Showing 6001 words to 9000 words out of 53693 words
Chapter 3 - LABARINA Series Complete by Mimi queen.txt
 hakuri hajiya....... " cikin fada ta daka tar dashi. "Me kakeso nace maka Alhaji ina zaune dakai shekaru da dama lokaci daya kace zakamin kishiya kuma karasa dawa zaka hadani kishi se da wacce nafi yarinya karama kuma yar cikinka, shima bacin haj.  Maryam da bazaka fadaminba ni ba abinda zance maka domin ko sedai ka zaba ni ko ita dan wallahi indai ita ka zaba ko sedai karabu dani ka bani takaddana.........., "ta fashe da kuka nan hankalin Alhaji yadada tashi, 
Nan ya shiga lallashi ganin ta kafe akan ita indai seya kara aure sedai ya saketa hakan yasa ranshi ya baci cikin kakkausan murya da kuma fada yace. "bazan fasa aureba kuma bazan sakekiba kiyi duk abinda zakiyi....... " ta sake fashewa da kuka. "to ai wallahi bada gidanka nazo duniyaba kuma sannan ba dauramin kai akai a kafaba zan iya tafiyana koba takardarka ai miji goma ba uba goma bane....... " wani mugun kallo ya bita dashi tareda daga yatsa yana nunata cikin tsawa yace. "Wallahi Asma'u kika kuskura kika tsalleke kafa kika bar gidannan to se ranki ya baci Mtsssww..... " yaja dogon tsaki ya wuce danshi tsayayyan namijine a gidanshi.... 
Zubewa haj. Asma'u tayi bisa three seater tafashe da kuka me cin rai, duk wannan abun da akeyi a idon zeeza, Aknan, da kuma diyam ne ganin Alhaji ya fice yasa dukkansu sukayi kanta suna lallashi, 
Zeeza ce ke fadin. "Aunty kiyi hakuri kada ki tafi kada kije ko ina ki zauna a gidanki ta shigo gidan mukuma zata gane aya zakine agunmu. " Aknan tace gaba daga zancen zeeza. "Eh mummy zata gane mu ba'a kishi da mummynmu.... " diyam kam babu abinda tace, hawaye haj. ta share cikeda gamsuwa da zancen su Aknan domin dama ko basu fadaba ba inda zata iya tafiya tabar mijinta farin cikin ta.. 
Wayan tane ta hau ruri ta sake share hawaye ganin haj. Maryam yasa tayi picking tareda kangawa a kunni. "Hello hajiya. " 
Acan bangaren haj. Maryam tace. "Ya dafatan dai kinyima Alhaji bala'i yafasa auren. "?  Nan haj. Asma'u tafada mata yanda sukayi da Alhaji ta dora da fadin. "Hummmm ni yanxu haj. Maryam ba yanda zanyi zan barshi yayi auren...... " haj maryam tasaki huci me zafi tareda naushin iska tace. "Kai hajiya baki iya abun bane Wallahi. ". "Hummmm ya zanyi hajiya kinsan halin Alhaji Wallahi ze iya rabuwa dani kuma yayi aurensa ko a jikinsa. "haj maryam tace. "Hummm to yanxu kiyi amfani da shawaran se zeeza inta shigo kuci ubanta ku bata wahakar da da kanta seta gudu.... " dariya haj Asma'u tayi. "Shiyasa nake sanki hajiyata. " nan ta tashi tayi ciki aka ci gaba da kulle kulle. 
Alhaji sadeeq kam waya ya daga yakira MK hankalinshi tashe yake bashi labarin yanda sukayi da haj.  Asma'u. 
