Showing 36001 words to 38921 words out of 38921 words

Chapter 13 - IMRANFAD By Maman Noorul Hudah-1-1.txt

23 Jan 2025

4037

akeyi?"


Zama yayi amina ta bashi babyn namiji,kallon yaron yayi gaban shi na fadiwa domin yaron sak shi harta blue eyes din


Gashi nan da nan yaji soyyayar yaron


Dr sageer ne ya katse shi da cewa "Amina kira farida ko ta fito daga wanka"


Tace"yaya"


Bayan minti biyar sai ga Amina ta dawo tace"wai tana zuwa"


Yace"OK "


Fadila ko shiyawa tayi cikin doguwar rigat atampa tayi kyau sosai


Tana fitowa tace"ina bakon namu ne?kullum a na bani labari...."


Ai IMRAN najin muryarta ya dago da sauri ya kalleta,ganin fadila ce da gaske yayi saurin mikawa Amina yaron ya mike tsaye


Itako rike kai tayi ai a take ta fadi sumammiya


Da gudu IMRAN ya taro ta Dr sageer yace "me ke faruwa ne a nan?"


IMRAN yace"dama kai ka boye min mata?"


Magana Dr sageer ke son yi amma IMRAN ya mike a fusace ya kai me naushi


Yace"meyasa kayi min haka sageer dama da gaske kake kana son ta tun tana yariya?"


Kuka Amina ta fara yi cikin kuka tace"kayi hakuri ba laifin shi bane,kuma bai aure maka mata ba,ni na bige ta da motar,kuma bayan nan mun ta cigiya amma bamu samu yan uwanta ba watan ta biyu a comma kuma ko data farfado bata hayyacinta"


Ajiyar zuciya IMRAN ya sauke yace"yaran nan fa,nasan ya'ya na ne"


Amina tace "da ciki muka since ta"


Tashi Dr sageer yayi ba tare da yayi magana ba ya goge jinin da ke bakin shi,


Haurawa sama yayi sai gashi ya fito da kayan aikin likitoci,duba fadila yayi yace"zata tashi nan da awa days


Rungumeshi IMRAN yayi yace"tanks man"


Murmushi dole sageer yayi,dan ba karamin so yake yiwa fadila ba,sai zufa yakeyi


Waya IMRAN ya ciro a aljihu ya kira mummy ya fada mata ya gan fadila kuma ta haifi yan biyu mace da namiji


Yace"mummy ashe da ciki fadila ta bar gida"


Murmushi ne ya subucewa mummy tace"alhadullillahi zan zo anjima"


Yace"no mummy ki bari yau zamu dawo"


Jira nake ta farfado


Mummy tace"farfadowa meya sameta?"


Yace"ba komai it normal mom"


Tace"toh sai kun dawo yanzu zanje in sanar da hajiya"


Yace"OK"


Daddy ne ya kalli mummy yace" menene naga kina cikin farin ciki ne"


Tace "ba dole ba an gan fadila kuma yau ta haifi yan biyu"


Shima murna ne ya bayyana a fuskarshi yace "kina nufi fadila na?"


Tace"eh alhaji"gyle ta dauka zata fita yace"ina zuwa kuma"


Tace"gidan hajiya zani in sanar da ita a nan zan yi wa ya'ta girki dan nasan nan zata sauka


Dadi ne ya kama daddy ganin hajiya ta sauya hallayenta ta ajiye maganar kunya gefe


'Bangaren zubys ko tana tafiya a titi da mahaifiyarta sai kawai ta fara cire kayan jikin ta


Ai sai ta fara surutai tana fadin muguntar da tayi bama wa fadila kadai ba


Cikin tashin hankali umma ta fara niman taimako amma babu wanda ya.taimaka mata


Ai da gudu zubys ta sallale titi,ummi taje binta wani mota yayi raga raga da kafafun ta ya gudu


Bayan awa daya IMRAN ne zaune da jaririya a hanunshi yana kallon kamarta da kausar


A hankali fadila ta fara bude ido ta sauke shi a kanshi


Da sauri ta dauke kanta tare da fashewa da kuka


Rungumeta yayi yana cewa"ki yafe min mata ta"


Ture shi tayi zaiyi magana sai ga wayar ummi ya shigo wayar shi


Yana d'agawa tace"bama fadila please "


Yace"OK tare da mika mata




Tana jin muryar ummi ta fashe da kuka cikin kuka tace"ummina nayi kewar ki"


