Showing 9001 words to 12000 words out of 38921 words
Chapter 4 - IMRANFAD By Maman Noorul Hudah-1-1.txt
sauri ta bishi a bata
Direct I C U yaje ya tarar da ummi a kofa,tana ganin shi tace"ya jikin ne?"
Ko amsata baiyi ba ya tuta kofa sai shiga ummi tace"an ce kar a shiga "
Juyowa yayi ya wasa mata wani kallo tuni tayi baya ta kalli mummy tace"hajiya ko dai kwakwalwar shi ta samu matsala ne?naga bai gane mutane"
Mummy tace"nima dai haka nike zato"
Tace"bari a kira Dr ya duba shi"
Mummy tace"toh bari in shiga in tsaya dashi sai ki kira dr "
Mummy na tura kofa ta ganshi tsugune gefen fadila ya rike mata hanun yana kuka sai surutai yake yi
Itama tsayawa tayi tana kuka tausayin shi ya kamata dan ita kadai ta San irin kaunar da yake yiwa fadila
A cikin wanan yanayi mummy ta shigo da Dr
Dr yace.......
Maman
Noorul
Hudahββ
Luv u my fans
Pls share
ππππ
IMRANFAD
ππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.F.π
Home of gorgeous,intelligent, and expert writers,we are the best among the rest.
π
Ώ2β£5β£&2β£6β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Dr yace"ashe ka tashi?"shiru yayi bai amsa ba
Dr yace"muje a duba ka har yanzu you are weak"
Shiru yayi kamar baya mummy ne ta karaso gaban shi tace"IMRANA tashi kaje a duba ka mana"
Shiru yayi hakan yasa Dr dafa kafadan shi yace"tashi tana bukatan hutu"
Ai a fusace ya mike yace"what do you mean by that,rayuwa ta na kwance a nan and you expert me in koma inyi kwanciyata,baka ganin ko numfashi batayi ne?"
Dr yace"amma kai Dr ne kasan rules d'in ko be kamata a bar mutane a kan ta ba gashi sai ihu kakeyi kuma ba a son hayaniya"
Yace"ba inda zani a nan zan zauna har sai IMRANFAD ta farka"babu inda Dr da ummi har da mummy basuyi da shi ba amma yaki fita karshe suka hakura
Gashi ya rike hanun fadila da karfi kamar za a kwace ta
Dare yayi mummy tace"kaje gida ka huta tunda kaima ba dadi kake ji ba"
Yace"no mummy vazan iya tafiya in bar FAD a wanan yana yin ba"
Shiru tayi dan tasan tunda yace ba zaije ba toh baza shi ba
Bayan kwana biyu,ranar jumma'a jama'a suka shaida d'auri auren IMRAN MUSA ADAMU da FADILA ABDALLAH akan sadakin dubu hamsin a masallaci,dan tuni Abba ya yanke hukuncin kin d'aga bikin,duk da daddy yaso a d'aga ganin fadila ita ba a raye ba kuma ba a mace ba amma sai daddy ya nuna me b'acin ranshi yace"ai dukan su ya'yan shine kuma yana da ikon yanke ko wani irin hukunci akan su"
Hakan ba karamin daddy yayi wa IMRAN ba
Bayan sati biyu da d'aurin auren su
IMRAN ne zaune rike da hanun fadila,mummy ta shigo tace" ya kamata ka je gida haka sati biyu kenan ko wanka baka yi sallah ma a nan kakeyi ga abinci baka ci sai tea shima da k'yar kake sha balle kayi barci,sai ka sata gaba kayi ta kallo wanan wani irin rayuwa ce haka?"
Yace"mummy wallahi bazan iya cin abinci ba,kuma bazan iya tafiya gida in barta ba"
Mummy taje ta bude flask ta had'a tea mai kauri tace"gashi kasha ko kuma in daddy ya zo insa ya tafi da ita wani kasar a boye inda baza ka ganta ba
Da sauri ya kalleta yace"wallahi zan sha mummy"bashi tayi ya karba,biredi ta d'auko tace"gashi ka had'a da shi"
Girgiza kai yayi yace"bazan iya ci ba"shan tea yakeyi kamar mai shan magani"da k'yar yashanye
Kallon mummy yayi yace"kefa kin ci abinci?"
