Showing 48001 words to 51000 words out of 82053 words

Chapter 17 - Ni Da Shugaban Kasa Complete Book Reefat Yahya .txt

10 Jan 2025

4848

xaki xauna dasu ? Kinga sultan ma yana can nasan kinyi kewarsa daz y"
Kai ta gyada masa alamar ta amince nan ya rike hannunta Suka tashi tsaye a dai2* bakin kofa Suka ci karo da shukrah tana shiga..๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ฑ๐Ÿ˜ฑta xare ido ckn takaici tace


"Me zan gani haka? Wanke wanken da na saki kenan? Shine zaki kira mijina a waya..sannan har da rike masa hannu?
Aikuwa shukrah ta daga hannu xata kaiwa umaima mari bash yayi saurin rike hannun ya fara magana
"Haba shukrah behave urslf mana.. Meyasa kike yin Abu as if u ar not matured"
"Which kind matured..wllhi bazan yarda ba ai wannan cin fuska ne"
"Naji..is ok toh kiyi hkri ni na rike mata hannu n am sorry ok! Batun wanke2* kuma kiyi hkri bata saba ba kinga amanarta aka bani n I have to takkia of her "


"Haba baban waleed ynxu aiki ma ban isa in sata tayi ba sabida an baka amanar ta? Allah is not fair"
Shukrah ta fara xubar da hawaye bash ya sake hannun umaima ya jawo shukrah a jiki yace
"Am sorry pls ki daina kukan nan kinsan bana so..n bawai na hanata bane wllhi am sure bata iya bah "
"Kai dai kace min sonta kake shiyasa dama ka kawo ta nan gida saboda Ku dinga ci min face toh wllhi baxan yarda bah"
Ya juya gun umaima yace

" kije dakin ki ina xuwa" daga nan ya ja shukrah Suka bar kitchen wani kishine ya turnuke umaima nan ta koma daki ta cigaba da kukanta tasan lallai ta rasa bash har abada idan ta tuna yanda yake lallaba shukrah sai ta ji wani tsananin kishinsa..hmmm anya burinta ze cika?
















Muje xuwa๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
[2/21, 2:41 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*67*
By *Reefat yahya*




A daki bash yake bawa shukrah baki
"Haba my love ki Dan rage kishin nan mana ai zata raina ki..kuma ni ban ce miki ina sonta ba meyasa zaki damu kanki she is just lyk a 6ter to me pls kidaina wannan haukan"
"Ohh..hauka kace koh? Toh shikenan zaka ga haukan wllhi xanyi maganinta..zancen so kuma ai naga kwayar idonta sonka ne zalla a ciki, wllhi bazan barta bah"
Dariya sosai bash yayi sannan yace

"Hohh..shukrah! Dama haka kike da kishin tsiya?
Ta tura baki ckn shagwaba tace
"Dariya kake min koh..wllhi ni nasan tana sonka kuma kaima kana sonta kawai boyewa kake"
"Ok naji tana sona ..amma trust me ba komai tsakanimu kinji? Ki kwantar da hnklinki , aiki kuma idan kina janta a jiki ita da kanta xataji shaawar koya ba sai kin nuna mata karfi bah pls my love kiyi respecting din kanki ok"
Kai ta gyada masa haka nan ya lallaba abarsa sai gashi ta sakko abunka da mata da miji har ya mantar da ita xancen wata umaima ckn salon soyayyarsa nan Suka lula sararin samaniya duniyar masoya๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ.
Umaima tun tana sa ran xuwansa har ta fidda rai tayi kuka mai isarta lallai namiji munafuki ne ynxu ya shanyata yana can tare da matarsa yana bata kulawa hmmm ke kuma a suwa? Hakane bata dawani matsayi a gunsa haka ta kwanta a gado ckn rashin kwarin guiwa.
Bayan 1hr ya shigo dakin tare da sallama ckn shigar kananan kaya yayi kyau sosai ga sajenasa kwance luf-luff se qamshin turare ke tashi a jikinsa yayi kyau sosai umaima ta kura mishi ido babu ko keftawa har ya karasa kan kujera ya xauna fuskarsa dauke da murmushi yace
"Em..sorry sis kinji ni shiru koh"
"Ah..ah ba komai "
Ta furta a hnkli se yaji tausayinta ya kamashi tabbas yasan kadaici na addabarta a rayuwa bata da abokin hira se TV ko waya don bai taba ganinta da kawaye bah toh saurayi fah?ya daga kansa Suka hada ido har ynxu kallonsa take ckn tsananin kunya ta dauke kanta


