Showing 54001 words to 57000 words out of 180982 words

Chapter 19 - CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE Book .txt

xauna kan table yace "Ya aikin?" El-ameen yace "Alhmdllh" faisal yayi murmushi yace "Abokin ka xai tafi da patient din ku Abeokuta soon..." El-ameen ya d'aga kafada yace "Dat's nyc, Allah ya bada sa'a, ita kuma ya bata lafiya," faisal yace "Ameen, and you know what?" El-ameen ya girgixa kai, faisal yace "Ta ki cin komai yarinyar, from all indication, she is missing you" El-ameen ya girgixa kai yace "No! Idan aka takurata kuma aka tsoratata xata ci" faisal yayi shiru, sai kuma yace "Don Allah ku bar wannan childishness din kai da Junaid ku hada kai ku taimaki baiwar Allah, ni banga abun xuciya a nan ba, ga yarinyar 'yar karama da ita...." El-ameen ya hade rai yana kallonsa yace "Look nace banyi kuma, ba gashi xai kaita asibiti ba, don Allah ka bar ni in ji da abinda ke damuna" shiru faisal yayi kafin yace "But ni ina tunanin anya ba asiri aka mata ba, banda haka me xai ja mata brain disorder at her young age...." El-ameen ya girgixa kai yace "Na fa yi diagnosing dinta, brain disorder ne, she's suffering from post-traumatic stress disorder!" Faisal ya d'an bude ido yace "And what's the cause?" El-ameen ya lumshe ido ya bude yace "Serious accident, sudden demise of love one, terrorist incident, a lot of them..." Faisal ya sauke ajiyar xuciya yace "Allah sarki, Allah ubangiji ya bata lafiya" El-ameen yace "Ameen!"


Kusan a tare Junaid ya shigo compound da Suhaima da tayi kamar bata san mota ce bakin gate din ba sai tafiyarta take, ya kusa bugeta da motar ya nufi parking lot abun sa, bude baki tayi bayan tayi tsalle ta bar wajen ta bi motar tasa da kallo, ya fito ya rufe motar ya nufi part din Mumy, tsaki tayi ta shige part din Hajiyarsu tun daga parlor ta dinga kwala mata kira ta fito da sauri, Suhaima tace "Uhn in gaya maki haka maganan take Hajiya, Mahaukaciya Ahmad ya tsinta yanxu haka tana gidan El-ameen ana kula da ita wai, don ma Sumayyar bata san gidan bane da mun je" Hajiya tana tafe hannu baki bude tace "Ikon Allah, mahaukaciya kuma? xan ko je in samu uwar Aminun yanxu ba sai gobe ba" Suhaima tace "Amma fa Hajiya xai ma iya yiwuwa Khadija ta san komai" Hajiya tace "Ae baxa tayi magana ba shegiyar, bari ina zuwa in je gun balki mu san abun yi" dankwali ta dauka ta fice tayi bangaren Umma. Junaid na bude kofar Mumy Humainah dake labe jikin kofar tayi masa k'ara a fuska, turata yayi har sai da ta kusa faduwa ya hade rai yace "baki da hankali ne" kallonsa ta tsaya yi kamar xata yi kuka, ya galla mata harara ya juya ya fita daga parlon, parlon sa ya tafi ya kwanta, duk ya rasa me ke masa dadi, bayan isha yana xaune parlor Fatima ta tace Abba na kiransa, bai tanka ta ba har ta fita sannan ya mike ya fita ya tafi part din Abban, Mumy ce parlon tana yanka masa watermelon sai Umma da ita ma shigowarta kenan, ya xauna kasan rug din tsakar parlon yana kallon Abban nasa yace " Sannu da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa, ya maganar mu ta ranan ban ji ka sake cewa komai ba" Junaid ya d'ago da kyar yana kallonsa, a hankali yace "ina sane Abba..." Abba xai yi magana Umma ta riga sa tana murmushi tace "Toh ko dai har yanxu baka samo mana surkar bace Ahmad" ko kallonta bai yi ba bare ya tanka ta, Mumy dai