Tace"eh"
Yace"mummy ba gaskiya bane ai inaji d'azun daddy nayi miki fad'a akan baki cin abinci"
Shiru tayi,tashi yayi ya karasa wajen basket d'in abinci ya bude kula ya dibo abinci
Yace"mummy gashi ki ci"
Tace"ba zan ci ba sai kaima ka ci"
Yace"mummy bazan iya ci bane wallahi"
Tace"ai nima haka"ganin bata da niyar cin abinci ne yasa yace"toh muci"
Zama suka yi a taburma suka fara cin abincin wanda dan dole suke ci bawai dan dadi ba"
Suna cikin cin abincin ne daddy da Abba suka shigo ba karamin dadi daddy da suka ji ba ganin suna cin abinci
Ummi ne ta shigo da feena,da sauri feena ta karasa gaban fadila tana kallon ta sai hawaye takeyi
Tace"duk laifi nane da ban kirata ta zo ta d'auke ni ba da haka bata faru ba"
Ummi tace"nafeesa ki daina bawa kanki laifi kaddara ne"
Shiru feena tana tausayin fadila daddy ne ya karasa wajen fadila ya shafa kanta yana yi mata addu'ar samun lafiya
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda yanzu fadila watan ta d'aya kwanciya amma ko motsi bata yi kuma IMRAN bai bar asibitin ba kullum yana tare da ita wanka ma bayin ward din yakeyi abinci ma sai mummy tayi da gaske zai sha tea a hakan ma ba biredi
Gashi ya tara uban kasumba ko aski bayayi
Yau ya kasance monday daddy da Abba sun tafi office mummy kuma na taje gida ta huta,wanda da k'yar ummi tayi da ita ta yarda ganin mummyn ma na fama da zazzabi
Ummi ne zaune da IMRAN a ward kallonshi tayi cike da tausayi tace"IMRANA ya kamata kayi aski nan haka ko so kake ne in amaryar ka ta ta shi ta gan ka cikin datti"
Yace"toh bari in kira zahra ta taho min da clipper"
Ummi tace"watoh kai baza ka bar asibitin nan ba kenan?toh bari in je gida in taho da abinci"
Yace.....
Maman
Noorul
Hudahββ
Luv u my fans
Pls share
ππππ
IMRANFAD
ππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.F.π
Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.
π
Ώ2β£7β£&2β£8β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Yace"toh ummi sai kin dawo"
Bayan tafiyar ummi da minti goma zahra ta shigo da sallama
Bayan sun gaisa da IMRAN tace"yaya ga clipper"
Yace"OK"
Bayan ya ansa yace"zaki iya tafiya"
Tace"toh yaya"
Tana fita ya karasa gaban fadila,pecking d'inta yayi a goshi yace"sleeping beauty,yaushe zaki farka ne?iam tired of seeing you like this my wife"haka yayi ta surutai shi kadai kamar tana jin shi
Yace"bari in yi aski bana so ki farka ki gan bushing face d'ina,my FAD ina ji a jikina zaki farka very soon,this condition doest suit you,you have to wake up for me love"
Bayi ya shiga yayi aski tare da yin wanka kaya ya canja ya fito
Ya zauna sai kallon ta yake yi
zubys ne zaune da zee
Zubys tace"zee wai har yanzu wanan shegiyar yariyan bata mutu bane wai?"
Zee tace "toh ai bata da maraba da mamaci,ai nasan wallahi bazai so ya aureta a wanan halin ba"
Zubys tace"amma naji an ce an d'aura musu aure tun wata d'aya daya wuce"
Zee tace"karya ne is just a rumors babu wani aure da akayi musu ba"
Zubys tace"ni na masu ya kirani ai malam yace da ta mutu zai kira ni amma shiru ba labari,this is more than a month now,kuma ko na kira baya picking"
Zee tace"toh ko zamu canja malami ne?"
