Showing 18001 words to 21000 words out of 33792 words
Chapter 7 - YAR MAKAFI 1 to END by Nabilancy Love .txt
da kato, walh gudowa xanyi in kwana ince dasu mama me?
Aminatu tace " toke da me zaisa ki kwana dashi baki san shiba in dan yankan kaine kuma fa, kedai kitabbatar kin shaka masa maganin da mallam yabayar da xarar kinga hankalinsa yagushe saiki gudo.
Aminatu tace "to ai kuma wata daban muda muke bukatar samun cindo.
Murja tace " ke murnar ganin kudi tasa ban miki albiahir ba naga cindon agefen hannunsa kato ma kuwa daya mikon kudi nagani kwantar da hankalinki kawata buri zai cika kedai kiyi abu ataka tsantsan.
Nan xuciyar Aminatu tayi sanyi hankalinta yakwanta jin akwai abinda suke bida atare dashi
Ta gyara yar jakarta suwaga me sarka akadarta sukai sallama ta tafi gun motarsa ta shiga da addu,a abakinta
Yakalleta da murmushi akan fuskarsa yace " to kyau muje ko?
Ta gyada kai kawai
Yaja mota sukai gaba.
Nan tabar murjanatu nata murnar samun makudan kudi ga burinsu zai cika tashi guda basu sha wata wahala ba
Tanaso ta kirga kudin tana jin tsoron mutane don mutum mugun icene kada ayi mata aika aika in anganta da kudi sbd gurin tamkar da rana haka yake da haske manyar fitilu burjuk koina ga mata sunfara cika
Ita tananan har kusan goman dare babu wanda yatsaya gabanta dan haka saita yanke shawarar tafiya gida kawai tunda dama ita kudi take bukata kuma tasamu wanda in wani xai bata hakan ma xata iya samu
Tana tafe kafin tasami abin hawa wata mota ta tsaya agabanta
Mamallakin motar yaita mata horn
Ta tsaya taba jiran fitowarsa
Yaxuro da kansa yace mata " hajiya shigo arage muki hanya mana.
Babu jan aji ba komai ta bude gaban motar tashiga tana fadin "wash amma kataimakeni fa don yau masu abin hawa sunyi karanci atitin.
Yakalleta yana kashe mata ido yace "sanyin yau aiyayi yawa dole wasu zasuki fitowa nima dole ce tafito dani
Yasunan malamar? Yatambaya yana mata makirin kallo
Takashe ido guda tace " murjanatu Amma ana cemin Janah.
Yace "nikuma sunana Alh Labaran ina unguwar koki sannan ina business a kasuwar kwari ina muka nufa?
Tace " gida mana.
Yace "to baxamu wuce musha ice cream ba?
Tace " ba matsala muje mana.
Nan yakarkata akalar motarsa xuwa fine time.
<><><>><><><><><><>
Mukoma ga Aminatu mana
A babban hotel yakama daki Tahir
Daki me tsada yabiya suna ciki yasa aka kawo kayan cima iri iri
Taki cin komai
Ya matsanta mata amma tace akoshe take
Dakyar tadau ruwan faro tabude tayi makwarwa uku ta ajiye
Shiko dayake yunwa yakeji yacika cikinsa
Yakalleta yace " kinsan anfiso in za,ai harka atabbatar ancika ciki komi zaifi tafiya dai dai kema yanzun in kika jiki da nauyi saikinfi min sha,ani ko?
Taso ta hade rai amma sai ta tuna wani abu ta dan murmusa idonta akan katon cindonsa dake hannun hagunsa
Yakai hannunsa yacire mata gyale yadora kan jakarta
Yahau kiciniyar cire mata riga
Tasa hannu ta turarsa tareda matse zip dinta tahade ranta
Yayi murmushi yace " sorry nafahimta wato ban biyaba tukunna ko? Aina sha,afa ne,
Ya dauko jakarsa yaxuge ya danko makudan kudi ya xuba mata cikin jakarta
Tasaki ranta kadan amma gabanta naci gaba da faduwa domin batajin zata iya bashi kanta don budurcinta da take adanawa na doctor ne insha Allah
Allah yataimaketa ya mike yace "bari nadan shiga toilet na fito pls tashi kicire kaya mana.
