Showing 12001 words to 15000 words out of 38921 words

Chapter 5 - IMRANFAD By Maman Noorul Hudah-1-1.txt

Advertisement

23 Jan 2025

4640

d'au dukar ta zaiyi


Ummi tace"za bawa zahra abincin ta kawo muku"


Yace"toh ummi" ba tare da ya kalleta ba


Bayan ya gama cirewa ya d'auke ta ya ajiye saman gado,ya d'auko first aid box ya fara treating ciwon,yana hawayen tausayin ta dan ya ga alamun tana jin zafin abinda yake mata


Ganin yana hawaye,tasa hanun ta goge me tana dariya shima murmushi yayi,ga mamakin shi sai ya gan ta rungumeshi a tare suka sauke ajiyar zuciya


Yace"IMRANFAD sometimes you behave normal please kar ki guje ni in kin warke ba zan iya rayuwa babu ke ba"


Girgiza mai kai tayi kamar tasan abinda yake nufi


Hancin ta yaja yayi dariya yace"kin gan fuskar ki kuwa kamar dodo,ai dole inyi mana selfie inki warke in nuna miki"


Waya ya ciro ya fara kashe musu hoto,zahra ne ta shigo da sallama da tray d'in abinci ta ajiye ta fita


Jawo abincin yayi ya bude ya shiga video a wayar shi ya a jiye wayar a table


Yace"kin san meyasa nike video?Saboda in ki gujeni nayi ta kallo,honestly basan me nike ji ba,murna kina tare dani ko bakin ciki zanyi baki haiyacin ki,gashi ina addu'ar samun lafiyar ki bangare d'aya kuma ina fargaban samun lafiyar ki,amma a ko wani hali kika sinci kanki ina son ki San ina son ki matata"


Kular abincin ya bude ya fara bata har ta koshi


'Bangaren zubys kuwa tana kwance zee ta shigo tace"na zo miki da labari mai dadi"


Zubys tace"shafa min kawas"


Zee tace"ai dana je gida na sami labarin fadila ta haukace"kasancewar zee yar kano ce makociyar su fadila ce,makaranta ne ya kaita yobe garin su zubaida amma ta kan je hutu gida


Zubys tace"ashe dai ina da hope amma me ya hanata mutuwa?"


Zee tace"ai boka zamu canja ai akwai wani a katsina shi zai taimaka mana raba auren"


Zubys race"aure?


Zee tace"eh ashe da gaske ne anyi auren"nan suka ci gaba da shawarar hanyar da za su bi dan raba auren IMRAN da fadila


'Bangaren mummy kuwa




Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IMRANFAD
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we the best among the rest.


πŸ…Ώ3⃣3⃣&3⃣4⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


'Bangaren mummy kuwa cike da tunanin fadila take ji take yi kamar ta je gidan ta d'auko ta amma ba hali dama tayi hakan ne saboda IMRAN ya samu damar kasancewa da matan shi kuma bata son shiga hakkin shi tunda an musu aure ,amma bawai dan tana gudun kiriniyarta ba


Bayan ya gama bata abinci ya dauke ta zuwa bayi wani wanka sukayi sanan yayi mata alwala suka fito


Dadduma ya shifid'a ya d'auko hijabi yasa mata nan suka fara sallah ko me ta gan yayi sai tayi har suka idar


Zama sukayi har aka kira sallah isha'i suka baya sun gama ya gyra gado ya cire mata dogon rigar jikin ta


Akwatin da mummy ta kawu mata ya bude ya ciro kayan barci yasa mata,shima sawa yayi


Ya zo ya rungumeta suka kwanta bedside lamb ya kashe


Barci ne ya gagare shi domin sha'awar ta na niman illarta shi tunda ya ganta ba kaya yake ji kamar komai ma ya faru a wuce wurin,a ran shi ya yace"no bazan iya ba ai sai ta d'auka jikin ta nike so ba ita ba,bari dai in jira ta samu sauki mu ga abinda zai faru"


Wani zuciyar kuma yace"amma ai zaka iya rage zafi ai" da wanan tunanin ya fara romancing d'inta kuka ta fashe mai da shi amma ina yayi nisa sanda ya tabbatar ya rage zafi son ran shi ya koma gefe tare da rungumota


Shafa bayanta ya fara yi har ta fara barci,ajiyar zuciya ya sauke ganin nauyinta ya karu alamun tayi barci