"Yadai ko nayi kama da wani ne?
"Wani? Kamar waye kenan?
"Oho..maybe mr right"
"Hmmm..kai kasan wannan"
" ohh..ke baki sani ba kenan, yawwa gskiya fa umaima baki taba hadani da bro-inlaw na bah ko rowarsa ake mana"
Haushin maganganun take ji wato shi bata taba burgeshi bah koh..Allah sarki baisan tana yi bah , nan kwalla ya cika mata ido


"Umaima lfy..ko tambayan da na miki ne? Am sorry pls"
"No..is ok ba komai"
"Akwai mana..gashi kina Neman xub da hawaye ko kun rabu ne shiyasa kika tunashi kina son yin kuka"
Ckn haushi tace
"Ya mutu"
๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜bash yaso yin dariya amma ya gimtse don daga ganin yadda tayi maganr yasan karyace don haka yaja bakinsa yayi shiru.haka Suka xauna har tsawon minti10 babu Wanda ya sake cewa komai don haka bash ya tashi yabar mata dakin ta fada gado ta cigaba da kukan rashin masoyin nata.haka rayuwa ta kasance ba laifi ynxu shukrah na amsa gaisuwarta kuma ta daina takura mata , waleed ya fara sabawa da umaima haka nan sultan ma yana xuwa su yini idan babu makaranta.umaima kuwa tana xuwan tasu makarantar amma har yau bata da kawaye ko abokai, mr Joshua kuwa shi yake kula da al'amuran kasar..Rayuwa kenan.




****************
Shuairat ta share wata 2 da xuwa hong Kong ynxu wata3 kenan da kwanciyar mr president rashin lfy amma har yau bai farfado bah..wani lokaci shuairat gani take tmkar ya rasu kawai boye musu akeyi bayan likitoci kuwa sun bata tabbacin cewa zai warke don haka ta dage da adu'a ba dare ba rana tana yawan karanta masa Qur'an a saitin kunne haka nan tana tofa masa wasu ayoyin, nafilar dare kuma ba'a magana .daddy da momsi kafarsu2 suna xuwa haka nan bash ma yaje sau1 umaima kam duk nacinta daddy ya hana sabida cewa yayi idan taje hnklinta zai tashi.
Shuairat tana xaune apple ne a hannunta tana taunawa a hnkli mr president yana kwance a gadon marasa lfy na'urori ne iri2* makale a jikinsa ga kuma ledojin ruwa. Jankim CE ta shigo tana murmushi ta fara magana da turanci

"Maman bby gskiya babyn nan namu mayen apple ne..kusan kullum shine abincin ki fah"
"Jankim sarkin xolaya..wani bby kike nufi"
Ta karasa kusa da mr president ta fara dudduba na'urorin tana gyarawa tace
"Shu..ai..zaki cemin baki San cikine da ke bah"
"Watt??๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณda gaske?
"Ehh..tun farkon haduwarmu na lura kina da ciki"
Mamakine ko murna ko bakin ciki wanne xatayi? Jankim ta bude Jakarta ta dauko kayan aikinta tace


