Showing 36001 words to 39000 words out of 82053 words

Chapter 13 - Ni Da Shugaban Kasa Complete Book Reefat Yahya .txt

10 Jan 2025

4872

kyau ba, kuma Allah yasan nayi iya bakin kokari na but umaima is rily stubborn"
A hnkli ta sarke hannunta ckn nasa tace
"I knw dat but a hnkli zaka lallaba ta ba sai ka hada da duka bah, kuma adua zaka mata kaji koh my man"
Kai ya gyada mata sai kuma ta tashi ta debo pineapple drink me sanyi a firji ta xuba a cup ta dawo ta mika masa ba gardama ya karba ya kurba sau 3 sannan ya ajiye cup din a kasa yana kallonta yace


"Nagode Allah ya miki albarka tnx a lot ..am..


"Shhhh....yatsa ta dora a bakinsa tana murmushi tace
"Is my duty as ur wife, ina alfahari da kai kana da matukar girma da daraja a ido na I can do anything for u.kuma ina jin dadin aduar da kake min nima nagode sosai"


Shi kam yana mamakin hali irin na shuairat tana da tunani da kaifin basira sosai abun mamakin ma shine, bata nemi sanin laifin umaima ba kawai ta hau bada hakuri duk da irin kiyayyar da umaiman ke nuna mata Amma bata taba nuna damuwarta bah hakan ba karamin dadi yake ji ba ta wani bangaren kuma idan yayi la'akari da kulawar da take bawa sultan yakan jinjina mata tabbas yayi dace da mace ta gari.
( mata mu kula pls..mu rike ya'yan mazajen mu da xuciya daya muyi koyi da kyawawan halaye irin na shuairat banda hassada da kyashi , hakan zai sa mijinki ya girmamaki kuma ya kara sonki..Allah yasa mu dace Ameen)


"Mr president tunanin me kake ?
"Uhmm..ba komai nagode zan koma side dina ina Dan wani aiki ne"


"Ok muje na ma rakiya"
"No..don't worry kiyi xamanki ki huta "
"A'a muje zan tayaka hira idan kana aikin"
Ba musu Suka fito tare suna tfy har xuwa bangaren sa.
Umaima kuwa family doctorn su ne yaxo ya dubata ya bata magunguna nan kuwa zazzabi ya rufeta.
Kowace safiya shuairat tana xuwa tana duba jikinta duk da cewa umaima bata kulata Amma bata fasa xuwa bah haka nan sultan ita ta cigaba da kulawa dashi tana kuma kulawa da mijinta ba laifi ynxu ta saba da mr President sun fara shakuwa Amma ba wai can bah.


***********
Haka rayuwa ta kasance yau da gobe sai Allah ynxu shuairat ta share wata3 a gidan mr President kullum sai tayi waya da mama da babanta su Suka hanata xuwa , umaima kuwa babu abunda yake hadasu kowa na sabgar gabansa sultan kam ya gama shakuwa da ita kullum basa rabuwa idan yana gida dai suna tare a can bangaren mr President. Haka nan suna waya da momsi da daddy mah kullum, rayuwar gidan de gwanin shaawa masu aikin ma suna yaba halayen shuairat bata da girman kai ko kadan.matan ministoci da sauran abokan mr President duk sun saba da ita suna yawan kawo mata ziyara saboda faraarta.
Yau weekend babu aiki tun karfe7 shuairat tayi ado na gani na fada sultan ya koma bacci don haka ta fito ta wuce bangaren mr President , bedroom ta shiga yana zaune da carbi a hnnunsa a gefe ta xauna ta sunkuyar da kai kasa ya juya yana kallonta Murmushi ne ya subuce masa yasan akwai maganar da take son fada Amma ta kasa


"My lady ya dai"
"Ina kwana dad sultan"
"Lfy ya kuka tashi"
"Lfy alhamdulillh"
Sai kuma tayi shiru ta rasa me zata fada
"Fadi bukatar ki my lady"
Kai ta daga Suka hada ido yana murmushi yace
"Kina mamaki ne? Just tell me mene ne..
"Umm..ehmm..dama..
"Mom sultan go 2d point ok"
Ya fada a yayinda ya tallabo habarta ta runtse ido a hnkli tace


