Showing 3001 words to 6000 words out of 38754 words

Chapter 2 - UWAR GOYO COMPLETE BOOK Hausa Novels .txt

Nil   

19 Feb 2025

2011

dogon
buri
Duk idan ya dawo daga kasuwa bai shigowa
hannunsa haka kawai dole saiya taho Mata da
wani abu dukda basonta yakeba da kuma
kyamatar halinta da yake gamida irin zaman da
suke to yana qoqaru wajen ganin ya farantamata
Rai kyautatawan da yake Mata da haquri Ga irin
zaman da yake da ita hakan yasa ta fara
saukowa harta fara masa magana gamida Bashi
duk wani kulawa da maigida ya cancanci ya
samu a wajen matarsa wannan sauyi da aka
samu daga wajen fanne shiya dinke barakar dake
tsakaninsu don daman ance mahakurci mawadaci
dukda iya qoqarinta da take wajen ganin ta
kyautata masa hakan baisa abbakar ya game
yarda da Ita Dari bisa dariba don masu iya
magana na fadin Mai Hali bai sauya halinsa
domin tsoron kar saiya Saki jiki da ita sannan ta
bullo masa da wani halin Amman dukda haka Bai
fasa yin Mata addu. A akan Allah yasa ta gane ta
gyara halaiyarta va
Har yanxu fanne bata gyara halaiyyartaba Kai
hardama Wanda abbakar din Bai San dasuba
wani lokacin idan abin ya taso Mata saiya baka
mamaki abin harya farabama abbakar tsoro sai
yanxu ya yarda da maganan yayanta da yai masa
a baya akan akwai shafar aljanu a tattare da Ita
don harya fara tunanin daukarta zuwa wajen
kalamai domin Ai Mata ruqiyyah
Abin mamakin shine ta bangarensu basa fada
jama, a da dama Suna mamakin yaddah akai
auren abbakar da fanne ya Dade haka ba tare da
samun wani matsalaba harda mahaifan fannen
kullun cikin sama abbakar albarka suke don yayi
namijin qoqari kasancewar Basu taba tunanin
fanne zata zauna gidan aure lfy Lau ba tare da
fitintunu sun biyo bayava domin sunfi kowa sanin
halin yar tasu
Don Mai haquri sosai ne Zai iya zama da ita duk
wani irin salon iskanci da zata bullo dashi
abbakar yasan ta yaddah zaibi ya shawo kan
lamarin wani lokutan idan ta taso da iskancin
Nata fita yake yabar Mata gidan don ya rigada
yayima mahaifin Nata alqawarin duk runtsi Zai
danne duk wani rashin mutunci da zatai masa
Ita kanta takan tazauna taita tunani tace haba
sai kace bada mutun nake zauneba kaita
tsokanan mutum Amman ya nuna baimasan
kanayiba Kai wannan mutumin inage Bashi da
zuciya kodai yabama kare ya cinyene oho
Kai Allah ya wadaran nake ya lalace ta girgixa
Kai gamida cewa wlh abbakar ba irin mijin da
nakeson aura Bane Ni Wanda idan na takaloshi
zai biyemin nakeso idan ta Kama mu dambace
duk Wanda ya kada wani to shine jarumin
Amman wannan wani solobiyo dashi tirr da irin
wannan Hali na abbakar
Abbakar kuwa tunani da irin zaman da suke d
fanne yasa harya fara ramewa a tsaytsaye bayan
Shiba ciwo yakeba sai yar waya Ita kuwa inka
ganta kumbura kawai take ba ruwanta yin abinda
takeso kawai take ba ruwanta game da mijina
kuwa ko ruwan wanka bata kai masa shida kansa
yake fita dibo ruwan da zaiyi wanka abinci kuwa
saidai idan ya dawo yaje wajen da ake aje
kwanuka ya dauka ya zuba da kansa Ko sau daya
