Showing 27001 words to 30000 words out of 33792 words

Chapter 10 - YAR MAKAFI 1 to END by Nabilancy Love .txt

25 Dec 2024

3082

jigun iyayan Aminatu sunsan Komai, bude idonta tai ahankali Tace" Ina Aminullah Dan Allah, Nan ma'aruf ya tsareta da ido be gane me take cewa ba, Mamanta ne tazo kusa da ita tace" Aminullah, Allah yai mai rasuwa, wani rintsa idonta tayi hawaye suka fara zubu mata, da ita kadan tasan me take ayyanawa a zuciyar ta


Ma'aruf ne Yace" Aminatu ganin iyaye sai yasa be ambato sunan da yake kirantaba zinariya ko Sweet baby, Yace" Dan Allah kiyi hakuri, though bansan ya kuke dashi ba kiyi hakuri, Nasan dawainiyar da yakeyi da iyayanki kiyi hakuri, Allah yafi mu sonshi, Nan ta kalle mamanta, Mamanta ta kashe mata ido alamar ta hakura karta nuna komai,


Nan ta Dan tashi daga kwanchan, Da jin kina a jikin gadon, nan mummy tai ta mata sannu, kowa yana ta mata sannu, ana cikin haka saiga murjantu ta fado


Wani kallo Aminatu tai mata da saida yan hanjinta suka kada, Murnajatu, ta gaishe da kowa da kowa tai musu ya hakuri, Kamar Aminatu bazata amsa ba se Kuma tace" Alhamdulillah, Nan murjanatu tace" Su mummy kui tafiyarku zan tsaya da ita nai jinyarta kuje Ku huta,


Sukace" kai amma mungode, Allah sa miki albarka, Murjanatu tace" Ameen Ameen


<> <> <> <> <> <> <> <> <> <> <> <>
Bangaren Lubna kuwa, shuru shuru har dare ma'aruf be dawo ba, gashi a dakinta yake, Ta hada mai abinci da juice me dadin gaske, tasha kwalliya kamar Sabuwar amarya, Ga ko Ina na dakin Kamshi yakeyi, har 9 taji shuru, kasa hakura tayi tazo har part din Aminatu ta kwankwas taji ko Ma'aruf na part din, nan taji shuru, zama a kofar part din tayi, Hannu tasa akai tana kuka wannan wani irin tsane Ma'aruf ke mata, da taga bame bata amsawa daki ta wuce ta dakko wayanta


Kira tayi ringing 1, 2 yai picking, Yace" Lubna, tace" my Dr kana inane najika shuru, Yace" eyyah I wanted to call you bansa ma natsuwa ba, Aminatu ne ba lafiya ta fadi dazu a toilet, So I'm inanan zuwa anjuma, Eyyah tace duk da bason Aminatun take ba seda ta tausaya mata sannan ta kashe wayan tace kuma mtswww Allah ya Kara, se tauyemun hakkina ake akan wannan *YAR MAKAFI*


Ma'aruf yana gama waya Aminatu ta kalleshi tace" ka tafi gida Ga murjanatu nan zata kula dani, Yace" kin tabbata? Murja da katsalandan tace" yap, Aiko yai tafiyarshi, Yace" idan akwai wani Abu a kirashi




Bayan ya fitane, Aminatu ta kalle murja tace" meye ya kawo ki? ba mun raba jaha ba?


Murjanatu tace Dan Allah kiyi hakuri, Wallahi nima mutuwar Aminullah dinnan ya sa na dawo hanya, na gane lalle duniya bata da tabbas, nima INA rokon Allah ya yafemun duk laifukan da nayi, Kuma Nima ki sani a addu'a Allah ya fito min da miji na gari da sauran yan'uwa da basui aure ba, Allah ya hada kowa da miji na gari


Aminatu tace" *Ameen* yanzu naji magana, Nan dai Suka kamo wata hirar, Aminatu tace" hirafa ba Namu bane, Mui ta istigfari da hailala da salatin monzon Allah har bacci ya kwashe mu, Murja natu tace" haka ne


