Showing 21001 words to 24000 words out of 180982 words

Chapter 8 - CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE Book .txt

na doki Suhaima, meyasa idan basu yi karya ba basu ji ddi ba 'yan gidan nan?" Mumy tace "Ae tun ba yau ba na sha fada maka ka daina shiga hurumin da ba taka ba, to yanxu gashi sun hada ka da Abban ka ae" ya fuzar da iska yace "Na tafi Mumy sae na dawo" tace "Ina xaka?" Yace "Gidansu faisal xan je" Mumy tace "Toh shknn kar ka dde, and drive carefully" yace "Ohk Mum" har bakin mota ta rakosa, su Umma dake xaune da Hajiya suka bi su da kallo suna tabe baki, ko kallonsu Mumy bata yi ba har Junaid ya ja motarsa ya bar gidan, Mumy ta koma part dinta, Hajiya ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Wannan Yaro ya xame mana babban obstacle a gidan nan wllh, komae sae yanda yace ma ubansa, idan ba ina bakin ciki da numfashin da yake a duniya ba Shegiya nake" Umma tace "Uhm ke ko ni, da da yanda xanyi da shi da tuni ni dae nayi wllh, don ko uwarsa bata isheni kamar yanda ya ishe ni a gidan nan ba, na tsane shi wllh wllh, ko 'ya yan mu fa Hajja bata ji da kamar yanda take ji da shi wae don yana namiji mu kuma mata gare mu" Hajiya tace "Toh shine kike kokarin ganin yanda xa ki cusa masa Suhaima ya aura kuma" Umma tace "Toh ae ke ma da xae auri Muhibba so kike naga" Hajiya tace "Da kenan ba yanxu ba don nasan hakan ma baxae taba yiwuwa ba, bari mu shiga ciki ki ji shawarar da na yi a kan matakin da xamu dauka kan Ahmad a gidan nan" Umma tace "Toh me muke a nan, mu shiga kawae ki ban in sha" mikewa suka yi gaba daya suka yi palon Hajiya. Gidan El-Ameen junaid ya nufa, yana gama parkin a waje ya shiga ciki, wanki ya tarar mama nayi a compound din na kayansu, ya karasa inda take suka gaisa sannan yace "El-Ameen ya xo ne mama?" Tace "Eh ya xo daxu da safe" yace "Ohk, bacci take yi ne?" Ta girgixa masa kai tace "A'a idonta biyu sae dae ya kulle dakin," cikin gidan ya nufa ya haura sama, sae dae ya kasa bude dakin, ya kusa minti biyar tsaye sae kuma ya murda key din a hankali, bayan kusan second talatin ya murda handle din kofar, tsaye ya ganta jikin window tayi baja baja da gashinta tana sanye da doguwar rigar kanti pink colour da blue nd black flowers jiki, kallonsa take tana bobboyewa jikin bango, yayi murmushi ya rungume hannayensa yana kallonta.




鉁嶐煆�
*Haske writers association*馃挕
[16/10, 19:09] Hassan Atk: 鈿� *Captain_Ahmad Junaid*鈿�


_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�


11.....