Ijiyar zuciya maheer yasaki yace. "Yayah ai dama ni nasan haka zata faru domin kasan ko wata mace akace za'a wa kishiya dole ta nuna halinsu na mata, nidai shawarana anan shine kada ka fasa wannan auren Aunty kuma ka barni da ita. " ijiyar zuciya Alhaji yasauke yanajin dadin yanda dan uwanshi ke kara mai kwarin gwiwwa, 
Mk yace. "Yanxu saura kwana nawane daurin auren tunda kacemin ba za'ayi wani bukunkunaba. "? Alh yace. "Saura kwana takwas yanxu ni kin fadawa haj nayi tun farko saboda banaso ta sani se ana zan fada mata. "Mk yace. "To ai gara data sani tun yanzu duk abunda ze faru ya faru, wai wama ya fada mata."? Alh yace. "Hajiya maryam mana matar major Aliyu bello khaliyal. " Mk yasaki huci. "Okey Allah kaimu yaya. " Alh yace. "Wai yaushe zaka dawo,?   ya kamata kadawo kafin ranan daurin auren dan dani 
dakai da Alhaji musa kawai zamuje. ". "Hummm yaya zan dawo kafin lokacin insha Allah. " Alh yace. "Meyasa ba zaka dawo yanzu ba. "?  Mahir yace. "Yaya muna ordition ne yanzu amma by god grace zan samu nayi skipping nadawo before the day.... " Alh yace. "Allah kaimu kanina. "Nan sukayi sallama da naheer ze kashe yace. "Ka gaidamin aunty.......... "
da sauri Alh yace. "Wata aunty kadafa ka ballomin ruwa.. ": maher ya gimtse dariyar dake shirin kufce mishi domin yasan tonon fada yayi dan yaji me yayanshi zece, nan sukayi karayin sallama kowa ya kashe, 
 Maher dake office yayi shiru yana kallon wayan, shi yaushene zeyi aure gashi har yayanshi ze kara na biyu.? 
Daya tuna aure nufin Allahne se yayi murmushi. 
Toh rumana wannan shine badi barai anya an tsira na auren da za'a miki ko za'a koma ruwane?
π€π€π€π€§π€§π€§ 
. tare dani *ummu ramlat*βοΈ 
     *LABARINA*
πππππ
Alkalamin. βοΈ
      
       *Mimi.πΈ*
                   Haleemart Iserh
                 *(ummu ramlat)*
*πMANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπποΈ*
                   *M. W. A*
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
13&14
Tana rakube gefen famfoo se kuka take wanda tasaba kullum danya zame mata jiki tunda wannan abun yafaru na sharrin da aka mata tsakaninta da dan uwanta Faheed se wahala ya karu harma yafi wanda takesha da, dan yanzu yan aikin gidan sunfita galihu tunda yanzu a dakin karnuka take kwana tareda su ga kukan da yake zuwan mata duk lokacin data tuna aure Abbanta ze mata
. "Keeee!!. " aka fadi cikin tsawa firgigit ta dago. "Na'am Aunty umaima. " "Ke dan ubanki ba aiki aka sakiba kika zauna kinata kuka. "? tasa hannu tana share hawayen tareda tashi da sauri cikin rawar murya take fadin. "ba.... kuka..... nakeba...... Aunty... " ta duka taci gaba da wankinta da tun safe tafara.,. "Mtsssww. "Umaima taja tsaki. "dama nazone ki bani gyalena zan tafi school sauri nake.. " jikin rumana yadau rawa domin yanzu ta chanya ko bushewa beyiba balle ta goge,In ina tafara umaima na hango gyalenta a waya tace. "Kutumar ubancan dama yanxu kika wanke to bari naje na fadawa mummy. " Rumana na bata hakuri tawuce. 
Rumana na tsaye tsuru umaima tazo ta dubeta. "Mummy na kira. "Jiki a sanyaye tabi bayan umaima. 
A tsaye suka tadda hajiya se girgiza take cikin tsawa tace. "Ke dan uwarki ba awa daya na bakiba ki wankesu su bushe ki gogeba amma yanxu kinyi kusan awa nawa. "?  Shiru Rumana tayi kanta na kasa,  hajiya ranta ya baci tasa hannu ta gaurawa rumana marida seda ta kife,. "dan uwarki fara tsallen kwado se kinyi harkin gaji sannan zaki tashi kuma kikoma ga wankin can kici gaba insun bushe ki goge, bazaki faraba ko sena karyaki,. " batada zabin daya wuce tayi abinda haj. tace. "Mtsssww wawuya, jaka, sakarya ai uwarki jaka ta haifamin yanda rahma take shaidaniya haka kike harma kinso kifita yar matsiyaciya kawai Mtsssww. " takuma jan tsaki tawuce kan cushion ta zauna, wani wahalallan kukane ya kufcewa rumana jin ana zagin mahaifiyarta tatsani a zagi mahaifiyarta a gabanta amma hakanan tadaure taci gaba da abinda aka sata, 
Daga farkon falon zuwa karshen falon duk da yanada tsawo sosai amma hakanan tayi tanayi tana hawaye, 
Tayj sosai harta gaji danse bayan magriba akace tatashi nan taje taci gaba da aikinta, bayan tagama ta jira suka bushe ta goge takaima kowa dakinshi,  a takaicedai se cikin dare tagama aikin nan ta nufi dakinda take kwana (wato dakin karnuka). 
