Showing 165001 words to 168000 words out of 180982 words

Chapter 56 - CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE Book .txt

El-ameen, Hafsat dake ta mopping din Balcony ta gaishesa da fara'a tace masa yana sama a study room, yana haurawa sama ya bude kofar dakin, Xaune ya samesa idonsa lumshe ya karasa gabansa yana kallonsa, bude ido El-ameen yayi ya gyara xama ganinsa yace "Yahh, xaka iya xuwa kuwa?" Junaid yace "Ahmad I don't get what my parent are telling!" El-ameen ya shafa kansa yana murmushi yace "Wai na auren ku da Zahrah?" Buda ido junaid yayi yace "Aurena da Zahrah kuma?" El-ameen yace "Yeah" xaunawa junaid yayi jin ya kasa ci gaba da tsayuwar yace "You are getting me confuse, wace Zahran...." Murmushi El-ameen ya kuma yi yace "To ya na iya maka frnd? Ban son wani abu ya sameka mu rasa ka a kan Zahrah, ni na nema maka aurenta, isn't it nyc..... Nasan yea you are in love with her..... Son da kake mata ya take nawa so I have no option then to let go, ita ma na ga tana son ka sosai shi yasa nayi haka from the beginning, nasan dai yanxu no more love sickness nd the rest, just that kar ku cuci Humainah....." Tuni idon Junaid ya kada ya kasa ce masa komai yana kallonsa, El-ameen ya dunkule hannunsa ya kamo na Junaid ya kai masa knuckle yana murmushi yace "Chop knuckle frnd" Ana saukowa juma'a aka daure auren Capt Ahmad Junaid da Princess Zahrah El-ameen Moddibo a kan sadaki 1m wanda mahaifinta ne ya bayar, daurin auren nan ya samu halartan dubban mutane da 'yan gidan masarautu da dama daga ko ina na states din Kasar duk ta dalilin Sarki El-ameen Moddibo, masarautan bauchi ya xamo bbu masaka tsinke tsabar jama'a, kusan duk manyan da suka xo daurin auren mamakin mijin Zahrah suka dinga yi ganin shi ba basarake ba, shi ba yarima ba, shi ba jinin sarauta ba, shi ba kowa ba just a mere military personnel with CLASS, ba karamin alfahari sarki El-ameen yake da junaid ba da ya xamo sirkinsa, Junaid ya gaisa da mutane da dama sunfi dari kowa son ganinsa yake ta dalilin yanda sirkinsa wato sarki ke koda sa gaban abokansa sarakai da manyan kasa, baka taba fadin yanayin da Junaid yake ciki a lkcn sai dai kawai kaga yayi murmushi wani lokacin wanda iyakarsa lips, gam yake rike da hannun El-ameen dake gefensa don bai son su rabu, Su Abba basu suka bar bauchi ba sai kusan magrib don ba karamin walima aka shirya ba, xuwa bayan isha masarautan bauchi yayi tsit baka taba cewa anyi komai ciki don tuni aka tsaftace ko ina, Junaid dake xaune daki na musamman da aka basu shi da El-ameen, Aliyu, faisal da wasu frnds dinsa biyu, ya rike kansa har lokacin don ya kasa gaskata da shi fa aka daura auren nan yau, El-ameen ya dawo gefensa yace "Toh programs kusan goma ne fa gabanmu Mr man!" Dagowa