Zubys tace"gaskiya ya kamata"
(Niko nace aiki ya gan Ku,domin babu wanda ya isa yayi wa wani abin da Allah bai yi me ba sai dai in hakan yana cikin kadarar shi)
IMRAN ne tsaye gaban fadila yana kallonta ya rike d'aya hanun ta
yace"IMRANFAD ya kamata ki tashi haka na gaji,ki tashi nace,tashi FAD,saboda ke nike rayuwa tashi nace,ya Allah ka tashi kafadar ta,d'aga murya yayi cikin kuka yace"tashi nace"
Ai kuwa sai ta motsa hanun ta da ya rike,kallon hanun yayi sai ta kuma motsawa
Da sauri ya kalli fuskarta yace"that good IMRANFAD tashi please iam tired of seeing you like this,"na'uran dake jone jikinta ne ya fara kara alamun zuciyarta ya fara bugawa,kallon na'urar yayi ya gan percentage d'in heart beat d'inta ya karu from 17% to 54%
Cikin dariya mai had'e da kuka yace"there is progress"
Kallon fuskarta yayi yace"my dear ina jira ki bude ido"
Zama yayi a kujera ya zuba mata ido ko keftawa baya yi ga hanun ta cikin nashi
A fili yace"ba inda zani,ina so da kin farka ki fara ganina"
Bayan minti goma da zaman IMRAN fadila ta kara motsa hanun ta
Kallonta yayi yana murmushi,a hankali ta fara bude idanuwanta ta sauke su a fuskar shi
Murmushi yayi mata,itako sai kallon shi take yi
Da sauri ya rugu meta yana kuka yace"welcome back dear"
Bata yi magana sai kallon shi da takeyi
Ganin ta tsare shi da ido yasa shi cewa"welcome back IMRANFAD yau kuma kallona kike ne kamar baki sanni ba"
Shiru tayi yace"ko fushi kike ne dani?"
Yace"sorry bari in cire miki ruwa nan kije ki yi wanka da brush "
Juyawa yayi zai zagaya ya cire mata ruwan da sauri ta mike zata bishi
Yace"jira ni mana in cire miki"
Shiru tayi hakan ya sa shi zama,itama zama ta
Bayan minti goma ya tashi itama ta tashi
Agogon hanun shi ya d'auka yana kokarin saw a ai itama ta d'auki nata a saman drawer dan tun ranar da tayi asari aka ajiye shi wajen
Komai yayi sai ta yi cikin damuwa
Yace.........
Maman
Noorul
Hudahββ
Luv u my fans
Pls share
ππππ
IMRANFAD
ππππ
By maman noorul
Hudah
πGEORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.F.π
Home of gorgeous,interllinent,expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my LATE DAD
π
Ώ2β£9β£&3β£0β£
Yace"gaskiya akwai babban matsala"
Tashi yayi zai je ya kira Dr ta rike me hanun
Zama yayi yana tunanin,
Yana zaune sai ga ummi da mummy sun turo kofa,ganin fadila zaune ba karamin mamaki abun ya basu ba
Mummy tace"ashe ta farka?"
Ummi ko da sauri ta je wurin ta zata rungumeta,abun mamaki sai fadila ta tashi ta boye bayan IMRAN
Ummi tace"ikon Allah yau fadila ke guduna"
Mummy da murna ya gama cika ta,ji take kamar ta rungume yar ta,amma ta dake
Tace"kila fushi take damu mun tafi mun barta"
IMRAN yace"no mummy ina ganin akwai matsala ne tun da ta farka ko magana taki yi kuma ko ina naje sai ta bini,I think she is suffering from memory lost"
Ummi tace"naga alama domin na San baza ta taba guduna taje waje ka ba domin ai ba Ku jituwa"
Mummy tace" toh duba ta mana toh"
Yace"no mummy bari a kira Dr ni likitan mata ne bazan iya handling ta ba"
Mummy tace"toh bari a kira shi tunda ta like maka"
Ummi ne ta kira abba ta fad'a me fadila ta farka yace"toh gasu nan zuwa da daddy"
Bayan minti 40 sai ga daddy shigo da Abba
Abba na ganin fadila yace"zo y'ar Abba"itako kara kankame IMRAN tayi
Abba yace"ikon Allah"daddy shiru yayi dan mummy tayi me bayani a waya
Dr ne ya shigo yace"bari a kaita a duba ta"
IMRAN yace"OK"
Babu inda ba ayi da fadila ba ta je a duba ta ta ki,karshe da IMRAN suka shiga cikin d'akin,da shike asibitin kwararru ne kuma suna da kayan aiki a take aka sata cikin wata na'ura
Bayan minti 20 aka fito da ita Dr ya duba report a computer
Yace"muje office muyi magana
Suna fitowa dama su daddy na jiran waje,gaba d'ayar su suka bi Dr zuwa office
Zama yayi mummy da ummi ma suka zauna
Abba da daddy a tsaye IMRAN ma haka ga fadila makale dashi
Dr yace"fadila ta manta memory ta sakanakon buguwar da kanta yayi so zata dinga yin abubuwa ne kamar yariya domin komai sai an koya mata"
Da sauri IMRAN yace"Dr Amir toh meyasa bata magana ne?"