"Muje na gwada ki"
Ba musu Suka wuce dakin da aka tanada don likitoci babu abunda babu a ciki nan da nan ta gama test din ya nuna musu result shuairat tana dauke da juna 2 na tsawon wata 3 ciff sai kuma ta kwanta akayi scanning sun duba komi.murna ne fal ckn ranta sai kuma hawayen tunawa da halin da uban yake ciki sai kuma ta tuna cewa rabonta da period tun a najeriya daga nan suka fita sun sayi magunguna da abubuwan kara lfy har nafila shuairat tayi ta godewa Allah sannan ta roki Allah ya bawa mr president lfy .
Haka ta cigaba da rainon ckn, jankim CE ke debe mata kewa first lady ma ta dawo daga tafiyar da tayi ta jajantawa shuairat haka nan manyan mutane na yawan xuwa duba mr president wasu abokanan aiki ne wasu kuma shuwagabannin kasace daban2* ga tarin duniya da suke xuwa dashi kudade kam ba'a magana shuairat tana turawa a account don bata bukatar komai Chinese president yana matukar kulawa dasu.
Ynxu ckn nata ya shiga wata4 ta kara cika tayi kyau sosai gwanin sha'awa tayi haske kamar me...ta shigo dakin tare da sallama kamar yanda ta saba duk tasan cewa babu me amsawa ta nemi kujera kusa dashi ta xauna ta kura masa ido
"Masoyin yaushe zaka tashi ne we rily missed u nida little... Pls get well soon Allah ya baka lfy"
Hawayen idonta take sharewa sai me??? Alamar ya motsa ta gani tayi waje da ido ta kara masawa

"My man...mafarki nake ne ko da gaske๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ
Nan ma ya Dan motsa yatsa ckn hnzri ta gudu kiran jankim..tare Suka shigo nan ta kira likitoci ta sanar dasu ckn kankanin lkc Suka taru a dakin tabbas ya farka ynxu yana jin komai kuma memorynsa is ok a kowane lokaci zai tuna da rayuwarsa na baya don haka ake bukatan shuairat ta dinga zama kusa dashi don ya tuna komai, yana jin komai amma ba lallai bane ya fara magana ynxu .ranar shuairat ta kwana da farin ciki nafilfilu ta dinga yi bata samu bacci sai da safe sannan ta koma bacci.
Haka ta kasance ckn kula da mijin nata kullum tana bashi lbri kala2* na najeriya tare da nuna masa hotuna ..har ynxu motsi kawai yakeyi idanunsa ma a kafe suke sai daga baya ya fara ita kefta su.daddy ya xo ya dubashi yaji dadi sosai haka ya xubawa shuairat albarka nan ta nemi alfarma a gina musu gida a can najeriya kan su dawo, daddy ya shaida mata mr president yana da gidaje da dama sai dai a gyara hakan kuwa akayi yana komawa aka turawa bash kudi ya bada kwangilar sake gidan Nas dake garki babu bata lokaci aka fara aiki.


*****
Bayan wata2 Alhamdulillh mr president yaji sauki sosai har ya fara takawa tamkar karamin yaro haka ake koya masa tfy shuairat kuwa cknta ya Dan fito ta zama abunda shaawa duk Wanda ya kalleta dole ya maida ido ita take koya masa tfyar ya tuna komai na rayuwarsa na baya amma har ynxu baya son yin magana shiru kawai sai dai murmushi.
Yau suna xaune a masaukinsu ta ajiye masa magunguna a gaba ya hada fuska da alama baya son sha nan shuairat ta juya masa baya alamar tayi fushi ba shiri taji ya rungumeta ta baya
"Am sorry swt hrt"
Ya mata rada a kunne ckn mamaki ta juya suna fuskantar juna
"Mr..mr president dama kana magana? Na dauka ka samu problem fah"
Murmushi ya mata sannan ya jawota a jiki ya kankameta sosai har bata iya motsi mai kyau hawaye ne ya fara diga yana kuka ya fara magana a hnkli
"Nagode!! Nagode!! Nagode!! Nana Aysha ke ya'r aljannah CE insha Allah..Allah ya miki albarka ya baki duk abunda kike bukata duniya da lahira..ya baki ya'ya masu albarka bazan manta dake ba har karshen Rayuwata ..bazan tozartaki ba..ya Allah ka bani ikon rike wannan baiwa taka..ya Allah ka yafe mata dukkan zunubanta..ya Allah ka bata gida a aljannah ka biya mata bukatunta ameen...I love u Aysha"
Ya kara kankameta shuairat ma kukan farin ciki take ya Dan raba jikinsa da nata yana kallonta yace


"Swt hrt ke kuwa kukan me kike yi"
"My man..dole nayi kukan farin ciki saboda Abu 3"
"Menene wanna?
"Na farko ka warke Wanda har na cire tsammanin sake xama kusa da kai kamar ynxu na dauka na rasaka har abada kaga kuwa farin ciki ya zama dole"
"Hakane rahamar ubangiji kenan baya karewa ..uhmm na 2"