Tace " to.
Yashiga toilet tayi saurin janyo jakarta ta dauko wata " yar hoda ackn leda ta rike ahannunta tana jiran fitowarsa
Minti uku saigashi ya fito dashi sai dan fant
Ta rintse idonta domin bata taba ganin tsiraicin namiji hakaba
Yaxauna daf da ita yahau ahafa yana son ya xuge mata riga
Allah yabata sa,a babu wata wata bai fargaba ta shaka masa hodar ahanci
Nan take yahau yin tari ahankali idonsa yajuya take yakada yaji ya masa nauyi yahau lumshesu
Jikinsa yasaki yajishi yai week
Ko hannunsa baxai iya dagawa ba
Yafado jikinta ita kuma ta wullashi kan kujera yafada rigijaaaa
Bacci ne yai awon gaba dashi baccin sihiri domin ko munshari bayaja tamkar wanda ya mutu
Anan tasami damar bude gefen jakarta ta dauko sabuwar reza agidanta
Ta lulo hannunsa na hagu tayanke katon cindon
Saida tsikar jikinta tayi yarrrr!
Bata zaci zata iya ba amma data tuna a inda suke komi zai iya faruwa kada wani yaxo a ma,aikatan hotel din debar kayan abincin da aka shigo musu dashi saitahau azamar boyewa
Jini saida ya bata gurin tasa cindon aleda ta wulla
ajaka
Ta mike da sauri ta rataya jakar akafada ta rufa gyalenta tayi hanyar waje
Kafin tafutan saida ta juyo ta kare masa kallo taganshi jipgi guda akwance
Da ace kudine yakawota da saita sake bude jakarsa ta loda to amma ba afabanta suke ba tunda tasami abinda takeso
Saida ya leka koina taga babu masu tahowa kana tafito
Tamkar mara gaskiya inka ganta kafafunta sai sassarfa suke tamkar zata fadi
Ta wuce reception mutum biyune bata kula suba ko kallonsu batayiba
Daya yana mata magana tayi banxa dashi gabanta na dakan uku uku
Taja ajiyar xuciya dataga ta wuce su babu wanda yabiyota abaya
To ashe ba anan gizo ke sakar ba
Saida taxo get zata futa taji wani security yakwalla mata kira
Tun daga nesa yafahimci kamar batada gaskiya shiyasa yatsaidata
Ya iso kusa da ita yace mata "ke daga ina haka?
Tayi shiru kanta akasa tarike jakarta kam
Yasake tambayarta ckn daga murya
"Nace daga ina kk?
Tace " ciki mana.
" ciki room nawa?
Gabanta ya fadi ita inama ta duba.
Kai tsaye tace masa "walh ban rike ko room nawa bane.
Data fada masa dakin da saiya sakata agaba sunje to amma duk da hakan saiyace da ita
"Meye kk sauri kamar xaki tashi sama
Tayi shiru yace "badake nakeba
"Ina sauri inje gida nayi darene fada nake gudu.
"To meye ajakarki haka?
Takalleshi atsorace gabanta yafadi akaro na biyu "nashiga uku asirina yatonu ni Aminatu shikenan sai kwanan gidan yari nasan baxan tsiraba ayau.....
*Auntyn S&S*π
Da
*Ummiey Xeey*
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: β¦ β¦ β¦ β¦
π π π π
*'YAR MAKAFI...*
β¦ β¦ β¦ β¦
π π π π
```written by.....```
*FRESH UβMIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUVπ*
*UβMIEY XEEY* _Kutayamu addua, Bata da lafiya...Allah ubangiji ya baki lafiya yasa kaffarane... Allah ya kawo maki sauk'i dear...Ina yinki sosai...Karki damu Allah na Sonki sosai domin bayinshi na kwarai yake jarabta da ciwo....Get well soon dear..ππ_
*PAGE 75-80*
gaban Aminatu bai daina faduwa ba,haka jikinta yafara rawa dakyar tasamu ta dake tareda kankame hakarta akada kam
Securityn ya matso dab da ita yana karewa fuskarta kallo yana wani miskilin murmushi
Bata yadda sun hada idanu ba kanta na kasa tana addu,ar kubuta aranta
Yakawo hannu zai karbi jakar yana fadin "bari na duba jakar inga nawa muka samu intayaki kirgawa ko kanwata.
