Showing 6001 words to 9000 words out of 38921 words

Chapter 3 - IMRANFAD By Maman Noorul Hudah-1-1.txt

23 Jan 2025

4034

tashi tsaye zaki yi"


Zubys tace"kamar ya?ban gane ba"


Zee tace"ai shiryawa zakiyi muje wajen malam gone dan niman biyar bukata"


Dariya suka yi har da shewa


IMRAN ne kwance cike da haushin FAD amma ya rasa dalilin da yasa gaban shi ke fad'iwa tun a matsalaci


Tashi yayi ya zauna waya ya d'auka ya kira zarah yace ta duba me ko FAD na nan,dubawa tayi tace bata cikin d'akin"


Duba agogo yayi ya gan 9:20pm a fili yace"FAD ba lafiya"


Da sauri ya fita ya kama hanya gidan kwallon amma yana zuwa ya gan me wurin na kokarin kullewa


Karasawa yayi yace" please ina FAD ne?"


Yace"ai tun d'azun ta wuce bata kaiwa 9 waje


Wani ne zaune yana shan sigari ya taso yace"oga bani wani abu in gaya ma Inda take tun kan ayi mata illa"


Da sauri IMRAN ya kalleshi yace"illa?"


Yace"oga kana b'ata lokaci fa"


Kud'in IMRAN ya fito dasu masu yawa ya bashi


Dariya yayi yace"biyo ni mai gida"


Bin shi IMRAN yayi zuwa wani lungu da ake kira ihun ka banza tsoro ne ya kamashi tunani ya fara yi meya kawo ta irin wanan wurin


Suna shan kwana ya hango samari biyu watoh nazir da umar




Fadila ko na kwance idon biyu amma bata da karfin jiki dan ko motsi ma bata iya yi




Nazir na kokarin cire rigarshi ai da sauri IMRAN ya karasa ya naushe


Nan fa aka fara dambe




Umar ya d'auko sanda zai kwala me yayi saurin tarewa


Ganin baza su iya da shi ba yasa suka gudu


Kallon fadila yayi dake kwance yayi ball da ita Marin ta ya dingayi amma ko motsi bata yi


Lura yayi da bata hayyacin ta yayi sauri d'aukan ta a kafad'a suka bar wurin


Suna kaiwa gida ya ajiye ta falon mummy


Daddy yace"meke damun ta ne"


Cikin haushi da tausayin daddy nan yayi me bayani




Daddy yace"........






Maman
. noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IMRANFAD
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

πŸ…Ώ1⃣7⃣&1⃣8⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Daddy yace"Allah na gode ma"cikin fushi ya fara dukan ta mummy ma haka sai kuka take yi ta Marin fadila


Tace"ka ji yariya zata d'auko mana abin kunya"


Ruwan sanyi IMRAN ya d'auko a fridge ya wasa mata a jiki a firgice ta zare ido ganin mummy na kuka yasa ta shigar tashin hankali


Tace"nashiga uku"


Marin da daddy yayi mata ne yasa ta dawowa hayyacin


Yace"fadila kafin ki kashe ni,ni zan kashe ki"


Kuka take yi tana bashi hakuri tace"wallahi na tuba"


Shiko IMRAN shiru yayi ya tausayin ta dan ba karamin duka abba keyi mata ba


Sai ihu take yi ta na cewa"yaya IMRAN ka dubi girman Allah ka rufa min asiri ka ceci rayuwa ta daddy zai kashe ni"


Ganin bayi da niyar taimakonta yasa tace"daddy wallahi in ka kashe ni zaka nadama kuma za a kama ka,shi dama IMRAN mugune noba 1 nasan ba zai taimake ni ba"


Mummy ne ta halbe ta da takalmi tace"yiwa mutane shiru ana dukan ki amma baki yaki mutuwa"


Bayan daddy ya gama dukan ta ya ya kalli IMRAN yace"kai kira mun alhaji"




Yace"toh daddy"


Kiran abba yayi tare da yime bayani


Da sauri abba ya gayawa ummi suka kamo hanyar gidan mummy


Da sallama abba ya shigo falon


Fadila na ganin ummi ta taso da gudu ta boye a bayan ta


Tace"ummi ki taimake ni ki fito dani daga gidan nan kashe ni zasu yi dan Allah"


Abba yace"d'auke ta Ku je gida"


Ummi tace"toh"


