Showing 24001 words to 27000 words out of 33792 words

Chapter 9 - YAR MAKAFI 1 to END by Nabilancy Love .txt

25 Dec 2024

3080

haushi aka?


Amina ckn karaji tace " siya kikayi kuma har dakina kk shigo dole ki karbi abinda kk gani dan haka kada ki kara xuwar min gida da wannan fuskar inhar baki canxa kudirinki akan aurenaba kin dawo hanyar arxiki toki rike xumuncinki kawai wanda mukai ada ya isa amma nikam ayanxu natuba nabi Allah, Da ma tun farko ba halina bane, Kece kika jani kuma Alhamdulillah, yanzu na gane gaskiya...


Murja tayi galala tana kallon amina da takaici cike fal rai tace " yanzun waini kike kora harda min gorin gida. Eh lallai dama haka dan talaka yake .


"Nagode Amina"


Kinzama kaxa samu kiki dangi dan haka kirubuta ki ajiye ni murjanatu isyaku inhar nafuta daga gidan nan baxaki kara ganina ba inko kk kara ganin kafata tokiyi duk abinda kk ga dama da ita.


Tana gama fadin hakan ta figi jaka da gyale ahanu tafice harda guntun hawayen bakin ciki. ( yalla maxa ki kara gaba makira uwar shagalallu abi wani sarkin dama Fans din Aminatu basa qaunarki barema yan taskar Nabilancy da zauren ummiey Xeey akule suke dake da kika bata musu Zinariya lol




murjanatu nashirin futa daga cikin gidan ta tura get zata futa afusace ita kuma lubna tana shigowa gidan


Sukai kicibus


Tsayawa sukai suna yin kallon kallon


Babu wacce tacewa kowacce ko kanxil suka kara gaba kowacce na wassafa magana aranta


Ita murjan ayyanawa take tabbas taga kyan lubna kuma taga wayewarta dole ne takwace miji gata yar masu kudi


Dariyar mugunta tayi data futa a get din domin tasan wataran sai aminatu tayi kuka sbd tirjiyar datayi mata don tasani lubna yarbin malamai ce ba barinta xama zatayi agidan ba


Ta kada kafada " jiki magayi ai. Idone nawa ta baya ta rago


Itako lubna rayawa take "watoma har Aminar ta sami guri dahar danginta suka fara musu zarya agida toko sunkusa zuwan karshe tunda ba gidan ubansu bane kuma basuga guri ba takusa koro musu yar,uwa gida domin tasamo wani magani mesuna bankada kishiya dawa wasu kuma kance masa korata gida. Ba kowane malami keda basirar hadawa ba don yanada wahala wajen samun mahadinsa takashe kudi sosai kafin ta mallakeshi.....


<> <> <> <> <> <> <> <> <> <> <>
Bayan tafiyar murjanatune Aminatu tai tagumin bakin cikin akan abubuwan data aikata, tana mai nadamar aikata Hakan, kukane yazo mata wata zuciyar tace ba kuka zaki ba, ki tashi kiyi abun da ya kamata,
Aiko ta mik'e ta shiga toilet ta dauro alwala tazo tai Sallah tai karatun Qur'ani ta dakko charji tana ta ja tana Neman gafarar Allah, haka ta wuni tanayi seda Aka kira magrib sannan ta tashi saboda ma'aruf ba part dinta yake ba




Bayan ta idar ta Sallah, Ta dakko wayanta ta tura ma ma'aruf text din love kamar haka... _Mijina INA alfahari dakai, Allah ya bar mana kai mijin Lubna da Aminatu, A gaskiya ina kewarka sosai, Ka kula mun da kanka Kaji mijina_ tai sending, On his way back, yana driving yaga text dinta murmushi yayi, a ranshi Shima ba karamin kewarta yakeyi ba, Driving yakeyi but be hana shi tura mata reply ba.. shima ya tsara text dinshi kamar haka
_"Baby Luv, I miss everything about you, please take good care of your self kafin na dawo, I love you so much_ yai mata sending
Tana karantawa taji wani Sanyi a ranta tace awwn...then ta ajiye wayar ganin ba part dinta yake ba, ta tashi ta dafa indomie da kwai se mango juice...