Kamar kullum yauma sunata haushi suna fito da harshe dan da ba'a daure sukeba tsaf zasu lasheta, abincine da aka kawo musu masu rai da lafiya sunci wasu sun barwasu dan wasu kadan suka taba domin abincin da yawa Kala kala, wanda suka barin tajanyo domin rabonta da abinci takai kwana biyar sedai taja ruwan famfoo, hannunta har rawa yake saboda yanda take tura abincin seda ta cinye tas ta kara janyo rahowan karnukan ko a jikinta burinta itadai tasamu abunda zataci domin yunwan da takeji, seda ta cinye sannan taji ta koshi tashi tayi ta gabatar da sallolin da bata yiba, 
Bayan ta idar kamar kullum kafin tayi bacci tafara karanto Alkur'ani tana kuka domin yawamci tasan fassararta kuma tana tausayawa kanta Ainun. 
Tun ranan da haj. taga megadi yana koyawa ma rumana karatu tasa Alhaji ya koreshi aka kawo wani acema Alhaji ai shine abokin iskancin Rumana, seda tayi kukanta ma'ishi tana kai kukanta ga Allah har seda ta denajin kukan karnukan dare yayi sosai sannan tasamu da kyar ta iya bacci jikinta yayi zafi rau zazzabi fal jikinta. 
Allah sarki. 
******************************
Tun randa akayi abun nan tsakanin Alh sadeeq khan da haj. Asma'u ta canxa tadaina mai komai. Ko abu yakeso sedai yaranshi su mishi tadena kulashi, itama zeeza an dau action ita a dole ana taya sisto kishi.... 
Alhaji sadeeq ne ya cika mata bangare daya a kasa inda ba kowa da kaya tun daga italy yayo mata order domin major yace baze bada ko sisinshi a bikin rumana ba, hakan yasa shi Alhaji sadeeq yayi mata,Ya hado mata akwatuna set biyu ya hado mata komai iri daya dana haj. Asma'u sema wa'insu abubuwan da akasa ana haj. Ita ana rumana ba'a xubaba, ya kawo ko takansu bata biba ya hada mata da miliyan biyar ko da abinda take bukata shima batabi takansuba, akwatunan rumana kuma ya ajiye mata domin baza'a kai mataba dan sunce ita dai zasu bashi basusan komai dan haka ya bari se tazo tayi amfani dasu. 
Ana gobe daurin aure. 
Be jima da sauka a kd ba amma ya lura akwai matsala duban zeexa yayi. "Wai meke damun auntyne naga tunda nazo taki sakewa... "?Zeeza ta taba baki."Nima dai bansaniba. "Tashi yayi yaje kusa da haj. dake zaune bisa one sitter hakan yasa ya zube bisa center  carfet din dake tsakiyar falon yace. "Wai Aunty me yake faru wane. " ko kallonshi batayiba hakan yasa yace. "Wai aunty duk akan batun auren nanne kikayi wannan sauyin.... " wani kallo tabishi dashi. "Au ashema kasani, ai dama ninasan maheer harda kai za'a hada baki aci amanana............ " da sauri yace. "A'a wallahi aunty ko daya bacin amana bane domin Allah (SWA) be haramtaba, kisani aunty wannan bayin yaya bane ko yina yin Allah ne domin kinsan mu bamu isa muyi abinda Allah tsaraba.... ", nan yashiga mata nasiha yana mata bayani sosai yanda zata fahimta, a tunaninshi wa'azinshi ya ratsata dan yanda har ayoyi da hadithai yaita janyo mata amma seyaga tayi tsaki ta tashi tsaye. "Wannan kuma kayya dama ni kuma bazan hanata shigowaba gidane gayinan tashigo lafiya ammafa wallahi da kafarta seta gudu Mtssswwww. " takuma jan tsaki ta wuce, baki sake yake kallonta a ranshi yace. "Uhmmmm Aunty tayi nisa se addu'a... "dan haka kawai ya rabu da ita... 