Dr yace"zatayi because in most cases patient suffering from memory lost basa magana sai ranar da suka yi regaining memory su"
Mummy tace"toh meyasa bata yarda da kowa ne sai shi"
Yace"that because shi ta fara gani dole dashi zata saba,kin San yanzu ta koma kamar yar shekara biyu ko biyar,zata ta abubuwa ne cikin yaranta"
Abba ne ya hango fadila saman gadon dake cikin office d'in Dr tana kokarin cire agogon bango
Yace"Dr yariyar ma me kiriniya ko?"yayi maganan ne tare da nuna musu fadila dake b'arna"
Ai basu San lokacin da dariya ya sub'uce musu ba
IMRAN ne ya karasa inda take ya sauke ta
Ummi tace"ai aiki ya same mu har na tuna da kiriniyar fadila da tana yariya"
Mummy tace"aiki ya same Ku dai ke da IMRAN dama ai Ku kuka raine ta,Ku kukasan kiriniyar ta"
Abba yace"fadila ma ta girma ya aka kare balle an koma yar shekara biyar"
Daddy yace"Dr ina fatar har da kwallo ta manta ko?"
Dr yace"kai yariyar nan akwai rashin ji"
IMRAN yace"Dr ya kamata ka sallame mu haka"
Ummi ne ta Ciro waya ta fara trying noban zahra bata d'aga ba sai saki takeyi
Abba yace"lafiya kika tsaki?"
Tace"kiran zahra nike yi ta boye min roses d'ina kafin mu tafi da fadila gida kasan guda shida ne da,da fadila ke karama ta fasa biyu,ranan data je kwallo ta dawo da murna wai ta ci go biyu ta zo wai tana gwada min inda tayi taci kwallon,ai alhaji tana worga kwallo sai show glass d'ina a nan ta fasa biyun ya rage da k'yar biyu suka sira,shine yanzu dana ga alamun tahiri zai maimaita kan shi nike so a boye biyun wallahi kakata ta bani"
Dariya Abba yayi har yana rike ciki daddy yace"ai aiki ta same Ku"
Shiko IMRAN had'e rai yayi a dole a na ma matar shi tsiya
Mummy tace"hajiya ai ba iya roses ba gaba d'aya show glass d'in za boye in ba haka ba sai dai wani show glass"
Ummi race"ai kin kawo dabara hajiya"
Dariya mummy tayi tace"fadila gidan hajiya fati kenan"
Daddy yace"toh mai zai hana a kai ta gidan mijin ta tayi abinda taga dama"
Ummi tace"no gomma ta zauna da mu tukuna kasan IMRAN da zafin zuciya wallahi inta ishe shi zaneta zaiyi"
Mummy tace"nasan ai ba a shiga tsakanin Ku da fadila hajiya"
IMRAN yace"inshaallah zata samu lafiya zan yiwa Dr sageer magana kwarare ne ta wanan fanin"
Nan dai Dr ya sallame su
Suna kaiwa gida IMRAN ya fito a mota da sauri ta fito ta rike me hanun murmushi yayi yace"my FAD muje kiyi wanka ki ci abinci"
Ummi tace"toh kawu ta inje inyi mata"
Falon ummi suka zauna ummi tace"bari in had'a ruwan wanka"
Bayan minti biyar ummi ta fito tace"toh yi mata dabara ta bini inje inyi mata wanka"
Babu in IMRAN baiyi da FAD ba akan ta bi ummi amma taki
Abba ko sai dariya yake yi zahra dake zaune tana kallonsu
Ummi tace"ikon Allah toh haka zata tsaya ba wanka"
Abba yace" ai sai mijinta yayi mata"
Zahra tayi murmushi tace.....
Maman
Noorul
Hudahββ
Luv u my fans
Pls share
ππππ
IMRANFAD
ππππ
By maman noorul
Hudah
πGORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.F.π
Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.