Washe gari, Da safe da ma'aruf yazo, a dai dai lokacin da Aminatu tai amai, yana gani zuciyarshi ta bashi wani Abu, Anya ba ciki gareta ba Dan Sing of pregnant ne morning vomiting,


Nan ko ya kira Nurse, aka mata PT test, Nan take ya muna Positive+ Alamun Ciki ne, Nurse din tace musu congrats, Ma'aruf ya rungumo matarshi, kwanansu biyu aka sallamesu


Bayan An sallamesu ne, Ma'aruf Yace tai shuru Kar ta yarda lubna tasan tana da ciki, Dan sunsan halinta zata Iya zuwa tai asiri, duk da yanzu Alhamdulillah, ba abun Da zai Iya kamasu da yardan Allah


Lubna ta shugo tai mata Sannu da jiki bekai Zuciya ba, Ganin yanda dakin ya tsaru yafi nata nan ma hankalin ta ya tashi, Ta da koma Daki Maminta ta kira take Sanar da ita, tace karta damu, Lubna tace" ke mamin nan Kullun na kira sai kice karna damu kinsan bakin cikin da nake kuwa? maminta tace" ke baki da kunya ko? Nan ta fara wasu maganganu ta kashe waya, Maminta tai tsaki itama


°°°°°°°°°°°°
Bayan Sati daya, Ma'aruf na lura da Aminatu duk rai Dan baki ta rame, daga ganta kasan akwai abun dake damunta, Ma'aruf ne Yace tazo suje bedroom akwai maganar Da zai mata, tana tafe yana binta a baya, suka zauna ya janyota jikinshi Yace" Zinariya, what's wrong with you, Duk kin bi kin chanza ko abinci bakya ci sosai remember I'm your husband, be kamata kina boye mun Abu ba, Ta nunfasa tace Hakane, wlhi rasuwar Aminullah dinnan yake damuwa, Yaji kishi sosai ya dai daure Yace" ya kuke dashi?
Ta share hawaye tace" he was my 1st love, tun kan mu hadu da kai komai yake mana, Dukda Beda hali, amma ta dalilinshi na sama rayuwa me kyau, yana karatu lokacin a ABU zariya sai kai kuma ka kunno kai, Kasan Zuciya Murjanatu ta ziga ne wai Ga kai me kudi mezanyi da Aminullah, Lokacin da Kai aure baka kulani tayo Neman aure na namai wulakanci,


Yaje wajen Murja ko zata shawo mai kaina itama nan tamai tatas, Shine tunda ya tafi zariya wajen uncle dinshi bansake ganinshi ba, Aminullah ya soni kamar me, ya share mata hawaye,

Sai da Ga baya yana zuwa yana wa Su mama ihsani, Yakaita aka gyara mata ido yanzu haka ma ya gyara mana gida, shine a hanyarshi ta komawa yai accident taan gama fada Aminatu ta rushe da kuka a jikinshi tace" na cuceshi Amii ka yafemun


Ma'aruf ya tausaya mata sosai, Dakyar ya shawo kanta Yace" yanzu tashi ta kare, Addua za'ai mai kawai, sannan ko da taga bata aureshi ba ,haka Allah yaso, matar mutun kabarinshi, kuma wani beta auran matar wani, tace" hakane, Yace" ki dena kuka, Addua"a zaki mai kuma zan bada kudi asai butuci da charbi, da a fanso al'qur'anai akai masallatai da sunanshi, ladan wqjen shi zai kai, Nan ta kalle Ma'aruf tace" kai amma nagode. Nagide, Yace" Ba komai Allah ya gafarta mai tace" Ameen tun daga ranar ta sake jikinta amma Kullun cikin Addua ta kema Aminullah