Sulalewa kasa tayi ta xauna ta takure waje daya tana rufe fuskarta da dogon gashinta, dakewa yayi ya karaso cikin dakin kamar bai son taka kasa yana kallonta ya isa gabanta sae dae banda faduwa bbu abinda gabansa yake, bata dago har lkcn ta kallesa ba sae d'ada takurewa waje daya take, cire tsoro yayi ya durkusa gabanta a hankali, dago kanta tayi tana kallonsa a tsorace, murmushi yayi murya can kasa yace "Hello!" Kuri ta kura masa da ido, shi ma hakan yayi ma manyan fararen idonta, can ya lumshe ido ya bude cikin sanyin murya yace "Allah ya baki lafiya don son ma'aiki S a w." A hankali ya kai hannunsa kanta ta kuma shigewa jikin bango, murmushi yayi ya matsa gabanta ya tattare mata gashinta ya mayar baya yace "Ki daina kunce gashin ki idan an daure maki Kinji" yana magana ne yana kallon fuskarta, ita kuwa wani gun daban take kallo, ji yayi ana haurowa sama, ya juya yana kallon kofa sae ga El-Ameen, dauke kai yayi El-Ameen ya shigo yana murmushi yace "Uhnn! Ka daina tsoron nata kenan yanxu?" Mikewa Junaid yayi bae ce komai ba, El-Ameen yayi dariya yace "In gaya maka meyasa kaga ta kyale ka?" Junaid ya juya yana kallonsa, sai da ya dau kusan minti daya sannan yace "akwae alluran da na mata daxu shi yasa ta nutsu, but ina me tabbatar maka da xaran ya saketa xaka gane kuran ka idan ka tsaya gabanta" yana murmushi ya kare maganar, Junaid ya tabe baki ya juya ya fice daga dakin ba tare da ya tanka sa ba, El-Ameen ya bisa da kallo yana dariya sannan ya juyo yana kallonta, karasawa gabanta yayi ya durkusa ya dago kanta, hade rai yayi yace "Sae da kika kuma cire ribbon din koh?" Kallonsa kawae take ko kiftawa bata yi, ya hade rai yace "I will knock yhu idan baki bar kallona haka ba" kamar taji me yace ta dauke idonta daga nashi, mikewa yayi ya dauko ribbon ya dawo gabanta ya durkusa ya kama gashinta waje daya ya daure da ribbon din sannan ya dagota suka mike a tare ya kama hannunta, kin binsa tayi tana tutturjewa yace "Keehh" daga haka ya ja ta suka fita daga dakin tana bin sal, Palo ya sauko da ita ya xaunar da ita kasan rug, ya dauko ledan da ya shigo da ya durkusa gabanta ya bude, fried Irish ne da kwae, sae tomatoe ketchup, ya dauki potatoe daya ya dibi kwae ya kai mata baki, dauke kai tayi da sauri tana komawa baya, ya tsaya kallonta, kai wa bakinsa yyi ya ci, Junaid dae sai kallonsu yake yana yi yana danna waya, kara daukar wani chip din El-Ameen yayi ya dangwali ketchup ya kai bakinta, tsura ma dankalin ido tayi sae kuma ta matso a hankali ta lashe ketchup din, El-Ameen ya wara ido yana kallonta, sai kuma ya saka dariya, murmushi junaid yyi yana ci gaba da danna wayarsa, sae tsotsan ketchup din take a baki, El-Ameen ya kuma dangwala ya kai bakinta ta kuma lashewa, rike kanta yayi ya tura mata dankalin a baki ta fito dashi ya fadi kasa, ya hade rai yace "I will slap yhu fah" kallonsa kawae take ko kiftawa babu, ya dauki wani dankalin ya dangwali ketchup ya kuma kai mata baki, lashewa ta kuma yi ta bar masa dankalin tana tsotsan bakinta, yayi murmushi yana kallon Junaid yace "this shows tana son ketchup lkcn da take da hankali" shi dae junaid bae ce komae ba, El-Ameen ya dinga dangwalan tomatoe din yana kai mata baki tana lasa, exotic drink ya bude ya juya yana kallon Junaid yace "Get me cup plss a kitchen Captain, kaga dai patient dinka nake feeding" Junaid bai ce komai ba ya mike ya nufi kitchen ya dauko cup din ya kawo masa, ya karba ya tsiyaya drink din ya dauka ya kai mata baki, dauke kai tayi da sauri, ya juyo da ita ya rike kanta ya kai cup din lip