Showing 21001 words to 24000 words out of 33792 words

Chapter 8 - YAR MAKAFI 1 to END by Nabilancy Love .txt

25 Dec 2024

3079

🎗 🎗
*'YAR MAKAFI...*
♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗




```written by.....```
*FRESH Uâ“‚MIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUV💘*


😘 *Shout out to you guys.............*
_Emnoor Ahmad don💞_
_Neenah cool💞_
_Baby Ameesha💞_
_Muneerah💞_
_Mariam tijjani💞_
_Mar°ahmad 💕 And_
_All the members of Zauren UⓂmiey Xeey💞💞_
Thanks for your love, Ina matukar godiya da addu'anku kuma Alhamdulillah, Ina samun sauk'i....Allah yabar zumunci... *Ameen*




*PAGE......80..85*




Sati Daya yarage ayi biki aka kai lefe gidansu Aminatu akwatina takwas shakare da tsadaddun kaya kawayen momy da "yan unguwane sukai mata kara suka kai lefen


Yar uwarta ko leke balle suyi waya mahaifiyar Lubna hjy hauwa,u. abinda momy ma bata saniba hjy hauwa,un kara kullatar ta tayi aranta naganin Ma,aruf zaiyi Aure basu hanashiba tasanma da gayya akai hakan dan a bakantawa yar tane


Abin yataba zuciyar momy duk da tasan abinda yafi hakan ma na iya faruwa atsakanin su


Dr ma,aruf sai doki yake ji yake tamkar ayanzune zaiyi aure gani yake ma afankon sa yake domin lubna bata gabansa bata isheshi kallo ba kowa safgarsa yakeyi garama ita takanyi masa shishshigi alamarinsa shike gwasaleta


Ankai lefe da sati guda yana gida da safe yafito awanka yana shiri zaifita yaje suyi rabon IV shida Dr Lurwan


Lubna ta fito ta zauna akusa dashi ya matsa daga jikinta yana tattare katin daurin Auren daga kusa da ita


Takalleshi anutse tace " yaya inada magana me muhimmanci.


Batare daya kalletaba yace "abarta saina dawo daga rabon IVn Aurena.


Ta yamutsa fuska da takaici da qunci aranta tace " yakamata kasaurareni bawata doguwar magana bace.



Yace "ok inajinki kiyi sauri kada kibatamin lokacina. Yafada yana duba agogon hannunsa


Ta gyara xama tace " naje asibiti anyimin awon fitsari angano inada shigar ciki wata biyu.


Yakalleta da sauri


Tasaki ranta ganin kamar zataci nasara



Tace " Allah yasa abinda ke cikina yasami karbuwa agun mahaifinsa domin in kaki bashi kulawa bansan yazanyi dashiba.


Ya murmusa yace " to naji Allah ya inganta Amma ba haka naso ba naso ace matar danafi kauna Aminatu Autar mata itace zata fara samarwa momy jikan fari aduniya bake ba.


Ya mike tsaye yana zuba kati ackn wata leda


Tahau goge hawaye tana fadin " amma dai ko me xakace dai danka ne baka isa ka haramtawa kanka shi ba tunda kaikayi ajiyar kafin arabamu...."waye ya raba mu?


Yawatso mata tambayar baxata


Ido ckn ido tace dashi " kafi kowa sani ai tunda har marina tayi agabanka kuma tashiga tafuta taga kadaina sona alhalin ita ta kulla soyayyar.


Ya fahimci da mahaifiyar sa take sai yayi murmushi kawai baxai taba nuna mata damuwar sa akan duk wani abu daxatace akan abinda momy tasa akai masaba don karta samu kofar caccaba masa magama kullum


Tayita kuka tana fadin maganganun dataga dama


Shiko yai burus da ita yadauki jakarsa yafuce


Takaici yasa tahau cilli da kayan dakin tun daga kan bedsheet har filillika da kayan kan mirro