Bangaren Lubna kuwa ganin har 7:PM ma'aruf be dawo ba ta cika tai fam, Ta ayyona a ranta da ace Aminatu ne da girki da yanzu ya dawo, Wani tsaki taja taci gaba da makeup dinta, Ta sako wasu Riga da wando, Ba laifi dai sun mata kyau lol, Tana zaune tana cin cingum, taji horn din motarshi, Wani dadi aranta taji, Ta tashi ta feshi dakin da tirare,
Yana shuguwa Wani kamshi ya dakeshi, Ya kalleta dai, A zuciyar shi yana me Kyan dan majiji kawai, yai wucewarsa daki ba tare da Yace mata komai ba


Yana shiga yai wanka, Ya sako Riga da Wanda three Quater, yazo fallow ya zauna tazo kusa dashi ta makalkaleshi wai she's missing him, Matarsa Ce be koretaba domin tana da hakki akan shi, kallonta yayi Yace where's my dinner?
Nan lubna ta fara zare ido tace" am am inasha take away zakai mana
Ya kalleta wulakance Yace akwai komai a gidan nai maka take away?
Tace uhm uhm me kakeso to
Ya daka mata tsawa, bana bukatar komai,
Daki ya shiga ya dakko wayarshi, Ya kira zinariya, tana ganin call dinshi kamar bazatai picking ba sai kuma ta dauka, Yace hello baby
Tace" yes dear andawo lfy? Yace lafiya lau, dama na kirane in akwai sauran abinci nazo na amsa Lubna bata da lafiyane bata samu tayi ba, Yasa hand free lubna naji


Aminatu tace ayyah Bansaniba ai da gaba daya na hada nayi, Amma akwai indomie, kazo ka amsa to, inyaso sai na dafa Wani, Wani haushi da takaici ya is he Lubna, Yace" Ok ganinan zuwa.
Yana gama wayar ya ajiye wayarshi, ya wuce part din Aminatu, Ganin ya fita ta dauka wayanshi ta fara bubawa, Wani Haushi sosai taji da taga conversation dinsu na love, kaman ta fasa wayan Dan kishi wai har YAR MAKAFI, ta fita Iya Love


Shi ku ma'aruf Yana shiga part din Aminatu Wani Hug yai mata hade da hot kiss, yana sa mata albarka, Aminatu ta tureshi tace kaga Ba girkina bane Kar.......yagane nufinta kawai ya amsa Indomie ya wuce part din lubna na zauna yaci ya koshi, Lubna tace yunwa takeji yai mata nuni da kitchen alamar ta shiga ta dafa wannan na MATAR shi Shi ne. lolzzz














```Muje xuwa
fans muna godiya muna kallon kowa da tasa soyayyar Allah yabar kauna kunayin mu munayinku luv u```


[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗
*'YAR MAKAFI...*
♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗




```written by.....```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUV💘*




_❣❣Awwnn our fans...we heart you Dearies...muna ganin comments dinku da yadda kuke son wannan novel din namu.....We love you buhut buhut❣❣_


*PAGE.....90<>95*


Hakadai rayuwarsu ta ci gaba, Yanzu gaba daya Lubna ta rasa meke mata dadi, Ma'aruf kuwa Alhamdulillah daidai kwargwado yana ba kowa hakkinshi, amma kana gani ba sai ka tambaya ba yafi son Aminatu, Domin ta rike addua'a da addini Sosai, Idan ma'aruf na dakinta to rabi sallan dare ne rabi kuma suci soyayyarsu, Abun Ba karamin ma ma'aruf dadi yayiba, Domin tabbas yayi dacen mata ta gari, tana temaka mai sosai Wajen tsare addininshi


Lubna kuwa saboda jaraba ta rasa gane Wai me Aminatu ta keyiwa ma'aruf ne, wai yafi son ta this and that dai, Sau tari lubna na jefan Aminatu da mugun Abu amma da yake ta rike Allah, ba abun da ke Samunta, Shima ogon nasu da yake yanzu a tsaye yake wannan kenan


<> <> <> <> <> <> <> <> <>


Akwana a tashi ba wuya, Aminatu ne kwance akan cinyar ma'aruf da yake weekend ne, ba Inda zaije kuma ya fado kan girkinta, Ya kalle agogo yaga 10AM Yace" Baby please ki tashi mu shirya Yau zamu je ziyara waje da yawa fa, batai mai musu ba ta tashi ta shiga wanka har yana tsokanarta ko ya zo yai mata ne tace A'a da sauri Dan tasan indai yazo to se sun kusan azahar, yace See you wasa ma ni nake miki nima bari naje nai Wanka, aiko shima ya shige toilet yai wanka, Basu bata lokaci ba suka fito suka shirya dama yace Susa Purple shaddan da sukai Anko na ranar bikinsu, Aiko Haka akai suka fito tamkar yaune ranar auransu
Suka fito harabar gidan Aminatu ta jirashi yaje yai ma Lubna sallama tace" zata bishi yace Nop, ba yau ba, Wani haushi ya isheta Kaman ta kwalla ihu,


