Showing 57001 words to 60000 words out of 82053 words

Chapter 20 - Ni Da Shugaban Kasa Complete Book Reefat Yahya .txt

10 Jan 2025

3834

zakimin? So kike na ajiyeki nayi ta kallo?..ynxu idan wani ya shigo ya ganki tare da Aysha ma ai se a rasa wacece matata a tsakaninku"


Shuairat me xatayi inba dariya bah..umaima kuwa tamkar xatayi kuka nan ta tashi tana tafiya dad yace mata
"Mark my words girl..am not joking"
Shuairat ta juya tana kallonsa tace


"Da gaske kake?
"Yeah...am serious wllhi, matukar lokacin da na bata ya wuce bata gabatar da kowa bah ni zan zaba mata duk wanda naga dama"


"Haba swt hrt ya xakayi haka"
"Don't worry..u will c Allah ya nuna mana lokacin"
"Ameen...
Nan ya jawota a jikinsa yana cewa


"Com here!..kin ajiyeni ko wlcm kiss baki min ba kun cikani da surutu"
Wani passionate kiss ya fara mata dakyar ta kwace kanta tana cewa
"Haba falo muke fah..baka tunanin wani ya shigo"
Murmushi yayi yace
"Babu mai shigowa don kuwa na basu rules na gidan babu wanda zai shiga last floor matukar ba ke kika nemesu bah"
Bai jira amsarta ba ya cigaba da kissing nata salman ne ya farka yana Neman abincinsa ba shiri Suka sake juna mr president ya shafa kai tare da cewa


"Gaskiya daddy na kana yawan shiga hakki na fah"
Dariya shuairat take masa sannan ta dauki salman tana basa nono mr president kuwa ya xauna a gefe yana masa wasa yaron se dariya yake
Shuairat tace


"Kana sa shi dariya idan ya kware ba ruwana"
"Da ruwanki"
Suna hira suna dariya.


A can ckn daki kuwa umaima ta kwanta tayi shiru tunanin kalaman mahaifin nata take ..tasan halinsa idan ya fadi magana baya canzawa , hankalinta ya tashi tabbas akwai matsala ita tasan duk duniya babu wanda take so sama da bash amma har yau bai furta yana sonta bah shin ya xatayi?
Zuwa xatayi ta zayyana masa halin da take ciki ko kuwa mahaifin nata xata fadawa? Haka ta kasance ckn rudani dakyar ta tashi ta shirya kayanta misalin 4pm jirginsu ya daga xuwa kano tana faman Neman bash a airport Amma Sam bata ganshi bah.
Bayan sallar isha suna zaune a falonsu dama mr president yana da gida a garin kano don haka can Suka sauka falo 2 ne a gidan da dakuna 6 se kitchen da dinning area daga waje kuma bangaren baki ne. Xaune suke a dayan falon shuairat tana kallon news umaima ta xauna shiru ta buga uban tagumi sultan kuwa yana wasa da salman , kamar daga sama Suka jiyo sallamar bash ya shigo tare da waleed nan kuwa sultan ya ruga a guje yayi hugging dinsa
"Oyoyo uncle Nah..
"My boy ya kke "
"Lfy uncle nayi kewarka sosai kuma nagode da ka kawomin kani Nah"
Nan sultan ya rike hannun waleed Suka koma gun salman Suka cigaba da masa wasa. Bash ya xauna Suka gaisa da shuairat tna kallonsa tace


"Ina maman waleed na dauka tare xaku zo"
"Nop...na barta a gida"
"Y?...haba my yaya "
"Bazaki gane bane baby..dama ina son muyi wata magana amma se mun koma ABJ"


"Hop de lafiya"
"Umm..kedai ki bari mu koma"
"Toh..Allah ya kaimu"
"Ameen "ya amsa a gajarce yana satan kallon umaima wacce tayi nisa ckn tunani yayi Dan kasa da Murya yace


"Ita waccan meyake damunta"
Murmushi shuairat tayi sannan tace
"Ita da dad ne as usual"
Daga nan bash ya tashi ba tare da ya kalli bangaren umaima ba ya sallami shuairat yayi ficewarsa.




