Showing 9001 words to 12000 words out of 180982 words

Chapter 4 - CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE Book .txt

na bude kofar ya koma baya da saurinsa ya fiffito da ido, Junaid na ganin hka kan kace me sae gashi a tsakiyar compound cikin 'yan sakwanni, El-Ameen ya rike kai yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya nanata hakan ya kusa sau goma, Junaid na daga tsakiyar compound sae tambayar me ya faru yake, cikin tsawa yace "Junaiddd xo ka ga abinda ka jawo min"
*Haske Writers Association*
[16/10, 19:05] Hassan Atk: *Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
4.....
Washegari Karfe hudu da wani abu Junaid ya baro office, tun safe dama ya kira agents din Abbansa yace su sama masa apartment ko me dakuna biyu ne but kar su yrda Abba ya sani, driving yake yana kokarin kiran daya daga agents din yaji ko an gama komae, mutumin na d'agawa ya gaishesa snn yace "Yallabai an samu, amma xaka iya xuwa ka ga ko ya maka" Junaid yace "Alryt! Ohk, na gode" katse wayar yyi ya nufi asibiti gun El-Ameen sanin yana clinic, xaune ya samesa yana attending to wata patient, Junaid ya nufi bedroom dinsa da ke office din ya kwanta, bayan minti talatin El-Ameen ya shigo ya cire farin lab coat din jikinsa yace "Uhnn! Ko uniform baka cire ba tsabar xumudin taimakon mahaukaciya kenan" Junaid ya mike xaune ya hade rai yace "Yea daga office nake, na kuma samu apartment" El-Ameen yyi murmushi yace "Ohh dats gud for yhu" Junaid yace "But yau da nyt xa mu dauko ta ko" wani kallo El-Ameen yyi masa yace "Xa dae ka dauko ta malam, kai da wa xa ku dauko ta" shiru Junaid yyi yana kallonsa, ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh naji xan dauko ta" mikewa yyi yace "i will be on my way, but ina son ka min favour daya, plss motar ka xaka bar min a layin ku sae ka bar min key din karkashin motar ko in btwn flowers dake kusa da motar, I will then cum over to take it sbda Mumy baxata bar ni in fito so late ba" El-Ameen ya bude ido yace "What? A motar tawa xa a saka mahaukaciya, kuma tsabar walakanci sae in bar motar at risk da makulli a waje, you are dreaming" Junaid ya girgixa kai yace "Ka dae san ba sonka Allah ya fi yi a kanta ba da ya barka da hankalinka ita ya gusar mata da nata koh?" El-Ameen yace "Toh preacher, amma ni baxan bada motata ba period!" Junaid bae ce komae ba ya fice daga dakin, tunanin wa enda xa su taimaka masa ya dauko mahaukaciyar ya dinga yi, sae da ya biya ya duba apartment din da aka samar masa ya ga ba laifi snn ya nufi gida. Da daddare yana xaune palon Mumy yana cin tuwon shinkafa da lafiyayyen miyar vegetable da tayi masa, sae dae duk bae da appetite turawa kawae yake, ya kalli Fatima dake kwance parlon yace "Xo dauke abincin nan" ta mike tace "Baxa ka ci bane yaya?" Bai ce komai ba hakan yasa ta kwashe tray din tayi kitchen da shi, takwas da rabi ya mike ya shiga bedroom din Mumy don mata sae da safe, tace "Yau ba hiran kenan" yayi yake yace "Bacci nake ji momma" tace "To Allah ya tashe mu lfya, make sure yhu ablute nd pray b4 going to bed, kuma ka rufe windows ka ga hadari" yace "In'sha Allah mum" fita yyi daga bangaren nata rike da wayarsa. Bedroom