"Gida nake son xuwa gun mama"
"Mama's gal! Kin manta baba yace sai nan da 1 yr zaki fita?
Rau rau tayi xata fara kuka yana murmushi yana kallonta yace
"Oh no! Shagwaba again, gara ma ki Adana hawayenki cos babu inda zaki"
Hawayen da suke makale Suka fara gangarowa mr President ya zare ido yace
"Ohh...yi hakuri ba sai kinyi kuka bah tashi ki shirya muje koh don't cry pls"
Nan kuwa murna fal har ckn ranta taji dadi kawai ta rungumesa tare ta yi masa peck a kumatu tace
"Tnk u so much mr President nagode"
Daga nan ta tashi zata ruga a guje yayi saurin riketa yace
"Ke lafiyanki? AHakan zaki fita securities suna kallonki? Idan kinyi ma sai mu fasa xuwa sai ...
Bai karasa ba ta rungumesa ta baya ckn salon shagwaba ta fara magana
"Eyya fah...yi hkri toh na daina tsallen a hnkli xan tafi kaji"
Shiru yayi yana jin wani irin yanayin da ya kasa tantance ko menene dakyar ya furta
"Ok jeki ki shirya tare zamu je" nan ta bude kofa tana tfya tana murmushi ita kadai har ta fice daga bangaren nasa.




😘😘😘😘lov u all
[2/21, 2:40 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*54*
By *Reefat yahya*




Mr president yabi bayanta da ido yana murmushi tare da girgiza kai shuairat tana da shirme wllhi tana Abu kamar karamar yarinya.
Shuairat kuwa wani wankan ta sake yi tasha ado ckn wasu leshi maroon n golden da touches din milk color ta saka yan kunnen gwal tayi kyau sosai.
Karfe 8 ta gama shirinta tsaf haka nan ta shirya sultan ma ckn kananan kaya yayi kyau sosai sai qamshin turare ke tashi daga nan Suka wuce bangaren mr president a can sukayi kari ckn jin dadi suna ci suna Dan taba hira.


Karfe 10 na safe motoci sukayi parking a kofar gidan Alh bello maiha shuairat ta fito ckn xumudi ta fada gidan tare da sallama falon mama ta wuce suna zaune suna hirarsu ta fada jkn mama tana dariya farin cki ne bayyane a fuskar iyayen nata baba yace
"Ahh...ya'r baba wato kinfi son mamanki koh"
Nan ta tashi ta koma kusa da mahaifin nata tana dariya tace


"Ba haka bane fah..baba nayi kewarku sosai"
Daga nan Suka gaisa bash ne ya shigo yana hararinta yace


"Bansan yaushe zakiyi hnkli bah , dama kinzo da mr president shine kika baro shi a waje"


"Lalala..baby dama tare kuke shine kikayi zamanki baki sanar damu bah


"Toh baba nikam ba na manta bane"
Ta fada tana xumbura baki daga nan mama ta tashi ta koma ckn daki aka shigo da mr president dama sultan kam yana xaune a falon , ckn girmamawa Suka gaisa da surukin nasa sun Dan taba hira sama2 sannan yayi sallama ya tafi.shuairat kam ta haye gadon mamanta ta mike tana jin wani dadi, sultan kuwa ya sake sosai yana xubawa baba hira mama ta kawo masa abinci yaci sannan ta koma daki gun ya'rtata suna hira tana tambayarta zamanta kewar tasu , shukrah ta shigo Suka baje sunata surutu mama ta koma falo tabar musu dakin.shukrah ta gyara zama tace


"Mutuniyar kinga kyawun da kika kara kuwa? Sai wani shinnin kike ko dai..ta kanne mata ido daya shuairat ta buge kafadarta tace


"Munafuka! Toh ba abunda kike nufin bane
"Hmmm..wa yasani Abu a duhu..maybe rabo ya zauna naga sai wani kyau da haske kikayi"


"Shukrah kenan..baki da dama wllhi, don kina da ciki shine kike zaton kowa ma haka ne?