Bai taba nuna Mata ya damu ba
Matan gidan da suke haya da yake gidan hayane
Ko wacce a cikinsu Suna sha, awar yaddah
abbakar ya maida fanne sarauniyar Mata masu
hassada nayi fatan Allah yasa Suma mazajensu
gane su dinga Basu irin kulawar da abbakar
kebama fanne nayi wasu kuma wautar fannen
suke gani akan abinda takema mijin Nata domin
kuwa Kaman wautane kullun idan ya dawo daga
kasuwa sai an kawo masa qarar fanne idan yai
bincike saiya Gano itace bata da gaskia wani
lokacin kuma itace keda gaskia Amman tabi har
qofar dakin macen su kacame da dambe Ko kuma
cacan bake sau da yawa dashi ake hadawa acin
musu mutunci abin na masa ciwo sosai saidai ba
yaddah zaiyi don haka Allah ya qaddaro masa
Bashida wata mafita daya wuce ya dinga addu, a
d kuma godema Allah
Domin alah na fadin Bai daurama nawa abinda
yafi qarfinsa sannan kuka bawa Bai kujema
qaddararsa saidaima yaje ya sameta
Sauda yawa abbakar kan zaunar da Ita yai Mata
nasiha akan ta daima abinda take domin ba Mai
kyau Bane ya kamata ta aje duk abinda take Ada
ta gane cewa yanxu ta girma ba yarinya bace ita
amman me a maimakon ta dauki maganan mijin
Nata Ina Ai a lokacin dayai maganan Tana tashi
Anan take bar magan ganin abin Nata bamai
sauqi Bane kuma ance Mai Hali Bai canja halinsa
yasa yasa Ma sarautan Allah ido
Don bazai iya kai qararta gurin mahaifintaba
kasancewar girmnsa da yake gani sannan duk
sanda suka hadu Kalman dai dayace shine Ka
qara haquri hakan yasa koda yai niyyar Kai
qararta wajen mahaifin Nata yana tune
kalamansa sai yai duk jikinsa ya mace sannan
koda yayi quri yakai qararta din ya tabbata marar
haqurin Kenan
Tunda sukai aure har izuwa yanxu ba, a tabajin
kansuba kasancewar abbakar din Mai haqurine
Bai biye Mata Amman ta bangarenta
Idan Sanrantane bataqi kullun su kwashi Yan
kalloba don daman abinda takeso Kenan
Sai kuma akai rashin sa, a mijin Nata mai
haqurine sunansa abbakar saddik
Komai zatai masa cikin tsiwa take masa Kai
hartakaiga idan yasata aiki kai tsaye take ce
masa ba zataiba Gar take mayar masa da
magana ba tare da taji shakkarsava Kota karanta
masaba a matsayinsa na jikinta Ko kadan batayi
masa biyayyah irin wanda aka sani mace
tanayima mijinta
Bata gaisheshi idan gari ya Wye haka kuma bata
masa sannu da zuwa din ya dawo daga kasuwa
Kai koda waje take idan ya shigo da Kaya bata
zuwa ta masa a hannun Nasa
Ga almubazzaranci duk abinda ya kawo haka
zata dinga watsar dashi Ko kuma idan ta tashi
firkawa saita dafa da yawa Wanda ba zasu iya
cinyewaba a maimakon idan sun rage Ko
almajirai tabamawa Ina Ai barin abincin take har
saiya lalace sannan ta zubar a bola Ga rowa
wohoho fanne akwaita da rowa kamar qanuwar
qaruna hatta Mai nemowan ya kawo bata barshi
a bayaba saiya jibgo Mata name ya kawo Amman
idan ta girka daqar yake iya samun yanka uku
Allah sarki saikace ya roqa Amman dukda hakan
Bai taba nuna Mata ya damuba
Abbakar sai zabgewa yake a tsaye kamar wani
Mai jinya bacin kuma lfyrsa qalau ba abinda Ke
