Showing 15001 words to 18000 words out of 180982 words
Chapter 6 - CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE Book .txt
da ku ka je gidansu iman sa ta gaba kuka yi wae kuna ta dariya koh?" Junaid ya xaro ido yace "Dariya kuma Ummi, ae ko mun yi magana me ma'ana, nine ma nayi maganan don shiru El-Ameen yayi" Ummi bata san lkcn da tayi murmushi tana kallonsu ba, ta girgixa kai tace "Ahaf ai magana ta lalace tunda kai kayi! Wato ku baxa ku yi ma kanku fada ba ko, babu me ba wani shawara cikin ku kan ya kamata ku ajiye iyali yanxu," Junaid yayi kasa da kai yace "Ina yi masa wallahi Ummi" harara ta xabga masa tace "Common keep quiet my frnd ai har kai" El-Ameen yayi murmushi shi ma yayi kasa da kai, Ummi tace "Toh gaskiya it's high time ku san me ku ke, don ku ba yara bane, and yhu guys ain't getting younger, ku yi ma kanku fada ku fito da mata kuyi aure abun ku, as a mother nake gaya maku haka, in ma baka son Iman din sae ka nemo wata very soon, kai ma Junaid kayi kokarin yin hakan kafin wata uku, I want to see my boys getting married soon, in kuma kun ban wuka da nama sae in nemo maku mata wallahi" a tare kamar sun hada baki suka ce "A'a Ummi" dariya tayi tana kallonsu, Junaid ya shafa kai yace "In'sha Allah Ummi xa muyi ynda kuke so" tace "Toh Allah yasa, ya bamu aron ran ganin bikin boys dinmu" dariya suka yi gaba daya, Ummi tace "Toh ku tashi ku tafi, Allah maku albarka" mikewa suka yi suka nufi dakin El-Ameen bayan sun amsa da Ameen, xama Junaid yayi gefen gado yana kallon El-Ameen dake kakrin kunna desktop dinsa yace "Baxa mu je can gidan ba?" Ba tare da El-Ameen ya kallesa ba yace "Kai ka tafi mana, kaga ni am busy" Junaid bae ce komai ba sae kallonsa da yake, shi kam sae danne dannensa yake ba tare da ya damu ba, Junaid ya mike yace "Ohk am off" El-Ameen yace "So early, to ka gaida Mumy" Junaid bae tanka sa ba ya fice, El-ameen ya bi sa da harara yace "You think kowa ma bai da aiki kamar ka sai na mahaukaciya yanxu" Ummi dake Palo har lkcn ta kalli junaid tace "Har ka fito?" Junaid ya dan yi murmushi yace "Dama sako na xo karba Ummi, sae gobe" tace "Toh Allah ya kiyaye, ka gayar min da Hajiyar ka" yace "Xata ji." Sannan ya fita.
鉁嶐煆�
*Haske Writers Association*馃挕
[16/10, 19:05] Hassan Atk: *Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
7.....