Yana fita daga dakin tahau hawaye. Tana jin ya tada moto ta leka ta window, ganin shigar da sukai iri daya nan kanta ya fara juyawa saboda tsananin kishi aranta tace" metai wa ma'aruf ne haka...Mudai mukace ta bincika kanta lolz




Suna tafiya suna soyayya abunsu har suka Isa gidan Abokinshi Dr Lurwan da matarsa Zainab suma suna shirin fita shan ice cream, Nan dai suka gaggaisa a tsattsaye sukace se next time sunanan zuwa susha hira, Dr lurwan yace Lolz in zakazo kazo da dayar Matar naka musha hira Duka, Dr ma'aruf yace rufan asiri in ba ai hira ba Asha dambe kuwa Duka suka kwashe da dariya, Su sukai motarsu Suna Su Dr Lurwan hakahaka


°°°°°°°
Tafiya kadan Su dr da zinariya sukai se gasu gidan mummy (Maman ma'aruf) suna shiga mummy ta amshesu hannu bibbiyu, Ganin yanda ma'aruf yai kyau ko yana gidan ta be beyi ba, lalle namiji yai dace da mata shi yaji dadi kam, Aiko mummy ta Kara ja musu kunne akan Su kara rike addini sosai, sukace ba komai Insha Allah, Nan Aminatu ta cire gyelenta ganin mummy batai wani gyaran gida ba, ta gyara mata ko ina harda daura mata abinci kafin Su tafi, Ba abunda mummy take Ce mata illa sa mata albarka, Dr ma'aruf ne yace Su tashi Su tafi, mummy tace INA zasu yace gidan Su Aminatu, mummy ta tashi ta shiga daki dakko kudi masu yawa ta baiwa Aminatu ta kaiwa iyayanta kuma tananan zuwa insha Allah, Aminatu taji dadi sosai, tai godiya suka tashi suka tafi


<><><><><><><><><><><><>
Tafiya suke ba'a dau lokaci ba se Ga Dr ma'aruf a kofar gidan Su Aminatu, Aminatu duk ta kosa ta sauka taje taga iyayanta, yana kashe motar, Aminatu tai tai ta bude kofar ta kasa Ashe ma'aruf ne ya kulle, Ta kalleshi zatai mai magana kenan ya kashe mata ido yace" *I LOVE YOU, I'M FOREVER YOURS* sannan ya Sakar mata murmushi, Sunkuyar da kanta tayi, Tace _I love too my habibi_ kannan ya bude da sauri ta tafi cikin gidan da gudu, shi kuma ya tsaya sakko da kaya a bayan bot, Sega murjanatu Zata fita, tana ganin DR ne kuma tasan tabbas tare da Aminatu sukazo sai ta fasa fitar Da zatai a cewarta Aminatun zatazo ta sameta a gida


Nan dai Ma'aruf ya shiga aka zauna anata hira sosai, mama da baba se sa mai albarka suke, sukace Ga Aminatu nan amana, Yace ba komai,


Ma'aruf ya gyara zama Yace dama munzo ne akan maganar aikin Da Za'ai wa mama, Zuwa next week insha Allah zanzo a dauketa mukaita ai mata aikin a ido, Nan sukaji dadi sosai ma'aruf yasha addua kala kala, mama harda murna tace ikon Allah idan Allah yasa zan sake gani zangani, sukace hakane, ma'atuf yace zasu tafi sukai sallama suka wuce gida


Bangaren murjanatu kuwa har magrib, taga Ba labarin Aminatu, bata zoba ranta a bace tace lalle ma da ki kikeyi

*Bayan Kwana biyu* ranar Monday
*Aminullah* ne acikin mota yasha shadda me tsada yana hanyar zuwa Kano, tun randa Aminatu ta mai wulakanci be sake waiwayon kano ba...Ya tafi zaria har Allah yasa ya hadu da uban gida me kudi ya daurashi akan dukiyanshi, Da yake aminullah akwai tsoron Allah kuma baya cin abun da ba'a bashi ba haka ya sama karbuwa wajen uban gidansa,
Tafiya yake har ya Isa kano, bayan yaje gidan iyayanshi be wuce ko INA ba sai gidan Su Aminatu, Yana zuwa yai parking, Da yake uban Aminatu ya ganeshi aiko suka shiga har cikin gidan, Nan shima ya kawo musu sha Tara ta arziki, ya tambaya INA Aminatu akace tayi aure, beyi mamaki ba SBD ha rabuwan da sukai, Yace OK dama nazone zuwa gobe mama zan kaiki asibitin Makka ai miki aikin ido dama already tun kafin nazo anyi booking komai