Shima barcin yayi cike da tunani kala-kala


Washe gari ya shiryata breakfast suka yi sanan ya kama hanunta suka fito falo ummi


Ummi na ganin su tace"ina zaku ne haka"


Yace"asibiti wajen specialist"


Ummi tace"toh Allah ya kiyaye hanya"


Yace"amin


IMRAN ne gaban Dr bayan ya gama me bayanin matsala fadila tare da mika me file d'inta


Dr bashir yace"gaskiya ya kamata ku kiyaye abinda zai sata dogon tunanin domin in tana kokarin tunawa hakan zai iya sa ta manta komai da komai"


Yace"toh miye mafita ne?"


Yace"na farko ka yawaita kaita wuraren da take zuwa da,na biyu kuma shine ayi abubuwan da suka faru da misali ko fad'a haka ko wani event da ta tana zuwa,amma kar ayi mata dole in kuka yi haka kuka gan tunani na niman rikita ta toh kuyi gaggawar daina koma miye"


Yace"babu wani hanya kuma ne?"


Dr yace" akwai but is to risky"


Yace"fad'a min"


Yace"hanyar da zai sa ta dawo da tunaninta babu b'ata lokaci,amma yana da wuya shine ayi creating hatsari a gaban ta a saka wanda ta fi ko kuma a sata da Wanda tayi hatsarin da shi,ina ganin wanan zaifi sauri"


Yace"gaskiya Dr bazan iya bin wanana hanyoyin ba,na farko ina son ta manta da kwallo bazan iya kaita wurin da kaina ba,na biyu kuma wuraren da take zuwa da friends d'inta ne bani ba yanzu ma suna prison saboda abinda suka yi mata a bayan,na uku bazan iya taking risk d'in sata a mota ba dan a yi creating wani accident ba what if wani Abu da ya fi wanan ya same ta?"


Dr bashir yace"OK bari in rubuta maku magani tayi tasha inshaallah zata samu lafiya"


Yace"OK nagode"


Zubys ne gaban wani malami da kasa gaban shi bayan ya gama buga kasa ya kalleta yace"gaskiya bazan iya shiga tsakanin su ba domin soyayyar da yake yi mata a jinin shi yake,ina mai baki shawara kiyi gaggawar fita daga lamarin su in ba haka ba karshen ki baza tayi kyau ba"


A fusace ta kalleshi tace"yi mun shiru malam kai har ka isa ka hanani auren IMRAN toh wallahi baka isa ba,in baza ka iya ba zanje wasu suyi min"mikewa tayi tace"ni zubaida nayi alkawari auren IMRAN ko ta wani hanya"


Kallonta yayi yace"ko kin aure shi babu amfani"


Cikin b'acin rai ta bar wajen


Bayan sun dawo gida ya zauna falon ummi,fadila ta fara b'arna da kayan ummi


Wayar ummi ta d'auka zata buga kasa ummi tace"dan Allah karki fasa min waya"


Kafin IMRAN ya karasa ya ansa wayar a hanunta har ta bugs shi kasa


Dariya tayi tana tapi,shima dariya yayi


Ummi tace"watoh baki kuka had'a ko toh gama ku siyo min wata"


Yace"yanzu kuwa"


Hijabi ya d'auko yasa mata


Ummi tace"tare zaku?ka barta mana kaje ka dawo"


Yace"no ummi inta lura bana nan kuka zatayi nikuma bana son kukanta"


Baki ummi ta bude tana kallonsu


Yace......








Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IMRANFAD
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


πŸ…Ώ3⃣5⃣&3⃣6⃣


Bismillahi Rahmani Rahim


Yace"toh ummi sai mun da kenan"mikewa yayi da sauri itama ta mike


Hijabi ya d'auko yasa mata,ummi ko mamakin inda ya canja gaba d'aya take dan ita tayi tsamanin ba zai iya da ita ba dan zafin zuciyane da shi ga saurin hanun


Suna fita ya bude mata mota ta shiga sanan shima ya zagaya ya shiga


Shagon sar da waya suka je ya zab'i wanda ya keso,fadila sai d'aukan wayoyin take yi,inya ansa ta d'auki wani,mai shagon yace"ke meyasa kike abu kamar yariya ne?"