dinta, kadan ta kurba ta cire bakinta tana yamutse fuska, xae kara bata ta sa hannu xata karbi cup din ya sake mata, ta dade tana kallon cikin cup din kafin ta kifar da lemon nan tsakiyarsa, El-Ameen ya mike da sauri ya bar wajen cikin tsawa yace "Kehh!" Tsorata tayi sosae ta dinga shisshigewa jikin kujera, ya karasa kusa da ita ya duka ya mata knock a kai yace "kika sake min irin haka sae na tsula maki bulala" Murmushi Junaid yayi yana shafa kansa, El-Ameen ya dago ta ganin drink din duk ya bata kayan jikinta, tsaye ya bar ta nan wajen ya fita xuwa ya kira Mama, ta juya tana kallon Junaid dake kallonta, ya sakar mata murmushi ta dauke kai ta durkusa wajen ta jawo ledan take away din da Irish din ke ciki ta dauki wanda yake bata ta ajiye gefe, ta bude wanda bae taba ba ta tsura ma dankalin ido, kifarwa tayi a kasa, Junaid ya mike da sauri yace "Noo! Me yasa kika xubar" kallonsa tayi kafin ta maida hankalinta kan abinda take, ta dauki take away din da ya fara bata ta juye cikin na wanda ta xubar a kasa sannan ta mike tsaye, tattare gown din jikinta tayi ta juye dankalin a rigarta ta jefar da take away din, Junaid ya langwabar da kai yana kallonta ya ma rasa me xae ce mata, El-Ameen ne ya shigo Mama na biye da shi a baya yana mata magana, tsayawa yayi daga bakin kofa ya bude baki ganin barnar da tayi, tana ganinsa tayi kusa da Junaid ta tsaya rike da rigarta da ta juye dankali ciki tana kallonsa, El-Ameen ya karaso palon da sauri cikin fada yace "Whatt! junaid kana kallonta ta xubar min da abincin da xan ci?" Bai jira cewar Junaid ba ya nufeta, sake rigarta tayi dankalin ya xube gaba daya kasa tayi bayan junaid da sauri, har wani bari jikinta yake, Junaid ya dakatar da shi da sauri yace "Hey, Look Dr, naga in tana da hankali ae baxata yi haka ba, have you forgotten mahaukaciya ce kamar yanda kake kiranta, wannan ae xalunci kawae kake ma patient din taka, ba dae yunwar Irish kake ba, kar ka damu I will get yhu enough idan muka fita" El-Ameen yyi masa wani irin kallo yace "Da'alla my frnd ba kana kallonta ba ka kyaleta, Better tunda dai xaka siya min wani, but wnn ae iskanci ne ba rashin hankali ba, don bata da hankali sae ta dinga sa mu aiki?" Junaid yace "naji xan gyara wajen is that all" Mama dake tsaye palon tana kallonsu tayi murmushi tace "xan gyara wajen bokon turai, kasan sae a hankali, kuma ma wllh hauka me tsafta take yi bata da kaxanta ko kadan" El-Ameen yayi kwafa yana kallonta ganin yanda take lekosa daga bayan Junaid yace "Ni nasan maganin ki ae, kina wani leko ni da Idanuwan nan naki" Junaid ya d'an tabe baki ya koma ya xauna, Mama ta nufi kitchen don dauko abinda xata gyara wajen. karasawa gabanta El-Ameen yyi ya kama hannunta ta fasa ihu, kunnenta ya ja ta nufi sama da ita, Junaid ya bi su da kallo sannan ya girgixa kai a hankali ya jinginar da kansa jikin kujera. Bayi El-Ameen ya shiga da ita ya wanke mata hannayenta sannan ya fito da ita ya xaunar gefen gado sai kallonsa take, wani kayan ya ciro mata ya ajiye gefen gadon, yana kallonta yace "ki daina kallona haka keh, kuma kika kuskura kika tashi a nan sae na xane ki, clear?" ita dae kallonsa kawae take, sae ta basa dariya ganin irin kallon, ya rungume hannu yace "Uhhn! Halan dai kin san ni ne?" murmushi yyi ya juya ya fita daga dakin. Mama jummai yace ta tafi ta canxa mata kaya bayan ta gama gyara gun da ta bata, mama tayi shiru sae kuma tace "Naga idonta biyu fa" El-Ameen yayi dariya ya xauna yace "ae bata komae mama, shi yasa nace ki tafi ki canxa mata, kar ki samu damuwa bbu abinda xata maki, tana