Showing 1 words to 3000 words out of 38921 words
ο»Ώππππ
IMRANFAD
ππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.F.π
Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.
Dedicated to my fans I LOVE YOU All
π
Ώ1β£&2β£
Wata yariya na gani da baza ta wuce shekara goma sha takwas ba a filin kwallo sanye da jersey da wadon shi,ita kadai ce mace cikin su
Buga kwalo take cikin maza kamar namiji sai cewa" suke FAD bani nan"itako sai juya su take cikin kwarewa dan in ta rike kwallo sai anyi da gaske ake ansa
Mummy ne zaune a falo tana hutawa daddy ya shigo da sallama mummy tace"sannu da dawowa"
Yace"yauwa"zama yayi,ita kuma mummy ta tashi dan d'auko me ruwa a fridge
Bayan ta bashi ruwa yasha yace" wai ina FADILA ne?"
Tace"hmmm ai yariyar nan bata jin magana dubi duk irin duka da kayi mata jiya amma yau ma sanda ta koma filin kwallon yariya kamar mai aljanu"
Yace"ai laifin ki ne da kika bari ta fita a gidan"
Mummy tace"haba mana kai ma kasan yariyar nan ba jin magana take yi ba daga inje inyi sallah ta gudu yanzu ma rabonta da zuwa islammiya yayi kwana biyu"
Yace"ai zata dawo ta same ni "
Fadila ko sai kwallonta take bugawa hankali kwance suna cikin hakane sai ga hadari kowa ya fara gudu amma banda ita,NAZIR yace"FAD zo mu tafi gida ko baki ganin hadari ne?"
Tace"ai.wasan yafi dadi cikin ruwa"
Yace"toh ni dai na tafi"da gudu Nazir ya bar filin da abokan wasa su
Bayan tafiyar su da minti 15 aka fara ruwan sama mai karfin gaske sai dai ba iska,dama fadila akwai son ruwan sama wasa tai tayi cikin ruwa sanda kayan ta ya jike har dogon gashinta sai tsalle take tana wasa da ruwa
Wani haddadiyar motar ne yayi parking gabanta cikin masifa ta je window motar ta kwankwasa
Tace"malam wani irin wulakanci ne wanan?"
Shiru aka yi ba a yi magana ba kuma ba bude ba gashi bata ganin ciki domin bakin glass ne amma wanda ke ciki na iya ganin ta
Gajiya tayi da tsayuwa ta bar wurin cike da haushi
Shiko dariya yayi yace"IMRANFAD"
Sauri takeyi cikin tashin hankali dan sai yanzu ta San dare yayi ga wuri yayi duhu tace"nashiga uku da daddy yau sai ya yanka ni da raina gaskiya bazan je gida ba gidan su umma zani gobe ta biyo ni muje wurin ta roki daddy"
Gidansu ummi take tayi sallama a gate,mai gadi yace"waye?"
Tace"ban sani ba"yana jin haka ya fito da sauri ya bude kofa,yi tayi kamar bangaje shi da sauri ya masa gefe tana shigewa yace"wanan yariya akwai raini yanzu sai ta zazzage mun rashin mutunci"
Tana shiga ta samu ummi zaune karasawa tayi
Tace"ummi ina yini?"
Ummi tace"lafiya lau dota"
Fati tace"wani laifi kika yi kuma?"hararrar Fatima tayi ta kalli ummi
Tace"ummina"
Ummi tace"na'am dota"
Tace"so nike kira mummy ki ce ina gidan ki tun d'azu"
Ummi tace"dota so kike inyi karya kenan ko?wai meyasa baki jin magana ne,gaskiya in baki canja ba zamu b'ata"
Tace"yi hakuri ummi"
Bayan ummi ta gama magana da mummy a waya ta kalli fadila
Tace"je ciki ki canza kayar ki kar sanyi ya kama ki inki gama kije shiyar IMRANA Ku gaisa yau ya shigo gari
Tace"toh ummi"
Tashi tayi ta haye sama d'akin da ta saba sauka ta shiga duhu ne a d'akin kunna wuta tayi amma ba wuta,tsaki tayi
Tace"ga duhu a d'akin nan ya zanyi yanzun nan?ga shi na bar wayana wajen NAZIR bari dai in lallaba in samo ashana
Lalube ta fara yi amma babu alaman ashana tace"bari dai in lallaba in Shiga bayi inyi wanka dama ai ni jaruma ce"
Bata lura da mutum a kwance a gado ba tayi shigewarta bayi
Tana shiga ta bude window bayi ta fara wanka bayan ta gama wanka ta fito d'aure da guntun towel ta zauna bakin gado
Tace"wanan IMRANA akwai iskanci wato dan bakin ciki generator ma wai sai 8:pm za a kunna dan shegen makon siya da kayi magana a ce yaya IMRANA yace kaza yace kaza ai ya gode bamu taba haduwa ba da sai na koya me hankali,ai nasan bai taba haduwa ba da jarumar mace ba irina shiyasa yake iskanci,ummi wai naje in gaishe shi ashe zai bushe dan ba inda zani shi ya zo ya gaisheni mana inda dadi"tsaki tayi tace"bari inje in kulle kofa da an kunna gen sai nasa kaya nayi sallah
Tashi tayi ta je ta kulle kofa ta dawo ta haye gado,jin ta jikin mutum yasa ta yin.........
