Allah Aunty umaima Kiyi hakuri bazan karaba. "Raudace ta dubi Faheed. "Taje ta fara gyara mana daki tukun ko bro. "? ya dubi Rumana. "Jeki gyara mana dakunanmu kidawo " a sanyaye tafara tafia umaima tace. "Salan Muga ba wani abu. " a sanyaye ta haye saman,
Ba tafi 30mints ba tasauko nan ta kariso. "Gani ya faheed. " ya dubi umaima. Umaima ta nuna gefensu "dawo nan ki kama kunninki... " tace cikin kuka. "dan Allah Kiyi.......... " umaima ta daka mata tsawa. "dawo nace banasan musu inba hakaba na tattakaki.. " bata sake maganaba tadawo gefen ta duka ta Kama kunninta fahid tace.




































































"Kuma kika kuskura kika dago se kinci ubanki. " haka taci gaba se kuka take tafi awa hudu a durkushe harta fara shaahsheka kafin raudat tace. "Bro ya isa haka ta gane ai yanzu Rumana tashi. " umaima tace. "Haba raudah da kin barta ai taci gaba. " fahid yace. "Yayi jekici gaba da aikinki. " tana shara kwalla tawuce,
Tana cikin aiki raudah ta kwala mata kira tafito da sauri tace. "Jeki soyamin kwai ki dafamin Indomie. " nan taje tayi yanda raudah tace, a lokaci kalilan ta kawo mata nan ta harhada plates da cups din da suka bata taje ta wanke, a ragowar wanda suka cine ta kalata tasa a bakinta, nan tasha ruwa takoma ta gyara dinning room din.
Fita tayi taje ta share haraban gidan da dakin karnukan Infact dai se wajen two tagama aikace aikaccenta tun safe nan ta koma shashinsu,
Jikinta dukya mata tsami saboda kama kunnin da tayi ga wani mugun zazzabi daya sauka a jikinta nan ta kishingida.




















































































Uku nayi tatashi ta zura hijabinta ta dau littafinta tafito bakin gate ta nufa inda me gadi yake koya mata karatu domin yayi karatu, yana ganinta ya washe baki. "Rumana har an fito. "? Tace. "Eh na iya na jiya ka karamin wani." Ya matsa daga bencin da yake yace. "Zauna. " can nesa ta zauna, nan suka fara karatun boko harma dana arabi koya mata yakeyi, bako bata lokaci ta iya dan haka ta tafi sukai sallama se kuma gobe.
































Tana shiga falon ta shiga kitchen tafara wanke wanke kira Faheed
Ya kwala mata daga sama da sauri tayi saman, dakinshi ta nufa yana tsaye harara ya watsa mata. "Dazu da kike gyaramin daki bakiga wasu abubuwaba. " shiru tayi can tace. "Nagani nasa maka a drower ne. " yace. "Maza daukomin. " ta karisa ta duka ta janyo drowern ta fiddo da bottles na giya πŸ€” guda uku, yace. "Samin a fridge. " tashi tayi taje ta bude fridge tasaka.
Har Zata wuce ya kirata juyowa tayi taga yana mata wani irin kallo duk se taji ta tsargu kan gadonshi ya nuna mata. "Zauna. " jikintane ya hau rawa tsawa ya daka mata da yasata karisawa da sauri ta zauna yazo ya tsaya Idonshi nakan kirjinta. "Inaso daga yau kidinga bani hadin kai inyi abinda nakeso dake ni kuma na miki Alkawari bazaki kara zaman kunci a gidannanba ni dai burina ki bani hadin kai mu dirji juna.. " kallonshi takeyi se yanzu ta yarda Faheed jahilci na dawainiya dashi kuma bashida tarbiya yana matsayin wanta uba daya aiko a kasar kafirai ba'a wannan dabbancin.
Bakinta na rawa tace "dan Allah kayi hakuri ya faheed ina ganinka da mutumci a, matsayin ka na babban wana dan Allah kada kasa wannan mutumcin ya zube...... " bata rufe bakiba saboda wani wawan Mari daya watsa mata.
"Ke ni kike fadawa magana to yau se nayi sex dake ko kina so ko bakiso... " nan ya turmusheta yana matsa boobs dinta da sukafi komai daga mishi hankali
















































Kuka take sosai tana ihu tana kokarin kwatan kanta da kyar ta samu ta kwace tayi waje da gudu.
A bakin kofa sukayi kicibus da haj. Wani kallo tabi rumana dashi cikin kuka tace. "Mummy ya faheed ne... " nanta fada mata komai
Tsawan da yasa jikinta yadau rawa haj. ta daka mata. "Yimun shiru munafuka kawai sharri zakimai. " bakinta na rawa tace. "Wallahi mummy...... ". "Yimin shiru wuce ki bani guri...."
A sanyaye tawuce. Mummy ta karisa dafa faheed tayi. "Kada ka damu takan dan wannan abun bari abbanku ya dawo yau zamuyi maganin yarinyarnan, kai in banda abunka meye abun sha'awa a jikiin yarinyarnan. "? Yayi murmushi. "Mummy kenan Abubuwa da dama kuwa. "












































πŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€”
Kadan ma kukaji indai a cikin Labarina ne kuci gaba da kasan cewa dani *Mimi* danjin yanda labarin ze fara har yanzu ba ai komaiba.


