Showing 96001 words to 99000 words out of 180982 words

Chapter 33 - CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE Book .txt

ki ba" dawowa tayi ta cire Hijab din ta ajiye, ya bi ta da kallo har ta shiga toilet din sai dai bata rufe kofar ba, mikewa yyi ya fita ya koma dakin sa. Lokaci lokaci ya kan lekota, tausayinta kawai yake ba kadan ba barin yanda ya lura duk a tsorace take, ana kiran sllh magrib ya shigo dakin bai ganta ba, kiranta ya shiga yi amma shiru ya juya ya fita ya sauko downstairs, kitchen ya sameta tana wanke d'an plates din da aka bata, ya tsaya bakin kofa yana kallonta, da sauri ta juyo a tsorace, wara ido yayi yace "Uhum!" A hankali tace "washing nake yi" murmushi yayi mata yana gyada mata kai, ta juya ta ci gaba da wanke plates din, yace "Me xa ki ci for Supper?" Ta juyo tace "Supper?" Ya gyada mata kai yace "Yea dinner" ta d'an langwabar da kai a hankali tace "na koshi" wara ido yayi yace "me kika ci?" juyawa tayi ta ci gaba da wanke wankenta. Har ta gama yana tsaye bakin kofar, ta juyo tana kallonsa, murmushi yayi mata ya fita daga kitchen din ta bi bayansa suka haura sama, yace "Tafi kiyi sllh" kai ta gyada masa ta shiga dakin da take, shi ma ya shiga nasa. Ana idar da sllh ya tafi siyo masu abinci, ajiye abincin yayi a parlor bayan ya dawo ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujera, can ya mike ya shiga kitchen ya dauko plate ya dau take away daya ya juye ya sa spoon ya dau ruwa ya tafi sama, xaune ya sameta bakin kofar dakin tana ganinsa ta mike tsaye, yace "uhum!" a hankali tace "Tsoro nake ji" kallonta ya tsaya yi kafin ya shigo dakin ya ajiye mata abincin hannunsa yace "Toh xo ki ci abinci" ta karaso ta xauna inda ya ajiye mata abincin, bin sa da kallo tayi har ya fita sai dai bai rufe mata kofar ba. Har xai shiga dakinsa ya tsaya ya kalli dakin Humainah, karasawa yayi ya bude kofar, xaune ya ganta can karshen gado kanta hade da gwiwa, a hankali ya karasa kusa da ita ya xauna yace "Still crying?" Mikewa tayi xata bar wajen ya fixgota ya ce "Ina xa ki?" Ta fashe da kuka sosai, rungumeta yayi a hankali yace "Alryt am sorry, kiyi hakuri... She's going tomorrow tun da baki so" boye fuskarta tayi jikinsa tana kuka a hankali, yace "Toh ba nace kiyi hakuri gobe xata tafi ba" muryarta na rawa tace "Toh wacece ita" dago kanta yayi yana kallonta, can yace "Ohk I will tell who she is" janyeta yayi a jikinsa ya koma baya yana kallonta yace "Amma fa it's a long story" sunkuyar da kanta tayi, nan ya fara bata labarin ynda ya hadu da jasmine har xuwa wannan lokacin, kallonsa kawai take ko kiftawa bbu bata kuma ce komai ba, ya lumshe ido ya bude yace "Tana regaining memorynta Idan Allah ya yarda xa ta koma gun iyayenta, ita din abun tausayi ce, a yanxu bata da kowa sai mu da muka taimaketa" dauke kai Humainah tayi, ya matso kusa da ita yace "Baki ce komai ba" turo baki tayi tace "Toh ka kai ta gidansu El-ameen