Showing 1 words to 3000 words out of 180982 words
Chapter 1 - CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE Book .txt
COMPILED BY ESHATT SMILER
HOME OF HAUSA N ENGLISH NOVLS DOCUMNTS
WASPP 08066360176 FOR MORE
CAPTAIN_AHMAD JUNAID
_By Khaleesat Haiydar_
*Dedicated to......*
*Ya Allah! Ya Allah! Ya Allah, Ya ubangiji kamar yanda ka bani ikon fara littafin nan ka bani ikon kare shi cikin aminci da yardar ka, Ya Allah ka min katanga irin ta China da duk wani soul da xai daga min hankali a Media ya Allah ka rabani da sharrin mahassada da duk 'Yan uwana musulmai baki daya, ya Allah ka kara hada kawunan musulmai a duniya ka tsare mu a duk inda muke, Ya Allah ya ubangiji kasa mu gama da iyayen mu lafiya, kasa mu cika da imani da tsoron ka a xuciya don son ma'aiki S.A.W*
Uhnm! my greetings goes to my die hard fans nd frnds dat are alwayz their for me
My Phatiemarkh
Habibah Marafa
Hafsat (Ummu Ilham)
My Humainah bala Abkr
Eeshatullah Goni
My Maryam Aliyu
Rukky Usman
Saknah Ibrahim
Sallynah
Ummu Lailah(AY)
My Salmah
Maman Shakur
Fiddo s dangi
Waow to mention but a few, Khaleesat heart you all. Shout out to my lovely fans. Allah bar min ku.
1.....
Ya jima xaune kan darduman bayan ya kai Ayan karshe a Surah At-tawbah, ganin har shidda da rabi ya sa shi mikewa a hankali ya rufe qur'anin ya ajiye a bedside drawer, jallabiyan jikinsa ya cire ya nufi bathroom, ya dau lkci yana wanka sabulai masu dadin kamshi da shower gel duk ya cika dakin, sanye da bathrobe ya fito yana goge lallausan bakin gashin kansa da karamin towel, gaban mirror ya nufa ya dauko lotions dinsa daga tsaye nn ya shafa, yana gamawa ya jawo mayyukan gashinsa ya shafa ya shiga combing gashin nasa, closet dinsa ya bude ya fiddo well ironed wear din da xae sa dake jikin hanger, farar singlet ya fara sawa, cikin mintuna bakwae kacal ya gama shiryawa, ya dauki silver wrist watch dinsa kirar Emporio Armani ya sa, shoe rack dinsa ya nufa ya dauki bakar cover shoe kirar Haggioti ya koma gefen makeken gadonsa ya xauna ya sa bakar safarsa na kafa snn ya sa shoe din, duk wnn abinda yake kwata kwata bae da walwala, mikewa yyi ya shiga tucking din farar uniform din jikinsa kafin ya dauki belt ya sa, wayarsa ya dauka da hularsa ya koma gaban mirror ya feshe jikinsa da turarruka ya nufi kofa ya fita, Captain Ahmad Junaid kenan, A Certified seafarer (Merchant Navy) Kmr bae son taka kasa yake tafiya a makeken compound din, sai yake ga kamar yayi shekara rabonsa da gidan nasu, Where as sati biyar kawai yayi a Egypt, kai tsaye part din Hajiyarsa ya nufa, bbu kowa falon se kamshi me ddi dake tashi da ya hade da kamshin soye soyen da ake a kitchen, falonta ya nufa da sallama cikin sanyayyan muryarsa, fitowarta daga bedroom knn ta amsa sallamarsa, xama yyi kan kujera yana kallonta yace "Gud morning Mumy" ta dan yi murmushi tana kallon agogo tace "Baka makara ba, dubi har bakwae ya gota ko duk gajiyar ce haka" Shafa lallausan gashin kansa yyi yace "Jiya da headache na kwana Mumy duk na gaji" tace "Ba na baka magani ba? Baka sha bne" a hnkli yace "Na sha" tace "Toh taso mu je kayi break, sae ka kuma sha, kar ka makara" mikewa yyi ya bi bayanta suka koma falo yace "Ina su Fatima?" Tace "Sun tafi makaranta" da kanta ta jera masa breakfast kan dinning, ta hada masa tea me kauri, snn ta koma falonta dauko masa magani, ko kan ta dawo ya shanye tean, don ba da xafi ta hada