Showing 3001 words to 6000 words out of 33792 words

Chapter 2 - YAR MAKAFI 1 to END by Nabilancy Love .txt

25 Dec 2024

3086

♦
πŸŽ— πŸŽ— πŸŽ— πŸŽ—
*'YAR MAKAFI...*
♦ ♦ ♦ ♦
πŸŽ— πŸŽ— πŸŽ— πŸŽ—




```written by.....✍🏼```
*FRESH Uβ“‚MIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUVπŸ’˜*




*β™»REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*




*Pg 15-20*
Tunda Dr ma,aruf yatafi Aminatu takasa sakat da ranta na tunaninsa domin ta zurma itama taji yai mata bawai don bata taba yin soyayya ba ayanxun hakan ma akwai wanda yake mata matukar So


Aminullah yana son Aminatu itanma tana sonsa sbd yanda yake dawainiya da ita tun tana karamarta duk abinda yasamo ita yake kawowa naci kona amfani acan bayan layinsu yake talaka ne bayada aikinyi domin karatu ma yakeyi ajami,ar Zaria agidan kawunsa yake zaune


Aminullah saurayi ne shima kyakykyawa dogo saidai baki ne bakinsa me kyan nan


Yarone shi me zuciyar neman nakansa don duk lokacin dayaxo hutu kano baya yarda ya zauna zaman kashe wando amajalisa yakan futa garejin yayansa kokuma yai yn buga bugarsa a kasuwar yan wayoyi inya samo ya amfanawa kansa ko yazo ya saiwa masoyiyarsa Aminatu wani abun


Har tausansa Aminatu takeji na yanda yake mata dawainiya shi bame shiba


Aminatu nada burin taga tayi auren jindadi sbd yanda take ckn kuncin talauci babu mataimaki sai Allah sai makwabcinsu mutumin kirki baban kawarta


A yau da Dr ma,aruf yaxo mata da soyayyarsa sai tunaninta yafara canxawa ya burkita mata lissafi domin hankalinta yafara karkata akansa


Nafarko taga yafi Aminullah kyau sannan tasan agareshine hutun da take fata zaixo mata


Gidansu murja tashiga kawarta domin ta labarta mata wannan abu amma saita tarar murjan bata nan taje gidan yayarta karkasara




<><><><><><<><><><>


"Momy yau naxo miki da wata magana me dadi dafatan zaki karbeta hannu bibbiyu. Cewar Dr ma,aruf yana zaune kusa da mahaifiyarsa


Hjy Zulaihat ta gyara zamanta tace '"to Allah yasa ta gamsheni babana.


Yace "wato momy akwai wata yarinya da muka hadu da ita kwanan nan ina sonta momy kuma so nake ayi aurenmu da wuri...


"Dakata ma,aruf!


Takatseshi da bacin rai


"Kana so kacemin wata kake da niyyar aure ba lubna ba? Dan ma wulakanci harka dubi kwayar idona kace da wuri kk so ayi muku aure to kasani hakan bazai yiyuba har sai inka amince zaka Auresu atare




Ya canxa fuska da bacin rai shima yace "hakan bame yiyuwa bane momy yama za,ai kice haka nifa ban taba fada muku cewa ina son lubna ba to ana me zan aureta ni walh da in aureta gara naita zama haka ba aure..."haka kace min babana?bakaji kunyar idona ba harkake ikirarin bazaka auri diyar yar uwataba danma kiyayya har kace da ka aureta gara kaxauna haka ba aure lallai nagode da wannan tijarar da kk shirin yimin


"Momy ba tijara zan miki ba kawai dai nafadi gaskiyar xuciyatane bana son lubna Aminatu nake so kuma ita zan aura


Ya mike tsaye "to bada yawuna ba bakuma zan amince ka auri wata aminatu ba inhar ba lubna aka fara aura ba.


Ya kalleta zai magana kuma ya fasa yafice ransa na quna


Lubna dake labe tanajinsu ta fashe da wani kuka me tsuma rai hajiya zulaiahat ta kallo inda lubnar take ta yafito ta tace "zonan Autar Mami kada ki bata hawayenki abanxa kiyi shiru.


Ta taho da sassarfa ta fada jikin momyn tana gunsheken kuka "wayyo nashiga uku momy yaya ma,aruf zai auri wata ba niba.


"Ke dena fadar hakama in har ina duniyar nan ma,aruf baida matar data wuce ke kada ma ki bata hawayenki abanza dole ne ya aureki


"To momy yace fa baya sona yasamu wacce yake so.


"Eh ahakan zai aurekin inkunyi auren ai dole zai soki kiyi shiiru in dady yadawo zamui maganar ayau za,a gama magana dolene yazaba ko ya aureku duka kokuma ya hakura da aminatun dan baxan bari wata tafara shigowa ba bakeba.




Tahau goge mata hawaye ita kuma tayi shiru tana maida numfashi don momy ta faranta mata ranta


Lubna kyakykyawa ce fara ce siririya doguwa mahaifanta masu kudine ajahar yola karatu take a BUK tun da tafara karatu take agun hjy zulaihat shekara biyar knn digree takeyi sosai take son yaya ma,aruf tun tana nuna masa yana burus da ita har ta iya furta masa koda kuma tafada masa baiyi accept da soyayyarta ba bata hakuraba taci gaba da nuna masa So din


Har gyaran dakinsa takeyi donta burgeshi akullum


Kafin yafuta yake baiwa atika yar aiki mukullin dakinsa yace ta gyara masa


Ita kuma saita karba ta gyarashi fes ta turare dakin da turaren kamshi na meduguri original me faranta zuciya


Ranar da yagane ita keyi ma haushi yaji bai kuma gode mataba daga ranar ma yadaina barin mukullin


Duk wata hanya da zasu hadunma baya bari


Ko waya ta masa dakyar yake dagawa amma ita ko ajikinta


Kawayenta Aziza da Nabila sunsha bata shawara akan ta hakura kawai tunda bazata kaita gaci ba amma sai tace dasu mahakurci mawadaci wataran za,a dace kuma tana masa son da bazata iya rayuwa ba inbashi


_To fa nan fa ake yinta muje zuwa_










*Auntyn S&S*πŸ’˜
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦
πŸŽ— πŸŽ— πŸŽ— πŸŽ—
*'YAR MAKAFI...*
♦ ♦ ♦ ♦
πŸŽ— πŸŽ— πŸŽ— πŸŽ—