mana" murmushi yayi yace "In tambaye ki" ta dago kai tana kallonsa, yace "wai kishi na kike Humainah?" Hade rai tayi tace "Kamar ya? Sbda me xan yi kishin ka" yace "Toh me sa baki son ta xauna nan?" Tabe baki tayi tace "Ta xauna mana ni ina ruwana, kawae abinda na sani ka kai ni sch next week" murmushi yayi ya mike ya fita daga dakin, abinci ya dauko mata ya ajiye dakin yace "Ga abinci!" Ko kallonsa bata yi ba ya fita daga dakin. Karfe tara da wani abu ya mike daga kwancen da yake ya fita xuwa gun Jasmine, xaune ya sameta bakin kofa tayi jigum, ya d'an bude ido yace "kina nan har yanxu" mikewa tsaye tayi kamar xata yi kuka tace "Ni kadai xan yi bacci a nan?" Kallonta kawai yake ya ga hawaye idonta, girgixa mata kai yayi yace "A'a ba ke kadai xaki kwana ba, ina xuwa" daga haka ya fita ya shiga dakin Humainah, xaune ya sameta daure da towel gaban madubi, hade rai tayi tace "Kaya xan sa" yace "Uhm did I hold you?" Marairaice masa tayi tace "Ka fita plss" karasowa yayi kusa da ita ta mike da sauri, ya d'an bude ido yace "what?" Kamar xata yi kuka tace "Ka fita plss" yace "Alryt xan fita, amma abokiyar kwana xan kawo maki" kallonsa tayi da sauri tace "Kamar ya?" Yace "ku kwana tare da yarinyar plss" da mamaki take kallonsa tace "Mu kwana?" Matsowa yayi kusa da ita ta koma baya da sauri tace "Wayyo ya A jay ka fita plss" ya langwabar da kai yace "Toh in kawo maki ita?" Gyada masa kai tayi da sauri, yayi murmushi ya juya ya fita ta bi sa da kallo, tsaye ya samu Jasmine a daki tana ganinsa ta nufesa da sauri ta juya masa baya tace "Cire min abun" kallon Zip din kawai yake daga sama xuwa kasa na kusan minti daya, ta juyo a hankali tana kallonsa, kifta ido yayi da sauri yace "Na'am" a hankali tace "Ban iya cirewa ba, Mami da farida suke cire min" gyada mata kai ya shiga yi kamar kadangare, ta kuma juya masa baya, yayi baya da sauri yace "Ohk Ohk mu je a cire maki nima ban iya ba" daga haka ya nufi kofa ta bi bayansa, dakin Humainah ya shiga ita ma ta shiga, kallonta kawai Humainah ke yi daga sama xuwa kasa gabanta na faduwa, karasawa Jasmine tayi kusa da ita ta juya mata baya a hankali tace "ki cire mun abun" kallon Junaid Humainah tayi, ya gyada mata kai yace "Help her wai bata iya ba" da kyar Humainah ta daga hannu ta xuge mata Zip din, kokarin cire rigar ta shiga yi da sauri Junaid ya juya har yana buge kofa ya fita daga dakin, Jasmine ta kuma kallonta tace "Baki cire dayan ba" Humainah ta balle mata bra din ta koma gaban madubi, bin ta da kallo Jasmine tayi tace "Ina san inyi wanka" ko kallonta Humainah bata yi ba, Jasmine ta bi ta tace "Xan yi wanka" ba tare da Humainah ta kalleta ba ta nuna mata kofar bathroom, Jasmine ta nufi kofar ta bude ta shiga, a bude ta bar kofar, Humainah ta mike ta koma gefen gado ta xauna xuciyarta na bugawa, har Jasmine ta fito daure da towel dinta, ta gefen ido kawai Humainah ke kallonta, ta iso kusa da ita tace "cloth