Hmmm...wace irin magana bash xeyi da shuairat kodai batun umaima ne????πŸ€”πŸ€”πŸ€”πŸ€”


Muje xuwa.....
[2/21, 2:41 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*79*
BY *Reefat yahya*




10pm mr president ya shigo ya sanarda umaima ta hadawa bash tea ta kai masa yana dayan falon xuciyarta na harbawa dole ta tashi ta hada sai kuma ta xumbula dogon hijab ta nufi falon ta shigo tare da sallama firgigit ya amsa dama yayi nisa ckn tunani suna hada ido tayi saurin dauke kanta nan ta ajiye masa cup din ta juya xata tafi ya kira sunanta a hnkli
"Umaima!
Cak...ta tsaya ba tare da ta juya bah ya sake cewa


"Dawo ki xauna"
Ba musu ta dawo ta xauna a kujerar da yake kallon nasa
"Umaima meyake damunki"
"Kaima meyake damun ka?
Murmushi yayi wanda ya Kara fito da kyawunsa yace
"Ni nace miki wani Abu yana damuna ne?
"Toh.. Ni na gaya maka nawa ne?


"Umaima fuskarki ta nuna kina ckn matsala tell me"
"Kaima ai fuskar taka ce ta nuna hakan"
Shiru yayi daga bisani yace
"Bansan yaushe kika fara boyemin matsalolinki bah..da can baya har nemana kike idan kina ckn matsala Amma ynxu ki canzamin I donno y"


"Hmmm...naga babu amfanin hakan ne shiyasa"
"Haba umaima...don na kasa furta miki Kalmar so?
😳😳😳😳 ta daga kanta Suka hada ido tayi saurin sauke nata daga ta mike zumbur ta bar masa falon.tagumi bash yayi..shidai yasan yana matukar kaunar umaima tun ba yau bah Amma Sam ...ya kasa gaya mata hakan don gani yake tamkar tafi karfinsa bata dace dashi bah, mahaifinta babban mutum ne mai arziki shiyasa yake ganin kamar soyayyan nasu baxata yiwu bah..duk da cewa ya gane irin tsananin son da take masa Amma shi bazai iya tunkarar mr president da wannan zancen bah.


Umaima tana kwance bacci ya kaurace mata sai tunanin kyakkyawar fuskar bash take gani ..tana sonsa kamar ta hadiyeshi Amma tayi alkawarin danne wannan son matukar bai fito ya furta cewa yana sonta bah ta gwammace sonsa ya zamo ajalinta akan ta bude baki ta gaya masa duk da yagane halin da take ciki.
A bangaren bash ma hakan ta kasance sai faman sake2* yake ga uwa uba canjin da ya fuskanta a gun shukrah. ..kwata2* ta daina kulasa abinci ma sau1 take a rana ga kuma bukatarsa Sam ta daina amincewa dashi..abun duniya ya masa yawa dakyar bacci barawo ya saci wadannan masoyan biyu.




Taro yai taro jamaa ne makil duk inda ka duba ga kuma yan Chinese yawanci sune ma'aikatan katafaren kamfanin mai suna
*AS4 textile industry* bayan an kaddamar da bude sabon kamfanin aka raba abinci da sauran abubuwa daga karshe aka rufe taro da adua ga yan jarida nan birjik sai daukan rahoto suke..ckn kamfanin Suka shiga tare da iyalansa da sauran abokan arxiki daddy ma ya halarci taron yana rike da salman duk yawon da suke story building ne mai kyawun gaske ga ofishin maaikata nan birjik abun de ya hadu.
Har bayan azahar Suka dugunxuma xuwa gida dama da masu aiki Suka zo don haka bayan sunyi sallah Suka baje a dinning, daddy shuairat mr president umaima sultan bash waleed se kuma salman take hannun kakansa suna cin abinci suna barkwanci gwanin sha'awa daddy yayi gyaran murya ya fara magana


"Dama zancen umaima ne boy, akwai wani abokina yace yana nemawa dansa aurenta shine nace sai nazo zamuyi maganar"
😳😳😳😳 umaima ta zare ido tace
"Haba daddy...


"Ke rufemin baki shashasha kawai..kina ajin karshe a jami'a me ya rage miki?
Mr president ne yace


"Yi hakuri daddy daman nima na gaya mata idan ta gama da 1week zan aurar da ita kuma...


