Showing 6001 words to 9000 words out of 180982 words

Chapter 3 - CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE Book .txt

dinta ya sameta har ta kwanta, xauna wa yyi daga gefenta yace "Kin kwanta mum?" Tace "Har ka fito?" Yace "Eh mum" peck din goshinta yyi yace "Gudnyt mum, xan tafi in kwanta" tace "Toh Allah tashe mu lfya, make sure kayi alwala kayi addu'a kafin ka kwanta" yace "In'sha Allah mum" mikewa yyi ya kashe mata wutan dakin ya rufe mata kofa ya fita, dakin da kanninsa suke ya bude, Aisha ce ke waya ita ko Fatima tayi bacci, ya rufe kofar ya fito parlor, xaune ya tarda Muhibbah tana jiransa, yyi mamakin rashin ganin Hijab a jikinta don da hijab ta shigo palon Abba, kauda kai yyi ya fita daga parlon ta mike ta bi bayansa, yana isa part dinsa ya bude ya shiga ya juya yana kallonta ganin tana kokrin shigowa yace "Ki jira ni a nn malama" rufe kofar yyi, ta hade rae ssae tana kallon kofar, tsaki tayi ta bude ta shiga, ganin bae palon ta nufi bedroom dinsa, ya dauko kudin zae fito suka kusa cin karo, wani tsawa ya daka mata yace "Are yhu insane xa ki biyo ni daki" kallonsa ta tsaya yi, yyi tsaki ya bangajeta ya fice a fusace, bin bayansa tayi ba tare da ta ji haushi ko kadan ba, a palo ya jefar da kudin ya nufi kofa ya bude yace "Leave yanxu!" D'an tsaki tayi ta duka ta dauki kudin ta fice, ya kulle kofarsa ya sa key don wani mugun haushinta yake ji a gidan. K'asa bacci yyi daren ranan, duk juyin da xae yi sae mahaukaciyar nn ta fado masa, hankalinsa ne ya tashi don shi dae bae mata komae ba illah taimakon yaron da yyi, mikewa yayi daga karshe ya nufi bayi ya dauro alwala ya fito ya shimfida pray mat ya shiga nafila, sae kusan Karfe uku da rabi bacci ya daukesa. Da asuba ruwan sama ya sakko kamar da bakin kwarya, kmr jiya yau ma bae fita mosque sllhn asubahin ba sbda ruwa, ruwan dumi ssae ya hada yyi wanka don ko kadan bae son sanyi shi, ya shirya cikin uniform dinsa ya dauki babban kadigan na uniform me kalan Navy blue ya sa snn ya fito falo rike da rain coat dinsa, sae da ya tabbatar wayoyinsa na aljihun wandon uniform din jikinsa snn ya fito balcony ya saka rain coat din da hulansa ya nufi bangaren Mumy, a balcony ya cire rain coat din ya bude kofa ya shiga, tana kitchen da mai aikinta sai fatima suna hada breakfast, ya shiga kitchen din ya gaisheta ta amsa da cewa "Ka tashi lfya, ya ruwa?" Yace "Alhmdllh mumy" Fatima ta kallesa tace "Gud morning ya Ahmad" yace "Morning" ya fita kitchen din, tea kawae ya sha da kwae shi ma sae da mum ta takura sa wae ya makara xuwa aiki, har balcony ta rakosa tace "Baxa ka shiga gaida 'yan gidan da Abba ba kenan" ya dan tsuke fuska yace "Am late mum," tace "Toh Allah ya tsare" rain coat dinsa ya sa yace "Ameen" snn