```written by.....✍🏼```
*FRESH Uβ“‚MIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUVπŸ’˜*




*β™»REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*




page.....20-25


Aminatu na zaune atsakar gida ta zabga tagumi tana tunanin rayuwarta da kuma soyayyar Dr ma,aruf data kunno gareta


Sallama taji daga zaure saida gabanta ya fadi jin muryar Aminullah ta manta shaf yana zuwa duk karshen sati


Ta amsa masa sallamar ahankali tana kallon shigowarsa ta xuba masa idanu sai taga yakara wani kyau


Ya karasa gareta yana murmushi yaja kujera yr tsugunno yaxauna kusa da ita


Tace "sannu da zuwa ashe kana tafe,


Yace '"yawwa Aminata ashe kunanan baku futaba.?


tace "eh ai mundaina ma futar.


Yace " amma naji dadin hakan sosai dama ba son zuwanku bakin danjar nake ba aminata dan bayanda xanyine banda karfin rikeku amma naji dadin daina xuwanku bara domin keba kalar yin bara bace Amina dan dai bakyajin maganata ne.


Tace "to yanzun dai aita wuce ya karatun?


yace "Alhamdulillah gashi munfara exam ta semester karshe ayau xan koma baxan kai monday ba sbd gobe 8:00am munada exam bandama naxo karbar wasu kudade gun kawu bala da baxan zo ayau ba.


Tace "to Allah yataimaka


"Ina maman ko bacci sukeyi?


tace "mama tana daki ba bacci takeba shiko baba yakwanta wai kansa ke ciwo tun safe wataqila ma yai baccin


Aminullah yace "yasha magani kuwa?


Tace "nabashi panadol daxun,


Yace "to Allah yasawwaka bari naje gidan kawun ina ganin baxan dawo tanan ba zan wuce sbd kada nayi dare dandai ma baxan iya shigowa kano inyi uxuri injuya banganki ba da baki ganniba.






Tayi murmushi tace "bakomi Allah yataimaka yasa kagama karatun lfy.




"Amin. aminata bari nakoma.


Ya mike tareda lekawa dakin maman yagaidata tasa masa albarka dayake tagane muryarsa


Ya ajiyewa maman dari biyar yafita


Aminatu tarakashi har kofar gida suka dan taba hira ta mintina sukai sallama takoma ckn gida


<><><><><><><><><>
Aminatu tana gama baiwa murjanatu labarin Dr ma,aruf murjanatun ta hau tsalle harda juyi ta rungume Aminatu tana cewa " wayyo dadi kasheni Allah mun gode maka daka kawo mana hutu ammafa naji dadin wannan labarin kawata kai jindadi oyoyo kinga abinda nake gaya mk ko,nasan ke kalar manyace shiyasa akullum nake fada mk kirabu da Aminullah kima cire sonsa aranki kinga dai yanzu ko ban fadaba nasan zakiyiwa kanki fada tunda nasan babu yanda za,ai ki dau madaci ki bar xuma.