"Hee...wa yagaya miki ciki ne dani?
"Ahaf..tun yaushe naji labarin a gun Yaya"
"Hmmm..zai dawo ya sameni ai tunda Allah yayi shi da shegen suru2"
Shuairat ta fashe da dariya tana tsokanarta shukrah tace
"Ke dinma na baki nan da wata daya..naga wani kalan soyayyan da kuke har rakaki anguwa yake hmmmm"
"Oho dai..ki fama dashi "


"Baby me sirrin ne, naga alama fah mr president ya fada kuma naji labarin xuba love da kukeyi a gaban kowa ma Baku jin kunya"
"Ikon Allah..shiko Yaya dan sa ido ya koma! Lallai zan gayawa mr president "
"Keee..rufamin asiri wasa nake miki"
Haka Suka kasance suna yiwa juna shakiyanci .
Yinin ranar curr..tare sukayi ckn farin cki da walwala har xuwa 7pm sannan aka zo daukan su shuairat ta koma gida.


Karfe9 ta gama shirin baccinta tsaf xata kwanta sai kuma ta tuna tabar wayarta can falon mr president kuma tana son shiga watsap dole ta tashi ta Dora hijabi kan kayan baccinta ta nufi bangaren mr president.
Yana xaune a falo yana shan coffee idanunsa nakan TV yana kallon news, ta shigo tare da sallama can cki ya amsa ba tare da ya juya ya kalleta bah.wayar na gefensa akan kujera batayi masa magana ba taxo wucewa zata dauka ckn rashin saa tayi tuntube da kafar mr president tayi luuu...ta fada jikinsa jagwab Suka kurawa juna ido , turo kofar akayi tare da sallama umaima CE ta shigo suna hada ido da shuairat ta saki wani shuumin murmushi nan kuwa ta Dora bakinta kan bakin mr president ba shiri ta fara kissing nasa tamkar xata cinye shi.
Mutuwar tsaye umaima tayi ta fara jin haushin kanta tayi regretting xuwan da tayi ckn axama ta juya tabar falon shuairat na ganin haka ta cire bakinta mr president kam saura kadan ya suma..tunda yake a rayuwarsa bai taba shiga irin yanayin da yake cki a hlin yanxu bah, shuairat kuwa wani irin kunyarsa take ji ta kasa tashi daga jikinsa kuma ta gagara hada ido dashi.sun share minti 10 ckn wannan halin sannan ta tashi tmkar Mara gaskiya ta fara tafiya a hnkli rike hannunta mr president yayi sannan ya damka mata wayarta a hannu daga nan ta juya tayi tafiyarta.
Bacci ya gagaresu mr president shuairat da kuma umaima kowanne da kalar tunanin da yake dakyar bacci ya sace su.
Asuba tagari ....




😘😘😘
[2/21, 2:40 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*55*
By *Reefat yahya*




Haka rayuwa ta kasance shuairat ta share shekara daya a gidan mr president zaman nasu ba laifi tana bashi kulawa irin Wanda baa rasa bah, sultan kam ya manta da cewa shi maraya ne cos shuairat ta maye masa gurbin uwa tana basa kulawa fiye da komai.shukrah ta haifi danta namiji mai kama da ubansa sak aka rada masa suna Bello ana kiransa waleed. Ynxu kam duk fadin Nigeria babu inda baa San fuskar shuairat bah tana yawan xuwa gidan marayu tana tallafa musu haka nan ta bada shawara aka bude makarantun islamiyya da dama ga kuma masallatai, bangaren asibitoci ma sun bada gudunmawa.