da nutsuwa sosai" mama jummai bata musa ba ta nufi sama cikin rashin kuxari. Tana nan xaune inda El-Ameen ya bar ta a dakin ta sameta, kin rufe kofar Mama jummai tayi in case, ta karasa kusa da ita tana d'ari d'ari ta dauki blue gown din da ya fiddo mata, a hankali mama jummai tace "Baiwar Allah kaya xan canxa maki kin ji" ko kallonta bata yi ba, hakan ya kuma tsorata mama jummai, juyawa tayi a sanyaye ta koma Palo tana kallon El-Ameen tace "D'an nan wallahi tsoro nake ji ni kam, kaga sae tana bacci nake shiryata" dariya yayi ya mike ya nufi stairs din suka koma sama a tare, junaid ya bi su da kallo. Xaune suka tar da ta har lkcn sae dai wannan karan windon dakin ta tsura ma ido, El-Ameen ya karasa kusa da ita, ta juya da sauri tana kallonsa, kayan ya dauka ya mika ma mama jummai yace "Gashi mama" karasawa tayi ta karba, ya dago ta yana kallonta ya hade rai yace "Mama xata canxa maki kaya yanxu, stay still kin ji" ita dae kallonsa kawae take, ya juya ya kalli Mama jummai yace "Toh karaso Mama" a hankali ta karaso kusa da su, hannunta na rawa ta kai kan maballin rigar xata cire mata, ta fasa wani ihu tayi bayan El-Ameen da sauri, cikin sakwannin da basu wuce uku ba sae ga mama jummai can bakin kofa a mugun tsorace bayan ta sake kayan hannunta nan gabansu, dariya sosai El-Ameen yake yana kallonta yace "Mama baxa fa ta maki komae ba wllh" tace "A'a d'an nan nafi gane tana bacci wllh" a tsorace take maganan daga haka ta juya ta koma kasa, murmushi yayi ya juya yana kallon ta bayansa, dawo da ita yayi gabansa, ya kusa minti biyu tsaye kamar me naxari sai kuma ya leka rigar jikinta don ganin ko akwai kaya a ciki yaga akwai vest, rufe idanuwansa yyi a hankali ya balle dogon rigan jikinta snn ya fara cirewa idonsa kulle, ajiyewa yayi bayan ya cire har lkcn idonsa na rufe ya duka a hankali ya shiga laluban kayan da Mama jummai ta yar a kasa, yana tabawa ya dauka sannan ya mike, lalubawa yayi yaji bata wajen kuma, ae ba shiri ya bude ido da sauri yana waige waigen inda xae ganta, tsaye ya ga perfect fair figure dinta can jikin window, daga ita sai white vest da ya kusa cinyarta, vest din ya kamata sosai kasancewarsa very elastic, gaba daya shape dinta ya fito ga long fresh legs dinta da bbu tabo ko daya, kamar xaka latsa ta jini ya fito tsabar haske, juyawa yayi da sauri kamar wanda ya ga abun tsoro ya nufi kofa da hanxari, ko me ya tuna kuma sae yyi still bakin kofar ya kusa 3 mins kafin ya juyo a hankali ya dawo dakin ya nufeta ba tare da ya kuma kallon jikinta ba, hannunta ya kama yana kallon fuskarta ya shiga sa mata rigar hannunsa, yana gamawa ya xaunar da ita gefen gado ya hade rai ya dunguri kanta yace "Don't try dat again" cup ya dauka ya dauraye yayi mata diluting drugs dinta da ruwa sannan ya dawo kusa da ita ya rike kanta ya kai cup din bakinta, kauda kai tayi da sauri, yayi mata tsawa ita ma ta fasa masa ihu, rike kanta yyi ya tura cup din bakinta har sai da ta bude ya xuba mata, sae da ya tabbatar ta hadiye sannan ya kyaleta tana yatsinan baki tana komawa baya, jinin da ya gani bakinta yasa ya tsura ma lips din ido, handkerchief ya ciro aljihunsa ya goge mata bakin yace "Sorry!" Mayar da handki din yayi ya kwantar da ita ya mike ya fita daga dakin ya ja kofar. Palo ya sauko ya ga ba Junaid, ya kalli mama dake xaune yace "Mama Junaid fa?" Tace "Ya tafi wai" shiru yayi bae ce komae ba, can yace "Ohk xan tafi yanxu, da daddare xan dawo, bacci xata yi yanxu" tace "Toh Allah ya kai mu, Allah kuma ya bata lafiya" yayi murmushi yace "Ameen" sannan ya fita.