masa ba sanin bae shan abu me xafi, tana tsaye kansa ya kora maganin snn ya mike yace "Mumy bari in tafi am almost late" tace "OK, amma ka shiga ka gaida 'yan gidan, tun da ka dawo baka shiga ba" bude dara daran idanuwansa yyi bae ce komae ba ya kafa hularsa sai dai da gani kasan ransa bai so ba, ta rakasa har bakin kofa don ta tabbatar ya shiga gaida mutan gidan, part din Hajiya Fati ya nufa, ya tura kofar da sallama, xaune ya sameta tana karyawa a babban falo, xaunawa yyi yace "Ina kwana Hajiya" ta dan kallesa tace "lfya lau mutan misra, an ga daman shigowa gaida mu kenan" shiru yayi bai ce komai ba sai kuma ya mike yace "Na tafi aiki" daga haka ya fice daga falon, ta bi sa da kallo ba dae ka iya gane ma'anar expression din fuskarta, ta dan yi murmushi ta ci gaba da cin kwan gabanta, Part din Hajiya Bilki ya shiga, ita kuma ya sameta tana kunduma ma 'yan aikinta xagi kmr xata dokesu, 'yar ta Sadiya na kwance tana danna waya, daga bakin kofa ya tsaya ya dan duka ya gaisheta, harara ta 6alla masa tace "Ehh lallai Ahmad a 6akin kofa ka gaida Uwarka yau d'an rainin wayo, sai yanxu kasan da mu a gidan?" Hade rae yyi wanda hkn ya kara fito da ainahin kyansa na dan fillo, tsaki tayi ta ci gaba da 6abatun ta ma 'yan aikin ya juya yyi ficewarsa, parkin lot ya nufa ya dauki motar da xae dauka ya bar compound din bayan masu gadi sun bude masa gate, today at work was so stressful for Captain Junaid don duk a gajiye yake from yesterday's journey.
Karfe biyar da 'yan mintuna ya isa gida, ya jima xaune cikin mota yana latsa waya, ganin motar da ya shigo compound din ya sa shi kashe motarsa ya fito ya rufe ya nufi bangarensa, tuni itama ta fito daga motar tare da step sis dinsa Sadiya, bin bayansa tayi tana kallonsa cikin sanyayyan murya tace "Ya Junaid Ashe ka dawo!" Juyawa yyi har lkcn bae tsaya ba ya kalleta snn ya dauke kai yana ci gaba da tafiyarsa yace "Eh!" D'aga hka ya shiga balcony din bangarensa, dariya ta ji daga sama ta d'aga kai taga Muhibba dake xaune balcony macbook dinta a gabanta tana taunar cingam ta tabe baki tace "Cusa kai ba kwarjini" Suhaima ta dauke kanta xuciyarta na tafarfasa ta nufi bangarensu kmr xata tashi sama, Sadiya tayi 'yar dariya ta rufe motar ta bi bayanta. Shi kam dakin sa ya nufa ya cire uniform din jikinsa ya shiga bayi, wanka yyi ya fito ya shirya cikin kananun kaya, jeans baki da polo blue duk hankalinsa na gun Mum dinsa, wayarsa ya dauka ya nufi bangaren ta, xaune ya sameta falo ita da kanninsa Fatima da Aysha, gefenta ya xauna yyi mata side hug ya kwanta jikinta cikin murya me shige da ta shagwaba yace "Momyna am back" Fatima ta kalli Aisha suka tabe baki a tare, Mumy kam murmushi tayi ta dauke fuskarta tace "Welcm! ga abincin ka can dinning, ga dai kannin ka suna kallon ka" yayi 'yar dariya yace "Toh ina ruwana da su" gaishesa suka yi a tare, Fatima tace "Ya A.jay ina tsarabar mu" mikewa yyi ya nufi dinning yace "Aiki na tafi ba holiday ba ai" abinci kusan kala uku ya tarar dining din, farfesun naman rago ya soma diba yana ci. Ko da ya gama bai bar dining din ba yana ta danna waya ganin shidda ya kusa ya mike ya dawo parlor yace ma momy xae je gun abokinsa El-Ameen, tace "Maimakon ka huta kai da kake ciwon kai Ahmad!" Girgixa kai yyi yace "Mum ni ba ddewa xan yi ba" tace "toh shikenan Allah ya tsare!" Bangarensa ya koma ya canxa kaya xuwa farar shirt da blue jeans ya dauki makullin