Fara ce sosai ba kadan ba don kamar ka latsa ta jini ya fito, dama ashe wahala ce ya maida kalanta baki, ko kadan bata da jiki sai tsayi, bakin gashin kanta ya rufe kusan rabin fuskarta sbda yanda tayi kwanciyar, d'an karamin bakinta me kalan baki da ja Junaid ya kalla yyi murmushi yace "Uhnn! Kamar me hankali koh? Da xata tashi ynxu duk sae mun yi bayani ryt?" murmushi El-ameen yyi ya mike yace "Yea! Exactly!" Juyawa yyi ya fice daga dakin Junaid ya bi sa da kallo sae gashi ya dawo da wasu alluran har uku, ya dawo gabanta ya durkusa, Junaid na ganin haka ya mike ya fita daga dakin, ya sakko palo ya dauki ledan abinci daya ya ba Mama, tayi masa godiya yyi murmushi kawae ya xauna, bayan kusan minti goma El-Ameen ya sakko falon ya xauna gefen junaid yace "Kana ji na, akwae drugs din da xa'a siya har biyar, kuma duk pack daya kusan dubu 40 ne kafin ayi diagnosing dinta...." Junaid yace "Ohk xan maka transfer ltr" El-Ameen ya mike ya dauki ledan abincin da ya rage da ruwa ya nufi sama, ajiye mata yyi bayan ya bude snn ya fito ya sa ma kofar key, ya dawo palo yana kallon Junaid yace "Let leave!" Mikewa Junaid yyi, El-Ameen ya kalli dattijuwar da ke xaune yace "Mama za mu tafi sae gobe, duk buge bugen da xata yi kar ki bude mata kofar" tace "Toh Allah ya tashe mu lfya, yayi maku albarka," duk suka amsa da Ameen suka fita palon. A bakin gate El-Ameen ya tsaya yana kallon Junaid yace "ka ba mai gadi kudi ya siyo ma tsohuwar abinci da safe ya kai mata ciki don am not coming here da safe" Junaid ya ciro dubu uku aljihunsa ya mika ma mai gadin snn suka fita, Suna isa gun motocin su El-Ameen yace "Gobe kuma foodstuffs xaka siya idan xaka xo" Junaid bae ce komae ba ya shige motarsa ya tada ya bar wajen, El-Ameen ya bi sa da kallo yana murmushi, snn shima ya shiga tasa motar. Karfe takwas da wani abu Junaid ya isa gida, bangarensa ya nufa yyi wanka snn ya dauro alwala ya fito yyi isha yana xaune kan darduma ya ji an bude kofar palonsa, bae motsa daga inda yake ba har aka bude kofar bedroom, ya daga kai don ganin waye, Mumy ce ta shigo dakin, yayi murmushi ganinta yace "Yanxu fa xan shigo d'a Mumy" ta xauna gefen gadonsa tace "Sae ynxu kake isha Junaid?" Yace "Mun hadu da traffic ne sosae a hanya Mumy" ta tabe baki ta mike tace "Toh taso mu je ka ci abinci" ba musu ya mike ya linke pray mat din ya ajiye ya bi bayanta, Mai aikinta ce ta dauko abincin nasa daga dinning ta ajiye nan tsakiyar lallausan rug din falon da ya ke xaune, Mumy ta sakko gefensa ta bude warmern dake dauke da Shinkafa fara ta dauki plate ta dibar masa iya yanda tasan xae cinye snn ta bude miya ta xuba masa k'adan a gefe don bae fiye son miya da yawa ba, sae cow meat da ta cika masa a abincin, spoon ya dauka yace "Thanks sweet mum" snn ya fara cin abincin ita kuma ta dauki wayarta da ke ring, ganin Abba ne yasa ta nufi daki. K'asa cin abincin Junaid yyi ya kuma rasa dalilin hakan, ya lumshe ido ya jinginar da kansa jikin kujera, ya kusa minti goma a hka sanin Mumy na fitowa sae ta sa shi ya cinye abincin yasa ya kira mai aikinta, yarinyar ta taho daga dakinta da sauri, ya dauki abincin ya mika mata yace "ina fatima?" Tace "Ta kwanta" yace "Ohk tafi daki ki ci na koshi" ba musu ta koma dakinta da abincin, juice ya diba ya shiga sha a hankali, a hka Mumy ta fito ta samesa tace "Har ka cinye?" Yace "Eh Mumy" ya ajiye cup din hannunsa yana lullumshe ido yace "Nafara jin bacci mumy" tace "Toh Allah ya tashe mu lfya, kayi alwala kafin ka kwanta, don't forget to pray also" ya mike yace "In'sha Allah mum" wayarsa ya dauka ya fita ya nufi side dinsa, sae da ya dauro alwala yyi shafa'i da wutr snn ya kwanta ya ja bargo. Washegari yana office yayi ma El-Ameen transfer din dubu dari da hamsin, yana barin office dama kasuwa ya shiga ya siyo food stuffs sannan ya wuce gidan El-Ameen, mai gadi ne ya shiga da kayan abincin palo, Junaid ya xauna bayan