Yafada yana kallon fuskarta da murnushi kan fuskarsa
Ta hade ranta tare da fadin "kada ka sake katabamin jaka tunda ba aikena kayiba inkudine sai abaka konawa ne amma banyarda da sai ansamin hannu ajakaba
Tana gama fadin hakan ta xuge cikin jakar yana lekowa yana muzurai ta bashi yr one k biyu ta zuge tayi masa sallama agaggauce tayi gaba tafice ahotel din tana hamdala ckn ranta da Asirinta bai tonuba gashi cindon yana gefe gefen jakar acan ciki aleda baka
Tana futa tayi saurin tarar dan sahu sai unguwarsu
Alokacin data isa gida tayu sa,a bakowa a unguwarsu anyiyyi bacci domin goma da rabi da muntina
Ta tura gidansu ahankali tashiga duk da makafin iyayan nata ba fada zasui mataba insunjiyo tayu daren
Da Sassafe bayan ta gama dumamen tuwo ta xubawa iyayanta takai musu daki tashige bandaki tayo wanka sannan tashirya ta xumbula hijab tafuce gidansu Murjanatu
Itanma tashirya tunda tasan da tafiya gun dan tusbbun don shikam da safiyar Allah akafi ganinsa don in rana tadaga layi ake tararwa makil gun yakeyi da mata
Sun sami ganinsa da wuri yayinda suka bashi abinda suka samo wato cindon yakarba yabata turare yakumace ta saurari yau zuwa gobe zataji kiran ma,aruf awaya ko kuma taganshi akofar gidansu.
Da murna suka baro gunsa yayinda murjan keta famfata akai
<><><><><><><><><>
Abangaren momy kuwa takwashe komi tagayawa dady tun dawowarsa daga lokojan
Shima saida idonsa yagane masa don yafi sati da dawowa amma ma,aruf baixo masa sannu da zuwaba yaimasa waya ma baixo gidan ba saidai yasameshi a office yatausayawa dan nasa domin duk yarame ya futa hayyacinsa
Basuyi wata kwakkwarar magana ba sai gaisuwa kawai daya hadasu
Yayinda dadyn yatashi hankalinsa yahada kan manyan malaman unguwa unguwa yabasu abin sadaka suka dukufa yiwa dansa addu,a
Akwai wata juma,a ma dayaje har office din Dr ma,aruf din yasakoshi agaba suka tafi masallacin juma.ar sbd za,ayi masa saukar karatu
Bayan an idar da sallar juma,a aka tsaya yin saukar karatu
Wanda akeyi dominsa ma saida suka bashi qur,anin yana kusa da dadyn yana rike da alqur,anin jikinsa asanyaye yabude inda yaga kowa ya bude yafara karatun dayaga suma sun fara
Ma,aruf yanada sani akwanyarsa tun yana shekara goma aduniya ya sauke alqur,ani sannan dayakai matashima yayi saukar hadda
Tabbas banda asiri kaddara ce da baxai cishiba kuma yaci ma,aikin Allah ma banda haka ma,aruf akwai ibada kuma yana amfani da saninsa
Yayinda aka gama saukar karatun akayi sadakar yan qur,anai masu ixu bibbiyu sannan aka raba carbuna
Anan wani amintaccen malamin dadyn me suna malam badamasi yabaiwa Dr rubutu yace maza yashanyeshi agun
Ba musu yasha kana malam badamasin yace nasati guda zairinga bashi don haka ko yazo ya karba dakansa kokuma zairinga aikawa dady saiyaje can gunsa yakarba kada yayi wasa fa
Yaja kunnansa sosai
Dady shiya dage akan dan nasa domin akullum in ankawo masa rubutu daga gidan malam badamasin saiyaita yiwa Dr waya har saiyabiyo ta office dinsa yasha kana hankalinsa ke kwanciya