Zama abba yayi yace"ai mun gode da basu yi nasara ba"


Daddy yace"rabu da yar iskar yariya"


Abba yace"kul babu kyau iyaye na furta mugun kalamai a kan ya'ya su hakan na tasiri"


(Iyaye please mu kiyaye musan irin kalamai da zamu dunga furta in rai ya b'aci domin yana matukar tasiri,Sai ka ga mace bata da wani zagi sai, yar iskar yariya sha-shash,toh kin kira ta yar iska tun bata san me ake nufi da iskanci ba har ta gane,toh me kike gani zai faru?"Allah ya shiya mana ya'ya ya kare su daga fadawa hallaka)


Daddy yace"toh Allah ya shirye ta"


Abba yace"yanzu kayi magana"


Daddy yace"alhaji aure zanyi mata"


Abba yace"toh tana da Wanda take so ne?"


Nan fa gaban IMRAN ya fara dukan-dukan uku-uku


Daddy yace"ko da messenger ne wallahi had'a ta zanyi"


Kallon IMRAN mummy tayi ta ga tashin hankali kara-kara


Tace"IMRAN je part d'inka zan nime ka"


Da k'yar ya ja kafanshi da tayi me nauyi ya bar falon


Yana fita direct gidan ummi yayi


Abba yace"me zai hana a had'a ta da IMRAN"


Da sauri mummy tace"eh hakan ya fi"


Daddy yace"no!bana son a takura shi"


Abba yace"babu wani takura ai ko da a ce yau an yi mata fyad'e ai shi me rufa mata asiri ne,balle babu komai da ya same ta"


Daddy yace"toh,Allah ya zaba mana abin da yafi alkairi"


Amin suka ce a nan suka sa nan bikin nan da sati biyu


IMRAN na kaiwa gida ya tarar ummi zaune yace"ummi ina FAD?"


Ummi tace"tana d'aki ina ganin sai tasha magani"


Yace"yanzu zan bata"


Zama yayi sai tsaki yake yi ummi tace" lafiya?"


Yace"ummi ki duba fa wai FAD za ayiwa aure yar yariyar nan"


Ummi tace" toh ina ruwan ka ai ko fadila ta isa aure"


Tashi yayi ya fara up-down


Ummi tace"toh miye na damuwa?"


Yace"hmm bazaki gane ba"


Tace"ko dai zargi da nike gaskiya ne?


Yace" wani zargi"


Tace"ko san fadila kake ne?"


Yace"Allah ya kiyaye wanan yar cikular yariya"


Ummi tace"toh ba damuwa"amma ban dan ta yarda ba


Abba ne ya dawo yayi wa ummi bayani


Tace" toh Allah ya sanya alkairi"


Ranar IMRAN da fadila da zazzabi suka kwana nashi na fargaban waye za a aurawa FAD,ita kuma na duka da daddy yayi mata dan bata masan da zancen auren ba


Washe gari zubys ne da zee gaban wani boka da


Bayan me bayani ya d'auko wani farin yadi ya rufe da kwarya bayan yayi wasu surutai


Ya bude ya kalli zubys yace"gaskiya baya son ki,kuma in kin ga bai auri yariyar ba sai dai in d'ayar su baya raye,domin soyyayar ta a cikin jinin shi yake"


Tace"malam ba wani hanya?"


Yace "hanya d'aya ne a kasheta"


Zee tace"toh boka me ake jira?"


Yace"toh amma sai aljani ya huta da ita na kwana goma tukuna,zata dawo nan da zama"


Da sauri ta kalli zee,zee tayi mata alama data amince


Tace"ta amince"


(Allah ka rabu mu da San zuciya irin na zubys)


Gari na wayewa IMRAN na tashi daga barci ya tafi gidan mummy


Yana kaiwa ya zauna gaban ta yace......








Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IMRANFAD
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.