ya nufi parkin space, kusan a tare suka jero da Suhaima dake rike da lema tayi shirin makaranta, ko kallonta bae yi ba ya bude motarsa ya shige ta nufi tata motar tana kallonsa, jan motar yyi ya danna horn aka bude masa gate ya fice. A hnkli ya ke driving din har ya iso inda mahaukaciyar jiya take, samun kansa yyi da parking gefen titi yana kalle kallen inda xae ganta idonsa ya sauka kanta, xaune take cikin ruwan ta hade kai da gwiwa, duk ta jike da alama tun da ruwan ya sauko bata bar wajen ba, Junaid ya jinginar da kansa jikin kujera yana ci gaba da kallonta, duk jikinsa yyi sanyi, da kyar ya iya jan motarsa ya bar wajen ganin yana bata lkci, shi mutum ne me tausayi da raunin xuciya kamar mace, har ya isa office bae da sukuni, colleagues dinsa duk suka lura da shi suka kuma tambayesa ko Lfya yace bai jin ddi ne, Karfe biyar saura ya bar gun aikin, driving kawae yake cikin rashin kuxari, bae bi hanyar da xae ga mahaukaciyar ba ya canxa hanya, ko parking din arxiki bae yi ba ya bude motar ya nufi part din mumyn sa, kwanciya yyi kan dogon kujera ya rufe idonsa gam, Mumy ce ta fito daga kitchen ganinsa a kwance tace "Lfya Ahmad" jin bae ce komae ba yasa ta karasa kusa da shi tace "Ahmad!" Bude idonsa da ya kada yyi ya mike xaune ya dafe kansa, taba jikinsa ta shiga yi da damuwa tace "baka da Lfya ne?" Lumshe ido yyi ya kwanta jikinta ta rungume sa tace "Talk to me mana son, me ya faru?" A hnkli yace "Kai ne ke man ciwo Mumy" tace "Ci abinci mu tafi asibiti" da sauri yace "No mum, xan sha magani" hade rai tayi tace "Wani maganin xa ka sha, sau nawa kke sha bae maka aiki ba, so kake ka dauko min magana gun Abba koh" shiru yyi ta mike ta nufi dinning ta dawo rike da kulan abinci da plate da spoon, fried rice din ta dibar masa ta ajiye snn ta koma kitchen ta hado masa tea, bae son mum din tasa ta daga hankalinta shi yasa ya daure ya dinga cin abincin don kwata kwata bae da appetite. Mikewa yyi da ya gama Mumy tace "Ka tafi ka canxa kawae mu tafi clinic" yace "Toh" snn ya fita xuwa bangarensa, wanka yyi ya canxa uniform din jikinsa xuwa kananun kaya, ya d'an kwanta yana tunanin karyar da xae ma Mumy ta hakura da xuwan su asibiti, dubara ce ta fado masa ya mike da sauri ya dauki wayarsa ta fita, xaune ya sameta palo ta shirya tana jiransa, murmushi yyi yace "Mumy ynxu El-Ameen ya kira ni, I told him m nt ok, shine yace I shud cum over ya duba ni" hararansa Mumy tayi tace "Yhu should come over dai kuyi hira, my frnd mu wuce clinic" marairaice mata yyi ya mata side hug yace "Haba mum, ga ni da amini likita kice mu je clinic, kinga baxae ji ddi idan ban je ba plss"
*Haske Writers Association*
[16/10, 19:05] Hassan Atk: *Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
5.....