Tayi tsammanin zaiso abinda ke cikinta domin da likita yagaya mata tanada cikin ba karamin farin ciki tayi dashiba


Tunda tasan dole in akace dan fari za.a soshi fiye da komi zakuma adokanta dashi haka tasan jikan fari nashan tattali agun kakanninsa


To amma tun ba,aje koina ba taga hakanta baxai cimma ruwa ba tasan tunda uban dan yaki nuna farin ciki ba tantama kakannin ma baxasuyi dokin zuwanba


Tayi shiru tana tunanin mafita


Can tace aranta "dolene na sake wani shirin zanyi maganin ka yaya ma,aruf da duk wani da xai hanani rawar gaban hantsi koda zan rasa raina ne.








Ankarbi lefe daga gidansu Aminatu anyi karamci da mutumtawa yan unguwa da makwabta sunyiwa maman Aminatu kara sosai


An yaba kayan lefe yayinda aka basu tukuici me tsoka suka tafi suma suna yaba musu


<><><><><><><><>><>


Anyi biki cikin kwanciyar hankali yayinda amarya tace ba wata bidi,a da zatyi itakam albarkar aure take nema


Angon yaji dadin hakan kuma ta burge kowa


Amma su murja ba.a so hakanba


Part din aminatu komi need yasha tsaddadun furnitures da ango yaxuba mata komi shiyasiya labulaye masu tsada yan ubansun haka kayan wuta da kayan kicin shida Dr lurwan sukaita zaryar siyayya


Duk abinda sukai a part din Aminatun lubna bata san sunyiba balle wataran aiyiwa aminatun gori


Kayan gara kuwa taxo dasu na burgewa da yabawa iyayanta sukai mata


Babanta yayi bajinta


Sadakinta dubu hamsin ta mallakawa babanta kyauta tace yakara jari domin su rike kansu


Iyayanta sunyi mata addu.a sosai don sun rabu lfy


kafin akaita gidanta saida aka fara kaita gidan surukanta sukai mata nasiha


Dady yaji dadin ganin wannan rana Dan sa ya auri cikar burinsa


Haka momy tamkar ta lashe aminatu dan so da qauna


Kai tsaye aka wuce da ita gidanta amma har dakin kishiyarta lubna aka kaita akai musu nasiha tareda danka amanar amarya ahannun uwar gida


Ba yabo ba fallasa tace ta karba badan tasoba ganin idon mutane ne yahanata yin tijara don taciwa zuwan aminatu gidan wani buri ta kudiri aniyar saita axabtarta ta yanda xata bar mata gida da kafarta......


<> <> <> <> <> <> <> <> <> <>
Bayan Aminatu Amaryar Dr ma'aruf, Sun fita daga dakin Lubna, Hannu tasa akai ta fara kuka mecin Zuciya, Wani bakin ciki taji a ranta wai yau ma'aruf zasu raba wajen kwana, Wani zuciyan kuma tace Karki damu Ba dadewa a gidan zatai ba zan koreta


Bangaren Su mumy kuwa anyi biki Alhamdulillah, Ita kanta dataga Aminatun hankalinta yafi kwanciya da ita, Take Sanar da Dady ita YAR MAKAFI ta mata da ganinta akwai biyayaya
Dady" Yace uhm Allah dai yasa albarka ai tun farko abun da naso na Nuna miki kenan kika kasa ganewa, Dadyy Yace nima yarinyar tamun Gaskiya, Sai mui musu fatan zaman lafiya, mumy tace Hakane


*Su Dr ma'aruf Ango*
Suna zaune da matarsa Aminatu, Ya kalleta Yaji wani farin ciki ya mamaye ko INA na jikinshi dan har kwakwalwarshi, Murmushi yake tayi, Duk da akwai mayafi a cikin Aminatu bai hana taga Murnar da mijinta yake ciki ba, Bude fuskarta yayi, Yace Amarya ta bude mana in Ga Kyan fuskarnan naki



Tana Dan jin kunya amma haka nan ta sake jiki saboda ita ma burinta ya cika