motarsa bayan ya feshe jikinsa da turare ya fito ya nufi parkin lot ya dau motarsa ya bar gidan. A hankali ya rage gudun da yake ganin d'andaxon jama'ar da ke gefen titi a tsaye, da yawan motoci ma sun tsatsaya gefen titi masu shi duk sun fiffito ko wanne na son ganin abinda ya janyo taron, a hnkli ya gangara gefen titi don a tunaninsa hatsari ne kuma bae ga alamar taimako mutanen dake tsatstsaye suke badawa ba yasan kallo kawae suka tsaya yi, bude motarsa yyi ya fito ya nufi cikin taron jama'ar ya kutsa kai, sae a snn ya dinga jin ihun da wasu ke yi, wata ya gani xaune tsakiyar taron hannunta rike da wani yaro da baxae wuce shekaru goma ba sae dukansa take iya karfinta, ga jini na xuba goshinta ba kadan ba, duk tayi dukun da daud'a cikin wata yagaggiyar doguwar riga, wasu samari biyu ne ke kokarin kwace yaron dake kurma ihu hannunta amma sbda irin rikon da tayi ma yaron suka kasa, da ganinta ka ga mahaukaciya, karasawa Junaid yyi da sauri inda suke ganin xata ma yaron lahani ya fixgo gashin kanta da yyi wani dukun dukun da datti, ta saki kara don ba rikon wasa yyi ma gashin ba, amma duk da hka ta ki sake yaron, kara damke gashin yyi da karfi ae ba shiri ta sake yaron tare da kwala wani k'aran, samarin biyu suka dauke yaron da ya rage kiris ya suma don wahala, ta yunkura xata cakume Junaid, ae da sauri ya hade hannayenta da karfi ya murda su xuwa bayanta, ta dinga ihu tana shure shure, kallon samarin gun yyi yace a samo masa igiya, ae da sauri suka juya xuwa neman igiyan, wata 'yar dattijuwa dake cikin taron ne tace "Baiwar Allahn nn ta kusa shekara unguwan nn bata taba kama d'an mutum tayi masa haka ba sae wannan karan, kuma wllh yaran ne suka addabeta da tsokana shi yasa tayi hkn" wata mata ta karbe tace "Yo dama idan ba tsokanarta suka yi ba me suka mata, dubi goshinta dutse suka jefa mata, yara basa ji sae daukan magana da tsokana, ni ko kadan ban ga laifin Baiwar Allahn ba, sae ma tausayin da ta ban, haba jama'a" nan dae aka dinga jajantawa, ko wa na fadin albarkacin bakinsa, shi dae yana rike da hannunta ta baya, ta sunkuyar da kai, duk farin shirt din jikinsa ya bace da datti, samarin ne suka dawo da igiya babba, da taimakonsu ya shiga daure mata hannu da kafa, ba karamin kokuwa suka sha da ita ba yyi mamakin karfinta hka, Suna gama daureta ya koma baya yana kallonta don ganin ko xata iya kuncewa, hawaye ne ke sakkowa daga idonta, jikinsa ne yyi sanyi yana kallonta, lkci daya tausayinta ya ratsa sa, a hnkli ya shiga kakkabe hannunsa, idonsa ya kai kan goshinta da har ya gaji da fidda jinin da yake ya daskare, ya girgixa kai yana kallon samarin yace "Ku taimaka a sa min ita a mota in kai ta a duba goshinta" 'yar dattijuwar daxu tayi wani k'ara tace "Wani asibitin yaro? Ynda Duniyar nn ta dawo ba gskya ynxu, kai waye? Kuma d'aga wani anguwa kake?" Nan jama'a suka fara cece kuce a wajen ana kallonsa, shiru yyi bae ce komae ba, can ya sauke ajiyar xuciya ya juya ya nufi motarsa cikin rashin kuxari, nn aka bi sa da kallo ana cewa "Kun ga rashin gskyar knn, don da yana da ita da dole xae tsaya ya amsa tambayoyin da aka yi masa, kaiii Allah ya raba mu da sharrin mutum" shi kam motarsa ya shiga ya ja ya bar wajen, nan aka fara watsewa kowa na fadin albarkacin bakin sa, wani tsoho ne ya karasa ya kunce mata daurin yana d'an ja da baya kadda ta cafkesa har ya gama ya bar wajen bata d'ago ba bare ta kallesa.