_Too faaa Ga Ma'aruf kuma fa aminullah Duka sunada burin kai mama ai mata aikin ido...kuci biyumu hope kuna jin dadin labarin_


Mama tace" dannan da ka bari mijin Aminatu munyi magana dashi, Yai murmushi Yace" mama karki damu duk dayane, Kinga ni munyi maganar na bada kudin komai da komai, nan ko suka amince washe gari suka tafi asibitin duk bada sanin Su Aminatu ba... ikon Allah cikin sa'a anyi dayake ba wani aiki sosai bane se Ga mama ta fara gani garau, Kwanansu 4 aka sallamesu, bakuga murna ba wajen mama da da baba gashi basu da waya balle Su Sanar da Aminatu, Aminullah kam yasha addua kamar ba gobe


°°°°°°°°°°
Murja najin labarin Aminullah yayi kudi ta fara Neman hanyar da zatamai magana, Ko zai aureta, Aiko yai banza da ita Dan be manta wulakancin da tasa Aminatu tai mai ba, yasan ita ta zige ta tsab, sai yasa Yace duk randa ta Kara mai magana se ya babballata lolz


Murja tace yau na shiga uku, Aminullah nan da na ke mai kallon a wulakance yau shine yai kudi harda moto, Ikon Allah naga ta kaina ni murjanatu


Bayan an gama Komai Aminullah ya koma zariya abunshi,


Bangaren Su Aminatu kuwa, Ran Saturday, sukazo gida da Dan maganar yanda za'ai ma Mamanta aikin, Suna zuwa sukaga abun mamaki, Mama a tsakar gida tayi kyau tana shara, nan ma'aruf ya kalle Aminatu, itama ta kalle shi. Har suna hada baki mama kinfara ganine da kike shara? Dagowa tayi ta kallesu tace mu shiga daga ciki mana yayana


Nan suka shiga ta basu labarin yanda akai tundaga farko har karshe Aminullah ne ya biya komai akai mata,!!


Ma'aruf kuwa se Tambaya yake waye wannan Aminullah, a INA yake ganin no need ya sani Aminatu tace" wani bayon Allah ne dake kula damu tun kan Mu hadu sai ya bar garin nan


Ma'aruf be kawo komai a ran shi ba, Yace Allah sarki, Allah ya saka mai da alheri. Amma munyi murna sosai


Tun alokacin Aminatu ta saura, Jinta take wani iri, inama Aminullah ta aura, Ganin yanda tayine Ma'aruf Yace menene? Ita mahaifiyarta ta gano setai mata nuni da ido tace ba komai


Haka nan tace Ba komai, dakyar dai suka wuni agidan ta koma gida cike da tunanin *Aminullah*


Bayan kwana biyu kuma still Aminullah ya dawo akai ma gidan kwaskwarima, akai fenti Sosai yayi kyau matuka kamar sabon gida


Iyayanta sunyi Murna sosai sukasa mai albarka,


Allahu Akbar Aminullah, ahanyar komawarshi gida yai hatsari ya mutu...Rayuwa kenan


Nan danan aka kira gidan Su Aminullah akace ya rasu, kan kace meye labarin ya bi ko INA a unguwar domin Shi mutun ne me tausayawa mutane, duk ansanshi


Nan Murjanatu ta kira Aminatu sanar da ita, Wani jiri ya kwashe Aminatu ta fada kan kado




Kash......kuci gaba da biyomu








TEAM YAR MAKAFI
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗
*'YAR MAKAFI...*
♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗




```written by.....```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUV💘*


_When Someone Walks Out Of Your Life, Let Them. They Are Just Making More Room For Someone Better To Walk In!_


*PAGE.....95...100*
_QUARTER FINAL_


Ma'aruf ne ya shugo ya ganta a kasa, ya girgizata yaga alamar kamar bata nunfashi.

Da Sauri ya dauketa sai asibiti, Akai mata temakon gaggawa sannan daga bisani ta farfado, Ma'aruf ne ya sanar dasu mumy, Sannan yaje gidan iyayan Aminatu ya dakko Su ya Sanar dasu besan meke faruwa ba


Nan dai kowa yai jigun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login