Nan dai suka tashi sukai yanda addini ya koyar damu kafin a kwanta idan an kawo amarya...lol


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Lubna kuwa tana ganin 11pm yayi hankalinta ya tashi, Ta ayyana a Zuciyarta yau dai ba Su ba 1st night Toofaa


Su Ma'aruf kuwa sunyi wanka sunyi Sallah, Ma'aruf ya mike, yasa jallabiya, Gaban Aminatu ne fadi, A zuciyarta tace tabdijam, Tana kan sallaye Yace zo muje mu kwanta ko zinariya, Uhm hmmm uhmm tace" ya gane nufin ta se yai shuru, yazo gabanta Yace" haba dear ki tausaya mun mana, ki duba halin fa na shiga some month's back, kwata kwata se ahankali,
Aminatu Tace" uhm hakane, Nan ta mike duk jikinta a sanyaye hade da kunya Taje gefen gado ta zaune, zuwa kusa da ita yayi ya cire mata mayafin dake jikinta sannan ya koma ya kashe wuta toofaa, Ya dawo gareta ya fara cire mata kaya, tun tana bata so hardai Mu kaji wasu sound na tashi ....Nan muka bar dakin da gudu nida _Nabilancy_ lol




Suna cikin tsakiyar soyayyarsu sun tsunduma, Tun Aminatu na kuka har ta hakura, Makira kuma lubna tana jin abubuwan nata wakana ta fara bugu musu Kofa tana kuka, Tana ma'aruf cikina, Cikina, Cikina, kazo ka kaini asibiti, Shi kwata kwata baiji ba Dan hankalinshi baya jikinshi, Aminatu taji nan ta tureshi tace' Ya habibi...matarka na kira, Wai cikinta, Wani tsaki yaja ya kara kankame Aminatu Yace" please forget about her,


Ita kuma Lubna haushi yabi ya isheta kaman tai hauka, ganin Ma'aruf be fito ba ta shige daki, Cikin tsakar Daren nan ta kira maminta, Ta Sanar da ita abun da ma'aruf yai mata


Maminta tace" karta sama damuwa badai Yar makafi bace, Sai sun Ga bayanta Lolz..ranar dai Lubna batai Bacci ba Dan takaici da bakin ciki




Su Dr kuwa an kwana an hantse, Tun asuba Suka tashi suka gyara jikinsu Yai mata godiya sosai da ta Adana mai budulcinta, Ita dai Meenah uhm kawai tace Dan taji abun da taji,


Haka dai Suka ci gaba da cin amarcinsu, har One week


Aranar da Aminatu tacika sati agidan mijinta aranar ne yatara su dukansu afalonsa domin yayi musu nashi nasihar tareda tsara musu yanda kwanan girkinsu zai kasance


Sunfi minti talatin azaune suna jiran uwar gida lubna amma shiru bata fito ba


Harya gaji yasake kiranta awaya saicewa tayi yayi mata hakuri gatanan dai zuwa cikinta ke juyawa amai tagama yanzu


Yana kashe wayar yakalli Aminatu data kagara takoma dakinta


Yace ""kiyi hkr fa xinariya kinsan harka inta hada daku mata dole saida hakurin kinji wai batajin dadin cikinta ne amai ma tagama ayanzun xata fito inta gama kintsawa nasan kin gaji ko baby nah?


Yakarashe fada yana kashe mata idanu


Tayi murmushi tace " bakomi habibi muyi mata uxiri tunda ba ita kadai bace


Tana rufe bakinta saiga lubna tafito tana yatsina duk fuskarta acukule kamar tafasa kuka ganin yanda Aminatu ke zaune ajikin ma,aruf gashi ta tsula kwalliyar burgewa tayi kyau kamar a saceta


Wani kishi yatsaye mata arai


Ta nemi guri kusa da ma,aruf itama very tight ta zauna kusa dashi ta matse dashi sosai tana wani shagwabe fuska


Yagano nufinta


Sai ya kyasawa Aminatu ido alamat ta matsa itanma


Aminatu ta fahimta wayis, sai ta matsa adabarance