Da sauri ta koma bayan IMRAN dan ba karamin tsoro ya bata ba domin yayi maganan ne cikin zare ido


Ciki fushi IMRAN yace"how there you shout at her?are you insane?"


Mai shagon yace"yi hakuri naga kana ta yi mata magana ne taki ji,shiyasa nayi mata ihu kar ta jawo min asara tunda ita ba yariya bane"


IMRAN yace" kar ka damu zan biya ko nawa ne"


Mai shagon yace"amma mai gida tana da tab'in hankali ko?"


Ai sai sauka mari a kumatun mai sayar da waya cikin fushi yace"kai ne mai tab'i hankali ba matata ba"ganin IMRAN na masifa yasa fadila nuna mai shagon da hanun sai girgiza kai take yi alamun fad'a


Mutane ne suka fara taruwa gaban shagon sai yiwa fadila dariya suke, abin ba karamin b'atawa IMRAN rai yayi ba cikin b'acin rai ya ja hanun fadila suka bar shagon ba tare da ya siyi wayar ba


Wani shago suka shiga a nan ya siye waya


Bayan sun bar shagon direct gidan mummy suka je


Mummy na ganin su tace"sanun Ku da zuwa"zuwa tayi zata rungume fadila,da sauri fadila ta rike IMRAN


Jiki a matukar sanyaye mummy ta koma gefe tana murmushin dole


IMRAN ya lura da inda jikin ta yayi sanyi yace"mummy kiyi hakuri fadila bata gane ki ba,nasan abin da ciwo a ce kina matsayin mahaifiyarta amma bata yarda ki tab'a ta please ki bata lokaci"


Murmushin dole tayi tace"no its ok I understand, ya su ummi"


Yace"lafiya"


Tace"toh zauna mana,nasan jira take ka zauna itama ta zauna"


Zama yayi,ganin ya zauna yasa fadila zama kusa dashi, amma taki sakewa sai wani manne me take yi


Mummy tace"ashe kana shan fama,sannu da kokari IMRAN"murmushin yayi


Kiran zahra tayi tace"kawo musu abinci"


Zahra tace"toh"


IMRAN yace"yaushe zahra ta dawo nan"


Mummy tace"shekaran jiya"


Yace"ni ban ma kula bata gidan ba"


Mummy tace"ina kuwa zaka kula an had'a ka da babban aiki"


Feena ne ta sauko suka gaisa


Bayan sun gaisa tace"yauwa in zaku wuce zan biku wajen ummi nan zan karashe hutuna"


Yace"toh"


Bayan sun gama cin abinci ya sallami mummy dama feena ta gama had'a kayanta jiran su kawai take yi


Mummy tace"ko zaku dan jira ga hadari"


Yace"no,bari muje kawai tunda ba nisa"


Suna isa aka fara ruwan sama,da gudu feena ta fita a motar ta shige ciki,ta bar su a mota


Fadila ko kokarin bude motar take yi tana son ta fita


Yace"no,IMRANFAD bana son ruwan nan ya taba ki,zaki yi zazzabi"


Kuka ta fashe dashi,zafi ya fara ji a zuciyar shi


Ganin taki dainawa yasa shi bude motar da gudu ta fita tana wasa cikin ruwan


Sai dariya take yi
Zuwa tayi ta jawo shi ta rungume ruwan sai dukan su yake yi


Shima rungumeta yayi a ranshi yace"FAD will never change watoh bata manta wasa a ruwa ba"


Feena na shiga ummi tace"toh ina su IMRAN ba kin ce tare kuke ba"


Tace"eh ummi suna mota ai"


Ummi tace"a motar ya bar y'ar mutane da wanan sanyi muje ki nuna min inda suke"


Fitowa sukayi,ganin su suka yi sai wasa sukeyi cikin ruwa hankali kwance


IMRAN ko ya fara kissing fadila,da sauri ummi ta shige cikin


Feena ko tsayawa tayi a balcony tana kallonsu dan ba karamin burgeta sukayi ba tace"what a perfect matce"


Shigewa tayi,sai gashi ta dawo da waya a hanun video ta fara yi musu


Ummi na shiga direct bedroom din Abba ta shige


Abba yace"lafiya kika shigo a hargitse"


Tace"hmmm IMRANA na bani kunya a nan gidan"


Abba yace"ni tunanin dirama da za a yi da fadila nike tunani in ta gane shine mijinta inta dawo hayyacinta"


Ummi tace"karka damu ai kafin lokacin ya d'ura mata ciki"


Dariya Abba yayi yace"ashe komai zai zo da sauki kenan"


Ruwan sama na tsayawa IMRAN ya........








Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IMRANFAD
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


πŸ…Ώ3⃣7⃣&3⃣8⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Ruwan saman na tsayawa IMRAN ya d'auki fadila ya bi kofar baya da ita,yana kaiwa d'akin shi direct bayi ya dire ta


Tube ta yayi,shima ya tube kayan jikin shi sanan suka wanka had'e da alwala suka fito


Dogo riga ya sa mata da hijab,shima yasa jallabiya sanan suka yi sallah mangrib


Suna idarwa ya fara addu'oi al-qurni ya bude ya fara karantawa sai kallon shi take yi,ana kiran sallah isha suka yi


Bayan sun idar ya lura fadila na rawar sanyi yace"kin ga abin da nike gudu ko gashi sanyi ya kama ki


Wardrobe ya bude ya Ciro mata kayar barci riga da wandon,cire mata dogon riga yayi yasa mata riga da wandon,shima irin shi yasa ya d'auko waya yayi musu selfie


Yace"I cherish this moment dear just in case kin guje ni shi zan yi ta kallo,ina tuna da ke"


Ajiyar wayar yayi bayan ya gama abin da yake yi ya kwanta,ganin ya kwanta itama ta zaga ta kwanta a d'aya gefe,blanket ya rufa musu


Ai sai yaga fadila ta maso kusa dashi ta had'e bakin su,kamar yana jira ya cafke ya fara tsosa kamar sweet


Shiru tayi alamun tana jin dad'i abin da yake yi mata


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda yanzu watanin fadila shida da manta memory d'inta kuma IMRAN ne ke kula da ita ko ina za shi tare za su,bai taba nuna gajiya ba


'Bangaren zubys kuwa ko wani boka cewa yake yi ba zai iya raba IMRAN da fadila ba wasu su fad'a mata gaskiya wasu kuma sun ci kudin ta,amma ba biyar bukata,amma ta sha alwashi raba su ko ta wani hanya


'Mummy ko yanzu ta bar ma Allah komai kullum cikin yiwa fadila addu'a take


Daddy ko hankalin shi kwance dan ya gan irin kokarin da IMRAN keyi akan fadila domin ko aiki baya zuwa in ba ta kama dole ba


Kullum addu'ar shi d'aya ne shine inda dawowa tunanin fadila alheri ne Allah ya tabbatar musu inda kuma babu alheri Allah ya barta haka ta rayu da mijinta cikin kwanciyar hankali


Yau ta kama Monday misalin karfe 7:am IMRAN ne cikin shirin zuwa aiki da alama office za shi,fadila kuma tana kwance tana barci


Pecking d'inta yayi a goshi sanan ya bar d'akin,yana saukowa ya tarar da ummi a falo tana jera breakfast a dining


Ummi tace"ina zaka ne haka kuma ina ka bar jela taka?"


Yace"ummi office zani,tana d'aki tana barci,pls ki kula da ita in ta tashi ba dadewa zanyi ba"


Ummi tace"amma kasan ba yarda zata yi ba,balle in ta farka bata gan ka ba akwai daru"


Yace"ummi please try your best ba dadewa zan yi ba meeting d'in is important ne kuma in naje da ita zata yi distracting d'in na"


Tace"eh haka ne,bama dadi ka tafi da ita"


Yace"inshaallah zan dawo kafin awa biyu"


Tace"toh zauna kayi breakfast"


Yace"no,ummi zan yi latti"


Tafiyar IMRAN da minti talatin fadila ta farka saga barci,dube-dube ta fara yi ganin baya d'akin yasa ta saukowa da gudu


Su ummi ta gani a dining suka breakfast feena tace"ummi gata ta farka"


Ummi tace"na shiga uku"


Fadila na ganin babu IMRAN tasa kuka,tashiwa ummi tayi ta karasa inda take ta fara lallashin ta,amma taki ji


Fenna tace"toh a kira yaya mana"


Kiranshi aka yi amma bai d'auka ba


Da k'yar ummi ta lallashi tare da kai ta d'akin su


Ummi tace"yi shiru zai dawo yanzu kwanta ki jira shi"


Kwantawa fadila tayi,ummi race"Ashe tana jin magana"


Yi tayi kamar mai barci ummi tace "alhadullilahi gomma kiyi barci in ya dawo sai kuyi breakfast"


Fita tayi ta barta a d'aki,bayan awa biyu IMRAN ya kira ummi a waya


Yace"ummi FAD ta tashi?"