dinsa ya shiga ya canxa kaya cikin hanxari snn ya fito, gate ya nufa yana yi yana waige waige har ya fice, da kafa ya karasa titi iska na kadawa sosai ga walkiya alamar ko da yaushe ruwa xae iya sakkowa, yana tsaye yana jiran abun hawa abinda bae taba yi ba duk tsawon rayuwarsa a iya saninsa, bae ma san ta ynda xae tsaida adai daitan ba sae kalle kalle yake gashi kuma sae wucewa suke, yayyafi aka fara yi sosae, ya lumshe ido ya bude yana kallon motocin dake wucewa, wata farar lafiyayyen mota ce tayi parking gefensa, wata kyakkyawan yarinya ta fito sanye da hijab tana kallonsa tace "Bawan Allah shigo in rage maka anya if its ok by yhu, ka ga its raining kuma ruwan xae iya karfi at anytime, na wuce daxu xanje pharmacy na ganka kuma na dawo na kuma ganin ka" kallon motar yyi snn ya kalleta, yarinyar baxata wuce 18 ba, ta d'an bude ido tace "Noo! Am just being helpful" daga hka ta juya xata koma motar ta, sanin bashi da wani alternative yasa ya bude gaban motar ya shiga, dai dai lkcn da ita ma ta shiga maxaunin driver, ta kallesa ta ja motar suka bar wajen, tana tuki tace "Ina ka nufa?" Ba tare da ya kalleta ba ya gaya mata, tace "Ohk" wayarsa ce ta fara ring ya ciro a aljihunsa ya ga El-Ameen ne, da kmr baxae daga ba sae kuma ya d'aga ya kara a kunne yyi shiru, El-Ameen yace "Ya ka samu fitowan?" Cikin kaushin murya yace "Ba Matsalar ka bne wnn" El-Ameen yyi dariya yace "Haba name same, naga baka xo daukan motar bane har ynxu" Junaid yace "Ehh xan je in karba na Faisal" El-Ameen yace "Kai na fa fito maka da motar Wllh come over, yhu knw I can be annoying a times" Junaid yace "Noo dnt wrry ina hanyar gidan ynxu" El-Ameen yace "Look stop this plss junaid, na fito maka da mota Wllh, just teasing yhu daxu" Junaid yyi shiru sanin baxae iya fushi da abokin nasa ba, lumshe ido yyi ya bude yace "Ohk" snn ya katse wayar. Juyawa yyi ya kalli yarinyar ya gaya mata anguwarsu El-Ameen yace nn xani, tace "Ohk" dai dai bakin gate yasa ta tsaya ya juya yana kallonta yace "Thanks a lot" tace "Yhu are welcm!" bude motar yyi xae fita duk da ruwan da ake tsugawa, sae kuma ya juya ya kalleta, wayarsa ya ciro ya mika mata yace "Sa min digit din ki so I can thank yhu some other time" tace "Do yhu need to? Its ohk ba sae ka kuma gode min ba, it payz to be kind" murmushi yayi ya mayar da wayar aljihunsa yace "Ohk Allah saka da khairan" juyawa tayi bayan motar ta dauko raincoat ta mika masa tace "Hope yhu will cope with this" karba yyi ya kuma mata godiya ya fita daga motar, ta ja motar ta bar wajen. Bin motar yyi da kallo dai dai lkcn da aka dallara masa wutan fitilar mota, juyawa yyi yaga motar El-Ameen ce, karasawa yyi da sauri yana rike da raincoat ya bude front seat ya shiga, El-Ameen yace "Wani mota ce wannan?" Junaid yace "A good Samaritan" El-Ameen ya tabe baki yace "Ynxu ka mana adalci kenan Junaid, ko wani mahaluki na cikin bargo cikin ruwan nn kasa muna tsaye a titi?" Junaid yace "Look! Ni ae bn ce ka fito ba xaka iya komawa abun ka" El-Ameen ya hararesa yace "Ehh In koma ka ji haushi na koh" Junaid yace "No Baxan ji ba" tsaki El-Ameen yyi ya tada motar suka bar layin, sae da suka hau kan titi snn yace "Ynxu ina xa