Yakalli lubna da bacin rai yace " ke wane shirmen banzane wannan kinzo kinwani kwakubeni kamar zaki shige jikina ko kunya mutane bakyaji.


Cikin tsiwa tace dashi " wane kunya zanji nida mijina nasan babu wacce ta isa ta hanani ne tunda kafin asan dadin jikin namiji nina fara sani kuma kome za,a dandala dai ajikinka saura nane ba.a isa anuna min kwarewa ba walh dan ba wayewa akafini ba ato inma da rawar kai aka shigo to amaidashi bakin kofa....ke saurara haka.! Ya daka mata tsawa tayi shiru da sauri


Yafahimci inda ta dosa yakuma san sai yayi dagaske zata bar gasa wa aminatu magana


Yakara hade ransa yace "ki saurara da kyau kijini ba hauka yataramu ba kuma ba neman rigima akace muxo yi nan ba kibude kunne kijini dakyau


Lubna tayi tsai da ranta take ta nemo nutsuwa ta antaya akanta domin taga mutumin nata babu wargi


Ya matsa daga jikinta data kwakubeshi kamar takoma cikinsa


Yaxamo babu wacce ta rabeshi cikinsu


Yafara musu nasiha afarko kana yafara da tambayat lubna yanda zasuyi girki dakuma yanda xa.a raba kwana


Tayi yatsina taturo baki tace "nikam kwana dai -dai nakeso karinga mana don banison karinga nisa dani sbd muna bukatarka akusa damu nida son dinka.


Yayi murmushi kawai yakalli Aminatu yace " to kefa yayi hakan ko kinada naki tsarin?


Da sauri lubna ta tari numfashinsa " duk wani tsari nata ai ba tasiri zaiyiba garama tayi shiru domin tsarin danai dole shi za,abi


Ran Dr ma,aruf yabaci abinda yatsana da mutum kenan katsalandan fadi ba.a tambayeka ba


Yace " ke na tambaya ko yaya? Kada nasake nasake jin bakinki inhar ba tambayarki nayiba stupid


Ta kule tahade girar sama data kasa jin ya xageta agaban kishiyarta (Ke
Kikaja
Lubna Allah yakara)


Aminatu tace " habibi aiduk yanda kace hakan xamuyi koda satine ai kai zaka tsara tunda kaine damu kuma kaine me kwanan banda tacewa amma ni shawarata anan tunda yayata tace kwana dayan takeso to ayi hakan mana kaga kada danka ya cutu ko kuwa? tafada tana dan murmushi na kissa


Yace " babu wani zancen d'a na domin sai yazo duniya za.a kirashi da d 'an tukunna don haka kusani kwana bibbiyu zan ringa yi muku kuma kowacce tayi girkinta daban tunda kowacce nada store da kicin abangarenta don haka banison nan gaba inkama wata da neman rigima




Yanuna lubna yace" danhaka ke lubna yau ina sashinki fakat kowacce ta tashi ta koma bangarenta




Aminatu ta mike da sauri takoma bangarenta


Shikuma yamike yafuce don gidan momy yakeson yaje zasu futa da dady


Lubna tahau cixar yatsa tabbas inbatayi wani abun akaiba to zata xama koma baya agidan kirkiri ma kada taxo tana gani Aminatu taci abinci akanta don namiji shike badakai


Takira wani malaminta awaya tasanar masa abindake faruwa da ita


Nan yace mata saitaxo da wuri yahada mata mallaka da kuma magungunan tsari kafin tata taxo karshe agidan.....






*Wannan kenan*
For Comments
08164640126








*Lolz..I knw you guys are eager to see what will happen next...Awwnnn kuci gaba da biyomu a sannu*




TEAM YAR MAKAFI *(Y.M)*








_Ummiey Xeey and Nabilancy_
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY: ♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗
*'YAR MAKAFI...*
♦ ♦ ♦ ♦
🎗 🎗 🎗 🎗