Shuairat ta kara cika tayi kyau sosai alamar Hutu ya bayyana a jikinta ta kara haske sai sheki take yi, shuairat ce a kitchen tana bada umarnin girkin da zaayi yau surukan nata xasu kawo musu ziyara itama ta taba xuwa sau daya. Karfe 4 Suka shigo gidan ckn murna ta tare momsi direct dinning Suka wuce nan Suka gaisa ta xuba mata abinci ta tura a gabanta


"Hoo...shuairat daga xuwan mutum ki tura masa abinci a gaba "
Murmushi tayi tace
"A'ah momsi kamata ki fara da abinci kafin ki huta koh"
Ba gardama fara cin daga nan shuairat ta tashi taje gun daddy Suka gaisa.
Da dare suna xaune a babban falo a bangaren shuairat ita da momsi da sultan da kuma umaima suna ta hirarsu umaima bata sa baki bah don ta lura da shakuwar dake tsknin momsi da shuairat. Sultan ne ya juya gun shuairat yace
"Anty muje mu kwanta bacci nake ji"
Carab momsi tace
"Kaji min yaro! Dama kullum da ita kake kwana ne"


"Ehh..mana granny baki sani bah dakinmu daya da anty nah , ita take kula dani tana sona sosai"
Zare ido momsi tayi tana kallon shuairat har umaima tayi mamakin jin hakan shuairat kuwa ta sunkuyar ya kai kasa ckn jin kunya ta gane kallon da momsi take mata..Muryar momsice ta katse ta tana kiran ladi mai aiki ba bata lokaci taxo ta rintsina ckn girmamawa


"Ki raka sultan dakin baccinsa"
Dakyar sultan ya amince saida shuairat ta lallabasa tace masa tana nan xuwa.wayar hannu momsi ta fitar ta kara a kunne
"Ka sameni a falon matarka"
Daga nan ta kashe wayar ta juya tacewa umaima ki bamu waje xamuyi magana, nan ta tashi ta koma bangarenta.ckn kankanin lokaci mr president ya shigo falon tare da sallama ya nemi waje kusa da ita ya xauna nan ta fara magana


"Ina son jin meke faruwa a gidan nan"
Ckn rashin fahimta mr president ya daga ido ya kalleta
"Momsi wani Abu aka gaya miki ne? Nidai nasan ba komai muna xaman lfy da ita kodai tace na mata wani abun?


"Boy kenan.. Ka bani mamaki wllhi, ynxu da girman ka da ilimnka amma ka kasa sauke hakkin aure dake rataye a kanka?


"Momsi wane irin hakki? Wllhi muna xaman lfy da ita gata nan ki tmbayeta koh my lady na taba bata miki raine?
Sunkuyar da kai shuairat ta kara yi momsi ta ja tsaki sannan tace
"Ynxu irin xaman da kukeyi kenan? Tsawon shekara 1 da auren naku Amma ....
Ta kasa karasa maganar sabida nauyin Kalmar sai kuma tace


"Kasan idan Alh yaji wannan maganar ranku xai baci ba kadan bah, garama Ku daidaita tskaninku Ku wuce Kuban waje sakarkaru kawai"


"Kiyi hkri momsi Allah ya huci xuciyarki"
Shuairat ce ta furta a hnkli mr president kuwa kansa a kulle yake ya kasa gane me take nufi haka nan shima ya bada hkri sannan ya mata saida safe ya koma bangarensa, itama ta tashi tace
"Ni zan Kwanta maza ki shirya kibi mijinki ynxun nan"


"Mu kwana lfy momsi"
Daki ta wuce ta fada wanka bayan ta fito ta shirya ckn kayan baccinta ta fesa turaruka daban2 sannan ta wuce bangaren mr president wani irin kunya take ji gani take tmkar bodyguards din duka ita suke kallo.a hnkli ta turo kofar dakin tare da sallama yana xaune ya buga uban tagumi yana ganinta ya tashi a hnxarce ya karasa ya jawota tare Suka xauna a gadon yace
"Pls Aysha wane laifi na miki zaki hadani da momsi na Wanda bazaki iya gaya min bah..kinsan tunda muke bata taba fushi dani bah amma yau naga alamar hakan a fuskarta"
"Am sorry mr president wllhi ni...
"Just tel me Aysha me na miki"
Nan ta fashe da kuka tana cewa
"Ni..ni baka min komai bah kuma babu abunda na gaya mata"
Ya fara rarrashinta yace
"Ok naji ...ba laifinki bane , toh gaya min me ya faru"
"Umm...ba sultan bane ya gaya mata cewa kullum tare muke kwana "
"Ok..nagane, kinga ynxu sultan is 8yrs old tana ganin ya girma bai dace kuna kwana tare ba koh?
"Ah'ah..tana nufin cewa uhmm..uhmm"
Shiru tayi ckn jin kunya ta rufe ido tana murmushi dogon numfashi ya ja sai ynxu ya gane me momsi take nufi da cewa ya kasa sauke hKkin aure ...hmmm anya zai iya????