yayi da sauri yana kallonsa, El-ameen yayi dariya yace "Atoh, gwara ka bar rike kai this is just the beginning, Abdul yace ka shirya xaka gun Zahrah, wato xaka je ganin amaryar ka....." Da 'yar dariya El-ameen ya kare xancen daga haka ya shiga bathroom don watsa ruwa, Aliyu dake ta danna waya yace "Duk karya ce!" Faisal ya kallesa ya danne dariyarsa yace "Meye karyar?" Aliyu yace "Wannan ji da kan da miskilancin wani mana" dariya sosai Faisal da sauran frnds din Captain suka dinga yi, shi dai Junaid bai tanka kowa ba, El-ameen na fitowa ya shiga toilet din shima, wani kaya irin ta sarauta lafiyayye El-ameen ya ajiye masa gefen gado bayan ya fito yace "Wai kayan da xaka sa kenan suka ce" Junaid da har lokacin bai iya hada ido da abokin nasa ya shiga jujjuya kayan, can ya mike ya tabe baki yace "No, bai yi min ba" dariya sosai El-ameen yayi su Aliyu na tayasa wanda hakan yayi mugun kona ran Junaid, Aliyu yace "Ae ko ka ki malam dole haka xaka sa, coz that's the rule tunda gidan sarauta kayi auren" sai a snn Junaid ya kalli El-ameen ya hade rai sosai yace "Nooo, bbu wanda xae dinga kafa min rule, snn bbu wanda ya isa yyi forcing dina...." Aliyu ya fashe da dariya yace "Duk karya ce wnn" El-ameen da ya kasa daina dariya yace "See you. Ka dinga bin rules kenan har sai an kai maka matar ka can gidan ka" Junaid bai tanka sa ba xai dau kayansa ya sa El-ameen ya kwace kayan yace "Kasan Allah kar fa ka dinga mana taurin kai nan" faisal yace "Look Capt you just have to obey before complaining as a good militant, idan ka bar nan naga bbu wanda xai bi ka yace ga yanda xaka yi koh?" Daukan kayan Junaid yayi ya fita parlor don sa wa, Aliyu ya fashe da dariya yace "Wato abun sai da lallaba," ko da Junaid ya dawo dakin duk kallonsa suka tsaya yi don sak yarima ya dawo, yayi kyau ba kadan ba, Aliyu yace "Uhm yarima junaid, ka hadu" junaid bai tanka sa ba, misalin karfe tara da wani abu aka doka sallama can parlor El-ameen ya fita, wata yar dattijuwa ce tsaye ta duka har kasa ta gaishesa tace "Ance in yi ma ango iso har gun Gimbiya Zahrah" El-ameen ya juya ya koma daki yace "Toh an xo daukar ka Capt, if you like go nd misbehave mu dai muna nan" sae da junaid ya ga dama sannan ya mike ya fita, dattijuwar na gaba yana biye da ita a baya, haka kawai yaji gabansa ke faduwa, tafiya me nisa suka yi har suka iso wani babban kofa ta bude kofar suka shiga wani parlor me girman gaske xama yayi parlon ita kuma ta karasa ta bude wani kofa ta shiga ciki, ba a dau lokaci ba ta fito ta risina tace "xaka iya shiga ranka shi dade" mikewa yayi ya nufi dakin har lokacin gabansa bai bar faduwa ba, yana shiga dakin wani sanyayyen kamshi ya doki hancinsa bai san lokacin da ya rufe kofar ba ya juyo ya sauke idonsa kanta.