Tace"eh amma ta kama barci"


Yace"please a bata breakfast aiki ya rike ni"


Ummi tace"amma kasan ba yarda zatayi ba ko?"


Yace"ummi please ki lallabata zata ci"


Tace"toh bari in taso ta"


Dakin shi ummi taje abin mamaki tana zuwa ta gan babu fadila,bayi ta bude amma babu alamun ta


Da sauri ta koma falo tace"nafeesa ba gan fadila ba"


Feena tace"kila tana waje cikin gida"


Ummi tace"toh taso mu duba"


Babu inda basu duba ba amma babu alamar fadila


Tuni hankali ummi ya tashi noba IMRAN ta Kira ta fad'a me halin da ake ciki


Ikon Allah ne kawai kawo shi gida yana zuwa ya fito a mota yace"ummi ina FAD"


Ummi tace"bamu gan ta ba"


Tuni idonshi suka canja kala zuwa ja


Feena tace"calm down yaya zamu gan ta"domin ta tsorata da yanayin shi




Ai a fusace yace"dont tell me to calm down,my wife is missing and you expert me to calm down"


Gaban me gadi yaje ya shaqe shi yace"ina matata?ka fito min da ita"


Mai gadi yace"wallahi mai gida gudawa Nike yi toh ina sanmani dana he bayi ne ta samu ta bar gidan"


IMRAN yace....




Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IMRANFAD
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


Dedicated to MATA MASU HADI KAI group Allah ya bar mu tare




πŸ…Ώ3⃣9⃣&4⃣0⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


IMRAN yace"wallahi in wani abu ya sameta sai na d'aure ka"


Ummi ne ta karaso inda suke tace"IMRANA sake shi,kashe shi zaka yi ne?"


Da k'yar ya sake mai gadi ya shiga mota ya bar gidan


Direct gidan mummy ya je ya gan ta zaune a garden da sauri ya karasa inda take yace"mummy FAD ta zo nan?"


Tace"no,ai sai ka bari mu gaisa"


Hanun yasa a kai yace"mummy ba gan IMRANFAD ba"


Mummy tace"ban gane"


Yace"wallahi ba gan ta ba"


Cikin tashin hankali tace "what?hijabi ta saka tace" muje mu duba cikin anguwa insha allahu za a gan ta"


Wasa-wasa babu inda ba a duba ba amma ba labarin fadila gashi dare ya fara yi,IMRAN duk ya fita hayyacin shi kowa ya tausaya me


Abba yace"toh bari muje station ayi report"


Suna Barin gidan,IMRAN shima ya tashi mummy tace"ina kuma zaka ne?"


Yace"zan kara dubawa ne"


Tace"zauna ka huta ai mun duduba"


Yace"no ummi bazan iya ba ina ji ajiki na FAD na niman taimako na"


Ummi tace"bar shi yaje mu da muke nima ina muka gan Hutu"


Mummy tace"wallahi hajiya tausayi yake bani,wanan wani irin jarabawa ne?"


Tafiya yake yi yana duba lungu da sako na anguwan


Yana kaiwa wani lungu inda yan shaye-shaye suke zama ya ji wani daga cikin su na cewa" baba ya kamata mu yi Sauri mu huta da yariyar nan tun kan a kama mu"da har zai wuce sai ya ji


D'aya daga cikin su yace"ni dai ba ruwa na,kusan yar waye ne kuwa?yar gidan alhaji naira ne fa,ko Baku da labarin abinda aka yiwa su nazir da sani"


D'aya yace"ai yanzu an ce bata da lafiya ka ga ba me ganew...."bai karasa maganar ba sakamako saukan mari da ya ji


Jini ne ya fara fita daga bakin shi,ai sai IMRAN ya fara dukan su


Ganin baza su iya da shi ba yasa sauran guduwa suka bar gurin,sheke shi yayi yace"ina take ?"


Cikin azaba ya nuna me wai karamin d'aki,ture shi yayi ya shiga d'akin


Ganin ta yayi zaune

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login