damunsa sai rashin mutuncin da fanne Ke shuka
masa Kala Kala saidai duk rashin kirkin Nata da
take Mai bata taba zaginsaba harkar gabanta
kawai take Ga wata uwar kiba da tai kamar ta
fashe Ga surutu fanne akwaita da gulma da
tsugudidi ta saka wannan ta canja wancan
Shekararsu biyu d aure Amman Basu haihuba
shiru kakeji tamkar an shuka dusa lamarin ya
damu fanne sosai nanfa ta shiga sintirin zuw
gidan bokaye da kalamai harda asibiti taje
Amman ba, a samu nasaraba domin kuwa akwai
wani zuwa da tayi asibiti bayan likita ya gama
mata Yan gwaje gwaJensNe yace hajia saidaifa
kiyi haquri da yaddah allah ya halicceki bazance
ba zaki haihuba Amman zaki Dade kafin ki haihun
kuma ba lallai Bane ki samu zuri, a da yawaba
don bisa binciken da Naki koda zaki iya haihuwa
qarqari da dayane zuwa biyu bayan Nan kuma
saidai kiyi haquri hajia
Tur qashi Toya Kenan ya zatai da rayuwata Ita da
bataso abbakar ya kawo Mata kishiya tafison su
zauna su biyu sai kuma yaran da zasu Haifa lol
Tace Dole nasan abinyi Tun kafin ya sani hauka
don nasai idan abbakar da Yan uwansa sukasan
inada matsala a mahaifata lallai zasuyimin
saKiyar da babu ruwa don daman tasan ba sonta
yakeba duk a dalilin halinta marasa kyau Amman
ita bata ganin abinda takeyin musu
Shikam abbakar baimasan abinda ake tayiba
domin shi ya rigada yayi tawakkali Ga Allah ya
sani samu da tashi duk daga Allah suke hakan
yasa baima wani damu kansaba sannan kuma shi
, ain daman baso yake ya haihu da itaba don
lallai sai Dan data Haifa ya dauko halinta don
dama yaro a noon yakeshan hali sannan bashida
yaqinin zata iyama yaro tarbiya ta kwarai domin
kuwa ita kanta tarbiyyar ba ishenta yaiba
Fanne kuwa ba haqura taiba har yanxu neman
maganin haihuwa take duk Anan kudinta yake
tafiya tashi ba biyan buqata Amman wani
bangare na zuciyarta na fada Mata cewa taci
gaba da nem domin kuwa Mai nema yana tare da
samu haka kuma Wanda ya haji bau Saba Bane
Zuwa yanxu fanne ta fara damun abbakar akan
matsalan rashin haihuwarta da dare bata barinsa
yai barci sai Mita akan yaqi ya nema Mata
maganin haihuwa daman Aita gane ba Santa
yakeba Bashi Ita akai sadaq shiyasa Bai damu da
rashin haihuwar Tata ba maganganu dai marasa
dadi ta dinga fada masa shi kuwa Ko kallon inda
takema baiyiba balle ya tank mata wannan abin
da yake mata yana damunta sosai da yai shiru
yanajinta Tana magana yaqi tanka mata gwara
ya dauko sanda yaita rafka Mata da zaifi
Ana cikin hakane Allah yaima mahaifiyar fanne
rasuwa jinya Tai sosai Wanda har saida yakaita
Ga kwanciya a gadon asibiti jikin yai tsanami duk
yayanta wadand sukai aure saida sukaxo dubata
Tun daga garuruwan da suke auren jikindai ba
dadi sai, an kwantar an radar bata sanin Wanda
Ke kanta Ana cikin hakane ta soma samun sauqi
don har akan danyi hire da Ita a wani yammacine
da abbakar yaxo dubata don daman kullun sai
yaxo safe da yammah don ganin yaddah jikin
nata yake a lokacinne ta zaunar dashi Tana masa
nasiha Mai tsuma jiki gamida godia akan