sun gaisa da mama yace "El-Ameen din ya xo ne mama" tace "Eh ya xo da safe, ya kuma xuwa daxu, bae dde da tafiya ba amma yace xae dawo" Junaid yace "Ohk, bacci take ne?" Mama tace "A'a gskya, sae dae yace kar a bude kofar makullin na jiki ma" Junaid yace "Tana cin abinci kuwa?" Girgixa kai tayi tace "Gskya ban sani ba don kifarwa take duka, bana gane ko ta ci ko bata ci ba" Shiru yyi bae kuma cewa komae ba, yana son ganinta amma shi gskya tsoro yake, dama El-Ameen na nan ne, can ya kalli agogo ya ga har biyar yayi, mikewa yyi yace "toh ni xan tafi mama, bbu matsala dae koh?" Tana murmushi tace "Babu komae wallahi" xae yi magana aka bude kofa El-Ameen ya shigo, ya d'an kyabe baki ganinsa, shi dae Junaid bin sa da kallo yayi har ya karaso cikin palon, ledan hannunsa na magunguna ya ajiye yace "Ba dae har xaka tafi ba, kuma kama duba mahaukaciyar taka kuwa?" Junaid ya dauke kai bae ce komae ba, El-Ameen yace "Ehh Lallai ma, wato ni xaka yi ta bari da wahala koh, daxu da safe ma sae da na xo nan kafin in tafi clinic nasan kai ko tashi kila baka yi ba lokacin" yana kai wa nan ya nufi sama, Junaid ya sauke ajiyar xuciya ya bi bayansa, El-Ameen ya bude kofar dakin da key ya tura kofar a hankali, tana xaune ta rakube waje daya bayan ta kuma cire labulayen dakin gaba daya kamar yanda ta saba, doguwar rigar kanti ne jikinta ja da ya haska farin fatar ta, duk ta birkita dogon gashinta kmr ba da safe Mama ta kuma daure mata ba tana bacci, kayan ma da gani ta kasa cire shi ne don duk ta yamutse shi jikinta, El-Ameen ya balla mata harara yace "Wai ke wace irin mutum ce, wllh kika sake cire min labule sae na gaura maki mari, baki da aiki sai barna" Junaid dae na d'aga bakin kofa yana leko dakin, El-Ameen ya kallesa yace "Da'alla matsoraci shigo baxa ta ma komai ba" kin shigowa junaid yayi yace "Nan ma ya isa" El-Ameen ya hade rae yace "Ohh wato ni ne ban san ciwon kai na ba da nake shigowa koh, sae in daina shigowa nima in dinga tsayawa daga bakin kofa in ga ta ynda xa ayi maganin" a hankali Junaid ya d'aga kafa ya shigo dakin yana kallonta sae shishshigewa jikin bango take a tsorace, El-Ameen ya kalli Junaid dake tsaye shi ma duk a tsoracen, Junaid bae ankara ba sae gani yyi El-Ameen ya fixgosa ya tura sa har sae da ya fada kanta, a tare suka kwala ihu daga shi har ita, El-Ameen ya dinga kyakyata dariya har da rike ciki, da kyar Junaid ya mike, ita ma ta yunkura ta mike, tsorata junaid yyi ya nufi bayi da sauri, ita kuma ta wawuri d'aya daga karafunan labulen dakin tayi kan El-Ameen dake dariya har lokcin, xaro ido yyi ya hadiye dariyarsa ganin haka, ya juya da sauri xae fita ae da hanxarinta ta bi bayansa, me Junaid xae ban da dariya, ya dinga kyalkyala dariya ya bi bayansu, har downstairs ta bi El-Ameen, mama na ganin hka ita ma tayi waje da gudu, El-Ameen ya dinga cewa "Junaid wllh ka xo ka riketa, junaiddd" Junaid ya durkusa nan stairs ya dinga dariya ganin yanda El-Ameen ya rude yana xaga palon, ita ko sae binsa take xata buga masa karfen, Hadiye dariyar Junaid yyi ganin El-Ameen ya shige kitchen ya sa key ya barsu su biyun a palon, ta dade tsaye bakin kofar kitchen din, kafin ta juyo tana bin ko ina na palon da kallo, k'asa motsi Junaid yyi daga inda yake xuciyarsa na bugawa, ta jefar da karfen hannunta ganin kofa a bude ta nufi kofar da sauri, Junaid bae san lkcn da ya nemi tsoron ya rasa ba ya bi bayanta cikin hanzari ya riga ta isowa kofar ya rufe gam, juyawa tayi tana kallonsa tana maida numfashi, sae kuma ta fasa wani ihu tayi kansa ta fixgosa, rungumeta yyi ya riketa gam, ta dinga fixge fixge ya ki saketa, Sosae suka jigata daga ita har shi, don kin saketa yyi, ita kuma bata fasa kokuwa da shi ba, daga karshe tayi lamo jikinsa bata sake yunkurin kwatar kanta ba, a hankali ya saketa ta sulale nan kasan palon, hawaye yaga kwance fuskarta, jikinsa yyi sanyi ya durkusa gabanta yana kallonta.