*Bayan Watanni kamar uku*


Akwana atashi babu wuya agun Allah yau Aminatu nada wata biyar agidanta tana samun tarayraya agun mijinta yayinda take ganin soyayya agun iyayan mijinta domin kuwa har xuwar mata momy keyi part dinta kawai suyi hira takoma gida batare da taje sashen lubna ba sometime lubnar naganin fitar momyn a mota driver yatafi mayarta gida takanji haushi sosai naganin fifikon da akai musu tsakaninta da *yar makafi* tasan kuma dan a cisguna matane dan haka bata taba nunawa afuskaba takan dai hadiye bakin cikin ne amma maminta nayawan tausarta akan kada ta damu inta haihi dole zasu sosata don zasu shirya asiri sosai wanda baxai karyeba


Alokacin cikinta na wata bakwai ita kuma Aminatu cikinta yana wata hudu amma lubna batasan dashiba


Dayake ita doguwa ce sai cikin yabi jikinta takara yin mulmul ta gyagije tayi kyau da yar kiba


Cikin Aminatu nashan kulawa gun ma,aruf don har an fara zuwa awonsa




°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°


Sosai yake tarairayar cikin nan bayason yaga tana aikin wahala in yana part dinta shike mata wanka harda wankin undis dinta dasu bra abinci ma abaki yake bata itakon tayita yi masa shagawaba inta narke ajikinsa tayi lamo tamkar wata mage


Dayake lubna ba.a tare suke ba shiyasa batasan irin wainar da ake toyawa akan cikin aminatun ba


Da ace zatasan koda kadan daga ciki tabbas da ansha rigima don dole zatace ana nuna mata bambanci


Tunda akai scanning aka gano tagwaye ne maza acikin Aminatu sai abin yafi na da


Tamkar wata baby haka yamaida don kulawa da lele


Lubna da Aminatu, ya basu dubu dari na kayan baby, nasu kuma hamsin hamsin amma ita Aminatu dari biyu yabata tunda twins ne


Account ya bude mata ta xubesu aciki


Yakan yawan kaita gidan iyayanta amma sai awani karo tayi kusan wata bataje ba


Haka dai rayuwarsu taci gaba da wakana.....bakuga Love din da ma'aruf yake nunama Aminatu ba tamkar zai mai data ciki idan suna tare


Lubna kuwa ta zabga asiri amma INA duk a banza saboda Kadarinta yanzu ya Riga ya karyeeee