Falo El-Ameen ya sakko ya samu Junaid tsaye bayan kujera yana kallon mahaukaciyar, El-Ameen yace "Toh ae sae ka dauketa ka kaita spare room ka ajiye ta ka kunce rope din" karasawa falon Junaid yyi, yyi yanda El-Ameen yace masa, yana kunce igiyar a daki ya fice da sauri ya ja kofar, kulle kofar palon El-Ameen yyi bayan sun fito, har lkcn ruwan da ake bae tsaya ba, El-Ameen ya d'an yi tsaki ya sa kai ya shiga ruwan ya nufi gate, bin sa Junaid yyi a baya ba tare da ya damu da hakan ba, sae a snn ya dinga jin sanyi na shigar sa ba kadan ba, El-Ameen ya kulle gate din daga waje bayan sun fito suka shiga mota, suna hawa kan titi El-Ameen yyi murmushi ganin yanda Junaid yake rawan dari, yyi kwafa yace "Ai baka fara rawan sanyi ba tukun malam, sai randa 'Yan gidan ku suka samu labarin mahaukaciyar nan I assure you oven ma yyi kadan yasa ka daina rawan sanyi" Sharesa junaid yyi, El-ameen yyi dariya yana kallonsa yace "Mu je can gidanmu, idan ya so da asuba sae ka koma gida, don kana komawa gida ynxu Mumy ta kama ka har duka na tabbata xata iya maka, ni kam na girma bbu abinda Ummina xata ce min" yana maganar ne yana kyalkyala dariya, shi dae Junaid bae tanka sa ba don sanyin da yake ji ma kadae ya ishe shi, kuma yasan gskya ya fadi yana komawa gida ynxu Mumy xata daga hnkli baxa kuma ta barsa ba sae ya fadi daga inda yake cikin ruwan nn. El-Ameen na gama parkin a parking lot din gidansu ya juya yana kallon Junaid yace "Let move in frnd" bude motar Junaid yyi ya fito ya nufi cikin gidan da sauri don ba karamin sanyi yake ji ba, bbu kowa palon ya nufi dakin El-Ameen, bathroom ya shiga ya hada ruwa me dumi sosae yyi wanka, ko da ya fito El-Ameen na xaune yana shan tea, ya fiddo rigan sanyi babba a closet bayan ya goge jikinsa ya sa, wayarsa ya dauka yana dubawa ko bae jike ba snn ya ajiye gaban mirror ya dawo yyi kwanciyarsa ya ja bargo ba tare da ya kalli El-Ameen ba, El-Ameen yace "Baxa ka sha tea'n ba?" Share sa Junaid yyi, El-Ameen yyi murmushi sanin baxae kulasa ba yace "Toh fa gwara ka tashi ka sha magani kar ka k'asa tashi gobe, ana kuma tambayata ba'asi xan tona wllh" Dariya El-Ameen ya dinga yi jin Junaid bae tanka sa ba still, ya mike ya dauko paracetamol ya dawo da Goran ruwa ya xauna gefensa yace "Look frnd, tashi ka sha drug kafin ka kwanta kar ka tashi da mura gobe, yhu knw I may be annoying a times" yana murmushi ya kare maganar, mikewa Junaid yyi ya karbi maganin da ruwa ya kora ya koma ya kwanta don shi kansa yasan without dat baxae tashi lfya ba gobe. Washegari da asuba kafin ayi sllh Junaid yace xae tafi bayan ya daura alwala yyi Raka'atainil fajr, bae yarda ya dau motar El-Ameen ba don yasan hkn na iya tona masa asiri, ko mum din El-Ameen bata san yana gidan ba, El-Ameen ya rakasa bakin titi ya tsayar masa da a dai daita don ca yyi bae iya ba. Ana kokarin tada sllh ya iso anguwarsu na Government reserve area, masallaci kawae ya shiga, ana idarwa ya dde xaune yana Azkar har ya ga fitan Abbansa snn ya mike ya bi bayansa, part dinsa ya nufa ya gaishesa ya amsa masa snn yace "Kana mura ne Ahmad?" Junaid ya girgixa kai yace "Ya ma yi sauki Abba, ina shan magani" Abba yace "Gud! Babu damuwa ko?" Junaid ya shafa kai yace "Ehh Abba!" Abba yace "To Allah maka albarka" Junaid yace "Ameen Abba," Abba yace "Gobe xan fita xuwa Germany, tafiyar ya xo min da gaggawa ne, as usual am handing the family over to yhu