mu bi?" Junaid ya gaya masa suka kama hanyar inda mahaukaciyar take, banda tsaki bbu abinda El-Ameen yake, shi dae Junaid bae ce komae ba har suka iso, Junaid ya fara kalle kallen inda xae hangota, bae ganta wajen ba hankalinsa ne ya tashi, shi dae El-Ameen kallonsa kawae yake, ya juya ya kalli El-Ameen yace "Frnd bn ganta wajen ba kuma" El-Ameen yace "Toh me xan yi ni kuma, haka kawae ka shiga hakki na ka hanani kwanciya cikin sanyin nn" bude motar Junaid yyi ya fita cikin ruwan, ya fara nemanta, lkci daya ya jike jagab, can ya hangota rabe jikin bango kusa da wani kiosk duk ta jike jagab ta takure waje daya, wani tausayinta ne ya rufe sa jikinsa yyi sanyi sosai, ya kusa minti biyar tsaye cikin ruwan yana kallonta snn ya juya ya koma gun motar ya bude yana kallon El-Ameen cikin sanyin murya yace "I've seen her" El-Ameen yace "Gud for you, sai ka bude baya ka dauki igiya ka daureta ka dauko ta ai" shiru Junaid yyi yana tsaye cikin ruwan yana kallonsa, can yace "Ka xo ka taimaka min toh" El-Ameen yace "What! cikin ruwan nn xan taimaka maka, Noo" Junaid bai kuma cewa komai ba ya bude bayan motar ya dauki igiyan da ke nan ya rufe ya koma inda mahaukaciyar take, k'asa karasawa yyi don gabansa sae faduwa yake, da kyar yyi shahada ya isa gabanta, kallonsa take tana kara takurewa waje daya, sae a snn ya lura da rawan sanyin da take, a hnkli yace "Kiyi hkuri baiwar Allah, am only trying to help" kamar ta ji me yace ta yunkura ta mike xata bar wajen da gudu, fixgota yyi ya rike ta gam, ta shiga kokuwa da shi tana ihu, El-Ameen na daga mota yana lekansu, ban da dariya bbu abinda yake har da kyakyatawa, ba karamin wahala ta ba Junaid ba don da kyar ya kai ta k'asa ya daure hannunta shima din ba wae dauri sosae ba don taki tsayawa ga wani karfi dake gareta, bude mota El-Ameen yyi ya fito cikin ruwan ya karasa inda suke da sauri, karban sauran igiyar yyi junaid na rike da ita ya daure ta gam, ihu ta dinga masu tana shure shure, El-Ameen ya mike yace "Ae sae ka dauketa Mr Do good" bbu musu Junaid ya dauketa, ko kadan bata da nauyi ya nufi motar da ita El-Ameen na biye da shi a baya yana 'yar dariya, ya bude baya ya saka ta ciki ya rufe, yatsine yatsine El-Ameen ya shiga yi ya nufi driver seat, muryoyi suka ji daga bayansu duk suka juya, wasu matasa suka gani tsaye da gora da adda a hannayensu, da ka gansu ka ga masu gadi, cikin tsawa suka ce "Maxa ku fito da ita ynxun nn" kallon Junaid El-Ameen yyi, El-ameen ma haka, ae kan kace me sae ga Junaid cikin mota ya rufe, El-Ameen na ganin hka shi ma ya shige motar ya tada da sauri, samarin suka taho da gudu, cikin hanxari El-Ameen ya ja motar suka bar wajen, bin motar samarin suka yi da guda suna buga ma motar gora da karfi, El-Ameen ya dinga cewa "ya Salam! ya salam! ya salam!" har suka bar anguwar abinda yake maimaitawa kenan, juyawa yyi yana kallon Junaid dake ta kallon mahaukaciyar dake fixge fixge tana son freeing kanta, a fusace ? yace "Kai ka ji irin ynda suka tarwatsa min bayan mota kuwa Junaid" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Xan gyara maka motar ka idan Allah ya yarda" kwafa El-Ameen yyi yace "Better, kuma ka dinga lura da ita kar ta