Masu karatu ya kuke gani hakan zata faru kuwa??


Hmmmm...muje xuwa
Love u oll😘😘😘
[2/21, 2:40 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*56*
By *Reefat yahya*




Shiru sukayi dukkansu biyu daga karshe shuairat ta tashi zata fita yace
"Ina zaki ?
"Uhmm..falo zan koma can xan kwanta"
Wani irin kallo ya watsa mata ba shiri ta dawo ta xauna
"So kike ki tonamin asiri ko me? ..as from today ki tattara kayanki ki dawo nan da xama"
Ckn Sauri ta kura masa ido ya kada kai yace
" yes! Ki dawo nan mu xauna tare kinga babu wanda xaiyi magana koh, oya ki hau gado ki kwanta ba sai kinje falo bah"
Ba musu ta cire hijabinta ta hau saman gadon ta kwanta a gefe tayi aduointa ta shafa sannan ta rufe ido tana son bacci Amma ta gagara she is not comfortable.
Mr president kuwa ya tashi ya fada bayi ys watsa ruwa sannan ya fito ya saka kayan baccinsa ya fesa turare sannan ya kwanta a gfenta bata rufe da bargo ba ya kura mata ido na yan dakika sannan ya dauke kai.baccine yayi awon gaba dasu can tsakiyar dare ta mirgina ta koma kusa dashi ta kankame shi gam wutar dakin a kashe yake, ckn bacci mr president yaji alamar mutum a jikinsa a hnkli ya bude ido ya kunne side lamp tana baccinta ckn kwanciyar hnkli ya kura mata ido tana sauke numfashi a hnkli tayi masa kyau sosai ya juya zai kashe wutar ta Dan motsa nan ya koma ya kwanta a hnkli shima ya kara rungumarta.
Da asuba ita ta fara tashi a hnkli ta zame jikinta daga nasa ta fada bayi zama tayi a ckn bahon wanka tana lumshe ido tana tuna halin da ta farka ta gansu a cki, tana mamaki ya akayi hakan ya faru? Dakyar ta daure tayi wanka tare da yin alwala ta fito har ynxu baccin yake ta tsaya Jimm...hannu tasa a gefen fuskarsa tana shafawa a hnkli take ya bude ido tace
"Morning... Tym din sallah yayi"


Daga nan ta tada sallah tayi nafilfilu sannan tayi sallan asuba ta xauna tana Jan carbi ya fito ya gabatar da sallah haka Suka kasance har rana ta fito shuairat ce ta nade sallayar ta xauna a gefe tace
"Ina kwana"
"Lfy ya kike"
"Lfy alhamdulillh"
Da tashi ta kama hanyar fita dakin
"Ina zaki ?
"Nayi wanka Xan je dauko kaya a...
"Dawo ki xauna xaa kawo miki"
Ba musu ta koma kan gado ta xauna tana wasa da yan yatsunta.
Falo ya nufa bayan yan mintoci ya dawo ya shige bayin da alama wanka zaiyi.motsi take ji a falon ta fito don ganin waye ne ga mamakinta akwatunan ta aka jera da sauran kayayyakin da ta mallaka a dakinta , wani dakine da yake kusa da na mr president a can Suka shigar da kayan sai kuma mata masu aiki Suka shigo Suka gaisheta sannan Suka shige dakin take Suka ajiye komai inda ya dace Suka gyara dakin se qamshi ke tashi daga aka hada musu abinci a dinning.
Tsarin dakin ya birgeta kwalliya ta fara yi bayan ta gama ta saka wasu material masu kyau daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login