Wanshe kare 
Tun safe Alh sadeeq khan,Maheer khan da kuma Alh. Musa (Abokin Alh. Sadeeq) suka sauka a kanon dabo, (wai koda me kaje anfika amma wannan batu ba haka yakeba). 
Ba'a wani tara jama'aba aka daura auren Alh. Sadeeq khan da amaryarsa Ummu Rumana Aliyu bello khaliyal bisa sadaki naira dubu hamsin. 
Ana daura Auren maheer ya juya kaduna shida Alh. Musa saboda ordition da zeyi yayinda sukabar Alh. Sadeeq shikuma ze taho da Amarya. 
Toh π€π€π€
Masha Allah Allah sanya Alkhairy 
Ina masoyan rumana kufito mu fara shiri domin ko akwai babban walima na murnan auren rumana da Alh.  sadeeq. 
Kuci gaba da kasancewa dani *Ummu ramlat* danjin shin rumana ta tsira daga rayuwar kuncin da take gatacan dai zata hadu da haj. Asma'u taku. 
*Mimi queen πΈ*
Comments dinku shine kwarin gwiwwar mu. 
*Please comments*
*share*
*and vote βοΈ*
Babyn yaya...........ce
I luv yhu my nisful hayati Allah barmu tare forever uban yayana ππππ
8/20/21, 8:16 AM - Mimi: πππππ
     *LABARINA*
πππππ
Alkalamin. βοΈ
      
       *Mimi.πΈ*
                   Haleemart Iserh
                 *(ummu ramlat)*
*πMANAZARTA WRITERS ASSOCIATIONπποΈ*
                   *M. W. A*
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
15&16
Zaune yake bisa 3siter hajiyace ta fito tareda rumana ta kariso falon bisa carfet rumana ta zube tana sanyeda hijabi kanta na kasa se hawaye dake ambaliya a idanunta, haj. tace."to doctor ga amarya nan rumana mun baka amanarta." Firgigit yadawo daga hayyacinshi domin tunda rumana ta zauna yake kallonta dan ita wata iriyar macece da duk wanda yake tare da ita se yaji wani abu yace."eh haj. Insha Allahu zan rike. " se lokacin rumana ta iya daga idanunta da suka rine suka canxa kala saboda kuka ta cikin hijabi ta kalleshi wani kukanne yaxo mata ganin wanda aka aura mata yakai sa'an Abbanta, yanzu wannan mutumin aka auramin Wanda ya haifeni?  Wani wahalallan kukane ya kufce mata harda shashsheka, da sauri haj. tace."kukan me kikeyi kuma rumana haba kiyi shiru keda zaki godewa Allah kinyi aure ga yan uwan kinan se kiyi musu fatan Alkhairy. " kaman almara haka rumana kejin zancen Hajiya sedai tasan duk makircine domin kokadan acikin makircinta bata yiba. 
Alhaji ko kasa cewa uffan yayi se ido daya bita dashi ya mike da sauri. "To mu zamu wuce hajiya. " ta tashi da sauri ta riko rumana."toh Alhaji. " kudi yaciro wanda shi kanshi besan adadin suba danya tasamma miliyan uku ya bawa haj. tana godiya ta amsa, 
Tashi yayi yafice haj. ta dubi rumana cikin nuna isa tace. "Dan ubanki salan ki watsamin kasa a ido ki kula sannan kidinga diban kudinshi kina boyewa kidinga aikomin dasu. "Manya manyan idanunta da suka cika taf da kwalla tabi hajiya dasu tace. "Meye kike bina da wa'innan aljanun idanuwan naki masu kama da gujjiya. "?  Rumana tace. "Dan Allah ki barni nayiwa su aunty mairo sallama...... " bata rufe bakiba saboda mugun rankwashin da hajiya ta zabga mata tareda mata wani mugun kallo."rufemin baki munafukan banza kawai,  kindaiji abinda nace miki ko. "?  Ta daga kai. "To muje yana jira. "
Nan suka fice yana cikin mota yana jiransu haj. Ta bude gaban motan gurin me zaman banza ta zaunar da rumana tana fara'a kaman har ciki tace. "To Alhaji Allah tsare." Nan sukayi sallama, yayi horn me gadi ya bude wagegen gate din yafice. 