*Haske Writers Association*
[16/10, 19:05] Hassan Atk: 鈿� *Captain_Ahmad Junaid*鈿�
_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�
9.....
Gida Junaid ya nufa, yana gama parkin ya fito ya shiga bangaren Mumy ya gaida ta sannan ya tafi nasa part din, kwanciya yayi Palo ya lumshe ido, ko minti goma bae yi da kwanciya ba wayarsa ya soma ringing, daukar wayar yayi yana kallon mai kiran nasa ya ga abokinsa ne Faisal, d'agawa yayi yace "Yane Faisal!" Faisal yace "Are yhu at home capt?" Junaid yace "Yea ina gida" Faisal yace "Ohk gani nan shigowa" daga haka ya katse wayar, bayan minti takwas Faisal ya shigo palon, Junaid ya mike xaune yana kallonsa yace "Daga ina haka" Faisal ya xauna yace "Gida mana tun da kai baka neman mutane sae El-Ameen" Junaid yayi dariya yace "Kai haba ko ranan da daddare ban kira ka ba" Faisal dake kokarin kira a wayarsa yace "Really!" kallonsa kawae junaid yayi yana murmushi, faisal yace "Hello Muhibba gani gidan ku part din Captain" daga haka ya katse wayar, Junaid ya hade rae yace "idan gun ta ka xo ba sae ka je can bangarensu ba xaka wani kira min ita nan" faisal yace "Chill guy sako xan bata" ko rufe baki faisal bae yi ba sae ga ta ta shigo, murmushi dauke fuskarta tace "ashe da gaske kake" hade rae sosai Junaid yayi ya jawo waya yana dannawa, faisal ya ciro waya aljihunsa ya mika mata yace "Gashi nan na bada an gyara maki" ta wara ido ta karbi wayar tace "Waow am so happy ya faisal, kuma nawa?" yace "No don't bother" tace "Toh na gode kwarai, ya salima fa?" Yace "Tana gida," kallon Junaid tayi tace "Sannu ya Ahmad" ba tare da ya kalleta ba yace "Yauwa!" Tayi niyyan xama palon amma sanin junaid sae ya iya gwaleta yasa ta juya kawae ta fita tana tunanin yaushe ne wannan ranan da junaid xae fara sonta kamar yanda Hajiya ke yawan assure dinta. Faisal yace "Fatee fah?" Junaid yace "Oho!" Sae bayan Magrib faisal ya bar gidan bayan sun shiga ya yi ma Mumy sallama ya kuma shiga part din Hajja ya gaidata, a tare suka fita bayan Junaid ya ce ma Mumy bari ya rakasa, sai dai rakiyar iya bakin gate yyi sa, yana ganin tafiyar Faisal ya nufi titi don yasan in har yace ma Mumy fita xae yi sai ya amsa query, kalle kallen abun hawa ya shiga yi ya rasa yanda xae ce su tsaya, can dae wani mai adai daita ya tsaya yana tambayarsa ina xa shi, shiga kawae Junaid yayi yana kallon mai adai daitan yace "Mu je" sae da suka dan yi nisa kafin ya gaya masa inda xa shi, suna isa junaid ya sauko ya fara dube duben kudi a aljihu, dubu daya kawae ya gani aljihun nasa, mika masa yayi a hankali yana kallon mai adai daitan yace "Kayi hakuri malam ban san ban fito da kudi ba, dubu daya ce a hannu na nagani" dariya mai adai daitan yayi ya karbi kudin, ko ba a gaya masa ba yasan junaid sabon shiga ne a tricycle, canjin dari shidda ya mika masa yace "Ga canjin ka bawan Allah" dan xaro ido Junaid yayi ya karbi kudin yace "Har canji