"Gafara can...dama ba kai kake biye mata bah, idan ba kam dage bama da zan bari tayi karatun jami'an ne?...toh nidai na gama magana aure de dole tayi ko taki ko taso"


"Sorry daddy Nah..ba ina goyon bayanta bane but na bata damane ta fito da wanda take so sai ayi auren"


"Bana son shiririta ita wannan ka taba ganin wani yazo wajenta ne? Ba ta dauki girman kan tsiya ta dorawa kanta bah..gani take tmkar tafi karfin kowa "


Sai ynxu shuairat tasa baki tace
"Allah ya huci xuciyarka daddy insha Allah xaayi auren nan ba da dadewa bah"
Sai ynxu yayi murmushi ckn jin dadi yace


"Yawwa Ya'r albarka ynxu naji magana..kinga mijin naki da ya'rtaki duk mashirmata ne rabu dasu "


Murmushi shuairat tayi ta kashewa mr president ido sannan tace
"Don't worry daddy kam kwantar da hankalinka "


"Tank u my Dota...am now counting on u"
"Trust me daddy"
Daga nan Suka fara hirarsu mr president kam yasha jinin jikinsa bash kuwa sai Satan kallon umaima take ita kuwa ta cika tayi famm..murmushi yayi ya mata gwalo batare da kowa ya gani bah yace


"Gaskiya gara a aurar da ita da wuri daddy..don kuwa ta fara tsufa"


"Yawwa ganemin hanya dai basheeru..mu a zamaninmu mace tana 13-14 zaa aurar da ita Amma ynxu yahudu ya bata muku rayuwa kuna nan kuna biyewa bokon banza"


Umaima dama kiris take jira nan ta fara kuka ta tashi tabar dinning daki ta wuce shuairat ta harari yayan nata tace


"Se kaje ka lallabata ai..kasan halinta sarai Amma kake tsokanarta"
Daddy yace


"Rabu da wannan shagwababbiyar "
Dama abunda bash yake so kenan..don haka ya tashi yabi bayanta mr president kuwa ya cigaba da cin abincinsa sultan kuwa sun koma falo da waleed. daddy ya juya yana kallon Dan nasa yace


"Boy wai fushi kayi "
Shiru bai amsa bah daddy ya shafa kansa yace
"C'mon..smile my boy, kam tsufa ai fushi ba naka bane "
Ya hada rai yace


"Toh..daddy ba Kaine kake min fada akan laifin da ba nawa ba"


😳😳😝😝😝shuairat bata San lokacin da dariya ya kubce mata bah tace
"Oh...dad sultan yaranka suyi shagwaba kaima kayi?


"Daddy ka jita koh..
"Yi hakuri boy din daddy duk laifina ne OK"
Haka daddy ya cigaba da lallaba mr president tamkar wani karamin yaro shuairat kuwa sai tsokanarsa take tana mamakin irin son da daddy yakewa dannasa Sam baya so yaga bacin ransa ko kadan.


Umaima kuwa ta fada gado tana rusa kuka ..ita ba kalaman bash ne damuwarta ba aa xancen hadata da wani da daddy yayi ne ya daga mata hankali ..shikenan ta rasa bash har abada! Ya shigo ya tsaya yana kallonta bata ji shigowarsa bah ya nemi kujera ya xauna a hnkli ya furta


"Tashi ki xauna magana xamuyi"
Ta juya jajayen idanunta tace


"Baka da abunda zaka gaya min kawai ka fita ka barmin daki "
"Look umaima am sorry bansan kalamai na zasu bata miki rai haka bah...am sorry pls"


..hmmm lallai ma wato ba zuwa yayi yace yana sonta ba kawai yaxo bata hakuri akan silly maganar da yayi dazu? Bash y? Meyasa yake wahalar da xuciyRta?...umaima CE ke wannan tunanin hawaye wani na bin wani ta nuna masa kofa ckn tsawa tace


"Out of my sight ..now!
"Sorry...
"I said...out...nowww!
Ta karasa ckn daga murya nan ya juya ya fita ckn bacin rai ita kuwa ta kara fashewa da wani sabon kuka
"Shikenan na rasashi har abada"


"Baki rasashi bah matukar ina Raye...babu abunda zaki nema a duniya ki rasashi umaima"
😳😳😳 ta juya don tabbatar da abunda kunnuwanta Suka jiye mata ...carab! Suka hada ido....