dina" Humainah ta hade rai tace "ki saka wanda kika cire mana" "toh" kawai jasmine tace ta tafi inda kayan da ta cire yake ta dauka ta sa ta kuma dawowa ta durkusa kusa da ita tace "Sa min" xuge mata Zip din Humainah tayi ta kwanta abunta, jasmine ta mike ganin ta kwanta ita ma ta kwanta nan kasa. Junaid na fitowa daga wanka ya dau wayarsa dake ring ya ga El-ameen ne ke kiransa, dagawa yayi El-ameen yace "Matar taka ta hakura dai koh?" Junaid yace "May be" El-ameen yace "Kasan me, bata yarda fa ta kwana ita kadai ya xa ayi gashi amarci ku ke ci...." Junaid yace "Ko kuma angwanci ba" El-ameen yace "Serious xata yi ta maku ihu ne cikin dare bata yarda ta kwanta ita kadai" junaid yace "ta gaya min, tana dakin Humainah yanxu ma" El-ameen yace "Ohk bata waya plss" Junaid yace "Kace mata me?" El-ameen yace "kai dai ka bata" shiru junaid yayi can yace "Naji" katse wayar yayi hade da yin tsaki ya saka jallabiyarsa ya fita daga dakin, da sallama ya tura kofar dakin Humainah ya d'an bude ido ganin jasmine kwance a kasa ya karasa ya durkusa kusa da ita yace "Me ya sa kika kwanta a nan" shiru tayi bata ce komai ba, ya kalli Humainah ya ga rufe idonta ma tayi, jasmine ya kuma kallo yace "Tashi ki hau gado" mikewa tayi ya nuna mata daya side din gadon ta xaga ta hau ta kwanta, a hankali ta matso kusa da Humainah shi dai kallonta kawai yake, wayar hannunsa ne ya fara ring ya kalli screen din, sai da ya kusa katsewa ya daga ya mika mata, karba tayi tana kallonsa yace "Kiyi magana" wayar ta kai kunnenta tace "Na'am" El-ameen yace "Baki yi bacci ba baby?" Ta kalli Junaid da ke kallonta ta sunkuyar da kai a hankali tace "Xan yi" juyawa junaid yayi ya fice daga dakin, "Kin ci abinci kuwa" tambayar da El-ameen yayi mata kenan ta gyada masa kai tace "Eh da afternoon ya bani wannan small rice da miya, na ci kadan Saboda ba dadi sai ya xo ya bani a baki" shiru El-ameen yayi bai ce komai ba, Humainah ta bude ido da sauri tana sauraren abinda take cewa gabanta na faduwa, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "Da ya baki a bakin sai kika ci?" Kai ta gyada masa tace "Eh da ya bani na ci, uncle he's kind, I like him just like Abba" mijin Dr Sumayya kenan, katse wayar El-ameen yayi, Humainah ta mike xaune xuciyarta na tafarfasa can ta mike ta fice daga dakin, da sauri Jasmine ta mike ta bi bayanta ita ma, dakin Junaid Humainah ta shiga ta gansa tsaye yana saka pyjamas dinsa, juyawa yayi yana kallonta ta xube wajen ta fashe da kuka sosai, karasowa yayi kusa da ita ya durkusa gabanta da mamaki yace "Me ya faru?" Jasmine ce ta shigo dakin ta karasa kusa da su a hankali ta durkusa ita ma tana kallon yanda Humainah ke kuka.


鉁嶐煆�
*Haske Writers association*馃挕


Kar ku watsa min sand a ido my group members, ku kadai nake ma post da hannuna don soyayya.
[16/12, 00:57] Hussaini Atk: 鈿� *Captain Ahmad Junaid*鈿�


_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�


47.....




