Showing 39001 words to 42000 words out of 180982 words
Chapter 14 - CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE Book .txt
ya tuna abinda Abba yace sai gabansa ya fadi ba kadan ba, wai 3wks, kuma yasan ba lallai yayi kaffara a kansa ba, tunda ya dauki kudurin taimakon baiwar Allahn nan yake fuskantar challenges iri iri ga shi bashi da rest of mind as before, and he knows he is only doing it for Allah's sake ba da wata manufa ba, damuwar da yake ciki bai hanasa yi ma El-Ameen transfer din dubu dari da hamsin din da yace na drugs dinta ba, Hudu bai karasa ba ya bar gun aiki ya dawo gida, part dinsa ya nufa ba tare da ya kalli su Umma da Hajiya dake xaune balconyn Hajiya ba yayi shigewarsa parlor yyi banging kofar, Hajiya ta tabe baki tace "Ke maganar ki gaskiya ce wllh, tsinannan uwar nan tasa bata bari yaci girkin mu, ita ke masa da kanta kullum" Umma tayi kwafa tace "Ahaf Ba baki yarda ba da, ae wannan matar ae sai dai muyi adduar ganin karshenta" Hajiya tace "Toh wai meye kuma next move din da xa mu dauka tunda gashi ance ya fito da mata nan da sati uku, ke kar fa kuma yace wannan shegiyar Humainah take kowa, kinsan fa ba kula matan yake ba, kar uwarsa tace ya fito da Humainahr kawai mu shiga uku, wannan fa shine anyi ba ayi ba" Umma ta xuba tagumi tana gwalo ido yace "Yo ni ae wannan tunanin bai fado min ba wllh, kai da mun shiga uku, ni fa Humainahn nan ba karamin tsana nayi mata ba fa don duk da dududu bata fi sati gidan nan ba naga alama bata da kunya ko kadan, kuma ko shigowa gaishe mu bata yi, sai ma taga dama take gaishe mun in ta shigo gun Alhaji, kuma ina ga kamar tsinannar Aminan nan ke xuga ta" Hajiya ta sauke ajiyar xuciya tace "Xamu san yanda xa muyi da shegiyar ita ma, kuma ma ni ban ga alamar suna soyayya ba kin san halinsa ai, kuma ni shawarata kawai mu hade kai mu san yanda xa ayi Alhaji ya hada sa da Suhaima ko Muhibba shikenan sai yanda muka yi da shi" Umma tace "Toh ai matsalar ynxu kawai kullin da aka bamu mu barbada kofarsa ne, ya xa muyi? kinsan ba xuwa can bangaren muke ba, muna xuwa yanxu xa a gano mu, kuma don tsiya wai sai da magriba, dama da rana ne bbu wanda xai lura shi kuma yana gun aiki, ita kuma sallamammiyar 'yar ki khadija ba bamu hadin kai xata yi ba" Hajiya ta d'an yi shiru sannan a hankali tace "Suhaima xata yi mana aikin, nasan halin abata tsaf xata yi ba tare da an xargi komai ba" Umma tace "Toh Alhmdllh" da haka suka ci gaba da hirarrakunsu cike da rashin tsoron Allah.