bata ko kallesu ba tana ta yankar kankanar gabanta, Abba yace "Toh ina sauraranka, don kwanakin da na dibar maka ya kusa" kai kawai Junaid ya iya kada masa ya mike ya fita daga parlon jikin sa a sanyaye, part dinsa ya koma ya kwanta duk jikinsa ba kwari, shi yanxu a ina xai samo mata ana xaune kalau gashi sati daya da 'yan kwanaki kadai ya rage a kwanakin da Abba ya dibar masa, gaba daya daren ranan kasa baccin kirki yayi, ya mike ya dauro alwala ya fito ya hau sallahn nafila a dakin, washegari da safe haka ya shirya cikin rashin kuzari ya tafi gun aiki, da ka gansa kasan akwai damu tattare da shi sosai, after Asr ya nufi gidan El-ameen, driving kawai yake amma gaba daya hankalinsa bai jikinsa ga wani mugun sara masa da kansa yake, ya rasa wanda xai gaya ma damuwarsa a lokacin, da da ne da yanxu ya kira El-ameen ya sanar da shi, yana isa gidan yayi xaman sa cikin mota bai fito ba har bayan kusan rabin awa, can ya fiddo wayarsa yayi dialing number faisal, bugu biyu faisal ya d'aga, Junaid ya lumshe ido yace "Plss faisal ka taho gidan El-ameen if you are less busy" faisal yace "Ohk" katse wayar Junaid yayi, sai ya ji kamar ya kira El-ameen sai ya fasa, yana nan xaune har faisal ya iso layin bayan kusan minti ashirin, Yana gama parking ya fito Junaid ya danna masa horn don ya gane yana cikin motar, faisal ya nufi motar ya bude yana kallonsa yace "Mummy's boy...." Shiru yayi ganin yanayinsa, can ya shiga motar yace "Ya aka yi Captain" Junaid ya lumshe ido ya bude kamar baxai ce komai ba, faisal ya tabe baki yace "Haka fa, ni ba El-ameen ba ina kai ina gaya min, but kiran me ka min?" Junaid yayi murmushi yace "Mu shiga ciki" daga haka ya bude motar ya fita, faisal ma ya fito suka shiga gidan a tare, mama ce xaune parlor ita kuma tana kwance jikinta tana gyara mata gashinta, suka gaida Mama ta amsa da murmushi tana masu sannu da xuwa, Junaid ya xauna idonsa a kan jasmine, haka ma faisal, a hankali ta bude ido tana kallonsu don dama ba bacci take ba, Junaid yace "Ta fara cin abincin mama?" Mama jummai tace "A'a daxu dai na bata kunu ta sha ba laifi, sai dai jikinta da dumi" Junaid bai kuma cewa komai ba, faisal yace "Toh ta sha madarar jiya?" Mama ta girgixa kai tace "A'a" Junaid dai sai kallonta yake, faisal ya mike ya isa gabansu ya duka a hankali ya daura hannunsa kan forehead dinta, tayi wani kara da ya sa shi mikewa da sauri ya koma baya, mama jummai tayi dariya tace "Toh bata sanka ba" faisal yace "Uhun na ga alama" murmushi Junaid yayi ya mike ya nufi kofa, mama tace "Kai dai Ahmad ka iya tafiya ba sallama" juyawa yayi yace "A'a ban tafi ba mama ina waje " mama tace "Toh yaushe Aminu xai dawo, ka ga maganinta ya tsaya yanxu" yace "Xai dawo, amma ba yanxu ba shi yasa ma yanxu nake shirin kai ta asibiti a ci gaba da dubata a can kafin ya dawo" daga haka ya nufi kofa ba tare da ya jira cewarta ba, ta bi sa da ido lkci daya jikinta yayi sanyi jin abinda yace, faisal ya juya ya bi bayansa, hawaye ne ya cika idon mama jummai ta dago jasmine tana kallonta tace "Yanxu raba mu xa ayi?" Junaid na fita balcony ya xauna, faisal ya xauna gefensa yace "Nayi kadan in ji damuwar ka ko Junaid" Junaid ya kallesa yayi murmushi yana girgixa masa kai, bayan kusan minti biyu cikin sanyin murya ya soma gaya ma faisal matsalar da yake ciki, faisal yayi shiru yana