Sai naga comment zan cigaba da labarin
Your comment is important
No comments
No typing
Maman
Noorul
Hudahββ
Luv u my fans
Pls share
ππππ
IMRANFAD
ππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.Fπ
Home of gorgeous,interllingent,and expert writers we are the best among the rest.
Please ku fara karantawa tun kan nayi nisa,bana so sai nayi nisa a fara damu na da yaren daga farko dan bama zan saurari kowa ba pleaseπππ
WARNINIG:ban yarda wani ko wata ta canja min komai na littafi na ba ko amfani da shi ta wata siga ba.in kunni yaji jiki ya sira
Wanan labari na kirkire shi ne dan nishatar da masoyana suyi amfani da darusan da ke ciki.su wasar da Wanda bashi da amfani.bawai nayi shi bane da cin zarafin wani ba.(Allah yasa mu dace)
π
Ώ3β£&4β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Jin ta jikin mutum yasa ta yi ihu,tuni jikin ta ya fara rawa tace"waye?"
Shiko jinta jikin shi san da ya lumshe ido ya kuma bude su yana sane tun shigowar ta ya dai yi shiru ne
Tace"waye kai?"kallon fuskar shi tayi amma bata ganin komai sai inda blue eyes din shi ke sheki
Tace"inalillahi wa ina ilaihi rajiun aljani ne yau nayi gamo"
Shiko Kara rungumeta yayi jin na shanun ta a kirjin shi yasa shi cikin kasala ya ma rasa abin yi"
Tace"dun Allah aljan ka taimake ni kar ka kashe ni sai na zama shaharariyar footballer please"
Dariya yayi cikin ranshi ya canja murya yace"ke yariya na zo ne in tafi da ke duniyar aljanai in aure ki,ki haifa mun yar......"maganan ya makale ne sakamakon sauka fisari da yaji a jikin shi"
Tace"yi hakuri aljani ka rufa min asiri dan allah ba dan ni ba"
Ya kuma yin muryar tsoro yace"ai ke kika ce ke jaruma ce ni kuma ina son jarumai"
Tace"ai ni da kake gani aljani shegen tsoro ne dani,ni da nike sauna ina naga jarumtaka"
Yace"toh yanzu kin yi mun laifi fisari a jiki kuma sai na hukunta ki"
Ihu ta fara yi tana cewa" ummi ki taimaka min dan allah"
Ji tayi yace"hahahahahahaha ko kinyi ihu ba mai jinki"abinda fadila bata sani ba shine kofar gidan duk sound proof ne
Tuni ta rude da sauri ta bar jikin shi ta koma gefen gado ta rakube wuri d'aya
Ganin ta tsorata yace"na yafe miki na yau ki rufe idon ki inki ka kuskura kika bude toh tare zamu tafi"
Da sauri ta rufe ido gam yana ganin alamun ta rufe ido ya fita a d'akin yana dariya yace"hmmm IMRANFAD akwai tsoro ashe "
Yana fita da minti biyar aka kunna gen
Tana ganin haske ta mike da sauri ta nufi toilet tayi alwala still jikinta rawa yake yi,tana fitowa ta dauko rigar barci ta sa da dogon hijabi ta fara sallah
Ummi ne a dining table tace"lafiya kuwa fadila bata sauko ba?"