Yana driving amma Idonshi nakan rumana da keta kuka rage gudu yayi tareda dubanta ya mika mata handky ba musu ta amsa tasoma tsane kwallanta, a hankali yace. "Kukan me kikeyi. "?  Shiru tayi domin ita kanta batasan kukan me take yiba, kukan an aura mata sa'an Abbanta ne, ko kuwa na farincikin ta rabu da wahalan rayuwane, ko kuma na tunanin irin sabuwar rayuwar da zata fada take? 
ganin batada amsa yasa tayi shiru, ganin tayi shirunne yasa yace."kiyi hakuri rumana nasan baki sona auren dole aka miki kiyi hakuri nima tausayinki ne yasa na aureki. " da  sauri ta dada goge hawaye cikin daddadan muryarta data rine saboda kuka tace. "A'a ba haka bane. " murmushi yayi yace. "To dan Allah ki daina kuka hakanne zesa na gamsu da abinda kikace. " ganin ya damu yasa ta daina kukan domin dama ba ita takeyiba zuwa yake, ganin ta daina yasa yadan samu nutsuwa yaci gaba da tuki. 
Lokacin da suka isa zaria ya tsaya a wani babban restaurant dubanta yayi yace. "Muje. " ba musu tabude motan tabi bayanshi, menu card yabata akan tafadi me za'a kawo mata, amma ta fake akan ita batajin yunwa ganin taki fadi yasa yayi ordan chicken nugget, chicken pepe soup,  dambun nama,pizza,  sinasir da miyan kayan ciki, se soft drinks irinsu ice cream, shawarma, yoghurt da exotic da strawberry shortcake, badan tasoba taci sedan yanda Alhaji ya takura mata. Bayan sungama ya biya kudin suka fito seda yayi sallahn la'asar a wani masallaci sannan sukaci gaba da tafiya. 
Ba wani fira sukeba se rumana da take kalleΒ² shikuma duk inda sukazo zece mata ga guri kaza ita kuma sedai ta daga kai, a haka har suka isa kaduna garin gwamna, kai tsaye hanyar barnawa yayi da ita. 
 bayan yayi horn me gadi ya bude musu dankareren gate din ya shiga yayi parking a parking area na gidan inda motocine ke fake birjik kala da kala, dubanta yayi yace. "Muje rumana. "Rumana da gabanta yaketa fadi tunda suka shigo gidan tayi murmushin karfin hali tasa hannu ta bude motan ta fito tana karewa gidan kallo, hanyar falon ya nufa hakan yasa tayi saurin bin bayanshi har lokacin gabanta be bar faduwa ba.. 
Basu samu kowa a faloba hakan yasa ya nuna nata kujera yace. "zauna bari naje na kira matar gidan. " ba musu ta zauna shi kuma ya haye saman. 
Basu jimaba ya sauko tareda haj. Wacce ba musu ta biyoshi gaban rumana ne ya fadi ganin matar a ranta tace"yanxu da wannan matar zanyi zaman kishi"?  Amma afili dukunnawa tayi har kasa tana gaida haj. Murmushi tayi tareda falin. "Lpy klau rumana ki koma saman mana. " cikin sanyi ta koma ta zauna. 
Alhajine yafara musu nasiha da fadin. "Hajiya ga rumananan dukda nasan kin haifeta amma ki amsheta a matsayin kishiyarki ki riketa amana kaman yanda zaki rikesu Aknan. " murmushi haj. Tayi. "Insha Allah Alhaji ai rumana ya tacCike da jin dadin kalaman haj. ya dubi Rumana 
. "dafatan zaki yiwa haj. biyayya ki dauketa a matsayin uwa in wani abu na damunki ita zaki fadawa." daga kai rumana tayi ba tareda ta iya maganaba ya dubi haj.. "Tashi ki nuna mata dakinta. " ba musu ta tashi rumana tabi bayanta seda takaita dakin ta kawo mata abinci da kayan tabawa sannan ta fice. 
Tsaye rumana tayi tana kallon dankareren dakin da aka kira da nata, bedroom biyune a ciki manya manya kuma dukkansu ancikasu taf da kayayyaki se hadaddan sitting room wanda yake dauke da dankara dankaren royal chairs kitchen kuma









