Showing 1 words to 3000 words out of 33792 words
Chapter 1 - YAR MAKAFI 1 to END by Nabilancy Love .txt
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗
*'YAR MAKAFI...*
♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗
```written by.....✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUV💘*
*♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
PAGE..........1 TO 5
Tuk'i yake cikin nutsuwa da alamarsa yana cikin nishadine wakar larabawa yakeji yanabi yana gyada kansa da murmushi akan fuskarsa
Wayarsa ta dau tsuwwa kirane ya shigo saida ta kusan katsewa kana ya dauketa nan take yasha mur fara,ar fuskarsa ta gushe lokaci guda bakin ciki ya xiyarceshi baya qaunar mu,amalarsa da yr nacin nan Lubna sonshi take tamkar ta haukace shikuma kinta yake wulakanta ta yake amma taki hakura
Yaja tsaki tareda ajiye wayar amaxauninta ta sake kira akaro na biyu yakatseta tareda kashe wayar gabaki daya
Adai dai round about na danjar dangi yaja ya tsaya da saurinsa ganin wasu makafi zasu gifta ta gaban motarsa tareda yarsu data rike musu sanda
Allah ne yataimaka dabai gogesu ba yakurawa yarinyar ido fara ce kal gashinta har gadon baya bazata wuce shekara sha tara sha takwas ba amma dai baxatai ashirinba danma tanada garin jiki
Ta gaban motarsa suka gifta sukaje gindin motar dake gefensa suna bara
Take yaji zuciyarsa ta tsinke tausansu yaratsasa gasu dai fes dasu amma da alama babu karfi ba matallafi
Yarinyar ta dauke masa hamkali jinta yai har kokon ransa kyanta yafi tafiya dashi tamkar balarabiya haka ya fasaltata
Dai dai glass din motarsa sukaxo suna barar
Ya zuge glass din ahankali take Allah yabashi sa,a suka hada idanu da ita baisan sanda yasakar mata murmushiba
" Allah ya tsare Allah yak are mallam ataimaka mana da sadaka sbd Allah da annabi.
Muryarta ta sukurkutar masa da zuciya dan bakinta kawai yake kallo
Dubu daya ya miko mata yana murmushi
Da rawar jiki ta karba fuskarta cike da mamaki
Tace " banida canji "
"rike duka " yammata nabaki sadakarta sbd Allah da annabi kinji.
Da gaggawa tahau gyada kanta fuskarta da fara,a alamun jindadi ya ziyarci ranta tace " Allah ya karba ya biya bukata.
Kafin yai magana ta janyo hannun iyayenta dake gefenta sunyi gaba
Yabisu da kallon tausayawa tabbas saiya taimaka mata kota wata hanyar ne domin zuciyarsa ta kamu
danja tai musu alamar tafiya haka yaja motarsa yai gaba yana aiyano yarinyar aransa domin yaci alwashin saiya dawo gareta kota halin k 'akane
*****- ****** ******
Sai da Dr ma,aruf yajera kwana uku yana xuwa shatale talen dangi gun danjar nan duk don yaga wannan yr makafin amma baiganta ba sai hankalinsa ya tashi matuka gashi baisan wanda zai tambaya ba tunda ba sanin sunanta yai ba
Akwanakin ukun nan shiyasan halin daya kasance domin yanda yake ganin rana haka yake ganin dare
Fuskarta kawai ke mata gixo muryarta na masa burari akunne
Akullum sukuku yake wuni ko agida saida aka gano shi domin mahaifiyarsa gaba ta tusashi da tambayar meya faru dashi kwana biyu taga canji atare dashi
B 'oye mata yai domin ba yanxu yakamata tasaniba balle yasan ma babu fanin sanin ga mum din nasa tunda yasan halinta ba kaunar mu,amala da talakawa takeyiba gashi kuma tana so ya auri diyar kanwarta Lubna
Ko agun aiki baya da kuxari aikinma gefe yake dashi dan dai babba ne babu me takura masa balle abashi quiry.