Dago kanta junaid yayi yana kallonta ganin ta ki yin shiru yace "Ohh Pls ki gaya min me ya faru mana, What happened?" Nan ma dai bata ce komai ba sai kuka, juyawa yayi ya kalli Jasmine dake durkushe kusa da su ita ma ya ga hawaye idonta, mikewa yayi ya fita xuwa dakin Humainah, a hankali Jasmine ta dawo kusa da ita cikin sanyin murya tace "Sorry Anty" kallo daya Humainah tayi mata ta mike tana goge hawayen da ya ki tsaya mata ta koma kan gado, junaid ya dawo dakin yana kallon Humainah yace "Wai don Allah kukan kike haka har yanzu?, are you even okay?" Ta hade rai ba tare da ta kallesa ba tace "Ni a nan xan kwana" daga haka tayi kwanciyarta ta juya baya, kallonta kawai Junaid ke yi, can ya juya ya kalli Jasmine da ke kallonta ita ma, karasawa yayi gun gadon a hankali ya xauna kusa da ita ya kai fuskarsa kusa da nata murya can kasa yace "Haba Humainah, toh ita fa" bata tanka sa ba sai rufe idonta da tayi, ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Humainah!" bude ido tayi ta wani hade rai tana kallonsa, ya marairaice mata yace "Ita ina xata kwana mana" ta fixge hannunta tace "Oho!" Daga haka ta kuma juya masa baya, ya kusa minti biyar yana kallonta kafin ya mike tsaye yana kallon Jasmine dake ta kallonsu, duk tausayinta ya cika sa, a hankali ya isa kusa da ita yace "Tashi mu je" mikewa tayi ita ma tana kallonsa ya fara tafiya ta bi bayansa, juyawa Humainah tayi da sauri tana kallonsu har suka fita ya rufe kofar ta mike xaune ta fara wani sabon kukan kai ka ce an mata mutuwa ne, dakin da Jasmine din take ya shiga tana biye da shi, ya xauna gefen gado, jasmine ta iso kusa da shi ta xauna kasa a hankali tana kallonsa tace "bata son in yi bacci da ita koh?" Girgixa mata kai yayi da sauri yace "No! she's sick ne" gadon ya nuna mata yace "Taso ki kwanta kiyi baccin ki" tace "Kai ma xa kayi bacci a nan?" shiru yayi bai ce komai ba ganin yanda take kallonsa ya gyada mata kai yace "Eh! Zo ki kwanta" mikewa tayi ta hau gadon ta kwanta, yana kallonta yace "kin iya addu'a ai koh?" Shiru tayi tana kallonsa can kuma a hankali tace "Bismeeka Allahumma Amootu Wa Ahya" murmushi yayi mata yana gyada kai yace "Jayyid! To yi baccin ki hakan ma yyi" tace "Kai baxa kayi baccin ba" yace "Xan yi mana, amma sai na gama kallo" yana magana ne yana powering tv, lumshe ido tayi ya d'an saci kallonta kafin ya maida dubansa kan tv, ya kusa awa daya xaune dakin yana yi yana kallonta har ya lura baccin ta yayi nisa, ya lumshe ido ya mike ya rufa mata duvet ya isa kofa ya bude a hankali ya fita ya bar kofar bude, dakin sa ya shiga ya rufe, kwance ya same Humainah idonta rufe, ya kashe wutan dakin ya karasa gadon ya kwanta. Kusa da ita ya dawo ya kamo hannunta murya can kasa yace "Humainah?" Shiru bata amsa ba, ya kai bakinsa dai dai fuskarta ya kuma kiranta a hankali, mirginawa tayi ta koma can karshen gadon ta juya masa baya, ya d'an tabe baki yayi kwanciyarsa ya lumshe ido. Kafin asuba ya je duba Jasmine ya fi sau biyar, yana dawowa daga masallaci bayan an idar da sllh ya shiga dakin ya tada ta, mikewa xaune tayi tana mitsika ido yace "tashi kiyi sllh" gyada masa kai tayi ta mike xata shiga toilet sai kuma ta juyo tace "Wanne?" Murmushi yayi yace "Asuba" juyawa tayi ta shiga toilet din, ya fita daga dakin, xaune ya tarda Humainah kan darduma, ya karaso ya xauna kusa da ita yana kallon yanda ta hade rai, yayi murmushi yace "Ba gaisuwa" dauke kai tayi tace "Ina kwana" ya juyo da fuskarta yana kallon idanuwanta da suka kumbura don kuka, ya langwabar da kai yace "Su Abba