Junaid kam wankansa yayi ya dauro alwala ya fito ya shirya cikin kananun kaya yayi la'asar a dakin sannan ya fito yayi part din Mumy, suna xaune da Humainah tana mata tsifa, Ya xauna yana kallon Mumy yace "Ina yini Mumy" bbu yabo bbu fallasa tace "Lfya lau" shiru yayi, Mumy ta hade rai tace "Ka kyauta Ahmad ita 'yar uwar taka ka walakanta gaban idon makiyan ka koh?" Humainah ta bata rai, sai kuma ta fashe da kuka, Mumy tace "Ji walakanci, meye haka ke kuma" mikewa tayi fuu ta koma dining tana rera kuka, Mumy tayi tsaki ta galla masa harara ta shige daki. Murmushi yyi yana shafa kansa ya mike ya nufi dinning din, kujerar dake kusa da wanda ta xauna ya ja ya xauna ta mike xata bar wajen ya rikota ya mayar da ita ya xaunar yace "Wai dama daxu magana kike min" ta fizge hannunta tace "Ohon maka" dariya yayi yace "Ni fa nayi xaton da kofar mota kike, toh tunda da ni kike yi hakuri..." Ta fashe da wani sabon kukan tace "Allah bana so" murmushi kawai yake yana kallonta yace "Toh kar ki so din, har da wani kwalliyarta tayi xaton da El-Ameen xamu dawo" ta dago da sauri tana kallonsa ta tsuke fuska tana goge hawayen idonta tace "Wani kwalliya nayi" giranta ya taba a hankali yace "Ba gashi ba har da wani shafa baki kika yi anan irin yanda kuke yi" ya kuma kallon pink lips dinta yana murmushi yace "Har da wani shafa jan baki a nan duk don ki burgesa" buge masa hannu tayi fuskarta daure tace "Tun da kai ka shafa min ba" mikewa tayi xata bar wajen ya rikota da sauri yana dariya yace "Toh na dai ce kiyi hakuri koh" ta turasa tayi gaba abunta, murmushi yayi ya tabe baki, fatima dake bakin kofar kitchen tayi gyaran murya tace "Uhum ya A.jay Humainaj kadai yake ma dariya a gidan nan" wani kallo yayi mata, ta juya da sauri ta koma kitchen tana dariya, tsaki yyi ya bude food warmern dake dining din, kadan ya xuba shinkafar ya ci ya dawo parlor don duk bai da Appetite, kofa ya nufa ya koma part dinsa ya kwanta ya lumshe ido, yana son ya gansa can gidan El-Ameen ya ga halin da Baiwar Allahn ke ciki amma yasan baxai ma fara cewa xai fita ba, haka yayi ta juye juye kan kujeran duk ya rufe ido ita yake gani, shi kam tun da ya fara ganin yarinyar nan nutsuwarsa ya ragu, toh ko dai haushin taimakon nata da yayi take ji shiyasa ya kasa samun kwanciyar hankali, bude ido yayi jin an bude kofarsa, ya juya da sauri ya ga Humainah ce, ta hade rai ta dungure masa bowl din fruit salad din hannunta a kasa, murmushi yayi yace "da kin xubar ai," ko kallonsa bata yi ba ta fice. Washegari haka ya tafi aiki da safe as usual, ba laifi Mumy ta d'an kulasa da yaje breakfast, Abba kuwa dama da yaje gaishesa ca aka yi masa yana bacci, ko ta kan Umman bai bi ba yayi ficewarsa don ya saba in dai ba Mumy ce da girki ba to ba lallai ya ga Abba ba sae ko a masallaci, kasa samun natsuwa yayi gun aiki har sae da ya dau excuse din minti ashirin ya fita ya kama hanyar gidan El-Ameen, su biyu kadae ne parlon ita da mama dake mata kalaba daga tsaye don taki xama, sae xagaye parlon suke ana kitson a haka, tana ganinsa suka hada ido ta kurma wani uban ihu da yayi mugun tsorata mama don kan kace me har ta kai bakin kofa, shi kam tsayawa kallonta yayi, har lokacin ihun take da karfi tana shisshigewa jikin bango ko ina na jikinta na rawa, lumshe ido yayi a hankali ya bude ya kalli uniform din jikinsa White navy shirt ne jikinsa da dark trousers navy blue, ya kalleta ya ga yanda ta runtse ido tana k'uwa, bude kofar parlon aka yi El-Ameen ya shigo da ledoji a hannunsa, sake ledojin yayi da sauri ya karasa gunta, ya riketa, bude ido tayi a gigice ta kara