*Muje zuwa masoyan Aminatu*
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗
*'YAR MAKAFI...*
♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗




```written by.....```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUV💘*




*Neenah cool😍 and deejeh Queen😍*
_Wannan page din nakune,.. Awwn aci gaba da gashi Allah ya Kara Basira_, readers Ku nema book din *NIEMATULLAH da SIRRIN AL_AJAB* _na Neenah cool da deejah queen domin sunzo muku da salo daban...._❣❣❣❣


*PAGE....100-105*




RANAR wata Talata Lubna ta dawo daga awo gajiye ta shigo gidan domin tabiya kasuwa tayi siyayya


Tashigo cikin gidan kenan tahango Aminatu tafito daga part dinta


Ta tsaya jiran karasowar Aminatun tana kare mata kallo daga nesa


Tabbas ta diga ayar tambaya akan Amina da alamar cikine da ita dan gashinan ya dan turo


Doguwar riga tasaka takamata daga saman kirjinta takama hips dinta daya kara fitowa ga breast dinta sunfirfito suncika tantsan


Kyan da Aminatu takara shiya furgita lubna domin ita ayanzu bata son takalli madubi ma sbd yanda halittunta suka canxa tayi baki dama mai ne ga hancinta yayi fos ya kara girma bakinta yakara tudu lebe yafito sambal


Duk ta kumbura na masu ciki


Lallai tasan karamin ciki aminatu kedashi tunda tayi tsulelen kyau fiye da yanda taxo gidan


Wani kishi da tsanar aminar yakaru aranta


Aminatu tahau murmushi data kataso kusada lubnan tace mata


"Sannu da dawowa uwar gida.


"Yawwa amarya kin futo shan iska ne.?


Aminatu tace "walh wai me gadi zanbaiwa sautun inyaji duriyar me farin yalo yasiya min.


Murmushin yake lubna tayi takuma gaskata xatonta tave " ayya aidana san abukatarsa kike dana taho muki dashi daga kasuwa


" laaa bama komi nagode za.a samu ai tunda lokacin sane kuma sukan wuce akai akai.


Nan lubnar ta wuce kawai tana ta kallon Aminar tanajin wani abu cikin ranta me daci data kasa hadiya


Tana shiga dakinta ta zube akafet ta rafka tagumi


Ashe duk murnar datakeyi akan itace zata ajiye tarihin baby agidan ashe aminar ma nakan hanya azatonta ko aminar bame haihuwa bace duk da watan aminar na shida kenan agidan


Waya tasaka tayi kiran maminta


Mami na dagawa tace " to uwar yan korafi yau kuma meya faru?


"Meye ma bai faruba mami un expected naga waccan *"Yar makafin* da ciki walh mami bakiji yanda zuciya ta ke tafasa ba kamar in mutu nakeji


Mami tayi tsaki tace " waike lubna kishi haukane kina son ki kashe kanki abanxa alhalin wanda kk dominsa bakida fada agunsa har yanzun meye ne abin damuwa dan kinganta da ciki yanda fa yake mijinki itanma mijintane kuma abinda baki saniba ayanzun haka Yarinyar nan ba *YAR MAKAFI* bace domin iyayanta sunbar makanta inada labarin ma,aruf yayi ruwa yayi tsaki wajen gani buduwar idanunsu yakashe kudi sosai yakaisu asibiti anyi musu aikin ido yanzun suna gani radau dan haka kicire ma dawuwa aranki kiyi ta kanki ki kawarta daga sabgarki kawai.


Lubna tace " yanzu mami kenan goyan bayanta kkyi?


"Ba goyan bayanta nakeba aname xan goyi bayan wacce taxama makiyiyar "yata kawai dai so nake kicireta aranki kada kisaka damuwarta ta dameki In Allah yasaukeki lfy sai musan abinyi domin baxamu bari tahaihu ba zamu saka akashe dan ko yr tunkan taxo duniya sannan daga baya ita kuma muyi maya kurciya dan ki mallake gidan da me gidan da iyayan nasa koya kk gani?


Ajiyar xuciya taja tareda cewa " to mami naji nagode xanyi yanda kk ce sai anjima.


Tana kashe wayar tahau tunanin maganar mami datace mata iyayan aminatu sun warke daga makanta


Tayi mamaki ashe yaya ma,aruf shiya kashe musu kudi akai musu aiki amma kwata kwata bata saniba lallai namiji dan kunama ne


Yakuma cika munafuki duk wani abu na Aminatu baya tinkararta dashi ga cikima da aminar kedashi har yafito amma sai yau taji to asirinsu ya tonu kuma xatayi maganin abun






°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°


Sati biyu bayan faruwar wanna lamari Aminatu tana dakinta tabaje agado tana bacci ckn kayan baccinta tsalele ga dan cikinta kurbibi ya turo


Itace da girki ta ajiye komi need a dining tagaji da jiran me gida shine tagudo daki bacci yai awon gaba da ita don tagaji da yin kallon