"Na 2 kuma adu'oin da ka jera tabbas duk macen da ta samu irin wannan aduar a bakin mijinta toh lallai tayi dace a duniya babu kamarta..kaga Allah yana amsa aduar miji ga matansa kaga dole nayi murnan samun wannan Alhamdulillh ko ynxu nabar duniya nayi dace"
"Uhmm...Ayshata kenan.. Allah ya miki albarka, idan har ta hanyar kyautatawa miji ake shiga aljannah toh na daga kafata..Allah ya baki jannatul firdaus..tabbas kin cika alkawarin da kika dauka na cewa komin tsanani komin wuya komin dadi kina tare dani bazaki barni ba har abada,
[2/21, 2:41 PM] Reefat: ๐Ÿ’žNI DA SHUGABAN KASA๐Ÿ’ž
*68*
By *Reefat yahya*




Mr president ya cigaba da cewa
"Tabbas da ace duk matan duniya halayensu irin naki ne da lallai zaman lfy xata dore a kowane gida ..Allah ya miki albarka Allah ya barmin ke har a gidan aljannah"
Ya kara kankameta yana me kuka shuairat ta kwantar da kanta a kirjinsa tana jin bugun xuciyarsa , a hnkli ta daga kai tace
"Mr president kawo kunnenka "
Ba musu ya kai kunnensa dai2* saitin bakinta a hnkli ta furta
"Am pregnant"
๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ณ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ ya xare ido sai kuma ya fara hawaye ya rungumeta gam a jiki yana kuka tamkar karamin yaro
"Haba my man..me abin kuka a ciki ? Kai da zakayi farin cki "
"Kuka ya xama dole Ayshata..bansan wane irin farin cki nake bah tabbas babu abun bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammad manxonsa ne..Allahu Akbar! Allah mai ikon komai da kowa..yau ni Suleiman matata tana dauke da ciki? Allah nagode maka ..dama da rabon xan sake ganin jinina a doron kasa ..Allahu Akbar"
Haka mr president ya cigaba da sambatu Dakyar shuairat ta lallaba shi ya daina kuka har ya bata tausayi..eyya mr president๐Ÿ˜œ.daga nan ya tashi ya wuce bayi ya daura alwala ya fito ya fara nafila yana godiyarsa ga ubangijin talikai, shuairat ta kwanta a gefe tana kallonsa tana jinjina masa sabida ya kasance daga ckn bayi masu nuna godiyarsu ga ubangijin da ya haliccesu..bacci ne yayi awon gaba da ita a yayinda mr president kuwa yacigaba da nuna godiyarsa ga ubangiji.




************
Shukrah tana xaune a falo sai hura hanci take tana cika tana batsewa bash ya fito daga dakin bacci ya kalleta sau1 ya kawar da kai gefe yana mmkin wasu halaye irin nata ..
"Wllhi ina kan bakata, idan har bazaayi tafiyan nan dani bah toh sai dai kaima ka hkura don bazan yarda da wannan salon yaudaran bah..uhmm inaji ina gani ka dauko wata can ka tafi da ita turai da sunan zakuje duba jikin mahaifinta salon kuje kuyi soyayya a can koh..toh ban amince bah'"
Sai ynxu ya juya ya kalleta sosai ya girgiza kai yace
"Wai dama haka halinki yake ne shukrah? Kodak kin fara bin xugin kawaye ne? 4Allah's sake shukrah ina matsayin mijinki mu haifi waleed amma ace har yau baki yarda dani bah? Yaushe zaki daina zargi na ne..bayan kinsan cewa aure da zargi babu kyau"