Ummi ma kukan takeyi,mummy ma sai kallonta take yi tana tunanin ya zata hada ido da fadila


Ummi tace "ki shirya Ku dawo yau wallahi baza mu iya barci ba ba tare da mun gan ki ba fadila ummi"


Tace"toh"


Ummi tace"ga mummy Ku gaisa"


Ai da sauri ta kashe wayar,mummy sai hello take amma shiru,hawaye ta farayi dan tasan da gan ga fadila ta yanke


Ummi tace"kiyi hakuri hajiya komai zai wuce,wanan dama ne da zaki nunawa yar ki so"


Feena tace"bari nima in kira yaya mu gaisa da fadila"


Kiran noban shi tayi Dr sageer ya dauka


Tace"hello yaya bama FAD"


Kallon wayar Dr sageer yayi,ya kuma mayarwa kunni kafin yace"ba yaya bane yan mata yana,ciki yana had a kaya"


Dafe kirji tayi kafin tace"toh ta yanke wayar"


Kiran anty rukkaya IMRAN yayi ya sanar da ita an gan fadila kuma ta haifi yan biyu


Tace"wow ashe ita ne da gaske,toh ina kuke yanzu"


Address ya bata tace"gani nan zuwa"


Nan ta sanarwa mami,mami tace"suje tare Abbas kanin anty rukkaya ya sauke su a gidan cikin farin ciki ta shiga a fall ta tarar da fadila da gudu taje ta rugumeta


Kuka ta sake tace"ina kika shiga ne haka munyi kewar ki"


Itama fadila tace"nima bansan ya akayi Nazi nan ba"


Mami tace "ikon Allah Ku da ya kamata kuyi far in ciki miye na kuka?"


Wanka mai kyau mami ta sake yi wa jariran ta taimakawa fadila itama tayi


IMRAN yace"IMRANFAD shirya muje gida"yi tayi kamar bata ji ba Dan run da ta farfado bata kulashi ko yayi magana bata amsawa


Mami tace"Ku bar tafiyar nan sai gobe ta samu karfin jiki"


IMRAN yace"ana jirar mu a gida"


Mama tace "hada ni da ummi taka" kiran ummi yayi tare da mikawa mami wayar


Bayani mami tayi mata ummi tace "toh ba damuwa"


Mummy tace"meya faru?"


Ummi tace"wait sai gobe"jiki ba kwari mummy tace"toh Allah ya kai mu"dan ba haka taso ba




Washe gari suka shirya komawa Nigeria harda Amina da anty rukkaya Dan tace sai bayan suna zata koma yobe


Dr sageer yace "zai biyo su nan da kwana biyar"




Nigeria








Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
, pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IMRANFAD
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,intelligent,and expert writers we are the best among the rest.


Dedicated to masoyan wanan littafin


πŸ…Ώ9⃣9⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Nigaria.


Suna sauka a Nigeria a airport su tarar da Abba da daddy suna jiran su


Fadila na ganin Abba bata San da ta rugumeshi tana kuka


Abba yace"yi shiru baby ai kuka ya kare sai farin ciki"


Da dabara Abba ya zame ta jikin shi


Kallon daddy tayi ai da sauri ta rungumeshi tace"ka gafarce ni daddyna wallahi bansan meyasa na manta Ku ba"


Daddy yace"shhhhsh is OK my stubborn daughter ko da wanne aka dawo oho"


Turo baki tayi tace"ni daddy iam not stobborn ko Abba na?"


Abba yace"of cause my dear you are not "


Su dai anty rukkaya sai kallonsu take


Amina tace"nifa daddy ba za ayi min welcome ba an ga fadila an manta mu


Daddy ya kalleta dan be santa ba kawai yace"welcome my dear daughter "


IMRAN yace"watoh Ku an muku magana amma ni tun jiya ko unfa ba a ce min ba"


Fadila ta harare shi tace"Abba muje gida ina son ganin ummina"


'Bangaren su ummi kuwa mummy ta hada abinci kala-kala kallon ummi tayi tace"hajiya kina ganin fadila zata yafe min"


Ummi tace"me zai hanata ke ba mahaifiyarta bane?"