Muje xuwa...
[2/21, 2:41 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*80*
By *Reefat yahya*


*dis page is dedicated to Rabeah majeed😊 tnx 4ur kia*
N ~2all fanz of nida shugabankasa ina sonku sosai..mr president ma yana sonku. Jameelah feekah n co, tnx to u all~




Umaima tana daga kanta Suka hada ido da shuairat tayi saurin sunkuyar da kai shuairat ta karasa tare da rungumarta tana rarrashinta umaima kuwa sai hawaye ke fita a idonta tana kuka ..wani irin radadi take ji a ckn xuciyarta
"Umaima am sorry..I donno hw u feel abt dis but am very sory"
Ta share hawayen da yake xuba tace


"Mom pls..ki taimakamin ina sonsa bazan iya rayuwa idan babu shi bah"
"Zaki rayu insha Allah..ki kwantar da hankalinki burin ki zai cika ckn kankanin lokaci"

"Kina nufin zaki taimakeni"
"Matukar hakan zai sanyaya ranki umaima I can do dat 4u"
Nan umaima ta kankameta ta cigaba da kuka tana cewa


"Tnx so much...I Lov u mom sultan"
"Shhhh...ya isa haka bana son ki sake cewa komai, kiyi shiru da bakinki ki xuba ido..yaya zaixo ya durkusa a gabanki ya furta miki kalmar so harma ya nemi ixinin aurenki I promise"
Haka shuairat ta cigaba da bawa umaima hakuri dakyar ta daina kuka daga nan Suka tashi don gabatar da sallan la'asar.


D next day Suka koma ABJ daddy ya wuce Lagos umaima bata kara saka bash a ido bah duk tabi ta damu.
Da dare shuairat tana xaune a falo aka sanar da ita xuwan yayan nata nan ta bada ixinin shigowa dama ita kadai CE a falon ya shigo tare da sallama ta amsa Suka gaisa ya fara magana
"Baby magana zamuyi ta fahimtar juna pls..kada ki boyemin komai ok"
"Ok my yaya..go ahead"
"Baby.. Kin xauna da shukrah sama da 10yrs kinfi kowa sanin halayenta shin wai dama kinsan bata da halaye na gari shine kika bada shawara na aureta?


Tambayar yaxo mata a bazata..ita ta dauka zancen umaima zasuyi...muryarsa ne ya dawo da ita daga tunanin


"Answer me..."
"Umm..emmm yaya u knw wat"
"C...baby don't dare lie to me ki fadamin gaskiya"
"Calm down pls yaya...meya faru tsakaninka shukrah just tellmi"
"Babu abunda bai faru bah..shukrah ta canzamin gaba daya, she is now a monster"


"Subhanallah..yaya y u saying dis...
Idanun bash sun kada sunyi jaa dakyar yace
"Bazan boye miki u r my 6* n she is ur friend.. Baby nayi nadamar auren shukrah"


"Innalillahi...abunda shuairat take nanatawa kenan dakyar ta daure tace
"Yaya am very sory abt dat...but kowa yasan shukrah is a good person maybe zugin kawaye ne "
Tsaki yaja Sam babu mafita don haka xumbur ya mike ya mata sai da safe yayi tafiyarsa , shuairat ta kasa motsawa daga inda take lallai shukrah na ckn matsala dole ta nemi hanyar da zata bi ta daidaita tsakanin su. Dare yayi sosai tana nan xaune a falon gaba daya ta rasa me ke mata dadi, mr president ne ya shigo ya sameta da taimakonsa ta rage yawan tunanin da take sukayi shirin kwanciya.


***bayan 2weeks umaima ta gama jarabawar first semester dinsu saura semester daya ta gama makarantar Hutu na musamman mr president ya shirya musu dama sultan suna Hutu , tafiyar kasar China ya shirya musu xasu kaiwa Chinese president xiyara a hong kong daga can zasu je Singapore da kuma Korea ..murna tamkar suyi yaya nan kuwa ya kira bash ya sanar dashi cewa tare zasuyi tafiyar don haka ya shirya shi da iyalinsa duk zasu tafi.
Ckn tsananin farin cki ya wuce gida yasan dole zasu shirya da shukrah a Daren yau matukar taji wannan kyakkyawan albishir don kuwa zaman nasu har ynxu babu wani sauyi tana gallaza masa son ranta...bash yana da hakuri sosai samun irinsa a wannan xamanin se a tona, bai taba gayawa wani sirrin zaman nasu bah face shuairat itama bai sanar da ita komai bah...ya shigo falonsu babu kowa daki ya wuce kofar a bude take yasa kai xe shiga kenan Amma abunda kunnuwansa sukaji yasa yayi Saurin komawa da baya ya labe a gefe yana sauke numfashi... Shukrah tana magana ne a waya tana kuka tace