Dedicated to HAUSA SWEET NOVELS
π
Ώ3β£1β£&3β£2β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Zahra tayi murmushi tace"hmmm Abba ai bamu gama ganin daru ba sai ta warke ta San yaya IMRAN ne mijinta ai zamu sha drama"
Ummi tace"ai korar su zanyi su karata can"
Abba yace"amma za a sha fama kam"
IMRAN dai shiru bai yi magana ba shima tunanin yake yi ya za su kare inta warke
Abba ne ya dawo da shi daga duniyar tunani yace"toh tashi ku je ciki ta samu wanka,kasan baby ce yanzu"yayi maganar cikin zolaya
Tashi IMRAN yayi cike da kunya ya nufi part d'in shi direct cikin d'akin shi ya kaita
Bayi ya shiga ya had'a ruwan wanka ya dawo ya d'auke ta sai bayi suna shiga ya tube kayar jikin shi,tana ganin ya tube itama ta fara kokarin tubewa,taimaka mata yayi ya tube,wow yace ganin girman ta ga komai perfect a fili yace"allah yasa in iya jira ki samu lafiya kafin in kwashi dadi na"brush ya ciro yasa maklin ya bata
Kallonshi tayi,tana ganin ya fara goge hakora,itama ta fara
Suna gama brush ya shige bathtub tare da kunna shower jawo ta yayi jikin shi,ai sai ta kwanta luf a kirjin shi tana jin dadin ruwan
D'ago fuskarta yayi suna kallon kwayar idanun juna,ruwa ya wasa mata a fuska ai sai ta fashe da dariya
Ummi ne ta shigo d'akin da kayar fadila,jin su tayi suna dariya a bayi ta ajiye kayar ta fita cike da tausayi IMRAN
Bayan sun gama wanka ya d'aura mata towel ya kuma d'aura mata wani a kai,shima d'aurawa yayi ya d'auketa suka fito
Gaban madubi ya ajiyeta ya d'auka hand dryer ya fara drying kanta
Bayan ya gama ya d'auko bra yasa mata da pant Riga da skirt d'in atampa da ummi ta ajiye ne yasa mata,parking sumarta yayi da ribbon yayi ya shafa mata powder da lip gloss
Kallonta yayi yace"perfect IMRANFAD"wata ya ciro a aljihu ya shiga selfie,ganin yana murmushi yasa ta yin murmushi da sauri ya d'auke su
Haka yayi ta kashe musu pics,yana gamawa ya fara juna mata suns dariya
Yace"IMRANFAD bari in kira Dr sageer ko ya zo ya duba ki,gaskiya bana son ganin ki haka"d'aga mai kaita tayi alamun eh
Yace"good girl"ai sai ta fara tapi
Kiran Dr sageer yayi tare da yi me bayani halin da fadila ke ciki
Dr sageer yace"ashe har kayi auren kenan?"
Yace"eh please ka zo ka duba ta"
Dr sageer yace"gaskiya ina Adamawa ne yanzu kuma gobe zan tafi india,amma zan turo maka noban wani Dr shima expert ne a irin wanan cases"
Yace"OK thank you very much"tare da yanke wayan
Kallonta yayi yace"na San kina jin yunwa bari in d'auko mana abinci"
Fita yayi ya barta a d'akin,yana fita ta d'auki kwalbar tulare ta fasa a kasa,powder ta shafawa fuskarta ta zazzage sauran a jikin mirror
Juyowa tayi ganin ita kadai ne a d'akin yasa ta yin ihu tana kuka
Jin ihun ta yasa ummi da Abba harda IMRAN tashi da gudu suka tafi d'akin
Suna shiga suka ganta zaune a stool din mirror tana kuka ga d'akin duk ya d'au kamshi tulare,fuskar nan nata kamar dodo
Daddy yace"wanan yariyar anyi fitinaniyar jaririya"
Ummi tayi murmushi tace"alhaji jaririya kuma?ai ance shekara biyu zuwa biyar ko"
Fadila na ganin shi ta taso da gudu zata gun shi ai sai ta taki kwalbar tularen da ya fashe,ihu ta sake ummi ta je zata rike ta amma kafin tayi haka IMRAN ya je
Rungumeta yayi cike da tausayin ta yace"sorry my FAD"
Abba na ganin haka ya bar d'akin ganin IMRAN bai da mu dasu ba
Tsungunawa IMRAN yayi ya fara cire mata kwalbar a kafa
Mamaki ne ya kama ummi ganin IMRAN na bin fadila a hankali dan ta