fasa wani ihun tana ganin El-Ameen ta rungumesa, ya rufe bakinta lkci daya tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya a hankali, kallon Junaid yayi ya hade rai yace "Look captain, I've warned you not to come to this house on uniform again, look how you are scaring the life out of her, a haka xata samu lafiya? Plss ka daina xuwa nan da uniform" Juyawa Junaid yayi ya fice daga parlon, Mama dake bakin kofa har lkcn tace "Auuu wae khakin take tsoro? Allah sarki Baiwar Allah" dago kanta El-Ameen yayi yana kallonta ita ma haka, kama hannunta yayi yana rike da ita suka haura sama. Junaid na komawa gun aiki ya ci gaba da harkokinsa sai dai da ka gansa kasan there is something eating him inside, karfe biyar saura ya isa gida, ya jima xaune motarsa yana danne danne a waya, ganin motar da ke kokarin parking gefensa ya kashe motar ya fito ya rufe yayi part dinsa. Yana kwance parlor'nsa dab da magrib yana kallon wani program though absentminded yaji Humainah na kwalo masa kira daga waje, mikewa xaune yayi jin irin yanda take kiransa da karfi, ya mike da sauri ya nufi kofa ya bude, tsaye ya ganta d'an nesa da balconyn rike da kugu tana tafe hannu tace "Taho taho ka ga yaya" yana fitowa sai kuma tayi bangaren Mumy da sauri tana kwalo mata kira ita ma, wanda hakan ya ja attention din 'yan gidan da ido da kunnensu na kan duk wani motsi na gidan kamar masu gadi, Umma ta riga Mumy da fatima fitowa sannan Hajiya, su khadija Rabi'a, sadiya, Muhibba duk suka fiffito, shi kam Junaid abinda ya daure masa kai bai wuce na ganin Suhaima tsaye bakin kofarsa tana xaxxaro ido sai kokarin boye abu a hannunta take, Humainah ta dawo da sauri Mumy na biye da ita a baya haka ma sauran, Hajiya kam ko ina na jikinta rawa yake ji take kamar ta saki gudawa tsabar rudu shikenan asirinsu ya tonu, garin yaya Suhaima taje bakin kofar ba tare da ta sa ido taga bbu kowa a tsakar gidan ba, ita kanta umma sai da hanjin cikinta ya kada sai dai duk basu nuna a fuska ba, don Hajiya sai ma wani hade ran karfin hali tayi, A takaice Humainah ta rike kugu tace "Abu naga tana shirin barbada wa bakin kofar ya Ahmad, duk bata san ina can bakin pampo naje daurayo takalmana ina kallonta ba" ta fadi haka tana nuni da kusa da bangaren da Hajja ke sauka, Suhaima dake ta salati a rikice tace "Sharri xa ki min don kin gan ni a nan, na shiga uku na lalace, Hajiyanmu kina jin abinda yarinyar nan ke cewa" a fusace Humainah tace "koh ba sharri ba, ki bude tafin hannun ki munafuka, kin wani xo kina yi kamar mage baki san ina kallonki ba xaki wani ce ina maki sharri, wllh Mumy abu take shirin barbada masa bakin kofa" Hajiya ta hadiye yawu da kyar tace "Ke yanxu 'yar nan sharrin naki kan 'ya ta kuma xe sauka, duk shekarunta gidan nan bata taba barbada ma Ahmad abu ba sai da kika xo munafuka algunguma toh wllh sai Alhaji ya xo ya mana shari'a don baxan yarda da kaxafin nan ba" fuu Humainah ta haura balconyn ta fixgo hannun Suhaima dake jin kamar ta saki fitsari tana huci tace "Bude hannun to idan sharri na maki, ki bude, uwar me ya kawo ki bangaren sa da daddare ke da ko during daylight ba xuwa kike ba munafukaa, toh wllh sai kin fadi Meye wannan kike shirin barbada masa ko in gaggalla maki mari a nan don ubanki" Mumy ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "Humainah!" Humainah na girgixa kai ido rufe tace "Ni dai Mumy Allah sai ta fadi meye a hannunta ko kuma muje ta barbada shi a kofar uwarta ni baxan yarda ba"
鉁嶐煆�
*Haske Writers Association*馃挕
鈿� *Captain Ahmad Junaid*鈿�
_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�
20.....