A ckn satin ckn ikon Allah komi yafara dawo masa dai dai yafara dawowa hankalinsa
Hayyacinsa yafara komowa jikinsa saiya zauna yaita tunani shi kadai yana mamakin yanda akai ya auri lubna
Ko a office saida yarutsa abokinsa Dr lurwan yana masa tambayoyi akan ya akai ya auri Lubna dole yasan yanada masaniya akai
Dr lurwan bai boye masa komiba akan irin abubuwan daya ringa faruwa
Har hawaye yaxubda
Dr lurwan yaja kunnansa akan kada yanunawa lubna ta farat ta daya kurenta yabi asannu tukun
Kuma yace yadage dayin axkar da addu,o,in kwanciya bacci kada yaringa sha,afa don anfi cin mutum yaki in yai sake da yinsu
Dt Lurwan yaiwa dady waya yafara labarta masa yanda tafara kayawa
Sosai dadyn yaji dadin kasancewar abun
Lallai Allah Almusawwiru ne tabbas duk wanda yariki Allah da Alqur,ani zaiga haske ackn lamuransa koda aduhu yake to inya dage duhun xai yaye
Dady yaiwa momy albishir nakaryewar asirin jikin danta
Itanma murna tayi sosai tamkar tasa ruwa akasa tasha domin kullum itanma ackn addu,a take Akan Allah yajuyo da hankalin danta kansu yafitarshi atarkon shedaniya lubna abd afarko taci alwashin xuwa gun wani boka azariya yakarya sai kuma lurwan yaita mata wa,azi akan babu kyau xuwa gun boka yaita gaya mata dimbin zunuban da ake kwasa da kuma makomar me riko da zancen bokaye da yarda da abinda suka fada
To tunda ta wullar da shirka ta dukufa akullum yi masa addu,a
Ita yanzu abinda yafi daga mata hankali yanda yar,uwarta da suke subiyu rak aduniya ta juya mata baya akan " yarta tabbas ta tafka babban kuskure wajen hada wannan Aure gashi abin yasha mata kai
Dady yaringa tausarta yana kwantar mata da hankali
Taringa cewa dadyn " dole inyi kuka dady domin nasan Alhakin *yar makafi* ne yake bibiyata nayanda nashige hakkinta akan dana
Na tabbata da ita agidansa da wadannan abubuwan basu faruba
Dady yace "ai komi da kk gani arubuce yake agun Allah dole sai hakan ya faru kuma kaddararsa kenan dan haka komi yaxo karshe kuma.
Abangaren Lubna abubuwa sun fara tsaya mata cak lamarin yafara bata tsoro naganin yanda ma,aruf yaje juya mata baya a gadon Aurensu
Inta sakashi yai mata abu take zai hade rai ko yabita da mugun kallo
Jikinta yafara bata lamarin yai sanyi knn
In yana gida sai yaita tsare mata gida baya fara,a sannan yadaina cin abincinta ko wani lemo ahannunta tana gani xai shigo da take away yaci abinsa ko kallonnta bayayi
Data gayawa maminta ta waya saita dorata akan bata again sbd cemata tayi to xaman me takeyi dabata koma gun malamin nataba asake taro matashi kada abin yabaci
Haka tayi niyya kuwa domin komawa tayi gun dan tsubbun nata tayi masa jawabin komi
Wata dariya yaringayi mata yana cewa " saidai kiyi hakuri yarinya kibi wata hanyar domin kuwa kin gama cin duniyarki da tsinke abu yakarye tun tuni wanda baxai taba gyaruwa ba sbd iyayansa atsaye suke akansa da addu,a inkuma kk matsa zan mutu koke ki mutu saidai in wani wajen zaki canxa badai nan ba domin babu abinda xan iya mk.