*


























































*Leeymart Eirser✍️*
8/20/21, 8:14 AM - Mimi: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*LABARINA*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


Alkalamin. ✍️

*Mimi.πŸ‘Έ*


Haleemart Iserh
*(ummu ramlat)*


*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*
*M. W. A*


*Bismillahir Rahmanir Raheem*


5&6


Rumanace zaune se faman kuka take tanajin yanda haj. Ke shiryawa Abba maganan karya wai rumana ita ta nemi faheed da Iskanci kasa furta komai tayi saboda bakin ciki In banda kuka ba abinda takeyi.
Hajiya ta isa. "Hhmmmm. " kana ta daura. "dan haka Alh. Ka gaggauta daukan mataki akan yarinyarnan domin in bakai wasaba seta dauko maka abun kunya. " bakin cikine ya tasowa Abba besan sanda yashiga jibgar rumanaba, Itako inbanda kuka ba abinda takeyi dukkansu babu wanda ya hana Abba koya bashi hakuri Seda yamata dukar uwar wata sannan ya lafa yana huci fadi yake. "Nayi asaran haihuwarki rumana kirasa dame zaki sakamin seta wannan hanyar dan haka Wallahi nayanke hukunci aure zan miki bazan haifu karuwaba Wallahi. "
Inbanda kuka ba abinda takeyi jin yace aure ze mata yasata kara karfin kukanta, haj. baki a washe tace. "Aiko shawararka tayi daidai. " kallon tsana Abbah ya wurgawa Rumana. "Tashi ki bani guru. " a hankali ta tashi tafice se dingishi take saboda jibgar da taci.






























































Shiru mairo tayi tana jinjina wannan rashin adalcin a fili tace. "gasu raudat nan da in aurenne da tuni sun haihu su ba za'a musuba seke j
Kai wannan zalincin dame yai kama. Kiyi hakuri ummu rumana komai yai tsanani maganinshi Allah, Allah ubangiji yana kallon komai kuma baya zalunci Allahsa can yafi miki nan. "
Ba tareda tayi maganaba ta karisa kan tabarmanta ta zauna lumshe bold eyes dinta tayi da suke manya Sunyi jajawur tana tuna rayuwarta.






*Flash back*


Kaman yanda na fada muku Alh. Aliyu bello khaliyal haifaffan fulanin khaliyal ne dake kebbi state mahaifinshi nada tarin Arziki me dimbin yawa shi kadai suka mallaka a duniya yayi karatu me zurfi fannin aikin soja,Yana gamawa ba dadewa yasamu aiki,
Babban sojane ba karya da kasa ke alfahari dashi, a garin kano ya hadu da haj. Maryam ya aura inda suka haifi yara uku, Faheed shine babba se Raudah, Umaima itace karama.
A maiduguri ya hadu da Rahma kasancewarta cikakkiyar shuwa Arab ga kyau ga komai ya aura nan ya taho da ita kano,
Haj. Maryam macece muguwa mesan kan tsiya da san nata Rahma ta fuskanci abubuwa da dama a zamanta da haj. Maryam har Allah ya bata ciki ta haifi kyakykyawan yarinya wacce akasawa Rumana, zuwa lokacin haj. Maryam ta mallake Alh. ta yanda bayajin maganan kowa se nata bedamu da kowaba se ita da yaranta haka Rahma taita hakuri dasu, har zuwa lokacin da rumana takai shekaru biyar a lokacinne Allah yayiwa Rahma rasuwa tabar kyakykyawar yarta dukda a lokacin batada wani wayau amma taji mutuwan ba karya domin a yan shekarunta harta fahimci halin da mahaifiyarta take a cikin gidan,
Tun daganan rayuwarta ta canza takura zaman kunci wahalan rayuwa ba wanda bata ganiba domin a lokacin kaf aikin wahala babu wanda bata sanshiba.






































































Karshema koranta akai a cikin gidan ubanta ta koma shashin masu aiki makarantama aka hanata zuwa duk da ko tana bala'in san karatu ta zama bora a cikin gidan ubanta bame kaunarta bame nuna mata kulawa hatta mahaifinta daya haifeta, sautari in dangin mahaifiyarta sukazo haka zataita kuka tace Zata bisu domin ba wanda yasan halin da take ciki duk da ko suma sunasan tafiya da ita amma ba yanda suka iya domin Abbanta ya hana dangin mahaifinta lokacin da ummanta ta mutu sunso su dauketa amma Sam Abba ya hana acewarshi abarmai abinshi ze rike.




*Wannan kenan*


Bari nayi wani dan tsokaci a garemu mata sau tari kishiya Zata mutu ta bar mana yara semu dinga wahalar da yarannan acewarmu wai kishi to abinda baku saniba shine sufa wannan yara amanace a gurinmu kuma komin zaman da kukayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login