Showing 15001 words to 18000 words out of 33792 words

Chapter 6 - YAR MAKAFI 1 to END by Nabilancy Love .txt

25 Dec 2024

3083

yakasa katabus saima rarrashi harda cewa "barima kiga nafara daukar matakin


Yakira dady awaya yarattaba masa abinda yafaru


Dady yace " yaushe rabon daka kirani ma,aruf wato sai yau sbd anbatawa matarka rai shine yau harda kawomin karar momynka ayau lallai abu yabaci babana natabbata lubna ba haka tabarkaba dan bana garine amma da zarar nadawo zansa ayi maka wani taimakon tunda naga kafara xautuwa yau kaine dakai karar momynka guna....


Da sauri lubna ta warce wayar ta kashe dif! Domin a handsfree take taji komi takuma gane nufin dadyn


Shiko dady cixar yatsa yayi yana fadin "lallai xatona yatabbata yau babana ne ke kashemin waya sbd bangoyi da bayan abinda akayiwa matarsaba hakika yakamata yai axama yadawo koya saka ayiwa ma,aruf addu,a akan lamuransa don abin yafara bashi tsoro






<>¡>¡>¡>¡>>¡>¡>¡>¡>


Momy tana zuwa gida ta yarda gyale tafada kan doguwar kujera tana kukan bakin ciki da nadama


Ayau tun ba,aje koina ba tayi dana sanin wannan hadin bata zaci lubna zata iya yi mata hakanba


Wayarta tayi ruri da sauri ta daga saitaga hjy Hauwa,u ce kanwarta mahaifiyar lubna


Ta xaci abin arxikine to ashe bugowa tayi taji dalilin daya saka momyn ta marar mata " ya


Momy kasa magana tayi don tsananin.mamaki ganin yanda kanwarta taringa xazxaga mata rashin mutunci harda fadin itafa yarta ba jaka bace da za.a ringa jibgarta me tayi da harma ayi mata gori ga mari ga tsinka jka.


Cilli mimy tayi da wayar ta tarwatse domin bataga amfanin saurarar maganar hjy hawwaba don saisuyi uwar watsi


Dama saida dady yasha fada mata hakan xata iya faruwa domin xumunci yakam baci tahanyar auren hadi gashi tun ba,aje koinaba yabace abinda yake jiye mata knn


Taringa kukan xuci tana cixon yatsa takuma sha alwashin saita koma tayi gu. Mallam ankarya sihirin


To abinda bata saniba ita lubna komawa tayi daga baya takara kudi akai aka bata wasu kalolin mallakar masu xafi dayafi nafarko domin lubna da gaske takeyi....