son" Junaid yace "Toh Allah kai mu Abba, journey mercy dad, in'sha Allah" Abba ya shafa kansa yace "Ameen dear son" mikewa Junaid yyi yace "It's almost daybreak Abba, bari in je in shirya xuwa aiki" Abba yace "Its ohk, stay blessed" fita yyi ya nufi bangarensa, cikin mintunan da basu fice ashirin ba ya shirya cikin uniform dinsa na dark navy blue trouser da light blue shirt, kadigan yasa navy blue bayan ya feshe jikinsa da turare ya rike hularsa a hannu, waow yyi kyau har ya gaji lips din nan nasa kamar ya shafa jan baki, ya bude manyan idanuwansa sanin bae shafa komae ba ya daga kafada ya fita xuwa side din mum dinsa, fatima dake shara a balcony ta gaida shi, ya amsa ya shiga parlon, Mumy na jera masa breakfast dinsa a dinning ya sameta, ya nufi dinning din ya mata side hug ya kwanta jikinta a hankali yace "Sabahul khair Ummu na" Mumy tayi murmushi tace "How are yhu, baka rufe windows bne jiya naji kmr mura na neman kama ka" shagwabe mata yyi yace "Na rufe mana Mumy," ta hararesa tace "Toh ka bar Ac a kunne ko" ya girgixa kai yace "Not at all mum, kinsan ynxu lkcn ruwa ne kuma tun da na dawo ciki nake fita aiki shi yasa kmr muran ke son kama ni" tace "Toh I will get yhu an umbrella don ban ga amfanin Raincoat din da kake sa wa ba" yace "A'a ni nafi son raincoat dina, umbrella sae kace mace mumy" tace "Toh idan na baka kar kayi amfani da shi" langwabar da kai yyi ya xauna yana kallon ynda take hada masa tea, plate din potatoe'n da ta xuba masa ya jawo ya shiga ci yace "Aisha ta koma ne Mumy?" Mumy tace "Tun jiya" daga haka ta bar dining din ta shiga daki, a hnkli junaid ya ajiye fork din hannunsa tunawa da mahaukaciyar da suka dauko jiya da yyi, har Mumy ta fito bai kuma cin komai ba, ta kalli agogo ta kallesa tace "Kana kallon agogo dai koh" yyi yake ya ci gaba da cin potatoe'n, tutturawa kawae ya dinga yi don neman appetite yyi ya rasa, ya mike yana goge bakinsa da tissue yace "Allah amfana momy, thnks a lot" tace "Welcm, but make sure ka shiga ka gaida mutan gidan yau" d'an hade rae yyi amma da yake baya mata musu cewa yyi "Toh mumy" ta rakasa har balcony, yyi side din stepmums din nasa, bangaren Hajiya Fatee ya fara shiga tana xaune da Muhibba a palo da Rabi'a dake gugan Hijab, ya xauna kan kujera hannunsa rike da hularsa me kaman face cap me dauke da symbol din captainship a jiki, yyi k'asa da kai yace "Ina kwana Hajiya" a dakile tace "Lfya lau d'an gwal" hade rae yyi yana jujjuya hular hannunsa, Rabi'a tace "ina kwana ya Ahmad?" Yace "Lfya lau ya sch?" Tace "Alhmdllh" Muhibbah dake ta kallonsa ko kiftawa bata yi ganin ko kallon inda take bae yi ba cikin wani siririn murya tace "Ina kwana ya A.jay" ba tare da ya kalleta ba yace "Lfya lau" sae kuma ya mike ya nufi kofa yace "Na tafi aiki Hajiya," bata tanka sa ba har ya fita, Muhibba ta kalli Hajiya tace "Hajiya kinga ko amsa gaisuwata bai son yi ma" Hajiya Fatee tayi wani murmushi mai wuyar fassara ba tare da tace komae ba, Rabi'a tayi 'yar dariya tana guganta tace "Aiki" harara uwar ta wurga mata, ko sanin tana yi bata yi ba, part din Hajiya Bilki Junaid ya nufa, bbu kowa palon ya nemi gu ya xauna yana kallon agogon wrist dinsa, daga kitchen khadija ta fito ta d'an wara ido tace "Lah ya Ahmad ashe kana nan, Gud morning" yayi murmushi yace "Morning lil sis, ya sch?" Ta karaso kusa da shi ta shagwabe murya tace "Lfya lau, plss yaya ka d'an min transfer din 5k frnd