Aminatu tace "hhhhmmm kawata jinki kawai nake yama za,ai nabar Aminullah akan wani Dr ma,aruf kema kinsan innace zanki aminu naxama maci amana kinsanni da gudun wulakanci fa ina tsoron masu kudinnan na zamani da anga kai ba dan kowa ba sai aringa wulakantaka dan haka nikam baxan rabu da aminullah ba dan ina sonsa


Galala murjanatu tayi tana mata banxan kallo kana tace akufule " to wawuya wacce ke neman kulla aminta da wahala me nasama yaci balle nakasa me zakiyi da wani aminullah ayanzu ga me arxiki kuma ma saurayi shima danyen jini ko bakya sonsa shima.


Aminatu tace "bawai son dr Ma,aruf ne banayi ba yaburgeni tako ina kuma akwai abunda nake hange agareshi da zai min amfani kuma kinga nasan zai dauken wata kewar in Aminullah baya nan kawai dai ina ganin nafi cancanta da Auren Talaka kamata ne


Haushi yaturnike Murjanatu bata sake magana ba ta mike bako sallama ta fice tayi gidansu dab Aminatu ta qularta takuma ki daukar maganarta


Ita murjanatu haka take akwai saurin fushi dan dai Aminatun mejin maganar tane kuma batada zafi gashi suna son juna shiyasa amincinsu yai tsayi




<><><><><><><><><>
Yana zaune gaban mahaifinsa yasunkuyar dakansa yayinda dadyn nasa yake zaune akan 2 siter yana masa magana anitse


"Me sunan mallam naji abinda yake wakana akanka momynka ta gayamin komi jiya nakumaji dadin zakayi aure babana saidai me yasa zaka ki yruwarka ka kawo bare ckn gida alhalin ta dade tana sonka kana ganin inka kita bazaka wargaxa musu xumuncinsuba kada maminta taxo tanakin haushinka da momynka tace kun guji " yarta kun daukaki wata alhalin akanka taki zaman gabansu tadawo gidanmu da zama haba me sunan mallam kaduba lamarin mana


Dr ma,aruf yagyara xamansa anitse shima yahau nasa bayanin yace "wato dady bawai kin lubna nakeba kawai dai aurenta ne baxanyiba tunda ga wacce naiwa Alkawari ina son Aminatu fiyeda lubna don ita lubna ma son yanuwan taka kawai nake mata sannan akwai wasu dabi,unta da banaso nasan kuma baxan iya rabata dasu ba tunda akullum tana nuna ita yr kantace kaga kuwa dady maganin ayi kar asoma.


Dadyn ya gyada kansa ckn gamsuwa yace "tom zan tattauna da momynka anjima zanfahimtarta kabani lokaci zannemeka a ina yarinyar da kk so take?


Nan yai masa kwatancen unguwarsu Aminatun


" to nagane tashi kaje yanda duk mukayi zan nemeka gobe muji yanda za,ai.




Dr ma,aruf na futa gidan abokinsa ya wuce Dr lurwan dayake weekEnd ne yana gida


Matarsa Ummi taje unguwa shikadai ne agidan dan haka Dr ma,aruf yana neman rakiyarsa gidansu Aminatu yatashi yabishi ba musu amma tsiya yaringa masa "gaskiya tuxurun nan kaci sa,ar yau madam batanan amma da ba inda zanje tunda weekEnd dai ta ma,aurata ne