*Haske Writers Association*
[16/10, 19:05] Hassan Atk: *Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
6.....
El-Ameen ya juya yana kallon Junaid ganin ya ki karasowa da karfi yace "baxa ka xo ka ga abinda mahaukaciyar da ka sa na kawo gidana tayi ba, ya Salam!" Junaid na jin hka ya karaso da sauri yana leka parlon, kwalalo ido yyi yana kare ma palon kallo, palon komawa yyi kamar wanda aka yi karamin yaki, don duk ta tarwatse plasman palon da frames gaba daya, lafiyayyen centre table din ma bata raga masa ba, ko ta ina kwalabe ne a falo, duk ta tuttuge labulaye da karafunansu, kujeru kam upside down ta juyasu dukka, Junaid bae san lkcn da ya fashe da dariya ba har da rike ciki, El-Ameen ya bude baki yana kallonsa idon nan nasa ya kada, fixgosa yyi yana huci yace "Yhu see wat you've caused koh Ahmad, gud! this mad woman is adding not a minute more in my house" yana fadin hka ya turasa ya shiga palon, da sauri junaid ya hadiye dariyarsa ya rikosa yace "Haba frnd, Chill plss ka mance mahaukaciya ce ita kamar yanda kake kiranta, I promise wllh duk xan siya maka abubuwan da tayi damage, that's a promise frnd!" marairaice masa Junaid yyi yace "Plss!" El-Ameen yyi kwafa yace "Yanxu naji bayani, kuma ga motata ma can a gida bbu kyan gani, kasan yanda xa kayi da shi, I need it the way it was before, nd don't forget it's my favourite car" Junaid yyi murmushi yace "Kar ka damu xa a gyara" El-Ameen yace "Gud! Kuma ynxu idan mu ka shiga naga tayi fitsari ko otherwise wllh kai xaka gyara min waje" Junaid ya d'aga kafada yace "Na yarda" Nan El-Ameen ya sa kai ya shiga falon yana bin ko ina da kallo, sae a lkcn ya kula da jinin da yayi littering din falon alamar duk ta ji ciwo, kamar ance ya kalli bayan kofar falon ya ganta durkushe wajen duk jini jikinta, suna hada ido ta mike da sauri xata yi waje ya yamutse fuska ya fixgota da karfi, kokuwa ta shiga yi da shi ya mata wani lafiyayyen rankwashi ae sae ga hawaye a idonta tana kallonsa, Junaid da yyi shiru yana kallonsu a hankali yace "Haba El-ameen rankwashi kuma?" Ko kallonsa El-Ameen bae yi ba, ya ja ta suka koma sama xuwa dakin da aka ajiyeta, bude baki yyi ganin duk ta fasa glass din windunan dakin ma, ita nan duk neman hanyar fita take, kwalo ma Junaid kira yyi da karfi, Junaid ya nufi stairs da sauri ya haura ya shiga dakin, El-Ameen na huci yace "Ohh my God! Dubi windows dina Captain" Junaid ya langwabar da kai yace "Duk xan gyara maka as soon as possible" El-Ameen yyi kwafa yace "Allah kar ya wuce kwana biyu, kuma ni ka xo ka ajiye mata abincin my frnd, I have important things doing a office" karasowa Junaid yyi ya ajiye abincin ya bude yana kallon yanda ya rike hannunta gam sai mutsu mutsu take, El-Ameen ya kai ta k'asa ya nuna ta da yatsa yace "Wllh Kika sake min barna a gidana sae na gaggalla maki mari, wawiya kawai" ita dae kanta na k'asa, tsaki yayi ya mike yana kallon Junaid yace "Mu je