*Haske Writers association*馃挕


鈿� *Captain Ahmad Junaid*鈿�


_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�


86___87
Ya kusa minti biyar tsaye bai karasa cikin dakin ba, tun da ya kalleta sau daya bai sake kallon inda take ba, xaune take kan hadadden Royal bed din dake dakin ta daura har kafafuwanta kan gadon, har wani daukar ido take tayi wani kyau na musamman, hannunta da ya sha hyena na rike da waya tana ta danne danne, ko sau daya bata kalli inda yake ba, can dai ya karasa gadon cikin takunsa na kasaita ya xauna ya fiddo da tasa wayar yana dannawa, ajiye wayar hannunta tayi ta mike ta nufi gaban mirror, bin ta da ido yayi bayan ta wuce sa, lokaci daya gabansa ya shiga bugawa, wani ubansun fitted gown ne jikinta gold colour yana jan kasa, kasa daina kallonta yayi har sai da yaga xata juyo sannan ya dauke kansa, wucesa ta kuma yi hannunta rike da laptop, ta koma kan gadon ta xauna ta kunna laptop din, tabe baki yayi lkci daya yayi d'an murmushi yace "Za ki iya da halina" kallonsa tayi a karo na farko tace "Nima xaka iya da nawa halin?" D'ago kai yayi ya kalleta ta gyada masa kai tace "Yeah!" Murmushi yayi yace "Ke har kina da halin da baxan iya da shi ba" murmushi ita ma tayi tace "Toh nima baka da halin da baxan iya da shi ba...." Gyada kai yayi har lokacin murmushi dauke fuskarsa sai dai bai ce komai ba, sun kusa minti sha biyar xaune bbu wanda yace komai, ita dai sai danna laptop take, satan kallonta yayi dai dai lkcn da ita ma ta dago suka hada ido, ji yyi dama hakan bai faru ba, ya wayance da sauri yace "Amm, lastly xa ki iya da halin matata" jingina tayi jikin gadon ta matsar da laptop din gabanta ta tabe baki tace "Bata da halin da xai daga min hankali, sae ma dai ita ce baxata iya da nawa halin ba" mikewa tayi ta hade rai lokaci daya tace "Kar ka kaga ka sameni kusan a banxa ka dauke ni for granted, ka xo kana gaya min magana yanda ka ga dama, you know who I am, kuma ni ba don ina sonka na yrda da auren ka ba sai don kawai in maka halaccin abinda ka min, in kuma yi ma Abbana biyayya, banda haka nafi class din ka, snn ni ba gidanka xan xauna da matar ka ba, Abbana zai siya min gidan da xan xauna, nafi karfin xama tare da ku....." Tunda ta fara magana yake kallonta da mamaki, furucinta na karshe yasa ya mike yana mata wani kallo yace "Who are you? A princess? Just that????" Dariya yayi wanda hakan ya kara fito da ainahin kyansa, ta tsaya kallonsa ko kiftawa bbu, ashe yana dariya dai, ya shafa kansa yana kallonta daga sama har kasa murmushi dauke a lips dinsa yace "Ba ki da gun xama da ya wuce gidana tare da matata, idan an siya maki gidan sai ki ajiye shi aside kiyi xaman auren da ya kai ki kt a gidana!" Kallonsa take tana huci tace "Baxan xauna gidan ka ba, nafi karfin xama tare da matar ka, my dad will get me a house......" D'aga kafada yayi yace "Toh xan ga ko kece mijin...." Shiru yayi sai kuma ya juya yana mamakin kansa anya ma tunda yake ya taba tsayawa yana exchanging words da namiji dan uwansa bare mace, abinda bai taba ba kenan duk tsawon rayuwarsa, juyawa ya kuma yi yana kallonta, tabe baki tayi hade da murguda baki tace "Sai mu gani ai ko ni xan xauna gidan ka" bai tanka ta ba ya koma ya xauna cike da jin haushin kansa kulatan da yyi tun farko ya kalli makeken agogon dake manne bangon dakin ya ga goma saura yan mintuna dai dai lokacin da dattijuwar daxu ta rafka sallama can parlor, mikewa yayi ya nufi kofa ya fita, wnn karan su biyu ne, suka