Dry Dr ma,aruf yayi yace "naji nikam aje arakani basai anmin goriba nima insha Allahu komi yakusa zuwar min karshe...........
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦
πŸŽ— πŸŽ— πŸŽ— πŸŽ—
*'YAR MAKAFI...*
♦ ♦ ♦ ♦
πŸŽ— πŸŽ— πŸŽ— πŸŽ—




```written by.....```
*FRESH Uβ“‚MIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUVπŸ’˜*




*β™»REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*


_Muna matuqar jin dadi ganin yanda wannan novel ke functioning masoya muna godiya Allah yabar kauna masu kira da masu turo sako mungode muna sane daku muna tare daku ako da yaushe i love you all_






Pg 35-40
Da kuka tashigo falo tana qunsheken kuka tamkar wacce akai mata dukan tsiya da taga momy bata falon saita nufi bedroom dinta


Can ta tarar ta tana gyaran sif aiko saita kara sautin kukan nan momyn ta rude ganin yanayin Lubnan da alama ba lafiya ba wannan kuka haka take hankalinta ya tashi


Ta isa ga lubnan da sauri tajanyota jikinta ta kwantarta akan cinyarta tana shafa kanta


Tayita tambayarta me aka mata haka


Amma fur lubna takace ce mata komi don kukan yaci karfinta


Saida tayi me isarta kana ta dago da kanta ta kalli momy ido jajir tace "momy yayane yaci min zarafi gaban sakatariyarsa yaimin tatas ya xagen iyaye yace babu wanda ya isa yasakashi ya aureni babu kuma me hanashi auran Aminatu domin itace ruhinsa


Takarasa maganar tata tana shirin yin wani kukan


Momy tahau shafa kanta tace " yi shiru babyna kada kitada hankalinki abanza daina bata ma hawayenki bai isa ya zartar da komiba inba izininmu walh inhar ina raye saiya aureki lubna Aminatun banxa kima yi shiru yr nan.


Tayi lamo ajikin momy tana ajiyar xuciya ranta yai fari qal burinta yakusa cika


Momy tace "zaixo yasameni barima dady yadawo yau za,a yita ta kare gara asan abinyi inko ba hakaba xanbi dashi ta karkashin kasa tunda akwai malamai aduniya zansa ayi maganinsa zai amince da aurenki ko yanaso ko bayaso asa masa sonki asa masa kuma tsanar aminar bashikenan ba.


Taja ajiyar xcy ta kalli momy tana murmushi tace "dama hakan akai momy domin yaya yanada wuyar sha,ani kuma inba hkn akai ba zai iyamin wulakanci in anyi auren


Momy tace "yi shirunki diyata barni dashi kibarmin komi ahannuna .


<><><><><><><><><>


Dawowarta knn daga kasuwa tayo musu yar siyayya ta kunna wutar ice ta wanke tukunya ta dora ruwan tuwo


Tana xaune kan tabarma tana tankade taji sallamar kawarta murjanatu


Ta amsa tana kallonta


Murjanatu tanemi guri kusada Aminatun ta zauna tana fadin "kin dawo knn ainaxo daxun bansamekiba kinje kasuwa inji mama.


"Walh kam bandade da dawowa ba nayo mana siyayya.


Murjanatu tace "ah lallai tasamu knn ai haka akeso don babu batayiba kawata.


Aminatu tace "bari kedai kawata walh banda yau da Dr ma,aruf yaxo yabanikudi da bansan ya zamuyi ba yau.


Murjanatu tace "kai amma naji ddi wannan doctor gaskiya xa,aje dashi Allah yasa rabon kine shi.


Aminatu tayi shiru kawai


Murjanatu takalleta da mamaki tace "naji kinyi shiru bakice aminba kawata wai me kk nufi ne? Kina nufin bakya sonsa cin kudinsa xakiyi ki yaudareshi sbd wani banxa aminullah ?




Aminatu ta ajiye rariyar jikinta asanyaye tace "narasa ya xanyi murja inason burni inason kauye aminu mutum ne baikamata abarsaba sbd halinsa hk doctor ma mutum ne nasan yana sona shima amma munfi shakuwa da aminullah banaso aga kmr ni nayaudareshi ne.


"Aita fada mana kada ki biye ta mutane ki cuci kanki ko xakice min bakya son Dr ma,aruf?


ta girgixa kanta ahankali tace "ina sonsa mana.


" to walh bari kiji aminatu gara ki tsaida xuciyarki ta daina rawa inko ba hkba zamu bata ke barima kiji inhar baki daina batun aminullah ba zamu bata kuma inhar baki baiwa Dr ma,aruf damaba to zandaina shiga sabgarki sbd baxai yiwu arxiki nabinki kina guduwa ba me ake da soyayya da talaka awannan marrar haba aminun me.


Ho ! Murjanatu akwai fada gata yr baranbaran


Aminatu tazuba ido tana kallonta tasan halin kawarta sosai akan hakanma saitayi fushi me nisa da ita lallai murja ta dauka da zafi to ita ya zatayi?


murjanatu ta mike tana zura takalmanta tace "nina tafi gida saikin shigo...




"To inna gama girkin zanshigo.




Aminatu tai tsai da ranta tana neman mafita shin wanne zata tsayar Aminun ko ma,aruf din?????






*fans kutayata zabi mana*🀣🀣🀣
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login