Abokinsa Dr lurwan kawai yagayawa matsalarsa shima saida ya matsa kana yagaya masa
Aiko dayake shi din me damuwa da damuwar sane tuni akwana na hudun da baijeba yatusashi agaba suka je bakin danjar
Ckn sa,a suka hangosu daga nesa Dr ma,aruf nahangosu yaji wani sanyi aransa da murnarsa ya nuna wa Dr lurwan su da hannu
Dayake ackn go slow ake ta koina acunkushe gun yake da abun hawa
Gashi bata bangarensu makafin suke ba
Kusan minti sha biyar ba,a basu hannu ba
Gashi yadaina hango yarinyar da iyayan nata
Ko da cunkoson ma yarasu da aka basu hannun gefe sukai farking suka hau hange ko Zasu ganosu amma abin mamaki ko kusa ko alama babu makafin nan da yrsu
Ran Dr yai matukar baci yahau tsaki
Dr lurwan shiya kira wani me saida biscuit yahau tambayarsa makafin nan matashin yace dasu ai yanxu suka tsallaka titi suka tafi.
Dr lurwan yace " ko kasan gidansu kanina?
girgixa kansa yayi yace " walh bansaniba don basu dade da fara xuwaba bakine.
Dr ma,aruf ya doki gaban motar yana jan hucin takaici
Lallabashi abokinsa yayi suka hau mota suka tafi akan gobe zasu dawo...
*Auntyn S &S*💘
&
*Fresh Ummiey xeey*
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗
*'YAR MAKAFI...*
♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗
```written by.....✍🏼```
*FRESH UⓂMIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUV💘*
_Auntyn S & S_
*♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
*PG. 10-15*
Jikin Aminatu yai matuqar sanyi jin yaron yanuna mata wanda ke kiranta take tafassara wani abu ckn ranta a dabarance saita nemi gindin bishiya ta zaunar da makafin iyayan nata tace dasu tana xuwa
Ta nufi inda Dr ma,aruf yake da takunta ckn nutsuwa tafiya take gwanin burgewa tana wani rangaji fakistan ne ajikinta duk da sunsha jiki amma sunmata kyau
Yakurawa surarta idanu yana hamdala ga Allah " tabbas anyi halitta anan! Yafada ckn ransa
da sallamata isa gareshi yayindashi yaxurfafa a tunanin Aminatun
Saida tai masa sallama sau biyu kana hankalinsa yadawo jikinsa
Yayi murmushi yana kallonta yace "Ranki ya dade zinariya barkanki da isowa "
" ZINARIYA! kuma? Ta tambayai kanta
Tayi mamaki da saurinsa hakan zai mata inkiya me dadi
Saitayi farin ckn hakan har taringa ayyanawa aranta inama dai sonta xaice yake ai da kakarta ta yanke sa,a da burinta ya cika
Gashi kyakykyawa gamasu gdn rana wanda kullum take addu,ar Allah yakawo mata me nera wandaxata huta iyayanta su hutada bakar rayuwa me dauke da bakin talauci
Harkasa ta gaidashi fuskarta dauke da murmushi
Shima murmushin yake yace "ranki ya dade Allah yasa nakasance da sa,a akan abinda nazo mk dashi domin abin me muhimmancine.
takama baki tace "to! Wannan wane abune haka!?
ya fito sosai daga motar tareda jingina jikinta yace "dafatan dai kin " shaidani?
Ta
Girgiza kanta tace "ko kusa ban dau muryaba bankuma gane kaba.
Yai jim kana yace "Amma dai baxaki mance da mutumin daya baki sadakar dubu dayaba kwana hudu daya wuce ko.?
Tayi murmushi data tuna tareda daga kanta tace "na tuna kam,kamar ma kai ko? Tafada tana kare masa kallo
Ya gyada kansa yace "kwarai nine dafatan banyi laifin gaggawar dawowa gareki ba domin baxan boye mk ba nashiga wani hali akanki zuciyata ta azubtu akanki ckn kwanakin nan natakura da tunanin ki dafatan zan samu karbuwa ?
duk da jin hakan yaiwa Aminatu dadi amma saitaji wata kunyarsa ta rufeta kamar ta tsaga kasa ta shige dan wani kwarjini yai mata kawai saita rufe fuskarta da mayafinta
Ya fahimceta to amma yanason jin ta bakinta dan haka saiya canxa salon akalar hirar da cewa
"ikon Allah ban karbuba knn da har naga anrufe fuska lallai kice namiki tsufa kenan?