dita na birthday gobe xan siya mata perfume" yace "Kije ki samu Abba mana ae bai tafi ba" ta d'an bata rai tace "Shekaranjiya fa ya canxa min phone" yace "Ohk ltr" Hajiya bilki ce ta shigo palon, kallo daya tayi masa ta dauke kai, tana kallon Khadija tace "Ke don uwar ki me ya hada ki da Suhaima kike mata fitsara?" Khadija ta hade rai ta juya ta koma kitchen, junaid yyi k'asa da kai yace "ina kwana Umma" ba tare da ta kallesa ba tace "lfya lau" Suhaimah ce ta shigo palon da alamar muryarsa taji, tace "Ina kwana ya Ahmad" mikewa yyi yace "Lfya lau" daga hka yace "Na tafi aiki Umma" bae jira cewarta ba ya fice, ta bi sa da harara, Suhaimah ta samu waje ta xauna ta xabga tagumi tana kallon Umman. Junaid na xuwa gun aiki ya dauki permission Karfe sha daya ya fito, driving yyi xuwa clinic din dad din El-Ameen, Yana rike da hularsa ya haura sama xuwa office din El-Ameen, Nurses din suka bi sa da kallo ko kiftawa bbu, yana attending to patient ya same sa, ba tare da ya kallesu ba ya shige bedroom, xama yyi yana addu'ar Allah yasa baxae dau lkci da patient din nasa ba, ko minti biyar ba'ayi ba sae ga El-Ameen ya shigo yana kallonsa yace "Ya? Duty din naka ya kuma shifting xuwa yamma ne?" Junaid yace "No of course, yarinyar da muka bari kulle a gida fa?" El-Ameen ya hade rai ya galla masa harara yace "Kaga xaka fara daga ma mutum hankali da sassafen nn koh, Toh me xa ayi mata ynxun? Ba sae xuwa yamma in mun gama aiki ba" Junaid ya girgixa kai yace "Yanxu fisabilillah da xaka fito baka yi breakfast ba Dr? Ita ba mutum bace da xa a bar ta ba ruwa ba abinci har xuwa yamma?" El-Ameen yyi masa wani kallo yace "Toh wai wa ya hana ka xuwa kai mata abincin ynxu, iyaka ka xo kace in baka makullin gida in baka, pls let me be Captain, am getting sick of you," Junaid ya lumshe ido ya rike kansa don walakancin El-Ameen ya fara isan sa, mikewa yyi ba tare da ya kallesa ba yace "Ohk! Bani keyn" El-Ameen ya d'an shafa kai yace "Alryt am sorry, haka ne kuma fa ya kamata a kai mata abinci, tun da ita ma mutum ce kamar Junaid" ficewa Junaid yyi ya bar masa dakin, El-Ameen yyi dariya ya bi bayansa, makullin gidan dake table dinsa ya dauka ganin Junaid ya bar office din shi ma ya fita, kusan a tare suka iso gun motar junaid, El-Ameen ya bude gaba ya shiga, junaid ma ya shiga ba tare da ya kallesa ba yace "Kaga hand me dat key ka fice min a mota" El-Ameen ya gyara xama yace "Toh fitar da ni mu ga" Junaid ya fi minti biyar bae tada motar ba, El-Ameen kuma yaki fita, sanin ba fitan zae yi ba kawae ya tada motar ya ja suka bar asibitin, wani eatry ya fara biyawa ya siyo abinci da ruwa sae hollandia drink, El-Ameen ya rike kai ya dinga dariya da ya ga hollandian, shi dae Junaid bae tanka sa ba, sae da suka dau hanyar gidan yace "kaga malam da ka rufa ma kanka asiri ka bude hollandian nn mu shanye kawae, dama am thirsty, banda haka a ina ta san wani hollandia in ba neman magana irin naka ba" driving kawae Junaid yake bae tanka sa ba, El-Ameen yyi dariyarsa me isarsa yana mamakin Junaid, a waje suka yi Parkin motar, El-Ameen ya bude gidan suka shiga, kallon Junaid yyi da ya tsaya yace "A'a Toh ka shiga gaba mana goga" murmushi Junaid yyi bae ce komae ba yana shafa kai don shi har ga Allah tsoro yake, El-Ameen ya dinga kyalkyala dariya har suka isa kofa Junaid na biye da shi a baya, El-Ameen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login