πŸ…Ώ1⃣9⃣&2⃣0⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Yana shiga falon mummy ya zauna kasa yace"mummy na shiga uku za a raba ni da IMRANFAD dina mummy kin san inda nike sonta tun tana ciki please ki taimake ni mummy,ita ce rayuwata"


Tace"ai in ina da rai fadila taka ce har abada ko shi daddy yayi hukunci ne cikin fushi bawai dan baya sonka ba amma wallahi ya dade da baka fadila,kar ka damu yanzu a sansanta komai nan da two weeks ne d'auri auren ka"


Tuni ya fara washe baki yace"amma mummy fadila bata sona fa"


Tace"dole ne ma ta so ka in tana son farin ciki ne"bama zata san maganar auren sai an d'aura"


Fadila ne kwance a d,'akin ta zazzabi ya rufeta ummi ne tashigo d'aki tace" ya jikin"


Tace"da sauki"taba jikinta ummi tayi ta jishi da zafi


Tace"a'a fadila ba sauki bari in kira IMRAN ya zo ya duba ki"


Tace"ni dai ummi a kira min daddy na da mummy in basu hakuri,wallahi nayi nadama,ummi kaico na sanadiyata mummy na tayi kuka,wallahi na tuba"


Ummi tace"haka ake so ai ki gane kuskuren ki,please ki yi masu biyyaya"


Tace"ai dana ji sauki zan koma makaranta ai"


Kiran IMRAN ummi tayi a waya ta fad'a me halin da fadila ke ciki na rashin lafiya


Bayan minti biyar sai gashi ya shigo


Tana ganin shi tace"bakin mugu,"


Yace"me kika ce"tace"ba komai"


Duba ta ya fara yi baya ya taba jikin ta ya kalli ummi


Yace"gaskiya sai an kara mata ruwa da allurai,taci abinci kuwa?"


Ummi tace"bana sammanin ta ci abinci inaga rabobta da abinci jiya ne,amma bari inje in had'a mata"


Yace"toh nima bari kwaso alluran a d'aki na"


D'akinshi yaje sai gashi ya dawo da ledar drip da allurai


Kallonta yayi yace"gyra inyi miki"hanun ta mika me,a ranshi yace" wanan yariyar akwai rainin hankali me take nufi a hanun kena zan mata alluran


A fili kuma yace"no bana hanun bane a d'uwawo zan miki"


Tace"lah d'an iska ne"da k'yar ta yarda yayi mata aluran"


Bayan kwana goma zubys ne a d'akin boka wanda babu komai sai taburma ga uban duhu,ga mata a d'akin sunfi biyar da sunan aljani na huta da su dan samu biyan bukata


(Mata mu ji tsoron Allah ya kamata mu gane rayuwa bata da tabas kai ne yau gobe ba kai bane,shi boka ko malam bashi da abin da zai baka da sunan biyar bukata,asalima shima taimakon ya ke nima a wajen ubangiji dan wallahi da yana cikin wadata da kwaciyar hankali da ba zai zabi zama a dajin Allah ba,mata ina zamu kai wanan zunubin wai kaga mace har mace wai ta bude wa boka kafa yayi abinda zai yi,Allah ya kyauta


In damuwa ne yayi maka yawa ga gayawa Allah cikin dare ta hanya yin nafila,sadaka,azumin monday da alhamis,taimakawa maraya ko na kasa da kai,in ka gan bukatar ka be biya ba toh ka d'auka cewa wanan abun da kake so ba alkairi bane a gare ka,Allah ubangiji yasa mu dace)amin


Tana kwance bokan ya shigo yace"ke biyo ni"


Tashi zubys tayi jikin na rawa ta bishi dan ta kosa ta bar gidan


Wani d'aki ya kaita yace"aljani ne ya zo yace yana son ganawa dake"


Tace"malam yau fa na uku ke nan wallahi zafi nike ji gashi da k'yar nike tafiya"


Yace"hakuri zaki yi ai yace yana jin dad'in ma'amula dake ne kuma na da kwana biyu bukatar ki zata biya"


Tace"wallahi kuma wari ne da shi"


Ihu yayi mata yace"ke yi mun shiru ko in hallaka ki,waya ce miki ana yi wa aljani musu"


Shuru tayi yace"gyra ki kwanta dan ya karaso jira kawai yake ki tube ya shiga jikina"(hmmm Ku ji raini hankali)


Kwanciya tayi ya haye ta kamar matar shi


Bayan kwana biyu ya kama kwanan zubys goma sha biyu a wajen boka,bikin fadila kuma da IMRAN saura kwana biyu kuma fadila bata sani ba




Tana zaune mummy ta kawo mata d'inkakun kaya tace"ki gwada"


Tace"mummy na menene haka dayawa?"


Mummy tace"na fitar bikin ki ne?"


Gaban ta ne ya fad'i tace"bikina kuma?"