Fati tace"hmmm ummi kema kinsan halin fadila yanzu haka ma ta yi barci dan kin San bata cin abinci a wanan lokacin sai tace zata yi nauyi"
Shiko yamusa fuska yayi kamar zai yi amai yace" ummi wacece kuma fadila"
Ummi tace"yanzu kai ka manta fadila yariyar da ka yi reno tun tana cikin suma kafin ka tafi INDIA"
Cikin basarwa yace"no na manta"
Washe gari da safe ummi ne da fati suna jere abinci a dinning sai da abba ne ya sauko ya zauna
Yace"ina IMRANA ne?"
Fati tace"ai yana d'akin shi"
Ummi tace"je ki ta so fadila ta zo ta karya"
Kafin fati ta tashi sai ga fadila ta sauko cikin rigar barci riga da dogon wando kusa da Abba ta zauna
Tace"good morning Abba,ummi ina kwana"
Amsawa suka yi cikin sakin fuska Abba yace" ya kike ne"
Tace"lafiya"
Kallon ummi tayi tace"ummi ashe dama aljanai ne a gidan nan"dai-dai nan ya sauko amma yana jin ta kira aljani ya samu wuri ya boye dan jin mai zata ce
Ummi tace"aljanai kuma"Abba ko ya kalleta ya girgiza kai dan yasan daru irin na fadila fati ko abincita taci gaba da ci
Tace"hmmm in ba dun allah yasa ni jaruma bane da ai ya tafi dani amma yana magana na bude me ido tuni ya saki fitsari a wando"
Ummi tace"aljani?"
Tace"kwarai da gaske ummi ai cewa nayi kai koma inda ka fito kan raina ya b'aci"Abba bai san lokacin da ya furzar da tea d'in bakin shi ba yana dariya,saboda inda tayi maganan kamar wata babban
Fati ko tashi tayi Zata bar wuri
Ummi tace" ina zuwa kuma?"
Fati tace"ummi bari inje ciki dan in na cigaba da zama zan iya narkewa"
Fadila tace"ummi barta ta tafi kawai"cigaba tayi da bama ummi labari yayin da Abba sai kallonta yake kamar TV
Ummi ta bata soyayen irish da kwai sai tea"
Tace"ummi ni tea kawai zan sha saboda anjima zani match"
Abba yace" shidai wanan kwallon baza a bar shi ba"
Susa kai tayi tace"tukunna dai Abba"nasiha yayi mata wanda kullum sai anyi shi
Abba na cikin magana tace"lah ummi ina jin kamshin tularen aljani,"ummi ta zaro ido tace"aljani nasa tulare kenan?"
Tace"eh mana kuma kwayar idon shi kamar na mage,shi kawai nike ta gani yana sheki,kuma tularen dadi"
Ummi tace"toh"dan ta ma rasa abin da cewa
Wacece fadila?"
Maman
Noorul
Hudahββ
Luv u my fans
Pls share
ππππ
IMRANFAD
ππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.Fπ
Home of gougeous,interllingent,and expert writers, we are the best among the rest.
Ashe haka Nike da masoya?gaskiya nagode da kaunar Ku a gareni Allah ya bar mu tare.
π
Ώ5β£&6β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
FADILA ABDULLAH shine cikkeken sunan ta ya'ce ga alhaji abdullahi Mohammed Wanda aka fi sani da alhaji mai naira,saboda mai arziki ne sosai.da mahaifiyarta hajiya maryam hausawa ne yan garin kano,suna zama a nasarawa G R A. a kano ya ke gudanar da kasuwancin shi,bayan aure shi da hajiya maryam (mummy)sanda suka shekara goma sha biyar kafin Allah ya basu haihuwar fadila wanda tun bayan haiwarta basu kara haihuwa ba,tun abun na damun mummy har ta hakura ta barwa Allah komai
Hakan yasa daddy nunawa fadila gata da soyyaya wanda dole kesa yayi mata fad'a balle duka,kai bashi kadai ba har da makocin shi kuma aminin shi watoh alhaji musa adamu (Abba) da matan shi hajiya fati (ummi)ummi na matukan kaunar fadila domin ita ta raine ta in ka ganta wajen mummy toh nono zata sha,kuma in ba wanda yasan asalin fadila ba sai ya d'auka ummi ce ta haifeta domin suna kama sosai kasancewar ummi balarabiya ce
Sai dai fadila Allah yayi ta da balain son kwallo tun tana yariya ko a makaranta aka tambayi ta mai take son zama nan gaba Sai tace footballer
Tun abun bays damun daddy har ya fara Shiga damuwa domin kullum tana cikin maza da sunan buga kwallo,duk kayanta Jersey ne domin da k'yar ta ke saka atampa ko an d'inka bata sawa,
Haka rayuwa ta cigaba anyi-anyi da ita taki bari har ya kai ga daddy ya fara had'awa da duka amma ba canji,ko an hanata fita sai ta San hanyar da zata bi ta bar gida
Hakan ba karamin damun daddy yakeyi ba domin tun da ta gama secondary taki zuwa gaba dan say biyu tana rubuta jamb amma bata ci bawai dan bata da ilimin ba amma saboda karatun ba shine gaban ta ba
Ita dai babban burin ta ta zama yar kwallo nan ta fara samun Matsala da iyayen ta dan daddy ba karamin cin ubanta ya keyi ba,da ta gane haka duk ran da tayi laifi sai ta tafi wajen ummi dan har d'aki take dashi a gidan.