duka har kasa tana masa sannu da fitowa, kai kawai ya gyada masu ya fice daga parlon, ko da ya koma inda aka saukesu bai ko kalli su El-ameen da Aliyu dake xolayarsa ba ya shige bedroom. A kwanaki ukun da suka gabata ba karamin Buduri aka sha a masarautan bauchi ba sai ka rantse baxa a mutu ba, safe, rana, dare sae an samu wani program da aka ce xa ayi kuma duk ba na wasa ba, kudi kam sun yi kuka ba kadan ba wanda hakan xai tabbatar maka da cewa ba karamar yar gata bace Zahrah, abun mamaki ya dinga ba junaid don ko kadan bbu abinda ya burgesa a shagalullukan da aka yi duk ya kagu a kyalesa ya bar garin, sai dai fa shi kansa yasan jin sa yake daban idan ya tuna Jasmine matarsa ce ynxu. Ranan talata aka yi program din karshe da suka kira shi da farewell princess Zahrah, shi dai Junaid na xaune gun ne idonsa a kan wayarsa da yake ta dannawa, yawan ci gun duk 'ya 'yan sarakai ne, princesses din sun gama yrda cewa mijin Zahrah duk da he's not from royal home is just classic, cute and very handsome bbu warce xata ce taga dariyarsa tun fara events har xuwa ranan sai dai murmushi da iyakarsa lips, da ganinsa kasan baya son hayaniya, har wani farin ciki Zahrah take idan yace baxai xo gun event ba tsabar haushin kallon da taga mata ke masa, don a duk events din da aka yi guda uku kadai ya yrda da kyar aka yi da shi sai wnn na karshen, sai ka rantse El-ameen ne angon don yawanci shi kedaukan post din Junaid, duk da Junaid waya kawae yake dannawa amma hankalinsa gaba daya na kan Zahrah as in kyan da tayi na musamman ne ranan, sae wani sheki take cikin lafiyayyen sliver gown me adon stones din dake jikinta, satan kallonta kawai yake wanda duk El-ameen na lura da shi yana dariya, sai kusan magrib aka tashi taron. Bayan isha mai martaba yasa aka kira masa Junaid, Junaid ya nemi gu ya xauna a babban parlon sarkin kansa a kasa, mai martaba yace "Dama ina son sanar da kai nasa a nema min gida a can katsina da Zahrah xata xauna, hakan ya maka ko" Junaid ya d'ago yana kallonsa, duk da yanda ransa ya bace bai nuna ba, cike da ladabi yace "Ae ina da nawa gidan ranka shi dade" Sarki yace "Eh nasan da haka Ahmad, amma ina ga hakan xae fi gwara tayi xamanta a nata gidan....." Mamaki ne ya cika junaid, yayi shiru na kusan minti daya kafin yace "Amma bana son rabasu da 'yar uwarta ranka shi dade.... Nafi son su xauna tare" sarki yace "A'a ina jin xaman su daban daban xai fi...." Junaid ya kuma kallonsa yana kokarin danne bacin ransa yace "I think it's not proper ita kadai ta xauna gida...." Mai martaba yace "Hakan yasa xan tura mata bayin da za su xauna da ita, in kuma hadasu da jakadu biyu" Junaid bai kuma cewa komai ba, sarki yace "Hope it's ohk...." Dakewa junaid yayi yace "Toh xan so ace gidana aka fara kai ta kafin ta tare can gidan" Sarki ya d'an yi shiru sai kuma yace "Ohk, but baxata wuce kwana biyu gidan naka ba" Junaid ya gyada masa kai yace "In'sha Allah" Sarki yace "Toh bbu damuwa" junaid bai jima parlon ba ya mike ya fice bayan sarkin ya basa shawarwari masu ma'ana, takaici ya ishesa lkci daya maganan Aliyu ya fado masa da yake cewa ae an fara kafa masa rule kenan tunda 'yar gidan sarauta ya aura, wani tsaki ya ja a xuciyarsa yace ba shi Ahmad din ba knn. Washegari misalin sha daya suka dau hanyar kt, sai ka rantse kace maida masauratan bauchi xa ayi katsina gaba dayanta Tsabar tawagar da aka yi don kai Zahrah gidan mijinta, Kai da gani kasan Gimbiya xa a kai daki, direct gida