Mummy tace"eh jibi ba"


Daddy da ke dinning yace"jibi d'aurin auren ki"


Kuka ta fashe dashi tace"haba ai bayi mun adalci ba,ai na tuba kuma na gane kuskurena amma shine za a yi min auren dole dan ba a sona"


Mummy ne ta d'auki marfin kila ta halbe ta tayi saurin kwacewa da gudu ta bar falo ta tafi gidan ummi tana kuka


'Bangaren IMRAN kuwa farin ciki ne fal a ranshi zai mallaki matar da ya dade yana burin sure


Yana shiga ta tarar da Abba zaune yana hutawa


Rushewa tayi da kuka tace......






Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IMRANFAD
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


Dedicated to anty shamsiya (maman fati)nagode da kulawar ki gare ni Allah ya baki abin da kike so)


πŸ…Ώ2⃣1⃣&2⃣2⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Rushewa tayi da kuka tace"Abba auren dole za a min ka taimake ni"


Yace"fadila kiyi hakuri an Riga da an sa rana watoh jibi"


Tace"abbana ka taimake ni a fasa auren nan ni wallahi bana so"


Yace"fadila ina so kiyi wa iyayen ki biyyaya wanan karo please bana so ki yi musu gardama,ko kina so su yi fushi dake?"


Ta girgiza kai,nasiha yayi ta mata har tace ta hakura amma cikin ranta ba haka bane ta kudurta cin uban koma waye ne mijin nata




Tashi tayi ta shige ciki cike da bakin ciki


Bayan shigar ta da minti 10 wayarta yayi kara
Dubawa tayi ta gan nafisa ce yar yayar mummy


D'agawa tayi tace"hello feena yana gan kin kirani da noban nija?"


Feena tace"amarya baki laifi,ai yanzu na sauka nija ko gida banje ba na zo ayi biki dani tunda baki fad'a min ba"


Tace"hmmm ai ko nima ban gaiyaci kai na ba,yanzu ina kike ne?"


Feena tace"yanzu na sauka a airport ki zo ki dauke ni"


Tace"alright give me 30minit"


Tashi tayi ta Shiga bayi tayi wanka tana fitowa ta d'auki wani dogaon riga cikin kayan fita bikin ta tayi kyau ba karya ko dama bata yi make up ba


Hijabi tasa ta dauki makullin mota ta bar d'akin


Tana fitowa kowa falon yace"wow kin gan inda atampa yayi miki kyau kuwa?shine baki son sawa" ko ta kan su bata yi ba ta karasa wajen ummi


Ummi tace"ina zaki kuma ne?"


Tace"feena zan d'auko a airport yanzu zan dawo"


Ummi tace"ki dawo da wuri mai design zata zo anjima kar ata jiran ki"


Tace"toh"


Tana fita ta karasa wajen motocin gidan IMRAN dake tseye a balcony ya gan fitowar ta


Yace"ko ina zata?"wani tunani ne ya fad'o me


Yace"karfa guduwa zata yi,da sauri ya karaso wajen motar da tashiga


Shiga yayi tace"ya haka"


Yace"ai wallahi bin ki zanyi duk inda zaki,ance miki ni wawa ne zan bari ki gudu"


Batare da tayi magana ba ta ja mota ta tafi


Zubys ne gaban bokan ta yace"yanzu kuwa za a gama aikin"


Tace"toh"


Wani fari kalle ya bude sai ga wani madubi ya bayyana a bango


Yace"kalli da kyau yanzu zan cika aiki na"


Ganin fadila tayi da IMRAN a mota yasa ta zaro ido tace"boka ni bana son komai ya same shi fa"


Yace"kar ki damu babu abin da zai same shi ai bada sunan shi akayi ba"


Fadila na cikin driving ta ji kamar an wasa mata barkono a ido,ihu ta tace"idona bana gani please control the car"


Kafin IMRAN yace zaiyi wani Abu wani katon truck ya kwashe su ihu yayi yana sallati gagarawa motar su yayi zuwa daji


Cikin minti goma mutane suka taru a wajen nan aka yi gaggawan cire su a mota aka kira ambulance domin cikin su bama motsi




Wayar IMRAN aka ciro a aljihun wandon shi aka kira ummi aka fad'a mata halin da ake ciki,sallati tayi mutane suka fara tambaya ko lafiya


Bayani tayi musu,tuni gidan biki ya dawo gidan bakin ciki


Cikin tashin hankali ta kira Abba ta fad'a me dama yana tare da daddy


A na kaisu asibiti batare da b'ata lokaci ba aka kai su emergency dan basu taimakon gaggawa