鉁嶐煆�


*Haske Writers Association*馃挕




鈿� *Captain Ahmad Junaid*鈿�


_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�


13....


Junaid bai daga kiran ba ya juya yana kallon Khadija, Mikewa xaune tayi ta hade rai kamar xata yi kuka tace "Ni fa wllh ba chatting nake ba ya A.jay, ita Hajja bata san komai ba sai dai tayi ta magana" Junaid xai yi magana Humainah ta shigo palon fuskar nan nata a daure ta xauna gefen Hajja, Hajja tace "ke kuma fa? Ina aiken" Humainah tace "ko ba yi tayi kamar bata gan ni ba, kuma bata ce min komae ba sai aikinta take tana wake wake ta bar ni a tsaye" Junaid yace "Wa?" Ta kallesa tace "Anty sadiya mana" Hajja ta mike rai bace tace "Kambu!! Yaran nan sun raina ni wllh, don uwarta ni din sa'arta ce da xan aika tayi min abu ta share ki tana wake wake?" Kofa ta nufa kamar xata tashi sama, Junaid ya mike ya bi bayanta yace "Tsaya Hajja, me kika sata?" Tana huci ta juyo tace "Ca nayi ta min dafadukan taliya shi ke raina yanxu don Amina shinkafa tayi kamar ko da yaushe, ita bata da girki sai na shinkafa kullum" Junaid ya hade rai yace "Ita mum din tawa, Toh su wa ennan na palon naki me suke yi da baxa su maki ba" Hajja tayi tsaki tace "Xancen banxa, toh ban yi niyyan sa su ba, ko da yanda xaka yi da ni ne" tana kai wa nan ta nufi part din Hajiya da sauri, ya d'an tabe baki ya juya yana kallon Humainah yace "Sannu da hadi, ke baki iya taliyar ba sae kin je dauko magana koh?" Ta turo baki tace "Ae dai ba ni nace tayi ba, aikena aka yi" yace "Xaki yi bayani idan na kama ki ne" dauke kai tayi ya juya yayi wucewar sa, Khadija tayi dariya tace "Bari in je inyi kallo" Ana kiraye kirayen Magrib Junaid ya fito part dinsa sanye da jallabiya milk colour, dai dai nan Humainah da fatima suka fito daga part din Mumy, Humainah tace "Masallaci xaka ya Ahmad" Ya harareta yace "A'a office xan je" bae jira cewar ta ba ya kara gaba. Yana fito wa daga mosque bayan an idar da sllh ya tsaya da wani frnd dinsa da ke nan layin suna gaisawa, har sai da ya ga shigar Abba gida, snn yace "Abdul d'an ara min motar ka pls xan dan fita in dawo yanxu" Abdul yace "Toh mu shiga in baka key" junaid ya bisa suka shiga compound dinsu ya tsaya daga balcony har ya kawo masa makullin sannan ya nufi parking lot ya dau motar ya fita. Atm machine ya fara tsayawa ya cire kudi ya siya fruits nan wajajen sannan ya koma mota ya dau hanyar gidan El-Ameen. A waje yayi parking bayan sun gaisa da mai gadin ya shiga gidan, Mama jummai na kwance Palo kasan tiles ta shimfida xani da 'yar radionta a hannu tana saurare, ta mike xaune ganinsa tace "Sannu da xuwa Ahmad" xaunawa yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login