Sai dai fa duk rashin jin fadila akwai ilimin boko da addini domin tana shekara goma sha biyu ta sauke Qur'anic mai girma kuma tana da ibada sosai
Fadila fara ce Sol,bata da jiki,tana da tsayi da dogon,sai karamin baki da bob eyes kwayan cikin idon ta brown,infant she is perfect sai dai abin da baza a rasa ba
Fadila bata jin maganan kowa sai na Abba amma shima akan kwallo San da suka b'ata,dan shima yayi akan ta bari amma taki ji
Cigaban labari
Bayan ta gama cin abinci tar haura sama shiko dariya yayi yana mamaki karfin hali irin na IMRANFAD a ran shi yace"hmmm yariyar nan akwai rainin wayo,ta manta ita tayi fitsari kenan?"
Direct d'akinta ta shige ta koma barci
Ba ita ta farka ba sai 12 na rana,bayan tayi wanka ta saka yellow jersey,bayan rigar an rubuta FAD 3,pakin sumarta tayi a sakiya ta saka band yellow,ta kalmin yan kwallo ta saka ko kwalliya bata yi ba amma tayi kyau
Fitowa tayi ta gan ummi zaune a falo da Fatima suna kallo, shiko yana kwance ya basu baya.ummi na ganinta
Tace"ina zuwa ne haka?"
Fadila tace"match ummi yau ni zanyi ref"tayi karashe magana tana nuna mata wusir d'in wuyar ta
Ummi tace"ikon allah, fadila zauna muyi magana"
Zama tayi tace"ummi yi sauri bana so inyi lattice karfe d'aya za a fara wasan shiyasa na shirya tun yanzu"
Baki bude ummi ke kallonta tace"yanzu ke fadila baza ki hakura da kwallon nan ba kiyi karatu ba,haba fadila"
Tace"ummi nifa burina in zama yar kwallo,kuma kwallo baya bukatar karatu ki duba ki ga duk manya footballer d'in duniya ba wani karatu suka yi ba wasu ma ko secondary basu gama ba"
Ummi tace"kin ci gidan ku "tayi maganar hade dayi mata dankuwa
Tace"ina yar bahaushe ta gan buga kwallo?maganan aure kuma fa?"
Tace"ummi wa ke maganan aure, ni bazan yi aure ba ko zan yi sai d'an kwallo irin....."maganan ya makale ne sakamakon tari da IMRAN ya fara yi
Kallon gefen shi tayi dan sai a yanzu ta lura dashi
Tace"ummi waye wanan ne?"
Ummi tace"yayar ki ne IMRAN"
Tashi tayi ba tare tace"ummi sai na dawo,karfe hudu zan dawo"
Tana cikin tafiya ta ji wani murya yace"ke dawo nan"
Tace"..........
Maman
Noorul
Hudahββ
Luv u my fans
Pls share
ππππ
IMRANFAD
ππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.F.π
Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.
Dedicated to Rabi Hussein(hussainata)
π
Ώ7β£&8β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Juyawa tayi ta kalli ummi tace"wa yayi maganar nan?"
Kafin ummi tayi magana ya karaso gaban ta yace"nine ko akawai magana ne?"
Ko kallon shi bata yi ba ta zo zata rasa gefen shi.