*Auntyn S &S da Fresh Ummiey...muna sonku*
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗
*'YAR MAKAFI...*
♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗




```written by.....```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUV💘*




*♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*


_Dedicated to Zauren Ummiey Xeey and taskar Nabilancy_ you're Guy's are amazing domin muna ganin soyayya😍😍❤❤




*PAGE 65-70*


Lubna ta zage ta dage wajen ganin ta mallaki Dr ma,aruf ta koina ta yanda duk abinda zaiyi na kankin kansama sai yai shawara da ita inhar abin bai mataba hanawa take kuma dole yahanu


Account ta bude sabo tana shakeshi da kudi na ganin irin yanda ma,aruf ke jikata da nera


takan yawan turawa mahaifiyarta kudi dama itake dorata akai ayanzun


Hatta malaminta tana shaka masa nera koba aiki xai mataba saita ziyarceshi ta bashi makudai


Dr ma,aruf rayuwar kawai yake amma ankarkatar masa da hankali


Momy tashiga damuwa sosai naganin danta baya xuwa inda take ga dady baya gari


Takanyi kuka ita kadai ta goge hawayenta takanyi nadama mara adadi




Takira Dr lurwan abokinsa awaya yaxo har gida ta fada masa damuwarta da halin da ake ciki


Cixar yatsa yayi sosai najin abinda momyn tayi tun afarkon auren


Yace " zancen gaskiya momy ke kk bata abin kuma ke kk janyo masa koma mene duk halin da ma,aruf yake ciki kece yanzu gashi kinfishi shiga damuwa nasan shima dan babu yanda zaiyine amma zan samo mafita


Malamai yakamata mubaza ayita addu,a akan Allah yakarya kadarin


Baxamu zuba ido yana cutuwa ba domin lamarin na lubna babba ne


Momy tahau goge hawaye tana fadin " aini abin ma yadaina bani mamaki domin yafi karfin tunani na lubna taci amanar zumunci ban zaci xatayi min hakan ba ga mahaifiyarta ma tabi bayanta tadaina zumuncin dani akan naiwa yarta hukunci taji haushina harda bugomin waya tana cimin xarafi bakaji ba lurwan abin babu dadifa


Dr lurwan ya girgixa kansa yace " kayya amma abin ba dadin ji momy hakuri zakiyi kada kisa abin aranki yaxo yai mk illa ki kwantar da hankalinki Allah zai shige mana gaba zakiga tamkar ba,ai ba ya wuce kedai kitayashi da addu,a


Momy tace " to lurwan naji nagode Allah yabar zaman tare.


Yace " amin. Nan yai mata sallama yatafi


<><><><><><><><><>


Aminatu ce zaune jigun tayi tagumi hannu bibbuyu abin duniya yai mata yawa komi yatsaya mata cak


Dr ma,aruf yaki dawowa gareta koda wasa bai taba kirantaba tunda yai aure gashi harta gaji da kaiwa malamin tsubbu kudinta to inama kudin suke komi yakare mata dan abinda ke ajiye tayi dabara tasiya musu kayan abinci sai sauran kayan da suka rage mata lesika swiss kala biyu ta saidasu dubu ashirin ashirin faduwar dubu goma ta samu tabaiwa mahaifinta kudin yana juyawa domin danyen kayan miya yake kasawa abakin titi gwalgwaji dayake yanzun yana gani da idanu daya dayan kuma dishi dishi yake gani sai yake saka glass wasu ma sai anfada musu zasu sani ba,a ganewa akwai yaron dayake tayashi zama agurin


To rufin asirin da suka samu knn ta wannan bangaren don batajin ko sun rasa komi su dawo yin bara ayanzu tagane ba ajinta bane


Hawayene yaxubo akuncinta tasa bayan hannunta ta goge tana tuna Aminullah daya dawo daga karatunsa yagama yai final yaxo mata da murnarsa amma bata tareshi da farin cikiba asalima aranar tayi masa korar kare ta rufe idanu tace masa itafa ayanzu baya gabanta yanemi wata asalima Aure da soyayyar sun fice mata arai gara ma yabarta ta huta ya saurara mata kada yasake nufota


Aranar Aminullah yashiga matuqar damuwa kansa ya kulle don kasa fahimtarta yayi tunda yasan dai ba fada sukai ba kafin yatafi


Don haka yasami murjanatu ko zaiji wata maganar daga bakinta


Abinda murjan tayi masa saida yagwammace kida da karatu domin itanma rufe idonta tayi taringa masa zazzaga dama ba qaunarsa take da aminann ba


Harce masa tayi indai kai ba maye bane to yakamata karabu da aminatu tunda yanzu dai tace batayi gara kaje can gaba kanemi tsararka kaima inka duba ai xaka gane cewar miyar ba kalar tuwon bace.


Kai ranar aminullah yaga takaici da bakin ciki domin baisan yanaiwa amina so me yawa ba sai da yaga idanunsa sun kekeshe kasa dan dai bacci barawone amma baisan zai iya runtsawaba aranar


Yayi zaton ko wasu sabbin samari ne masu hali ke hurewa aminar kunne saikuma yaga sabanin hakan yakan kewayo da dare yazauna nesa dagidan yaga ko zaiga me mota yaxo xance gunta sai yaga babu me zuwa gun aminar


Kai ko da rana yasha zuwa yalabe anesa yaga ko suna futa yawo da murjane amma sai yaga duk ba hakan bane zarginsa dai bai tabbata ba


Don hakan saiya yankewa kansa hukuncin barin garin kano yakoma gurin wani kawunsa da zama acan zariya