Ummi ko pepper soup na kafarsa ta hada


Zahrah najin kara mota tayi ihu da gudu taje wake


Feena na wanka taji ihu zahra da sauri ta daura towel jikinta duk kumfan sabulu hijabi ta ta fita


Mummy ko najin muryar fadila ta fara dariya tace"hajiya wallahi itace hajiya Allah na gode ma da kabani wanan daman"


Fadila na shigowa ta rungume ummi tana kuka


Tace"ummi ina kika tafi kika barni inata kewar ki,nasha wahala ummi dani da kausar ummi kullum sai na kira sunanki"


Dago ta ummi tayi ta wanka mata mari,ko a falon sai da yayi mamaki,itako fadila ta rike kuncinta


Ummi tace"meyasa baki sanar dani damuwar ki ba kuma kullum sai munyi waya dake?ashe dama baki dauke ni mahaifiyar ki ba"


Girgiza kai tayi tace"ummi ba haka bane ki yafe min"da sauri ummi ta rungumeta cikin kuka tace"fadila kar ki kara tafiya ki bar mu please"


Jikin mummy ne yayi sanyi ta fara babe-rabe daddy ne ya kalleta yayi mata signal alamun ta karasa dan ya lura da yanayin ta


Fadila tace"ina kausar?"


Feena tace"tana cikin daki na tana wasa"


Su amina ko mamakin gata fadila suke


Mummy ne ta karasa tace"fadila ni baki yi kewa ta bane?"


Ai yi tayi kamar bata ji ba,mummy taje zata rungume ai da sauri ta haura sama,duk suka bi ta da kallo


Mummy ko barin wurin tayi ta shiga kicin,zama tayi a kasa tile tana kuka


Ummi ta ansa yara,direct daki fenna taje ta gan kausar na wasa da gudu ta karasa ta rungume ta tace"ina fatan basu ji miki ciwo yi miki komai ba"


Feena ta shigo dakin tace"I miss you sis,I miss you a lot my dear "


Fadila tace"i miss you more dear"


Daukan kausar tayi suka bar dakin


Mummy ko kuka take yi sosai a haka IMRAN ya shigo ya sameta


Goge mata hawaye yayi yace"mom nima bata kula ni"


Mummy tace"you won't understand dear,iam her mother but a I hot her a lot dear I won't be able to forgive myself"


Yace"mom I understand give her some space please understand dat IMRANFAD has gone through a lot,but please be a mother to her"


Murmushi dole mummy tayi tace"inshaallah dear"


Yace"toh muje dininga"


Suna zuwa suka tarar da Iowa a falon zaune


Ummi tace"fadila ga sakwara kici"


Tace"wow my favorite ummi nagode da kika yi min sakwara


Murmushi ummi tayi tace"ai bani nayi ba mummy kin tayi miki"


Ai fadila najin sunan mummy ta ajiye plate ummi tace"ya haka kuma?"


Tace"ummi bazan ci ba yana kumburan min da ciki"




Mummy na so tayi magana sai IMRAN ya girgiza mata kai


Shiru tayi,zuciyarta na kuna


Zahra tace"toh me zaki ci ai har da shinkafa a ka dafa"


Fadila tace"abin da ummina ta dafa min shi zan ci"


Ummi tace"ai ni na dafa shinkafar"


Tace"toh a bani"mummy ta ji dadi domin ita ta dafa ba ummi ba




Anty rukkaya ko da amina cin sakwarar suka yi tas


Da misalin karfe 8:na yamma fadila na kwance dakin ta da kausar feena ta shigo tace"yaya wai ki je yana niman ki"


Fadila tace"je ki ce bana zuwa"


Feena tace"please kije kiji mai zai ce wallahi abubuwa da suka faru ba laifin shi bane aiki asiri"


Tace"can ta matse musu shi da matan nashi"


Feena tace"ai ya dade da dakin ta"wani dadi fadila taji amma tace"oh haka akayi duk irin soyayyar da sukeyi?"


Kiran IMRAN ya shigo wayar feena tana dagawa tace"bata zuwa"


Yanke wayar yayi ya mike yace "me yariyar nan ke nufi ne?"


Fita yayi yaje d'akinta fenna na ganin shi ta bar dakin


Yace"IMRANFAD me nayi kike hukunta ni haka?fad nasan nayi miki ba dai-dai ba amma please karki yi min haka uwar ya'ya na,wallahi ba a haiyacina haka ta kasance ba please ki gafarce ni"




Hawaye takeyi tace......




Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IMRANFAD
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


Dedicated to MY BROTHERS REUBEN AND SAMUEL


Last page


πŸ…Ώ1⃣0⃣0⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Cikin kuka tace"kar ka kara kira na matan ka dan ka dade da sakina"


Yace"haba IMRANFAD kema kisan da ina haiyacina bazan sake ki ba pls ki yafe min FAD"


Tace"na dade da yafe ma amma bana so ka kara kirana matar ka"


Yace"haba IMRANFAD me yayi zafi haka ne? Kema kin san ke kadai ne matar IMRAN zuwa nayi mu sasanta a daura mana aure "


Dariya tayi tace"ni ba aure ne gabana ba,makaranta zan koma"


Yace"kina nufi Baki son aurena kenan?"


Tace"eh banso,me zan nima Allah ya bani ya'ya uku ai sai dai ince Allah ya raya mun su"


Yace"nashiga uku na"sungunawa yayi ya rike kafanta,yace'dan Allah ki min rai"


Rintse ido tayi jin saukan hawayen shi a kafanta,jan ye kafarta tayi a hankali


Tana so tayi magana sai ga amina ta turo kofa da jaririya tace"yariyar nan ta fiye kuka"


Amsanta tayi ta kalli IMRAN tace"ka fita zan shayar da ya'ta dan kasan bai hallalta ka ga jikina ba"


Kallonta yayi a ranshi yace"lallai yariyar nan da gaske take"


Bayan kwana biyar da dawowan su fadila Dr sageer ya zo a gidan su IMRAN ya sauka,kuma har yanzu fadila bata kula IMRAN da mummy kullum sai ta zo gidan amma da fadila ta ganta zata bar wurin ko mummy ta bi ta sai ta bar dakin


Ummi tace"feena tashi ki kai wa bakon nan abinci yana flat din waje"


Toro baki feena tayi tace"ummi ba ga zahra ba ni design din suna za a min"


Ummi tace"kai ki dawo kafin a gama wa fadila"


Tace"toh"


Tray din abincin ta dauka ta fita salama tayi ya amsa tana shiga ya lumshe ido jin kamshin tularen ta


Tace"ina yini Dr "


Yace"lafiya yan matan ya gida"


Tace"lafiya"har zata fita yace"zo mana yan mata"


Tace"design fa za a yi min Dr "


Yace "in baki zauna ba zanyi fushi"


Haka kawai ta sinci kanta da kin son b'ata mai rai"


Zama tayi,shima zamar yayi ya fuskanceta yace" yaushe zamu yi aure?"


Rufe fuska tayi da tafi hanunta yace"iam serious,iam seriously in love with you,infant it was love at first sight dear"


Shiru yayi yace"talk to me"


Tace"Dr kana sani jin kunya"


Yace"hakan na nufin na samu karbuwa kenan ko?"


Fita tayi da gudu,murmushi yayi


IMRAN ne zaune yayi tagumi abin duniyar ya ishe shi Dr sageer ya shigo yace"ya naga ka cikin damuwa?kai da ya kamata kayi farin ciki"


IMRAN yace"hmm baza ka gane ba,fadila taki sauraro na"


Dr sageer yace"nasan tana sanka domin ko da take cikin damuwa da memory lost aka kira sunan ka da kausar sai ta motsa,amma ban taba tunanin matar ka ba ce"


Yace"baza ka gane ba babu wanda zai iya predicting FAD"


Yace "kayi ta addu'a komai zai dawo dai-dai inshaallah,nima fa na samu mata ka sanar da Abba"


IMRAN yace"ina maganar mata ta kana maganar wata"


Dr sageer yace"in bazaka fada ba ni zan fada mai da kaina ai nima Abba na ne"


Tsaki IMRAN yayi ya bar Turin


Washe gari kowa yayi busy ana aiki suna su anty rukkaya ana soya nama wayar ta yayi kara,tana dubawa ta gan Abbas kaninta


Dagawa tayi tace"hello"


Yace"anty na iso gani a kofan gida"


Tace"toh shigo mana"


Ba karamin kudu mummy ta kashe ba wajen dinkuna kayan da fadila zata sa da kayan rabo


Washe gari yara suka ci sunan su sageer da rukkaya amma ana kirasu da amra da afra


Ba karamin dadi anty rukkaya taji ba da wanan kara ba,Dr sageer ma sai murna yake kuma ya kashe kudi sosai