Tayi saurin girgixa kanta " a,a walh bahaka bane
" to yane ?ai inhar ana sona to abude fuska inyi tozali da murmushi mekyau
Basaita saki mayafiba tana murmushi amma takasa hada ido dashi
Yaji dadin hakan dama son mace me kunya sai shima yahau murmushin yace "madallah naji dadin hakan to yaya sunan zinariyar nagaskiya ?
tace '" Aminatu "
"nice name nikuma sunana ma,aruf ni likita ne sannan Aminatu da Aure nake sonki niba yaro bane don natafi shekara arba,in babu wasa ckn lamarina da gaske nakeyi Aminatu ya kin amince inzo gdnku ingabatar dakaina ?
ta gyada kanta "Na amince.
"Da kyau naji dadi Amma inaso kiyi min abu daya danki farantamin rai.
Takalleshi da dara daran idanunta tace asanyaye "menene abun haka?
yace "inaso daga yau yazama rana ta karshe da zaki kara fitowa bara.
Dam!! Gabanta yabuga ikon Allah kajimu da mutum tace aranta " to inmunbar fitowa bara wazai ringa na abinci muda muke talakawa miskinai
"Ni zan ringa tallafa muku da komi Aminatu zandau duk wata dawainiyarku bazan gajiyaba
Tamkar yaji abinda take zantawa aranta yabata amsar datake sonji
" da wuri haka? tafurta ahankali
Ya daga mata kai " kwarai bazan gajiya ba kumaba,fatana kibani hadin kai inga nacimma burina na aurenki kinji.
Ita duk abin kamar a film take kallonsa kuga mutum me kyau mr kudi agaban " yar makafi yana nuna mata so harda batun aure anya gaske "?
" gaske ina sonki Aminatu kema kina sona?
taji ya watso mata wannan tambaya
kanta nakasa bakinta yamotsa ahankali tace " Eh ina sonka.
Yace " ok godiya nk yanzu dai ki koma gunsu dan muje gidan ingano
Ta juya ahankali takoma gun iyayanta takama musu sanduna suka nufi gida
Da yake gidan ba nisa har suka isa DR Ma,aruf nabinsu abaya dayaga sunshiga dan karamin gidan kasa saiya faka akusa dashi
Mintinanta kalilan dashiga tafito gareshi sukai sallama akan zai dawo gobe sui hira
Da zai tafi yakawo kudi yabata taki karba futuk haka yahakura
Har yaje gida yana tunaninta tabbas Matuka Aminatu tayi masa ta koina hanakalinsa kuma yakwanta sai tunanin ta inda zai fara taimakonta da kuma yanda zai gayawa momynsa zai Auri *"YAR MAKAFI....*
*MUJE ZUWA..*
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗
*'YAR MAKAFI...*
♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗
```Written by...👉🏽```
*Fresh UⓂmiey Xeey*
Da
*Nabilancy Luv*💘
*♻REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
*Page 5_10*
Aminatu yarinya ce me nutsuwa kyakykyawar yarinya asalin iyayanta "yan chadine basuda kowa agarin kano tun wata rigima data kacame suna garin meduguri da allah yabasu ikon guduwo garin kano basu komaba alokacin aminatu nada shekara biyar su biyu rak suka haifa Aminatu da kaninta Abdulrazak shi Abdul kyanda ce takasheshi yanada shekara biyu yarasu
Asalin faruwar makantar mahaifan Aminatu shine rashin lfy ta lokaci guda abin kamar almara mahaifinta shine yafara kwanciya ciwo dayake yanada sugar kuma suga nakama ido harta makantarsa tun yana gani dishi dishi har lamarin ya tsaurara ganinsa ya gushe gaba daya
Itako mahaifiyarta inna halima ganin nata yagusheni alokacin tana tsakar gida tana girki hadari yataso gari yai bakikkirin wata guguwa ta turnike gari anata iska tunda wata kura ta shigar mata idanu taga duhu yagilma mata shikenan fa tadawo gani dishi dishi wannan shine sanadin rashin ganinta tar
To wannan fa kaddara data samesu shine dalilin dayasa suke futa yin bara amma kafin faruwar hakan mahaifin aminatu mallam garba mutum ne me zuciyar nema domin tun dawowarsu kano yake yin aikin karfi don ganin yarufawa kansu asiri