```written by.....```
*FRESH Uâ“‚MIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUV💘*




_INA KUKE MAKARANTA...KUKASANCE CIKIN SHIRI DOMIN SHAHARRIYAR MARUBUCIYAR NAN *NABILANCY💘* NANAN KAWO MUKU WANI LITTAFI ME SUNA_ *TARAIRAYA* Karku bari a Baku labari




*PAGE 85...90*


Aminatu na zaune Afalonta tana kallon Arewa 24 Nabila Nasir nagabatar da shirin yan drama wato kundin kannywood


Ta bada hankalinta agun taji daga can _compound_ ana rafka sallama


Ta rage volume tana amsawa tareda xubawa _door_ din ido


saida tayi tsai kana tagano muryar kawarta murjanatu ce


Da murna ta tarota suka zauna a three siter suna fara,a


Murjanatu takama baki tana kallonta da mamaki da sha,awa tana cewa "kai kawata tabarakalla masha Allah kinganki kuwa?


Aminatu ta murmusa tareda gyara xama tace "bana son zolaya murja meye na mamaki da ganin nawa Haka?


"bari kawai kawata kin canza da yawa fa kalli fatarki har wani sheki take kamar silva ga wani fari da kk kara kodai anyi tintibe ne


Ta kama baki tana dariya tace " hhhhmmm to nagodewa Allah dana samu canji mekyau ammafa bawani tintibe danayi don nasan nufinki ciki ko? To babu komi. Tafada tana shafa cikinta


Murjan tahau fadin " haka dai kk ce.


Nan suka hau hira har kusan wani lokaci


Kana Aminatu ta tashi tashiga kicin tayi musu girki shaf shaf makaroni jalof tasha kifi sannan ta hada musi lemo me sanyi dake tanada furji a kicin din






Nan murja ta kwashi gara


Da suka gama sukai sallah biyu tayi


Murja ta karkace tace da Aminatu


" waini ina matar gidan ne naji bangarenta shiru kada dai xaman doya da manja kukeyi?


Aminatu tace " ni ina ruwana da shiga safgarta ai tunda nazo gidan nan sau daya muka hadu banda ranar dana shigo gidan nan


Murja tace " aikon dai kada kiringa shige mata dan walh inta sami guri zata iya cutarki


Domin lubna muguwa ce natabbata ayanzun hakan xatayi yanda tayi takoreki agidan nan balle tasan kece matar SO


Sannan kuma abinda nakeso dake shine kitashi tsaye kema ba zama xakiyi ba afitarki da asiri zagewa zakiyi kiringa mallakar mijinki baji bagani inkin zauna kiga zama ba ruwana


Aminatu ranta yabaci da kalamin murja tace " niko ayanzu me xanyi banda bautar Allah da rike mutumcin Aurena sabon Allah yayi hagu nikuma nayi dama masu yima Allah yaganar dasu amma nikam nabarshi wanda mukai ma ada kullum cikin neman yafiyar ubangiji nakeyi dan haka kada ki kara minxancen yin asiri ma dan baxan yiba


Murjanatu taringa kallon Aminatu da mamaki najin tana mata banzan kalamai


Tace " lallai aminatu kin haukace ashe wayonki yafara yin baya to aiko baki isaba dole ne kiyi abinda xaki kwatowa kanki yanci gun miji yaxamo kin wuce uwar gida akullum yaringa ganin haskenki akanta don...." ke dakata murja natu akullum mijina yana ganin haskena kuma inada " yanci agunsa wayo kuwa indai akan nabar yin sab'on Allah ne to daga yau akirani da gab'uwa ma ato.


murjanatu taga abin na Aminatu gaskene saita kule harda harxuko mata sbd tasaba yi mata hawan kawara ko tai mata dole


Sai taga sabanin Yanda sukeyi ada taga wannan karan Aminatu ta butsare mata harma taga kamar ba aminatun taba domin itanma kanta tayo da fada da masifa tana fadin " kada ki kara dagamin murya akan nafadi gaskiya baxai yiwuba kixo har cikin gidana kiyimin dole baki isaba mijina ne kawai ya isa yasani tilas shima bata wannan hanyar da kk biyomin ba don tunda nadawo hanya banga wanda ya isa yasani na koma b 'ata ba never walh


Murjanatu ckn bacin rai tace '" Aminatu yau nikikewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login