kallonsa cike da tausayinsa, can yace "Toh kai yanxu baka da budurwar da ta maka ne" Junaid ya girgixa masa kai yace "I don't have!" faisal ya sauke ajiyar xuciya yana kallonsa, bayan kusan minti daya murya can kasa yace "You know what Capt?" Junaid ya kallesa bai ce komai ba, faisal yace "ka auri yarinyar nan kawae...." Junaid yace "Wacce yarinya?" A hankali faisal yace "Baiwar Allahn nan da kake kokarin ganin an sama ma lafiya, I assure you ba karamin lada xaka samu ba, sannan yarinyar bata yi kama da 'yar kananun mutane ba, ina da yakinin 'yar babban gida ce, you won't regret it frnd....." Kallonsa kawai Junaid yake da mugun mamaki, faisal ya girgixa kai yace "Its for ur good, for her good Capt, yanxu misali kayi aure dole baxa ta ke samun attention gun ka ba as before and ba ko wace mace bace xata yarda da taimakon ta da kake, kaga wannan shine anyi ba ayi ba don gidan jiya yarinyar xata koma, but idan ka daure ka aureta kaga ka rufe bakin parent dinka, ita kuma sai ka ji dadin kula da ita sosai tunda you now have ur freedom har Allah ya bata lafiya, then sai ka sauwake mata idan baka da ra'ayin xama da ita ta tafi ta nemi 'yan uwanta, in ka mata haka ka mata komai na rayuwa, kai kadai ne gatan yarinyar nan Junaid, ka ajiye batun mahaukaciya ce ka aureta, I assure you dat you won't regret helping her...." Katse sa Junaid yyi yace "What the hell are you saying faisal, a haukacen xan gabatar da ita gun su Abba? Sai ince ina danginta da 'yan uwanta suke, kuma kasan dai dole sai na kai ta gida gun Mumy, this is totally out of it...." faisal yace "Uhmm! Toh nemo wani solution din" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Don nayi aure baxai sa in ki ci gaba da taimakonta ba, ni nayi niyyar nema mata lafiya, babu kuma macen da ta isa don na aureta tayi controlling dina, da aurena ko ba aurena I will help her kamar yanda nayi niyya, yanxu dai xuwa gobe nake son gama arrangement din tafiya da ita" faisal ya d'aga kafada yace "Ohk Allah ya shige mana gaba, yanxu mu je in siya drugs ka kawo mata don akwai xaxxabi jikinta"
El-ameen ne kwance dakinsa bayan magrib, Ummi ta shigo dakin tana kallonsa tace "What's ur problem Ahmad, are you ohkay?" Mikewa xaune yayi a hankali yace "Slight headache ne Ummi" tace "Toh ka fito ka ci abinci ka sha magani mana ko kwanciyar ne xai sama maka relieve" daga haka ta juya ta fita tana naxarin maganan da Hajiya fati ta xo mata da shi daxu, wai sun ajiye mace can gidansa shi da Junaid, she trust her son, ta kuma san abinda xai yi da wanda baxai yi ba, ganin condition dinsa tun da ya dawo daga gun aiki yasa bata yi masa magana ba, ta kuma yanke shawarar ba ma sai ta masa ba kawai sawa xata yi aje a gano mata kuma idan har hakan ne ta tanadi abinda xata yi masa don she's a no nonsense ita, bayan minti kusan goma da fitan Ummi dakin Faisal ya xo, yayi mamakin ganin El-ameen din kwance yana bacci, ya tada sa yace "Lafiyarka kuwa El kai da baka bacci da wuri" El-ameen ya kuma lumshe ido yace "ina jin xaxxabi ne ke son kama ni, am not feeling OK" faisal yace "Toh ka sha magani?" Girgixa masa kai El-ameen yayi, faisal yace "Saboda me? patient dinku ma na can ita ma xaxxabin take, na dai siya mata drugs Junaid ya kai mata..." Mikewa xaune El-ameen yayi da sauri yace "Xaxxabi kuma, tun yaushe? Wani drugs din ka siya mata?"