gare ni? Toh na gode" mai adai daitan yayi murmushi ya ja machine dinsa ya wuce, Junaid yayi mamakin ganin motar El-Ameen a parke waje, shi da yace baxae xo ba kuma, tabe baki yayi ya shiga gidan, mama ce xaune Palo ita kadae Junaid ya gaisheta da ladabi, ta amsa tana murmushi ta tambayesa ya aiki, Junaid yace "Lfya mama, ya kamata a siyo maki tv ya dinga debe maki kewa koh" dariya tayi tace "lallai kam" Junaid yace "El-Ameen ya xo ne" mama tace "Eh yana sama" mikewa junaid yayi sae dae duk bae da kuxari ya nufi saman, a hankali ya tura kofar dakin yana kallon ciki, xaune ya ga El-Ameen gabanta ya tankwashe kafa plate din abinci a tsakiyarsu hannunsa rike da spoon ga wayar rechargeable dake gefensa, ita ma xaunen take ya daure mata hannu sae shisshigewa jikin bango take hawaye kwance fuskarta, duk gashin kanta a birkice yake, Junaid ya rungume hannayensa yana kallon El-Ameen, El-Ameen yace "Uhnn! yau baka kwanta da wuri ba kenan mumy's boy" junaid dae bae tanka sa ba ya maida kallonsa kanta ganin yanda take kokuwa da bango kamar xata shige ciki, yunkura tayi xata mike El-Ameen ya daka mata tsawa ya dauki wayar rechargeable din gefensa ta koma da sauri ta xauna, shinkafar ya diba ya kai mata baki, ta dinga kauda kai tana boye fuska, tsawa ya kuma yi mata ya juyo da kanta ya matse bakinta har sai da ta bude ya xuba mata abincin da sauri, murmushi Junaid yayi ganin yanda jikinta ke rawa tana hadiye abincin ba tare da ta tauna ba, da ganinta kasan ba karamar matsoraciya bace, Haka El-Ameen ya dinga mata har sae da ta ci kusan rabin abincin sannan ya mike yana kallon Junaid yace "Bata cin abinci shi yasa na mata haka," Junaid ya buda manyan idonsa yace "So yhu do really care ashe haka?" El-Ameen yayi dariya yace "Darajar ka take ci ae" Junaid bae kuma cewa komae ba sae kallonta yake duk da ba ganin fuskarta yake ba don dogon gashin kanta ya rufe fuskar, wasu allurai biyu El-Ameen ya fiddo ya shiga hadawa, ae tana hango alluran ta mike tayi kofa da gudu, fixgota El-Ameen yayi don shi Junaid hanya ma ya bata da sauri, El-ameen ya jefa ta kan gado, yana hararan Junaid yace "kaji d'an iskan hanya ma ya bata" Junaid yayi dariya yana shafa kai, ta fasa wani uban ihu da ya tsorata Junaid xata mike El-ameen ya hau gadon ya rike ta yana mata wani mugun kallo yace "Keehh", Ribbon dinta da ke kan gadon ya dauka ya shiga daure mata gashin kanta, yana kallon fuskarta yace "Kika kuskura kika sake cire ribbon dinnan sae na gaggaura maki mari" banda rawa babu abinda jikinta yake tana kallonsa, murmushi yayi ya kwantar da ita a hankali ya kwance daurin hannunta sannan ya juya yana kallon Junaid yace "Miko min alluran ko shi ma tsoron sa kake" Junaid bae ce komae ba ya dauki alluran ya mika masa, juyar da ita El-Ameen yayi xae mata alluran Junaid ya juya ya fita dakin, El-Ameen ya bi sa da kallo sannan ya tabe baki yayi mata alluran, tsam