Bai taba kaiwa dare har goma irin hakaba


Atsammanin ta ko gidan Dr lurwan yatafi yashantake acan duk da bai taba mata hakan aranar girkin taba sai ana lubna yake hakan


Can cikin baccinta taji wayarta dake gefen stool din gado tadau tsuwwa


Ta bude ido da sauri takai hannu ta dauka takara akunne taji muryar habibi ne


"My habibi ina kashiga ne _i miss u, pls come to me my husband_


yace mata " pls sorry my zinariya bangaya mk tun wuriba muna hospital da lubna ne naso gaya mk na sha,afa yanxu ma akai min albishir ta haihu mace kena fara gayawa sannan yanzun zan gayawa momy


Ta tashi zaune da sauri ckn murna tace " _oh my god i am very happy my habibi_ Allah yaraya yasa cikon musulinci ce.


Yace "Amin. Nagode zamu dawo gida nan da 11 in angama gyara babyn da uwar.


nan sukai sallama tana kashe wayar taji "yan cikinta sun motsa


Takai hannu tashafa tana murmushi don tasan wannan murna kenan suke yi na xuwan yayarsu duniya


Itanma tayi murna domin itakam bata kullatar lubna tana kuma son su zauna lafiya itace dai lubnan mara son azauna qalau


Tunda cikinta yai wata hudu twins suka fara motsi amma motsin na yau na daban ne shiyasa ta raya cewa motsin taya murna sukeyi


Da ma,aruf yadawo yashigo yatararya har kan gadon yajata jikinsa yakai mata hot kisa yace " Allah yakawo ranar da kema zaki haihu ki huta sweet babyna


Ta narke masa " habibi haihuwa da wahala ko? Kamar zatayi kuka


Ya zaro ido da dariyarsa yace " huui! Babyna ina zan sani nida ba tayata nakuda nayiba


Kya tambayeta inkinje ganin babyn


Tace " tashi muje yanzun nagano "yata.


Yace " no!no! Not now abari sai gobe don yanzun its my time


Yakamo hannunta yace " lets go pls dear i am very hungry


Tace " to habibi muje kafara watsa ruwa tukunna ko?


Yace " dadai anfara bani abincin zaifi kinga inna koahi sai inwatsa ruwa daga nan ba sai gado ba.


Tayi dry tace " angama ranka ya dade.


<><><><><><><><><>




Momy tazo barka sau daya bata sake dawo waba


Balle dataga jaririya baka kirin me kama da lubna sai tahau cewa wanna yar ba gida tayo ba


Aiko dai lubna ta kullaci momy sosai bayama da mami taxo ta shirya karya da gaskiya ta gaya mata akan maganar


Maminta tahau taxauna ko gidan momy batajeba tana gidan yarta suna qulle qulensu na tsiya


Aminatu takan shigar mata su gaisa suyi yar hira tadawo sashinta


Wani xubinta bata ganin fuska da uwar ta taxoma kallon banxa take samu agunsa saita dauke kafa


Zainab din Dr lurwan ma dama bataxo ba sbd basa shiri da lubnar tadai ce sai ranar suna zataxo


Rigima sosai ta sarke atsakanin ma,aruf da lubna kan cewa ita dole sai anyi partyn suna a hotel kuma saniya takeso yayanka ba tinkiyaba


Shiko yace tabbas baxata masa doleba tinkiyoyi biyu yasiya kuma suna ba a inda za.ayiba inba acikin gidansa ba saidai in tahada kayanta tabar masa gida


To dama ko akan sunan da za,a rada wa babyn sun so suyi yaja taja dole yabar mata


Yaso yasaka sunan momy tunda yaga a scainiing Aminatu duk maxa zata haifa balle yasaka mata


Shikuma yana son yaga yafara da sunan mahaifiyarsa


Dole dayaga abin xai xama rigima aji kansu yabar mata sunan datake so na maminta Hauwa,u wai baby jeedah za,ace mata


Koda momy taji yanda sukaima dadin hakan taji tace ita dama yanda bata kaunar lubna to baxataso taga sunanta adakin taba yabari kawai in Allah yayi asaka nan gaba adakin Aminatu inhar ba haihuwa ce ta tsayaba tasan wataran xata haifi macen itama




To tunda taji yace mata inhar tadage akan ayi suna ahotel to saidai tabar gida


Saita kufulu ta gayawa maminta wacce ke zaune agidan anware mata daki


Dayake mamin nada kawaye akano shiyasa itanma takeson ayi suna ahotel din don sun shiryi karya itanma lubna duk kawayenta yan karya ne


Mami dakanta ta sameshi tace masa yabari ayi sunan ahotel tunda bada kudinsa zasuyi ba


Nan yarufe ido yace ga fili game doki ai tunda dai yagindaya sharadi yananna kan bakansa inhar lubna tafuta dasunan zuwa hotel partyn suna to abakin auransa


Ran mami yabaci ganin yarainata agabanta yagaya mata hakan


Ta nunasa da yatsa tace " agaban ma,aruf dama bakada kunya yaushe kaxama haka donka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login