Jawo ta yayi yace"ya ina magana kina kokarin tafiya?"
Tace"a matsayin ka na wa zaka bani umurni?"
Yace"rashin kunya zaki yin min?"
Tace"eh d'in kuma wallahi baka isa ka hana ni fita ba"tayi maganan ne cike da raini
Yace"haka kika ce?"
Tace"eh sai me d'an rainin hankali"
Kallon inda ummi ta zauna yayi ya gan bata nan dan tuni ta tashi
Fati ko yi tayi kamar mai barci
Yace"ki koma ciki da kan ki,ko in mai dake "
Sai a sanan ta kalleshi suka yi ido hudu,dafe kirjin ta tayi saboda wani fad'uwa gaba data ji,amma sai ta tsaya tana kallon shi dan idon kamar ta san kwayar idon nan
Katseta tayi dacewa"ina jiran ki fa"
Tace"masa min in wuce"
Yace"an ki,ko kina da abin yi?"
Tace"niko nike da abin yi,dan in baka bani hanya ba sai na,yi maka shegen duka bar ganina mace"
Yace"haka za a yi ko?"
Ture shi take da niyar yi ta gudu amma Kafin tayi hakan ya sinka mata lafiyayyen mari,Wanda yayi sanadiyar d'aukewa jin ta na wasu lokuta
Wani wawan ihu ta kurma tana kiran sunan ummi
Sai cewa"take wayau ummi wallahi na daina gani ko ji bana yi"
Fatima ko sai dariya take yi a kwance
Yace"zaki koma ko sai na b'ata miki rai"
Tace"tuni na koma,ai ni ban ma San inda nike ba"
Jan hanunta ya fara yi zuwa hanyar d'akinta dai-dai nan sai ga ummi ta fito
Ummi tace"kai meke faruwa?"
Ai tana jin murya ummi ta kurma ihu tace"ummi ina kika Shiga ne ake niman hallaka ni?har aka rabka mun ice a kumatu"
Ummi tace"ice kuma"
Tace"eh mana"
Kallon shi ummi tayi tace"meyasa ka rafka mata ice a kumatu"
Yace"ummi ba ice bane bafa"a nan yayi mata bayanin komai
Kallon fadila tayi tace"meyasa baki jin magana ne eh?toh Allah ya kawo dai-dai dake"
Ihu tayi tace"shike nan ummi ma bata sona, ni bamai sona a duniya,ni fadila naga ta kaina"
Ummi tace"nine bana sonki?laila fadila"inda sabo ummi ta saba da irin wanan maganganu a wajen fadila
Kallon shi tayi ta harrare shi tace"kai ka rage zafin ran nan"shigewa tayi ta barsu tsaya
Fadila tace"yanzu ummi tafiya zaki yi ki bar ni da roman reigns"
Dariya ummi tayi tace"ke fa jaruma ce nasan zaki iya"
Bude d'akin yayi ya ja hanun ta ciki sanan fito ya kulle d'akin
Komawa yayi ya zauna a falo
Itako bayan fitar shi ta ji duk d'akin ya manaye da kamshin tularen shi,tunani ta fata yi tace"wanan kamar kamshi tularen aljanin jiya"
Tuna icon shi tayi tace"oho wato shine aljanin hmmm ashe d'an iska ne,"shiru tayi na d'an lokaci tace"wallahi d'an iska ne toh wallahi bai isa inyi me biyyaya ba kuma sai na fita"
Dube-dube drawer ta fara yi har ta gan spare key,a hankali ta bude d'akin ta fits ta bi kofar bays
Bayan mai gadi ya bude mata kofa,ajiyar zuciya tayi
Bayan awa d'aya ummi tace"ya kamata ka bude ta haka ta zo tayi lunch"
Dariya Fatima tayi tace"ai ko ya je ba zai gan ta ba ta kara gaba"
Da sauri ya kalli fatima, ummi tace"ai karamin aikin fadila ne"
Tashi yayi ya haura sama yana zuwa ya gan d'akin bude
Zama yayi kan gado cike da b'acin rai yana tunanin raini irin na fadila
Yace"wallahi sai na gyra miki zama IMRANFAD kar ki yi tunanin ko dan ina son ki zan d'aga miki kafa,I will sure deal with you"tuni idonshi suka canja kala zuwa ja kishi na