cafko ni mu shiga uku, ynxu ina muka nufa?" Junaid ya gaya masa ya kama hanyar anguwar, cikin minti goma suka iso, har lkcn ruwa ake, parking El-Ameen yyi yana kallon Junaid ya bude motar ya fito, fitowa yyi shi ma suka shiga gidan a tare, gidan babba ne ba laifi, junaid har yasa anyi furnishing gidan kar ya tsaya empty, El-Ameen yyi tsaki yace "Lallai! A wannan gidan xa a ajiye mahaukaciya? ba sae ta balla windunan nn mara karfi ba ta yi ficewarta, bugu daya idan tayi ma kofar nn ficewa xae yi wllh" Junaid ya shafa kansa a hankali yace "Toh shi suka samo min ya xa ayi" El-Ameen yace "Oho, amma idan ta gudu wallahil Azim ba da ni xaka je nemota ba" da damuwa Junaid yace "Toh hw are we going to do it ynxu ga shi mun dauko ta" El-Ameen yace "Oho it's left to yhu" xama Junaid yyi ya rike kansa, can yace "Ohk, let bring her in I will stay nd guard her till 2morrow kafin nn sae a samo mata wani gidan." El-Ameen ya shiga hararansa can ya ja tsaki yana kallon agogo yaga har goma ya wuce, yace "Kaga mu je can gida na, don ni na gaji sanyi nake ji kar in yi ma kai na illa haka kawai" daga hka ya fice daga palon, junaid ya bi bayansa ya fita ya kulle gidan. Har suka isa gidan El-Ameen bbu wanda yace komai sae Junaid dake juyawa lkci lkci yana kallon mahaukaciyar, El-Ameen ya dauko makulin gidan dake motarsa ya fita ya bude gate don bbu kowa gidan, dawowa yyi cikin motar ya shiga compound din da motar, yana gama parking ya juya yana kallon Junaid yace 'Ohhw ni! yanxu mahaukaciya ce mace ta farko da xata fara shigar min gida bayan mahaifiyata maimakon matata" Junaid bae tanka sa ba, El-Ameen yyi tsaki yana girgixa kai ya fito daga motar ya nufi cikin gidan, Junaid ya fito ya bi bayansa, a balcony ya tsaya ya canxa change over din gidan don akwae wuta, ya juya yana kallon Junaid yace "Toh ni xan fito maka da mahaukaciyar?" Junaid ya girgixa kai ya juya ya koma gun motar, bae sha wahalan daukota ba don sosae El-Ameen ya daureta kuma duk tayi laushi, ihu take tana shure shure har suka shigo falon ya direta k'asa yana kallonta, El-Ameen ya rike haba yana kallonta yace "Ikon Allah, muna xaman xaman mu Junaid ya ja mana!" Juyawa Junaid yyi yana kallonsa, El-Ameen yyi tsaki ya nufi stairs, Junaid ya lumshe ido ya bude ya bi bayansa, daki ya samesa ya bude drawern kayansa da alamar kaya xae canxa, Junaid yace "It's late ynxu, muyi freeing dinta sae mu wuce koh" El-Ameen yace "wait tukun! Wae kai xaga dinga tsayawa da ita a gidan?" Junaid ya d'an yi shiru yana kallonsa, sae kuma ya sauke ajiyar xuciya yace "No, xan sa a samo min yar dattijuwa dat will be staying, nd I will hire a gate man" El-Ameen ya kyabe baki ya cire jikakken shirt din jikinsa da wando ya fiddo wasu kayansa ya sa, sae a snn ya juya ya kalli Junaid da ke xaune gefen gadon dakin yana kallonsa yace "Kai baxa ka canxa kaya ba?" Mikewa Junaid yyi ba tare da ya kallesa ba ya fice daga dakin, dariya El-Ameen yyi sanin haushin sa kawae Junaid ke ji.
*Sai dai da aka rushe katangar Chinan dai, ko wani katanga xan kuma cewa Allah yayi min da su*
*Haske Writers Association*
[16/10, 19:05] Hassan Atk: *Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
3.....