'Bangaren zubys ko yau ne kwana ta bakwai da boka ya fadi




Tana bakin titi jirgi yara na mata waka kawai sai ga jirgi ya zo wucewa da gudu ta je ta tsaya gaban shi aiko ya kwasheta,sai dai muce Allah ya jikan rai domin a buhu aka kwashi gabobin jikinta"


Suna yayi anci ansha IMRAN ko sai murna yake yi domin yau fadila ta dan sakan me fuska har Sunyi photo"




Bayan an wase ne da misalin karfe 8:pm ummi taje dakin fadila


Fadila tace"ummi zauna mana"


Zama ummi tayi tace"fadila na zo ne in roki wata alfarma"


Fadila tace"ummi babu alfarma tsakanin mu umarni zaki bani kawai"


Ummi tace"so nike ki yafewa mummy ki"


Kuka fadila ta fara yi tace"ummi na dade da yafe mata kawai dai fushi nike da ita"


Ummi tace"toh dan Allah a bar fushin nan haka ta wahala"


Ummi tace"hajiya shigo ga yar ki"


Mummy dake tsaye a kofa da kin ta shigo da gudu fadila ta rungumeta


Tana kuka tace"mummy ki yafe min"


Mummy tace"no fadila baki yi min komai ba"


A ranar mummy kamar ta maida fadila ciki


Washe gari daddy ya Tara su a nan aka saida maganar auren feena da Dr sageer amina da Abbas kanin anty rukkaya,zahra da yaya feena jamilu nan da wata data


Domin bikin.Dr sageer da amina a gidan daddy za a yi komai kasancewar su marayu,amina ma,yanzu gidan mummy take zama


Abba yace"IMRAN yaje su dai-daita da fadila inta amince a mayar da auren su


Mummy tace"nasan zata amince ko fadila ta?"


Tace"ta amince amma sai ya ta zuwa zance kamar inda dr sageer da Abbas keyi


Dariya Abba yayi yace"fadila case"


Gyera ummi ta farayiwa amare most expecially fadila fomin mahaifiyar feena tace ta bar ma ummi komai


Bayan suna anty rukkaya ta koma yobe,inda mijinta ya yanke shawarar dawowa kano da zama


Da dare IMRAN yayi kwalliya Lamar mace ya zauna a mota ya aika a kira me fadila, tana zuwa ta hade rai


Gyran murya yayi yace"da farko dai sunana IMRAN kuma ina son ki da fatan zaki bani hadin kai"


Tace"sai nayi tunani"




Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Inda kullum sai IMRAN yaje zance a mota


Bayan wata data aka daura auren fadila da IMRAN


Sageer da nafeesa


Sai amina da Abbas


Zahra fa jamilu


Sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya amin




A ranar da aka kai amare da kin su bayan sun gabatar da nafila IMRAN ya dauki fadila said bayi yayi mata wanka suna fitowa ya zame towel din jikin ta domin yara na wajen nanny


Wasa ya fara da boobs dinta ya fara sucking dinta kuka ta fashe dashi yace"menene?"


Tace"abimda kakeyi wa zubys kenan?'


Murmushi yayi yace"kar ki samu ban taba kusantar ta ba,ko da bana hayyaci na nasan ban kusance ta ba,ke kadai ne zaki San wanan sirrin nawa"


Kafin tayi magana ya hade bakin su waje guda


Bayan ya gama romance ai sai ya hau aiki


A ranar su jiyar da junan su dadi kwana akayi ana Abu data


Bayan shekara goma sha biyu


Hajiya fadila na gani a gidan ummi da AMina da fenna da anty rukkaya


Sai yara dake wasa domin fadila yaranta shida,amina biyar sai feena biyu zahra hudu anty rukkaya uku dan saga bays allah ya bata


Suna cikin hira sai ga mazajen su sun shigo


Barin yaran sukayi batare da sanin ummi ba suka kara haba


Fadila nashiga motar IMRAN yace"matar IMRAN muje gida in baki baby"


Zaro ido tayi tace"a'a bana so"


Yace"na,fada miki said muyi dozen"


Tace"Allah ya Bamu masu albarka"


Nace "amin"




Alhadullilahi nan na kawo karshe wanan novel da fatan na fadakar




Mai sharhi ko gyra yayi min magana ta wanan nobar 09090112846




Said kun jini a novel dina nagaba AMEER






Maman
,noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
,, pls share

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login