sun hada ni da aiki...." Mikewa ta shiga kokarin yi ya mayar da ita ta xauna ya kamo hannunta yace "Not until you tel me what ur problem is, jasmine or what?" bude kofar dakin aka yi duk suka juya da sauri, jasmine ta shigo dakin ta karaso inda suke ta duka kusa da junaid tana kallonsa tace "Nayi sallah, i want to brush my teeth" ya kusa second ashirin yana kallonta, Humainah ta janye hannunta daga nasa ta mike ta koma kan gado, gyada mata kai yayi da sauri yace "Alryt! Ohk" ya mike ya shiga bathroom, toothpaste da toothbrush sabbi ya fito da ya mika mata ta mike ta karba ta nufi kofa ya bita da kallo, har xata fita ta juyo tace "Xan yi wanka ma" ya d'an bude ido sai kuma yace "Ohk Ohk" ya koma bathroom ya fito mata da sabulu shower gel da sponge ya karasa ya mika mata ta karba tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Towel!" Juyawa yayi ya dauko mata towel dinsa ya dawo ya mika mata ta karba sannan ta juya ta fita, ajiyar xuciya ya sauke ya juya yana kallon Humainah da tayi kwanciyarta, karasawa gun gadon yayi yyi kwanciyarsa shi ma, tana ganin haka ta mike ta nufi kofa ya bi ta da ido har ta fice daga dakin. Karfe takwas da wani abu su fatima suka kawo breakfast, kamar jiya daga bakin kofar ya tsaida su ya karbi abincin hannunsu, khadija ta marairaice masa tace "Ya A jay xamu gaisa da Humainah mana" yace "Bacci take" Khadija ta turo baki ta juya haka ma fatima ya kulle kofar. Dawowa cikin parlon yayi yana kallon jasmine dake xaune kasan lallausan carpet din tsakar parlon, kusa da ita ya ajiye basket din abincin ya tafi kitchen ya dauko cup da spoon da plates sae kayan tea ya dawo parlon, tea ya fara hada mata, ita dai sai kallonsa take da sun hada ido xata sunkuyar da kai, har ya gama ya ajiye mata tean gabanta ya dibar mata potatoe da kwai da plantain ya ajiye mata yace "Gashi ki ci" girgixa masa kai tayi tace "Ni bana son milk" ya d'an bude ido yace "Uhhn!" Ta gyada masa kai, mikewa yayi ya tafi kitchen ya dauko wani cup din ya dawo ya hada mata Milo kadai ya ajiye mata, ta kalli potatoen gabanta a hankali tace "Ketchup" wara ido yayi yace "Uhun!" Ta kallesa ya mata murmushi yace "Tohm bari in je in siyo maki" daga haka ya rufe dankalin da tea ya mike ya tafi sama ya dauko makullin mota ya sauko parlon yace "ko xa ki bi ni?" Shiru tayi sai kuma tace "Ehh!" Komawa sama yayi ya dauko mata Hijab ta karba suka fita daga parlon, tara da wani abu suka dawo gidan da ketchup din, ya sake hada mata wani tean ya bata, kallon yanda take shan ketchup din yake yyi murmushi yace "You like it" ba tare da ta kallesa ba tace "Yes!" wani shayin ya hada ya dau dankali da kwai ya tafi sama, ya shiga dakin Humainah, xaune ya sameta kasan dakin ya karaso ya ajiye mata abincin hannunsa ya xauna yace "Ga breakfast" bata ko juyo ba bare ta kallesa, ya mike ya fita. Karfe sha daya da wani abu junaid na daki yana danna laptop aka danna bell downstairs, mikewa yayi ya fito ya duba dakin Jasmine don ganin ko ta tashi daga baccin da take yaga bata tashi ba, downstairs ya sauka ya bude kofa, gabansa ne ya fadi ganin Hajiya da Umma sai Aysha kanwarsa da su Muhibba da Suhaima, Hajiya na murmushi tace "Wannan kallo haka Ahmad ko mu koma ne" juyawa yayi ya bar bakin kofar ya dawo parlor duk suka shigo, Ya xauna ya gaida su bbu fara'a, duk suka amsa da yaken da bai kai ciki ba, Aysha ta gaida shi ya amsa ba tare da ya kalleta ba, haka ma su Suhaima Umma tace "Toh ina amaryar ko bata tashi ba" mikewa yayi ya haura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login