Wani kallo Mumy tayi masa tace "Kaga ka kiyaye ni Ahmad, baxa ka gun El-Ameen din ba asibiti xa mu" shiru yyi yana kallonta sanin baxae taba convincing dinta ba, a hankali yace "Toh kiyi hkuri mumyna mu tafi asibitin" jakarta ta dauka tace "Sake ni mu tafi" saketa yyi dai dai lkcn da wayarsa ya fara ring, fiddowa yyi a aljihu yana kallon me kiran nasa ya ga El-Ameen ne, ya juya ya kalli Mumy ya ga kallon wayar take, d'agawa yyi ya kai kunne daga daya bangaren El-Ameen yace "ya ne captain, kana gida yau?" Junaid ya d'an saci kallon Mumy ya ga kallonsa take, yace "Noo! Don't worry frnd Mumy tace mu tafi clinic kawae ba sai na xo ba" El-Ameen yace "What are yhu talking about guy?" Junaid yace "No ba komae wllh, kawae dae tace mu tafi asibiti ne" tsaki El-Ameen yyi yace "HeyJunaid are you ohk, wat are yhu sayin?" Junaid yace "Ohk Tnx for ur care frnd!" D'aga hka ya katse wayar ya kashe gaba daya ya mayar aljihunsa yana sinne kai, Mumy tace "Don me xaka ce Mumy tace, maimakon kace Abban ka ne yace kaje clinic" Junaid yyi shiru yana kallonta, komawa tayi ta xauna ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shknn, ka tafi can ya duba ka, amma yana prescribing maka magunguna ka dawo Ahmad, I repeat my self ka dawo" farin ciki ya lullubesa sae dae yyi kkrin boye hakan yace "Toh Mumy I promise" har bakin motarsa ta rakasa tace "Drive carefully" yace "Sure mum" tana tsaye har ya bar gidan snn ta juya xata koma bangarenta, xaune ta ga Hajiya Fatee da Hajiya Bilkee a balconyn Hajiya fateen suna kallonsu, Mumy ta karasa tayi masu sannu da xama, Hajiya Bilki kadae ta amsa da yauwa a dakile, juyawa Mumy tayi xata bar wajen Hajiya Fatee tace "Ynxu an ma hana d'an gwal din xuwa gaida mu tsabar mulki" juyawa Mumy tayi tana kallonsu tace "Ayya Bashi da lfya ne, ynxun ma gun likita xa shi" bbu wanda ya tanka ta cikinsu, ta nufi bangarenta ba tare da ta sa ma kanta damuwarsu ba. Junaid na isa ya tarda El-Ameen na clinic, bae so hkn ba amma bbu ynda ya iya hka ya nufi Babban asibitin Dad din El-Ameen din, don shima kwararren likita ne da yyi fice a Nigeria, da yake Nurses din sun san tsakanin Junaid da El-Ameen, bbu wanda ya dakatar da shi xuwa office din El-Ameen din, murda kofar yyi ya shiga babban office din, El-Ameen dake xaune yana dube duben files sanye da farin glass a idonsa ya dago yana kallon Junaid, ajiye pen din hannunsa yyi ya rike ha6a yace "Kan ka daya kuwa captain?" Dariya junaid yyi ya xauna kan table din office din yace "Kai da ban yi hka ba da Mumy bata bari na xo ba yanxu ai" El-Ameen ya girgixa kai yace "Mummy's boy, na ga randa xaka girma ka samu freedom din kanka" murmushi yyi yana shafa kansa yace "Uhm am 30 ynxu kace ban girma ba, ae kila har in mutu baxan samu wannan freedom din gun momma na ba" El-Ameen yyi dariya yace "Idan kayi aure xa ka samu" murmushi Junaid yyi yace "Aure kuma" kallonsa El-Ameen yyi ya cire glass din idonsa yace "Amma ba ka jin ddi koh, you look weary?" Junaid ya lumshe ido ya bude da damuwa yace "Kinda frnd! Am just disturb, bani da kwanciyar hankali kwana biyun nn, M just nt my self..." Rike kai yyi ya kasa ci gaba, El-Ameen ya dafa sa yace "What's wrong frnd, tell me ur problem, 'Yan gidan ku ko?" Junaid ya d'aga kai yana kallonsa cike da damuwa yace "No!

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login