Ba karamin tashin hankali iyayen su suka shiga ba,




Bayan awa uku sai ga likita ya fito,da sauri suka karasa inda yake mummy tace"ya jikin IMRANA ne"


Tana tambayar IMRAN ummi na tambayar lafiyar fadila,Abba ma bama iya magana ba jira kawai take ya ji bayanin doctor,daddy ne kawai mai karfin hali cikin su


Dr yace"muje office d'ina inyi muku bayani"


Bayan sun zauna a office d'in Dr yace"muyi kokarin ceton shi namijin zai iya tashi nan da awa biyu"


Ummi tace"macen fa?"


Yace"gaskiya akwai matsala"


Abba yace"wani matsala ne?look Dr money is not the problem do everything within your power to save her life"


Dr yace"........






Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IMRANFAD
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


πŸ…Ώ2⃣3⃣&2⃣4⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Dr yace"a gaskiya alhaji akwai matsala domin ba karamin buguwa kan ta yayi ba,tana da internal injuries so I can see anything for now"


Abba yace"komai zakayi ayi amma please a ceto rayuwarta"


Daddy ma kasa magana yayi domin a zahiri sai ka d'auka bashi da damuwa amma cikin zuciyar shi ba haka bane


Ummi tace "yanzu ina take ne?"


Dr yace"tana intensive care unit (I C U)shi kuma namijin na ward"


Mummy tace"toh Allah ya kyauta"ji take kamar tasa hanu tayi ta ihu jin yariyar ta guda na wani hali amma sai ta dake


Ummi ko sai kuka take


Dr yace bari ayi mata xray nan zamu San actual abinda ke damun ta apart from buguwa ta kai"


Bayan awa biyu da rabi mummy ne zaune da a d'akin da IMRAN yake,ita kuma ummi na kofar d'akin fadila tana kallon ta ta glass addu'a take yi mata a zuciyar ta,ganin fadila bata numfashi sai da taimakon oxygen hakan ba karamin d'aga mata hankali yayi ba


IMRAN ne ya fara motsa hanun shi da sauri mummy ta karasa kusa da shi,a hankali ya fara bude idanun shi har ya gama bude su


Mummy tace "alhamdullilah IMRANA Allah nagode ma"


Yace"mummy ina nike ne?"


Tace"asibiti d'azun kaka yi hatsari da fadil..."


Ai da Sauri yace"ina FAD take yanzu"


Shiru mummy tayi sai hawaye,ganin mummy na kuka yasa hankalin shi tashi


Yace"mummy please fad'a nun ina IMRANFAD d'ina take ne?"


Ganin mummy bata da niyar magana yasa shi tashi tashi ya zauna bakin gado yana kokarin cire ruwan hanun shi cikin kuka mummy tace"meya haka IMRAN baka ganin halin da kake ciki ne"


Yace"mummy please ki fad'a mun halin da FAD dina take ciki"


Mummy tace"calm down ka kwantar da hankalin ka inka d'an samu lafiya sai inyi ma bayani"


Yace"mummy mutuwa tayi ne?"


Tace"a'a tana nan"


Yace"mummy please na roke ki taimaka ki fad'a mun halin da take ciki wallahi bazan iya rayuwa babu fadila ba please"


Tausayi ya bata tace"fadila na raye amma a coma domin ko numfashi bata yi kuma Dr yace the chances of her survival is very slim dan tana da interna injuries most especially a kai"


Idon shine ya kad'a yayi ja cikin tashi hankali yace"tana ina yanzu?"


Mummy tace "I C U"


Batare da yayi magana ba ya fara cire drip d'in jikin shi


Mummy tace"son meye haka ne"


Yace"zan je ingan FAD dina"


Tace"you have to calm down"


A fusace yace"what do you mean i should calm down?my life is in coma and you expert me to calm down"


Shiru mummy tayi dan ta tsorata da yanayin shi sai abubuwa yake yi kamar tababe


Yana mikewa yaji wani jiri ya dibe shi,zama yayi hade da dafe kanshi


Da sauri mummy taje dan taimaka me,ga mamakin ta sai tagan ya d'aga mata hanun ya kuma mikewa


A zuciyar ta tace"kodai bai gane ni bane?"


Kafinta ta dawo daga duniyar tunani har ya bude kofa ya fita da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login