Junaid ya nufa don bai ma son yaje can gidan kansa ya fashe, bbu kowa gidan sai Hajja, Humainah da Mumy sai wasu frnds din Mumy wa enda basu je can tarban amarya ba, duk sisters din Mumy na can gidan da su fatima, bbu wani wanda ya amsa gaisuwarsa da mutunci ya nufi bangaren sa kawae, Hajja ce ta bisa har bedroom yana kokarin cire kayan jikinsa tace "Wato munafukin sarkin nn dan ya toshe bakina shi ne har da wani yi ma Humainah kayan daki da lefe irin ta yar sa koh, to yyi a banxa don ni bbu ruwana da wnn, kuma idan baka yi hankali ba sai nasa an ma uwarka kishiya kai ma irin yanda ka yi ma jikata," Murmushi junaid yayi yace "Toh ai ba haramun bane" daga haka ya shige toilet ya bar ta nn tsaye. Sai kusan yamma El-ameen ya zo gidan da Aliyu. Karfe shidda da wani abu Abba yasa a kira masa Humainah, tana isa parlon ta nemi jikin kujera ta xauna daga kasa, kallonta kawai Abba yake cike da tausayinta, ta sunkuyar da kai a hankali tace "Abba ga ni" ya nisa yace "Kina jina Daughter" kai kawai ta gyada masa yace "Kiyi hakuri kin ji, matukar ina raye baxan taba bari Ahmad ya kuma walakanta ki ba, ki dauka auren ki da shi kaddara ce don biyayya kika mana, promise me ba ke xaki xamo tsilar ko wani tashin hankali da xae faru a gidan auren ku ba, you promise me xa ki xamo mai kauda kai a komai...." Hawaye ne ke sauko mata tace "I promise Abba" maganganu masu kwantar da hankali Abba ya dinga mata, wayarsa ya dauka daga karshe ya kira Junaid yace ya samesa parlonsa, ba a dau lokaci ba Junaid ya iso parlon, kallo daya ya masu bai kuma dago kai ba har ya nemi waje ya xauna daga kasa shi ma, kallon Humainah Abba yayi yace "Tashi ki je ki shirya ku wuce gida" ba musu ta mike Junaid ya bi ta da kallo har ta fita, Abba ya juya yana kallonsa yace "In ma kun cuceta kai da Allah, kuma I assure you baxae bar ku ba, more especially kai, I won't say anything more than this, tashi ka je" kasa cewa komai Junaid yayi bai kuma iya ya dago kansa ba, can dai ya mike yace "Nagode Abba" daga haka ya fita daga parlon ya tafi bangaren sa, bai tarda su El-ameen ba wanda hakan ya tabbatar masa da cewa wucewa suka yi, ya gama shirinsa ya fito, ya jima tsaye yana jiran fitowar Humainah ganin bata fito ba ya shiga ciki, bedroom dinsu ya shiga ya sameta xaune kasa ta hade kai da gwiwa, karasawa yayi dakin ya isa kusa da ita ya durkusa yana kallonta murya can kasa yace "Humainah!" K'in dago kanta tayi hakan yasa ya dago yana kallon fuskarta da ya wanke da hawaye, finger dinsa yasa yana share mata hawayen kmr me rada yace "Am...am sorry wife.... You.... have a special place in my heart!" Dago idanuwanta da suka rine tayi tana kallonsa, ya sakar mata wani lallausan murmushi ya lumshe ido ya kai mata light kiss a lips dinta, kasa kallonsa tayi ya mike ya daga ta ya dau hijab dinta ya mika mata ta karba ta sa, ya dau karamar jakarta yana rike da hannunta suka fita, dakin Mumy ya nufa da ita, Mumy dake xaune da frnd dinta tayi masu kallo daya ta dauke kai, durkusawa yayi nan gabanta, Humainah ma ta durkusa yace "Mumy xa mu tafi" sai a snn ta kalle su tace "Allah ya kiyaye hanya!" Mikewa yayi suka fita daga dakin Hajiya Karima na masu Addu'ar xaman lafiya, ana kiraye kirayen Magrib suka isa gida, su sisters din Mumy na gidan har lkcn da wa enda suka kawo amarya su kusan bakwai, junaid dai na dawowa daga masallaci ya shige bedroom dinsa ya sa key, sai da 'yan uwan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login