Yai sana,ar saida icce akofar gida yayi garuwa sannan yana kan zuwa kasuwar singa dako tsautsayin yasameshi
Makwabcinsa mallam Ahmad mutumin kirki yana taimaka masa dama shi yafara sani zuwansa kano kuma yarikeshi rikon amana tamkar dan,uwa
Wani xubinma yakan biya masa hayar gidan dayake yi duk da shima bawani me karfi bane malamin makaranta ne a secondry ta maza daga bayane ma Yazama principal
Yarsa daya budurwa sa,ar aminatu ce kuma sun kulla kawance sunanta murjanatu saidai halayyarsu ta banbanta don murjanatu tanada tsageranci sannan tun tana karamarta yarinyace mr son abin duniya ga karyar tsiya da fi,ili
Yanda take son Aminatu tana mata alkairi yasa aminsunci yai karfi aminatu ta aminta da ita tare sukai pri da sec duk a makarantar gwamnati amma ita aminatu tana SS Two ta tsaya da zuwa ganin iyayanta sun makance take futa yi musu jagora akullum domin su samo abin da zasuci abaka
****--
Aranar da Aminatu tai gamon katarin haduwa da Dr ma,aruf yabasu sadakar dubu daya aranar ba karamin dadi tajiba murna fal cikinta domin tagaji da futa yin barar nan dan dai ma batada girman kai ne
Murjanatu tasha zugata akan tadaina futa bara amma ta kiya don batada matacciyar xuciya batason wataran agoranta mata da tana zuwa kwadayi gara ace mata tana bara yafiye mata hakan
Ko aranar da Dr ma,aruf yabasu dubu guda saida suka kare kana suka futa bara sbd cancana musu tayi kudin sukai kwana uku domin sunada garin tuwo da baban murjanatu yake dan yo musu awo
Aminatu itace komi na gidan shara wanke wanke da girki da kuma yiwa iyayanta wanki
Aminatu kyakykyawa ce yr duma duma fara ita ba gajera ba ita ba doguwa ba tana kama da larabawan misra
Gashinta har baya yake gata da dimple tana kokarin gyarawa don bata da kaxanta
******
Yana office zaune yana faman karkada biro akan file yai shiru da alama ya xurfafa tunani ne
Wayarsa ce takatseshi da ruri yai furgigit ya duba yana ganin me kiran yai tsaki tare da dagawa " hello meyafaru ?
daga can bangaren Lubna ta lumshe idonta tareda jan wani numfashi tace "Yaya kana ina haka? pls ina son ganinka.
Akaro na biyu yasake jan tsaki yace "kiyi min uban me? Lubna kinsan fa bana son damu ko ?
Tace "oh my god!wai yaya ma,aruf me yasa kk min haka ne dan Allah inkatsanine basaika fadamin ba walh akanka zan iyashan poison dan sonka zai iya cutarni inhar baka aminta daniba dom walh inaji ina gani bazan iya ganin ka auri wata ba niba... " ke! Dakata mahaukaciya!
Ya fada da karfi " kiyi duk abinda zakiyi ke kk jiyo tunda ke zararriya ce
Yadatse wayar yana huci
Ya mike ya hade files din dake table din ya fito ya kulle office din yabar asibitin batareda lokacin tashinsa yayi ba
Daga can tsalleken shatale talen rawun din yai fakin ya fito da kafarsa guda waje yana faman leka kansa ko Allah zaisa yaganota
Can kuwa Ya hango makafin tana tsakiyarsu rike da hannunsu yahango wani yabasu sadaka da sauri jikinta na rawa ta karba
Wani abu yaji ya tsaye masa aransa na tausan ta
Ya yafito wani yaro me pure water dasauri yaron ya iso gunsa ya mika masa ruwan
Dr ma,aruf ya girgixa kansa yace masa "ba siya zanyiba taimakona zakai ka kira min waccen yarinyar da take tare da makafin can.
Yaron yakallo inda take yace "to ' ya tafi da sauri kira masa ita
Dr ma,aruf ya kura mata ido daga nesa tabbas ayau za,a wuce gurin domin zai bayyana mata soyayyarsa sannan zai dakatar ta zuwa bakin danjar nan yin bara....
_Muje zuwa_
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