Suhaima da duk ta jike da xufa ta fara kokarin kwace hannunta daga rikon da Humainah tayi mata tana cewa "Na shiga uku ki cika ni, me na maki xaki min irin wannan sharrin?" Banda murmushi babu abinda khadija take, Hajiya dai da kyar kafafuwanta ke daukarta ga wani kullewa da cikinta yayi, Umma kuma sai wuwwurga ido take tana xufa, Sadiya ta haura balconyn a fusace tana kallon Humainah tace "Ke karamar 'yar iska cika mata hannu kar in baki mamaki yanxu....." Humainah ta juya a hankali tana mata wani matsiyacin kallo tace "Kambu! Ko kuma ni in baku mamaki ba, ai wllh sai ta fadi kullin uban meye a hannunta kuma wa ya aikota idan ba haka ba in karya hannun" Khadija tace "Toh ke Anty suhaima ki bude hannun a ga kullin mana, ko dai yaji xa ki kai masa?" Hajiya tayi kanta xata cafke ta ai da gudu ta bar wajen, cike da karfin hali Hajiya na huci tace "Ae sun yi kadan ta bude masu hannu wllh, sai dai duk...." Fitowar Abba yasa ta kasa karasawa ta fara girgije girgije ae kawae sae ta fashe da kuka tun kan ya karaso tace "Na shiga uku ni fateema me muka tare ma mutane a gidan nan ni da 'ya yana" A hankali Mumy tace "Cikata Humainah" Humainah ta girgixa kai ta cakumi rigarta tace "Noo! Ae sai ta bude hannunta mun ga ko menene wllh Mumy" shi kam Junaid tsaye kawai yayi ya kasa cewa komai duk jikinsa ba karfi, Abba na isowa ya shiga tambayar Meye haka, Humainah tace "Abba wallahi barbade take shirin yi ma Ya Ahmad Allah ya toni asirinta na kamata kuma ni sai taje bakin kofarsu ta barbada koma Meye xan kyaleta" Hajiya ta fashe da matsanancin kuka ko ina na jikinta na bari tace "Kana ji ko Alhaji, kana ji koh...." Abba kam kallonsu ya tsaya yi, can yace "Cikata Humainah" Humainah ta fashe da kuka tace "Ni wallahi baxan saketa ba Abba, sai ta nuna abinda ke hannunta kuma muje ta barbada shi a kofarsu, duk bata san ina can ina kallonta ba, ni wallahi baxan kyaleta ba" dariya khadija ta dinga yi can ciki ciki ganin yanda 'yar uwarta ke wurga ido kamar barauniya, da kyar Mumy ta haura balconyn ta kamo Humainah tace "Saketa Humainah" still taki sakinta ita fa sae ta bude hannunta, Junaid ya lumshe ido ya bude ya karasa kusa da su a sanyaye ya janyeta yace "Kyaleta Lil sis" fashewa tayi da wani kukan tace "Ya Ahmad abu fa tayi niyar barbadawa da ban ganta ba" ae Suhaima tun da ta samu Humainah ta saketa kan kace me har ta sauko kasa tana tuntube, ta fashe da kuka tana kallon Hajiya da Abba tace "Kudi fa na xo tambayarsa don ta ga ina leke leke shine take cewa barbade xan masa," Hajiya ta rungumeta ita ma ta fashe da kukan tace "Na sani Suhaima Allah xai saka mana kiyi shiru" Humainah ta kwace kanta daga rikon da Junaid yayi mata ta sauko tana kallonta da kyau tace "Kuma wallahi daga yau na kuma ganin kafar ki a nan wajajen sai na karya su duka biyun, munafuka kawai dama ni Hajja tace min boka da malamai kuke bi" tsawa sosai Abba ya daka mata, ta turo baki ta bangajeta tayi part din Mumy fuu tana gunguni, duk suka bita da kallo fatima ta ni bayanta, Abba ya kusa minti daya bai ce komai ba, can