Haka ta tashi jiki asalube takoma gida
Data fadawa maminta yanda sukai da bokan saita hauta da fada " to dan yafadi hakan ke kuma saiki zauna lallai kisani xaman gida yakusa faruwa akanki domin kinsan tunda akai hakan Zulaihat baxata barkiba agidan danta don haka maxa kinemo wani malamin ayi wani abun akai
Duk ta furgice ta baxama neman malami amma abin mamaki duk inda taje zance dayane akance mata tabari abun yalafa inko ta dage komi xai iya faruwa sbd ayanzu wutar tsanarta ke ruruwa zukatan mijinta da iyayansa
Dole ta hkr tasake dabara ta kwantar da kai tahau masa biyayyar karya
Itace gaidashi abinda batayi ada ko inxaisa takalmi tayi sauri tasunkuya tayashi
Baya hanata amma baya amsa mata gaisuwar ko fara,a yakeyi inyana waya data doso shi yake hade rai don baitaba jin irin tsanartaba sai alokacin
Haja taita jurewa tana ahnaye bakin cikinaa domin har hantararta yakeyi
Abinda yakeyi mata ada kafin aure kadanne akan nayanzu data saiwa kanta tsanar
Lurwan abokinsa shiya shige masa gaba sukaje har gaban momy yadurkusa har kasa yabata hkr akan abunda yai mata bada saninsa ba
Taringa share hawaye tana cewa " kayya babana ai ninajanyo nice ummul,aba,isin komi niya dace na nemi yafiya agunka
Fatana dai ayanzu inka yafemin kaje kabaiwa Aminatu hkr sannan in bata tsaida mijiba sai atura manya suyi magana
Wani sanyi yaji aransa data tuna masa aminarsa yasan amina nasonsa bakuma zatayi fushi dashiba
Addu,a yahauyi akan Allah yasa aminar bata fidda mijin aureba
Dr lurwan shiya rakashi har gidansu aminar
Alokacin tana kan sallaya ta idar da sallar ishsha,i tana laximi tana neman tuba nayanda ta aikata sabo arayuwarta
Saijin sallamar yaro tayi atsakar gida wai ana sallama da ita
Taji mamaki amma data ji yaron yace taxo inji Dr ma,aruf saitaji wani sanyi tareda cewa yaje yace tana xuwa.
Ba bata lokaci tafuta
Har kasa tagaidasu yayinda dr ma,aruf yatsira mata idanu
Lurwan ne yafara magana yace " Aminatu saikika ganmu ko?
Tace " Eh mana ainayi mamaki kodon ba abin mamaki bane tunda tunda ango natareda amarya wacce akafi sonta fiye da kowa....Dr ma,aruf yatsata da sauri " kada kice haka zinariya ina ckn wani haline wanda fadar sama babu dadin ji kada atsaya tone tone ma yanzu dai yafiyarki nazo nema na alhakinki dana dauka ba sonki nadaina ba amina har yanxu kece axuciya kuma nadawo da zummar in aureki koda agobene
Ranta fari qal tayi murmuahi tace " to ai babu matsala domin nima xuciyata har yanzun kaine saidai fatana karike alqawari kada asake kwatawa
Da sauri yace " insha Allahu hakan baxata sake faruwa ba yanzun dai yi mana magana da baba.
Tajuya ahankali tasami baba adakinsa tagaya masa zuwan su Dr ma,aruf
Shima baban yaji mamaki yakuma yi farin ckn dawowar Doctan
Sungaida babanta ckn mutunci sannan sukayi masa bayanin komi basu boye masa ba
Yatausaya wa ma,aruf nan yabashi addu,o,i na tsarin jiki
Godiya ma,aruf yayi yakuma cewa baban nan da kwana biyu iyayansa xasu zo don atsaida ranar aure
To tun daga nanfa hankalin masoyan yadawo jikinsu akwana biyu suka sake curewa tamkar basu rabuba
Murjanatu ta tayata murna sosai
Yayinda dady yahada tawagar abokai da wani dan.uwansa sukaje gidansu aminatu suka kai kudin Aure aka tsaida sati guda
Asatin momy tahado lefe da kudinta kuma taita jan kunnen ango akan kada yasake yanunawa lubna alamar ma zaiyi aure don tana tsoron kada tayi wani abin afasa
Dady yaringa dariya yace "yau naga uwa na tsoron makircin "yarta toki kwantar da hankalinki ma babu wanda ya isa ya tsaida abinda Allah yanufa komi xatayi akai baxai taba tasiriba don muna tayin addu,a akai muma
Momy tace " walh dady ni nafison ma yasaketa kawai ko hankali yakwanta.
Dady yace "akan me babu inda zataje barta ta zauna adakinta kuma gida daya xasu zauna gara taga takaici ko yayane tunda matar shige bata daraja ita dakanta zata kori kanta......
To wannan kenan
*muje xuwa nabilancy luv and Ummiey xeey*
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: β¦ β¦ β¦ β¦
π π