Zaman doke yaringayi badan yaso hakanba tunda bakowa yasaniba kuma xuciyarsa na kano gun Aminatu


Haka yaita hakuri harya fara sabo yasami aboki wanda ke alayin suka kulla abota ataikaice ma baban abokin nasa dayai ne yasama masa aiki ama,aikatarsu yafara xuwa kuma da taimakon Allah sai Allah yafara buda masa don awata guda saigashi yasai lipan sabo gadagau






Murjanatu tashigo gidan tanata kwada sallama taji shiru


Maman aminatu nacan daka tana bacci


Itako amina ta lula atunani


Murjan ta tako ahankali taxauna agefenta ta cire mata tagumin data xabga


Suka kalli juna ahankali aminar tahau goge kwallar dake malala akuncinta


Murjanatu tace " haba Aminatu wannan meye kuma hakan saikace wata me babbar matsala wacce baxata yankeba zaki saka kanki adamuwa haba kawata komifa yakusa xuwar mana karshe.


aminatu tace " kayya murja aidole nayi kuka tunda damuwar da nake ciki takasa yayewa banga kuma ranar da xatazo karshenba kullum kwanakin ja suke yi amma shiru dr ma,aruf ko waigen baya bayayi alhalin malam yace zai dawo gareni nan ba dadewa ba to waishinma sai yaushe?




Murjanatu tace " ki kara hakuri kawata yanzun ma nazo mk da labarin wani malami wanda aikinsa keda ban mamaki domin aranar daka aikata abinda yasaka zakaga aiki da cikawa.... " aiko ba indaxanje domin banida abinda xan bashi gara ma kibarni da takaicin wanda na barnatar abaya.


Murja tace " sha kuruminki kawata shi wannan har abashi zai iya mana yana lamuni harsai in burinka yacika xaka kawo masa kudinsa kuma akudi kalilan sannan ma zanbashi wani abin kada ki damu nidai fatana da burina naga doctanki yadawo gareki yasaki ballagaxarcan lubna.




Murmushi Aminar tayi tareda cewa " to naji yaushe zamuje.?


"Ko yanzuma tashi muje ashirye nake " cewar murjanatu




Nan takintsa ta xura hijab sukaiwa mama sallama data tashi suka fuce


Basu sha wahala ba wajen xuwa gun mallamin


Saidai abinda ya girgixa Aminatu tashin farko dataji abinda yabukata takawo masa zaiyi aiki dashi wai tasamo cindon hannun wani hamshakin mutumin zaiyi aiki dashi inkuma ba hakaba ta samu gashin gaban namiji baligi takawo inkuma da dama ta hado da cindon zataga yanda Dr ma,aruf xai dawo gareta agigice dakuma maganar Aurenta aranar da akai aikin.


Duk da aminar ta shiga tunanin inda zata samo wananna abun amma ranta yadau hasken jin ma,aruf xai dawo mata nan ba da jimawaba.


Ahanya da suka dawo daga gun malam murja nata bata baki da xugata cewa take "aikawata wannan abubuwan xagewa zakiyi asamo don ayi aikin nan da wuri.


Aminatu tace " towaike a ina zan samo wadannan kayan masu wahalar samuwa kowanne akwai hadari


Kina ganin inma inada wani me kudin dayake dauke da cindo ahannunsa tayaya zan yanko abu ajikinsa inkawo batareda yasaniba?




Kokuma tayaya zanyanki gashin gaban namiji nida ba kwanciya nake da maxaba inma ina kwanciyar dasu tayaya zan yanko abu ajikinka kana kwance bakajiba?




Murja tayi dariya tace " bakiji me mallam din yace bane ce mk fa yayi kije ki lalibo wanda duk kikaga yanada abinda muke nema sai axo asameshi agaya masa zai fadi dabarun da za,ai din asamo kk sani ko wani maganin da xai kadar da hankali zai baki?


Aminatu tace " to naji komi ma xai iya faruwa amma abinda nakeso kigane murja a ina xan sami hamshakin me kudi nida ko futa bamayi balle aganni sai intayi dalili xa.a ganmu atiti.


Murja tace " hhhjmmmm kece dai bakya futar amma ni ina futa fa hajiyata dan haka inhar xaki futa toki biyo layi don cimma burin....


Aminatu takatseta da cewa " """!! Kina nufin karuwanci kk futa? To bada niba murja


Murja tayi dariya tace " waya gaya mk karuwanci ne futan a,a sam abinda nake nufiba infuta inje titi intsaya innaci kwalliya kamar irin ina jiran wanin nan saikiga manyan masu kudi suna tsayawa zakuma kisha mamaki inhar akaga farar fuskar nan taki walh aranar sai an hada go slow


Aminatu tayi shiru tayi wani dan naxari na sakanni kan tace " to zanyi hakan nima duk dan cikar burina amma gaskiya gara inje inda ba,a sanniba domin bayan ansami abinda akeso basake xuwa zanyiba.


Murja tayi dry tace "dama mana kedai kawai kishirya muje da dare zakiga abnin mamaki saikin fi kowa kasuwa.


Amina takama baki da mamaki " Au, ashe da mutane dayawa knn agurin?


" sosai ma keda wa yake zama tabdijan kin dauka kowa kansa akwallaba yake kamar ke ai yanzu inka zauna zakaga zama dan haka kiyi shiri da dare atafi bulayi kawai.




Nan aminar tadau gurguwar shawara ta amince akan zatabi murjan nemo saurayi me kudi....




🤔 tabdijan Allah karaba mu da neman duniya dakuma shegun kawaye masu kaimu su baro.








*Ummeiy Zeey*


Da




*Auntyn S & S*
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗
*'YAR MAKAFI...*
♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗




```written by.....```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUV💘*






70-75


Da misalin karfe taran dare ta tsala kwalliya da wani material me shegen kyau sai walainiya yake stone ne rututu me shining ajikinsa


Riga da skert ne yafito mata da sharp dinta yakama mata kirji na shanunta sun nuna


Gyale karami ta yafa tasaka takalmi me tsini


Fuska tadau make up tafito dan zuwa gidansu murjanatu


Saida tafito tsakar gida gabanta ya fadi tuno abinda xai futarta wai yau itace da futa neman maxa da kanta! Oh masifa batayi ba walh! Ta fadi aranta


Takalli kofar dakin iyayanta taga harsun rufo


Yanayin sanyi ake ciki dama da wuri suke bacci da sunyi ishsh,i zasu kwanta balle dama su bamasu takura bane tasan ma batada matsala dasu


Tafuta ahankali ta janyo kofar gidan tarufota ta yanda inta dawo xata budeta cikin sauki


A zauren su murjanatu sukai kicibus itama ta tsala kwalliya da shadda doguwar riga anmata fitted me kama jiki


Dariya sukaiwa juna yayinda murjan tayi saurin toshe mata baki tace " yi ahankali idon baba biyu gashi can yana karatun jarida karya na sharara masa nace walima zamuje na saukar karatu tun 8 aka fara mune bazamu da wuriba dayake dake nace zani bai hanaba don ya yarda dake ta gidana.


Dariya Aminatu tayi ahankali tace ckn rada " to muje dan mudawo da wuri kada mubata lokaci.


Suka fito daga gidan Aminatu nata raba idanu tana kalle kalle dan bata son " yan unguwa su gane yawo zasu ji takema tamkar snfahimceta dayakema aranar ana mugun sanyi babu yawan jama,a alayin ko gun me shayin dake akan layin baifi mutum biyuba ba kowa


Hankali kwance suka futa a unguwar suka sami dan sahu atiti


Club road suka nufa titin central aka kaisu murja ta biya


Aminatu sai zare ido take abin na bata mamaki na ganin dai daikun mata akan titin suna tsatstsaye kowacce tasha make up tamkar zasuje gdn biki ko suna


Murja ta kama hannunta tace " kinga ba kallon mata yakawomu ba zo muyi ta can jikin falwayar can mu tsaya ko Allah zaisa adace.


Tabita xugui xugui abaya tana takun burgewa itanma murjan takun yauki take tamkar ta karye kafa tasha coge


Ko minti biyu basuyi da tsauwaba kuwa saiga wata katuwar jeep tatsaya agabansu murja taja ajiyar zuciya ita kuma Aminatu ta kalli can gefe


Ya ziro da kansa ta tagar motar yana cewa "yam mata ji mana.


Murjanatu takalleshi ckn yauki da yanga tace " dukkanmu daka ganmu educated ne ba jahila balle dakikiya dahar zakai mana kiran kucakai inxaka futo ka fito domin da ajinmu.


Yayi murmushi tareda kashe motar yafito yatako har gabansu yatsaya tareda fadin " ai girman kujerar kune dolene infito ko banyi niyya ba kuma ajin dana gani atare dakune ma ya tsaidani hajiya.


" ba sunana hajiya ba kirani murjanatu kai tsaye.


Yace " to malama murjanatu wannan kawar taki fa ansiya ko insiya?


Tayi wani shakiyyin murmushi tace " aiko tayawa ba,aiba don tsayuwarmu knn ka iso gurin da bakaxo da wuri bane badai zance maka daka makaro don bazaka tadda ko sahun kafar taba


Yace " lallai nacika me sa,a domin samun kamar wannan babyn agun nan sai an tona to gimbiya meye sunanki?


Aminatu tayi fari da idonta wanda batasan ma ta iyaba sai aranar tace dashi " sunana Amina'


Yace "gud suna me dadi first born dina ma sunanta kenan sunan marikiyata data rasune


Tace " Allah sarki.


Yace " to ya xa,ayi knn, atafe nake domin daga tafoya nake nabiyo tahanyar nan dan nasami abokiyar da zata tayani kwana domin niba dan kano bane daga yola nake zankuma wuce zamfara ko za,a biyoni hotel mukwana tare?


Murjanatu tayi caraf tace " me zai hana inzaka biya da tsoka kadai san akwai banbancin kudi kwana da yini ko?


" ah sosai kuwa ai wannan me kyan ma kudin kwana biyu xan bata a kwana daya kuma cash saita dankesuma ahannu kana zata faranta min


Yakalli Amina da gabanta ke faduwa taji xancen kwana tace " nashiga uku me nakeji.


Yace da ita "to mekyau kin amince?


Murjanatu ta gyada mata kai dayi mata alamun ta amince kawai.


Nan aminar tace masa " ba matsala na amince.


Yabude bakin aljihu yadebo kudi dabaisan yawan suba yabaiwa murja tace " ga tukuici yar,uwa


Takarba jiki na rawa tana godiya lallai wannan me gwabi gwabine za,a dashi


Yadubi aminatu yace biyoni mota muwuce


Yatafi mota ita kuma tace da murja " nashiga uku kawata xanko iya kwana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login