Showing 33001 words to 33792 words out of 33792 words

Chapter 12 - YAR MAKAFI 1 to END by Nabilancy Love .txt

25 Dec 2024

3085

nunfashi yaja Yace" kin ma kanki kuma ni NA SAKEKI SAKI UKU,


Da sauri Lubna ta kalleshi tana Yau na shiga uku ta sake kuka nan take ta kira mumyn Ma'aruf


Shi kuma ma'aruf yana gama fadan ya saketa yai ficewarshi. Aminatu kuma ta bishi tace" haba habeebieee meyasa kai saurin yanke wannan hukuncin


Kallon ta yayi Yace ta chanchanci hakane, Itadai Aminatu batace komai ba, Amma Sam abun be mata dadi ba


Mummy na zuwa direct dakin Da Lubna take , Nan ta ke Lubna ta fara kuka tana Mummy shikkenan yaya Ma'aruf ya sakeni. Na shiga uku, na mutu


Mumyy ne ta sake baki ita tama rasa me zatace mata, Dan abun da Ma'aruf yayi shine dai dai amma Ai an gudune ba'a tsiraba, Yanzu dai dole lubna hannunta zata dawo tunda Maminta ta rasu


Nan dai Mummy take ta bata hakuri, har ta sama Dan sauk'i aka sallamesu


Shikkenan yanzu ba Ma'aruf ba lubna aure ya kare


Koda suka koma gida daddy yayi fada sosai akan da be sake ta ba, Ma'aruf Yace hmm Dady ita ta ja ma kanta,


<><><><><><><><><><><><><><>


Bayan watanni biyu Aminatu ta Haifa yara yan biyu maza, dayan bezo da rai ba sai daya ya rage....Awwnnn bakuga murna ba wajen iyayansu, balle ma mummy da Dady sunga Farkon jikansu,


Aminatu kuwa haihuwar datai kamar an kara mata kyau, da Lubna taji Aminatu ta haihu kuka tayi sosai tace" tabbas Gaskiya ne za'a Dade anayi amma karya ba inda zai kai mutun yau Ga karshena nice a kujeran guragu, nan ta fashe da kuka


Mummy kam tausanta take akan tayi hakuri ko yanzu ma lokaaci me kura ba akan ta gyara halinta


Allah sarki Lubna nan danan nadama yazo mata ta koma koda yaushe cikin istigfari, Tana Neman tuba akan duk abun da ta aikata, Kullun Ma'aruf tazo tana Neman gafara Yace" ya yafe mata


°°°°°°°°°°°°°°
Ranar Suna aka sama Yaro suna Aminullah, *Al'ameen* dama ma'aruf ya mata alkawari zai sa sunan Aminullah tunda yaga yanda take damuwa kuma Kullun tana yimai addua'a


Anyi suna awwnn abun se Wanda ya gani, Murjanatu sune yan kan gaban Komai da komai, Itama ta sama miji bayan babban Sallah za'ai auranta lol


**********
Yanzu lubna ya fallawa wa Allah komai Nata, dama haka akeson mutun Ko yanzu 6e bace ba idan kana mugun halaye ka gyara, tun yanzu, Allah dai yasa mui cika da kyau da imani (Ameen)




Ma'aruf yanzu hankalinshi kwance, Aminatu namai komai, Ga Aminullah se kara girma yake yana samun kulawa sosai.

Ansake karawa Ma'aruf girma a wajen aiki, yanzu yasai fili guda biyu, daya ya ginawa Aminatu da gyaran da zata Haifaimai nan gaba, dayan kuma ya Gina mata gidan Gona....


Lubna kuwa idan taji abun alheri Setai musu addua tace" inama Ma'aruf ya maida ita, Da zatamai biyayya yanda beyi tinani ba...lolz Nabilancy tace" its too late awwn


Aminullah ya girma yana da shekara daya da rabi yayi kyau amma idan ka ganshi zakace yakai 2years, Aminatu ta sake samun ciki ta Haifa yara mata yan biyu kamansu daya da babansu, Daya aka sa mata Sunan mummyn ma'aruf dayan Kuma aka sa Mata sunan Maman Aminatu
Anyi suna Iya suna....




Time din da Aminullah ya ya cika shekara Biyu aka mai birthday


Ma'aruf ya kan kai Aminullah gidan Mummy, idan Lubna ta Ganshi tai tamai wasa tana son yaron har cikin ranta Allah sarki


Time din da Aminullah ya Dan fara magana, ranar sun zo dukansu gidan Mummy, Gaba daya suna zaune yan biyu sun fara rarrafe, Aminullah kuma yana wasa, Ga Aminatu, Ga Ma'aruf ya Mummy da Daddy

Aminullah Yace" Allah sarki, Mummy Anty Lubna naban tausayi, Kowa na cikin dakin yai shuru suna mamakin Kalaman Aminullah


Nan Lubna ta fara hawaye ta kira Aminullah yazo, tace" kai mun addua kaji?


Gaskiya kam taba kowa tausayi, balle ma Aminatu sarkin tausayi da akwai yanda zatace Ma'aruf ya dawo da ita da zai tace lol




Hakadai Rayuwarsu taci gaba awwn
.


Anyi bikin murja ita yanzu tana da ciki l


Yan biyun Aminatu suma sun girma har an sama wani cikin


Ma'aruf Yace ba a gda zata haihu ba Dubai zataje ta haihu.....




Awwnnn rayuwa ya musu dadi




Awwn Bamusu muka gama muku wannan littafin ba, Muna godiya sosai yanda kuka nuna kunason book dinnan MUNGODE


Munanan kawo muku wani littafin me dadin gaske and Kar ku manta Littafin Nabilancy *TARAYYA* nanan fitowa kar Ku bari a abaku labari










Nabilancy Love
And
Ummiey Xeey
Ke.ma.kowa fatan Alheri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login