鉁嶐煆�
*Haske Writers Association*馃挕




鈿� *Captain Ahmad Junaid*鈿�


_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�


28.....


Faisal yace "Normal drugs na xaxxabi mana" El-ameen yace "Ohk, Allah ya bata lafiya" faisal yace "Ameen, idan Allah ya kai mu gobe xa a tafi da ita kudu" El-ameen ya d'aga kafada bai ce komai ba, faisal yace "Kayi wanka ka ci abinci sai ka sha magani xaka fi jin dadin jikin ka," ba musu El-ameen ya mike ya shiga bathroom, faisal na ganin haka ya jawo wayarsa da sauri ya nemo number Junaid, cikin hanxari ya shiga rubuta masa text kamar haka "Ban yi tunanin akwai abinda ya isa ya shiga tsakaninmu da kai har ya hada mu haka ba, all the same Allah ya huci zuciyarmu, ba wai don ka hakura kuma na maka text din nan ba sai don in nuna maka ni babba ne...." Daga haka faisal ya tura text din sai da ya tabbatar ya tafi sannan ya maxa yayi deleting ya mayar da wayar ya ajiye, ko minti goma faisal bai kara a gidan ba yayi gaba. Junaid na xaune parlon Mumy yana cin abinci text din ya shigo wayarsa, yayi mamakin ganin sunan El-ameen, ya bude text din ya karanta content din, murmushi kawai yayi ya ajiye wayar, can ya mike ya dawo parlor ya d'an saci kallon Humainah dake kwance tana danna wayar fatima, karbe wayar yayi yace "Ke baki iya gaisuwa ba ne" mikewa tayi xata wuce daki ya fixgota, ta kusa fadowa kansa, turasa tayi kmr xata yi kuka tace "Ni ka kyaleni," ya matso kusa da ita yace "Anki" ta bata fuska xata yi kuka, yayi murmushi yace "Abinda kika fi iyawa kenan ai" saketa yayi ya fita daga parlon ta bi sa da harara. Karfe takwas saura na dare El-ameen ya fito rike da makullin motarsa xai tafi clinic a bisa umarnin dad dinsa, bin sa da kallo Ummi tayi har ya fita, yana shiga motarsa driver din Abbansa ya karaso kusa da motar, xuge glass yayi yana kallonsa yace "Ya aka yi Umar?" Drivern ya d'an sosa kai yace "Yallabai dama, ji nayi Hajiya xata aika wasu xuwa can gidan ka, ina jin akwai fa binciken da take, xuwa anjima xa su je, nine ma xan kai su wai...." El-ameen ya firfito da ido yace "Gidana kuma, me tace maku xa ku je ku yi?" Umar yace "Wllh ban san me tace masu xa su je yi can ba, ni umarni kawai ta bani in kai su" El-ameen da hankalinsa ya gama tashi yace "Ohk ohk nagode kwarai Umar..." Umar din yace "Amma yallabai ka rufan asiri, naga kai din mutum ne mai kirki shi yasa nace bari in ankarar da kai, in ma da matsala ne sai ka gyara" El-ameen yace "nagode kwarai umar, kar ka ji komai" daga haka ya ja motar ya bar gidan, sai da ya fara tsayawa a atm machine ya cire kudi sannan ya nufi gidansa direct. Yana isa gidan yayi parking waje ya fita ya shiga ciki, murda kofar parlon yayi a hankali ya tura ya shiga, bbu kowa parlon sai Jasmine da plate din potatoe gabanta ta kifar kasa, mikewa tayi jin an bude kofa ta kalli kofar da sauri, ya tsaya ya rungume hannuwansa yana kallonta, a hankali ta shiga tahowa tana kallonsa itama har ta iso gabansa ta tsaya, murmushi ya sakar mata