plss malam gashi ka kawo mata abincin hankalinka ya kwanta" Junaid yace "But ya kamata mu samo 'yar dattijuwa yanxu koh?" Wani kallo El-ameen yayi masa yace "Ya kamata dai ka samo" daga haka ya fice daga dakin, Junaid ya bi sa da kallo sannan ya kalleta, har lokacin bata d'ago ba, abincin ya matsar mata gabanta a hankali yace "Ki ci abinci kin ji, we are only helping yhu Baiwar Allah" ita dae kanta na kasa sai d'ada takurewa waje daya take, kwala masa kira El-Ameen yyi ya fito da sauri, El-Ameen ya sa ma dakin key yace "barnan ya tsaya iya dakin" shi dae Junaid bae ce komae ba har suka fito, El-Ameen ya tafi gun tap din dake compound din gidan ya wanke hannunsa yana tsaki ya nufi gate Junaid na bin bayansa, a cikin mota El-Ameen ya ciro waya ya shiga neman nmbr, yana dialing ya sa hands free, sallama aka yi masa ya amsa yace "Jibril kana ji na," d'aga daya bangaren aka ce ehh oga, yace "Gud mai gadi nake son ka samo min nan da 'yan awanni don Allah, wanda ka sani kasan halinsa fa" D'aga daya bangaren aka ce "Toh oga, in'sha Allah xa ayi hkn" katse wayar El-Ameen yyi, Junaid ya tada motar suka bar layin, sae da ya fara ajiye El-Ameen clinic bbu wanda yace ma kowa komae, yana fice masa a mota ya ja motar ya nufi office shima, El-Ameen yyi murmushi yace "Ina xaune xa ka dawo ka same ni ne ae"
Karfe hudu da rabi Junaid ya koma gida daga gun aiki, tunaninsa daya karyar da xae ma Mumy ta bar shi ya fita, don ryt from time shi ba mae xuwa ko ina bane daga gun aiki sae gida sai in kuma yaje kallon kwallo shi ma ba ko da yaushe ba don yafi son kallon a gida, ko da yaushe yana manne da ita shi dai, yawanci ma El-Ameen ne ke xuwa gidansu shi bae fiye xuwa can ba sosae, yana xaune bangaren Mumy bayan ya gama lunch, ita kadae ke hiranta sai fatima dake ta shirin islamiyya, shi kam duk hankalinsa baya tare da shi kawae ya kafa ma tv ido ne kmr me kallo, agogo ya duba ya ga har biyar, ya fiddo waya ya kira lambar driver yace ya xo ya samesa bangaren Mumy, ba a dau lkci ba drivern ya xo, Junaid ya ciro dubu goma ya mika masa yace "Gashi wannan ka siyo fruits din dare kamar ynda kake siyowa ka kai ma kowa nasa" Drivern ya risina ya karba yace "Toh yallabai," Junaid ya ciro Atm dinsa yace "ka d'an biya Atm Machine ka ciro min dubu talatin" Drivern ya karba yace "In'sha Allah yallabai" yana fita Mumy tace "Me xaka yi da dubu talatin Junaid" Junaid yace "Su Umma xan ba ko suna bukatar abu kafin Abba ya dawo jibi" Mumy tace "Ohk Hakan yyi" yana xaune sae kallon agogo yake a kai a kai har Ishaq ya dawo da ledoji hudu dauke da fruits kala kala, ya ajiye ma Mumy nata snn ya ciro 30k ya mika ma Junaid, Junaid yace "Yauwa ka raba dubu sha biyar biyar ka kai ma Hajiya daya Umma daya" Mumy tace "A'a kai ya kamata ka kai masu" bae yi musu ba ya karbi kudin hannun Ishaq, Mumy tace "Ajiye naku fruits din ka fara kai masu nasu" Ishaq ya ajiye leda daya ya fita da biyu don kai