"Kaga malam..ni ba jahila bace da zaka min wa'azi ehen, bazaka fake kana min dadin baki bah kawai ka fito fili ka gayamin aurenta zakayi ba sai ka tsaya yin wani kame2* bah"
"Allah sarki..yau kuma ni nake kame2* shukrah! Lemmi ask u..idan ina son umaima wai tsoronki zanji? Ko kina tunanin cewa idan ina son aurenta wannan haukan taki xata hanani yin abunda nayi niyya?"
"Koma menene..tafiya ce baxa ayi bah "
Ran bash ya baci sosai gskiya shukrah ta canza amma dole ya ja mata birki ( mata a kiyaye..wannan kishin hauka ne kuma hakan yake kara tunxura miji har yayi aurenda be shirya yi bah Allah yasa mu dace ameen).
Ya tashi kai tsaye dakin umaima ya wuce fuu..shukrah tabi bayansa, umaima tana kwance bash ya shigo tare da sallama ta gyara zaman ta kenan shukrah ta shigo kamar wata zakanya๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜(Wa ya gamin anti rabi ana kishi๐Ÿ˜œ)
Bash yayi banza da ita yace
"Umaima hop kin gama shiryawa cos jirgin 8pm zamu bi"
"Na gama but yaya I tot tare zamu tafi dasu sultan da gran mah"
"No..I change my mind mu 2 kawai zamu tafi su kuma jirgin 7am na safe zasu bi , zamu jira su @ Beijing"
"Ok..Allah ya kaimu"
Basuyi aune ba sai ganin shukrah sukayi ta makure umaima a jikin gado tana huci ta fara magana
"Shegiya munafuka..wllhi mijina yafi karfinki kije can....
Bata karasa ba taji saukan mari Tass! A fuskarta ba shiri ta sake umaima ta juya tana kallonsa tmkar a mafarki wai yau bash ne ya daga hannunsa ya mareta? Hawaye ne Suka cika mata ido a hnkli Suka fara sauka
"Shine ka mareni? Ak..kan ..akan wannan yarinyar? Baban waleed?
Ya runtse ido ckn jin zafin abunda ya aikata.shukrah ta juya tabar dakin shi kuwa ya jingina da bango kansa na kallon kasa, umaima kam tayi Kim..tmkar gunki ta rasa me xatayi tabi bayan shukrah ko kuwa ta tsaya gun bash? Shiru ya ziyarci dakin a hnkli ta karasa kusa dashi


"Yaya bash kayi hkri laifina ne da nazo gidanka..na hanaku kwanciyar hnkli am sorry"
Hannu ya daga mata ya juya yace
"Ki shirya ynxu xamu bar gidan nan"
Daga nan dakinsa ya wuce ya shiga bayi ya watsa ruwa gaba daya ransa a bace yake , ckn kankanin lkci ya gama shirinsa ya dauko wani Dan karamin jaka dakin shukrah ya shiga tana kwance rub da ciki tana kuka Mara sauti waleed kuwa yana gefe sai sharar baccinsa yake ckn kwanciyar hnkli.
Ya karasa kusa da ita yace
"Am sorry..nayi kuskure ki yafe min ni zan tafi kiyi hkri"
Daga nan ya ajiye mata rafar yan 1k ya juya ya fara tafiya har ya kai bakin kofa ya tsaya cak! Yace
"Ki gyara kwanciyar ki Allah yana fushi da masu irin wannan kwanciyar"
Daga nan ya tura kofa yayi ficewarsa shukrah ta cigaba da kukan da take.umaima ta fito da jakar kayanta ta sanya a mota bash ya ja Suka wuce gidan iyayensa don yin sallama dasu.


**********
Shuairat ta caba ado tana xaune a gaban mirror mr president ya fito daga wanka bayan ta taimaka masa ya kimtsa Suka fito falo sai kallonta yake ya lura cewa tana ckn nishadi yau ya juya yace
"Nana Aysha !
"Sir! ta amsa tana murmushi, saida yayi dariya sannan yace
"Sir! Kuma? ..anyway na lura dake yau tun safe kike ckn nishadi ko meyasa?
"Hmmm..ba komai fah haka nan nake jin kaina ckn annashuwa "
"Kin tabbata?
Kai ta gyada tace
"Na tabbata sir!
"Hmm..ke din ne somtymz u r amazing, kuma am sure u ar hiding somtin baki son gaya min koma menene dai nasan gud news ne"
Murmushi kawai tayi bata CE masa komai ba tana duba agogon hannunta , bayan 30min aka kwankwasa kofa shuairat ta mike a hnxarce ta bude kofan tare Suka hada baki wurin cewa
*surprise*!!!
๐Ÿ˜ณmr

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login