"Anti wllhi jinin yaki tsayawa kuma Dr ya gayamin cewa pills na tsarin iyali da nayi amfani dasu su Suka jawomin wannan matsalar"


Tayi shiru da alama tana sauraron me ake gaya mata daga dayan bangaren sai kuma tace
"Ni ba wannan bane matsalata..cewa yayi dakyar idan zan sake haihuwa saboda mahaifar ta lalace"


"Innalillahi wa innailaihi raji'un..abunda bash yake nanatawa kenan.hawayene ya fara gangarowa bisa kuncinsa ya runtse ido, shukrah ta cigaba da cewa


"Idan yaji wannan maganar nasan sakina xaiyi..kuma wllhi iyayena ma zasuyi fushi dani, pls anti ki taimaka min yau ya zanyi? ..wayyo Allah na wllhi sharrin shaidan ne da kuma fa....
Bata karasa ba taji takun mutum a bayanta ckn hanzari ta juya Suka hada ido ya bita da wani mugun kallon da bata ganin irinsa bah😳😳😳😳
Wani gumi take hadawa ga fuska chabe2* da hawaye ba shiri ta sake wayar hannunta ckn raxana.......
...
...nima na ajiye tawa wayar


Hmmm ya bash zaiyi da ita?
Sakinta zai yi ?
Wane mataki zai dauka?
Ku biyoni...Lov u all😘😘
[2/21, 2:41 PM] Reefat: πŸ’žNI DA SHUGABAN KASAπŸ’ž
*81*
By *Reefat yahya*




Hawayene yake gangarowa a fuskar bash ya durkusa a gaban shukrah yana kuka yace


"Shukrah me na tsaremiki a Rayuwa ...wace irin tsana kike min da har yasa bakison hada jini dani..wane irin laifi na aikata da nayi deserving irin wannan punishment din tell me plsss..."
Ya karasa maganar yana kuka me ban tausayi shukrah ta xauna dabas a gabansa ta cigaba da kukanta tace
"Yaya don Allah ka yafemin nasan na aikata laifuka da dama a gareka amm...


Bai bari ta karasa ba ya dauketa da wani wawan mari xuciyarsa se tafarfasa take nan ya tashi yabar dakin..shukrah ta cigaba da rusa kuka ta nadamar abubuwan da ta aikata masa itakam fatee ta cuceta kuma laifinta ne daga haduwa da mutum a watsap se ta biye mata ta rusa farincikin gidanta..kuka sosai takeyi tana jawa fatee Allah ya isa ( ni Reefat nace ..ohh dama ke bakida tunani ne kawai daga haduwar watsap...mtswwπŸ™„πŸ™„πŸ™„ duk masu biyewa kawayen banza haka zasu kare ..Allah ya tsare mu da sharrin mugayen mutane)
Bash yana fita ya shige motar sa ya hada kai da guiwa yana kuka tamkar karamin yaro , ya share minti 30 yana kuka sannan ya fara kiran sunayen ubangiji ya dan samu sauki a ckn xuciyarsa daga nan yaja motar be tsaya koina ba sai gidan mahaifinsa.ya fito ckn sanyin jiki ya karasa ckn gidan waleed ne ya rugo da gudu ya fada jikinsa yana cewa


"Oyoyo Abba Nah "
Murmushn karfin hali yayi nan kuma ya tuna da zancen shukrah ya jawo yaron ya kankameshi sosai a jiki nan hawaye ya malale fuskarsa , mama CE ta fito daga daki tana Neman waleed turus...taja ta tsaya bata taba ganin dan nata ckn wannan halin bah .tayi gyaran murya tace


"Waleed kaje daki ka jirani ina xuwa"
"Yawwa mama..zaki bani sweet koh"
"Ehh..je ka xauna banda kiriniya gani nan xuwa ynxu xan kawo maka sweet har da chocolate"


Yaron ya hau tsalle nan ya sake uban nasa ya ruga aguje xuwa dakin mama , bash ya xauna kasan carpet yayi shiru ya kasa furta komai.mama kuwa ta juya xuwa dakin mijinta ta kirasa tare Suka fito bayan sun zauna baba yace
"Ni bazan nemi jin matsalar ka bah..koma menene kayi kokari ka kasance mai juriya da jajircewa, shi zaman duniya iyawa ne kuma mai hakuri shi zai dafa dutse har yasha romonsa..Dana! Na dade da gane cewa kana ckn matsala tun ba yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login