ya kalli su Hajiya yace duk kowa ya koma ciki, haka duk suka juya Hajiya na kuka har lkcn tana rike da hannun Suhaima Umma da baki ya mutu na biye da ita a baya, shi ma ya juya yayi part dinsa ana kiraye kirayen sllhn magrib. Mumy ta juyo a sanyaye tana kallon Junaid, shi din ma duk jikinsa yayi sanyi ba kadan ba, kasa cewa komai tayi ta sauka ta koma part din ta, ya lumshe ido ya bude ya bi bayanta. Xaune suka tarda Humainah palo sai rusa kuka take bakin rai, Mumy tace "lafiya kuma Humainah" cikin kuka tace "Mumy ba shine baku bari na mata duka ba, wllh wani kulli ne hannunta tana shirin xubawa bakin kofar na kamata" Mumy ta xauna kusa da ita tana murmushi ta jawo ta jikinta tace "Kiyi hakuri mu bar su da halinsu Allah ya fisu da shi kuma muka dogara, in'sha Allah bbu abinda xai same mu kin ji Humainah" kallon Junaid dake tsaye ya kasa xama tayi tace "Kai kuma ya Ahmad maimakon ka faffala mata mari shine ka tsaya kallonta" Xaunawa yayi yyi murmushi bai ce komai ba, lallashinta Mumy ta dinga yi har dai ta samu tayi shiru, Junaid ya mike ya shiga bathroom din dake parlon ya dauro alwala ya fito ya fita xuwa masallaci, Mumy ta kalleta tace "tashi ki je kiyi alwala" ba musu ta mike ta shiga bathroom Mumy ma ta tashi ta shiga dakinta don yin alwalan. Ana idar da Sllh Junaid ya shigo, Humainah na xaune da Mumy da fatima suna cin abinci, ya xauna yana kallonsu, kwankwasa kofa aka yi lkci daya aka bude aka shigo, Sadiya ce ta shigo ta tsaya daga bakin kofar fuskarta tamke tace "Humainah kike ko wa? Abba na kiran ki" Humainah ta galla mata harara tace "A'a Mantawa kika yi dai, Sadiya sunana" Mumy tace "Ke kina da hankali Humainah?" ta turo baki ta ajiye spoon din hannunta, Sadiya tayi kwafa tana gyada kai ta fice, mikewa Humainah tayi, Mumy tace "Ki gama cin abincin tukunna, baxa mu kuma shirya da ke ba idan kina rashin kunya" kamar xata yi kuka ta nufi kofa Junaid ya bi ta da kallo yana girgixa kai. Da sallama Shukrah ta shiga parlorn Abba, yana xaune kujera Hajiya da Umma ma na xaune sai Suhaima da ke xaune kasa, can jikin kujera ta samu ta xauna tace "Abba gani" a nutse Abba yace "Daga yau kika sake abinda kika yi daxu sai na yi mugun saba maki, Ashe ke shashasha ce, kina daga can bakin pampo ta ya kika ga abu a hannunta" Hajiya ta goge d'an guntun hawayen idonta tace "Babu maganan taya ta gani, wllh sa ta aka yi Alhaji don wnn yar mitsitsiyar hankalinta baxae bata tayi abinda tayi mana daxu ba, to ni kam me na tsare masu xa su yi ma 'ya ta irin wannan mugun sharrin?" Kuka ta fashe da sosai, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Xancen ki gaskiya Hajiya, amma Allah ya san dai dai, kuma baya bacci" Abba ya kalli Humainah da ta wani hade rai kiris ya rage ta fashe, yace "Don uwar ki wa kike ma wannan kallon" mikewa tayi ta fashe da kuka tace "Na rantse da Allah Abba wani abu ne a hannunta tana son budewa ta barbada fa na kama ta, ni ba karya na mata ba, meyasa baka ce ta bude hannun ba tun a can..." Wani tsawa Abba ya daka mata yace "Ke!! Baki san ni ba koh?" Hajiya ta