murya can kasa yace "Jewel!" Ita dai kallonsa kawai take, ya matso kusa da ita a hankali ya ja hancinta yace "Did you miss me" taba nasa hancin tayi a hankali ita ma, ya wara manyan idonsa yana 'yar dariya sai ga mama jummai ta sauko daga stairs rike da jakunkuna biyu, ai tana ganin El-ameen tayi still, ya kalleta ya kalli jakar da mamaki, lkci daya murmushin dake dauke fuskarsa ya bace yace "Ina kuma xaki da jaka mama?" Ae sai ta fashe da kuka tace "Yo naji Ahmad na cewa gobe xai kai ta asibiti ta xauna a can, a gida ma ana yi bata warke ba sai wani asibiti can, ku bar ni in je a mata na gargajiya mana tun da ba a dace da na baturen ba, don Allah ni a bar ni da ita xan kula da ita har Allah ya bata lafiyan. Idan ya so sai in baku addreshin kauyena, ku yarda da ni baxan cuce ta ba..." El-ameen kallonta kawai yake da mugun mamaki, yanxu da Allah bai kawo sa ba tafiya da ita kawai xata yi, karasowa parlon yayi yace "Ehh wannan kuma gaskiya ne mama kin kawo shawara me kyau, Amma bari muyi shawara da Junaid din koh" tana matsar kwalla tace "Toh" xaunawa yayi yana kallon Jasmine dake ta binsa kamar xata shige jikinsa, yayi murmushi ya xaunar da ita ya jawo ragowar potatoe din da ta xubar ya dau daya ya kai mata baki, ta bude bakin ya saka mata, kallon Mama jummai dake kallonsu tana 'yar murmushi yyi yace "Mama xaki d'an siyo mata fruits a bakin titi don Allah," tace "Toh" ya fiddo kudi ya mika mata yace "Na dubu xa ki ce a baki" karban kudin tayi ta fita sabe da gyalenta, jasmine ta bi ta da kallo, mikewa yayi ya isa kofa yana lekan ko ta tafi sannan ya juyo ya kusa cin karo da Jasmine da har ta biyosa, murmushi yayi ya isa gun jakunkunan da mama jummai ta sauko da, ya bude yaga wanda ke dauke da kayan Jasmine din, duddubawa yayi ya fiddo da hijab ya sa mata, sannan ya dauki jakunkunan biyu ya rike hannunta suka fita daga gidan ya kulle da key, yana rike da hannunta ya nufi gun mai gadi, yace "Kana ji na Usman, xa mu dan yi tafiya ne amma baxa mu dade ba" ya fiddo kudi aljihunsa ya mika masa yace "Ga kudin ka na wannan watan, yanxu xaka tafi xan kulle gidan ne, sai ka tsaya bakin gate har mama ta dawo ka bata Jakarta da kudin nan ita ma, da xaran mun dawo xan neme ka" Mai gadin da ko kadan bai ji dadi ba yace "Toh shikenan yallabai, Allah ya kiyaye hanya, ya dawo da ku lafiya" El-ameen yace "Ameen, d'an je ka canja min wutan gidan xuwa na gen" ba musu maigadin yaje yayi yanda yace masa gidan ya dawo ba wuta gaba daya, ya dawo shima ya hada nasa kayan, suka fito gaba daya, El-ameen ya kulle gidan yace "Don Allah ka jira har tsohuwar ta dawo ka bata hakkinta da kayanta," mai gadin yace "In'sha Allah yallabai" daga haka El-ameen ya nufi motarsa da ita da sauri yana rike da nata jakar kayan, ya bude front seat yasa ta shiga, ya ajiye jakar kayanta a bayan motar ya rufe, ya xaga ya shiga motar ya tada ya bar wajen, kafin ya isa titi ya ga Mama jummai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login