riqemusu fanne da yai bisa Ga Amana don ta
tabbatar idan ba Mai haquri kamarsaba babu
Wanda zai iya zama da fanne zaman aure har
izuwa wannan lokacin sannan ta qara da damqa
masa amanar fanne a hannunsa daya riqe musu
Ita bisa amana sannan ya qara haquri domin duk
Mai haquri Allah na tare dashi a koda yaushe
yace insha Allahu goggo sannan ina godia da
wannan nasihar taki abbakar Ji yake kaman
wasiyyah take Bashi bayan ta gamane ya tashi
ya tafi hakan kuwa akai adaren ranar misalin
qarfe biyu na dare ciwon Nata ya dawo ta qara
birkicewa misalin asuba tace Ga garinkunan Allah
sarki Kullu nafsin za'ikatul maut washe gari aka
kaita gidanta na gaskia abbakar yai mutuqar
girgiza game da mutuwar baiwar allahn Nan
musamman idan ya tuna nasihun data dunga
masa a yammacin Jia sai yaji Hawaii na zubo
masa a fuska yace haqiqa duniya abin banzace
don duk Wanda yai damara sbd duniya to lallai
ya kamata ya kwance domin kuwa ita mutuwa
bat sallama
Su fanne anyi kuka Kaman rai Zai fita mutuwar
umar Tata ta girgizata domin bata taba ganin
mutuwa Kuru kuru da idontaba sai akan mamarta
saidai taji a bakin Jama a cikin yan kwanakin
ukunnan idan kaga fanne zaka rantse kace ba Ita
bace gaba daya ta sauya hakan ba qaramin dadi
yaima abbakarba donji yake kamar a jikinsa
kamar shiriyace taxo Mata saidai abinda Bai
saniba shine masu iya maganafa sunce mai Hali
baya sauya halinsa don a ranan addu, ar bakwai
din mamar Tata saida aka dubi yan kallo ita da
wata makwabciyarsu akan sosai lol
Chapter3
Haryanxu fanne bata sauko game da hayyarrArta
ba kullun qara gaba abin yake da zaran yayi
niyyar daukan mataki sai ya tuna da wasiyar da
mamar Tata ta Bashi a daren ran da zatabar
duniya hakan kesa gwiwowinsa na sanyi gameda
hukuncin da yai niyyar daukan har ya fasa cikin
halayyar fanne Abu dayane yafi qonama abbakar
rai shine rashin girmama na gaba da ita duk
girman mutun yanxu saita zumbudo masa ashar
wannan halayyah na fanne ba qaramin qonama
abbakar Rai yakeba wasa wasa abin Nata sai
qara ci gaba yake hakan yasa Jama, a ke kiranta
da fanne tsigalagala wasu su kirata da tsigai
wasu kuma su kirata da tsigala duk ta dalilin
halin fanne yasa basu dadewa a gidan haya ake
korarsu daga aurensu zuwa yanxu sun zauna a
gidan haya yafi Goma sha uku don akwai gidan
da sati daya sukai a ciki aka koresu waje duk ta
dalilin munanan halayyarta
Ba qaramin kudade abbakar Ke kashewaba don
ba duk gidan da suka Kama Bane idan sun tashi
ake maida musu da kudin nasuba haqiqa abbakar
Yaga rayuwa
Kodama Ana barinsu a gidan hayan
Halayyar fannema kawai ta ishesa
Ballentana yanxu data bullo masa da wani sbn
iskanci sai cikin dare zata tashi taita nemansa da
rigima idan yaqi tankata taita girgixa masa qafa
akan Dole saiya tashi wasu lokutanma a tsakar
gidan yake kwana nanma Bai mataba har tsakar
gidan take biyoshi saida Yaga alamun abin Nata
bamai sauqi Bane saiya soma kwanan qofar gida
Tun Bai sababa haryaxo ya Saba
Daga baya kuma suka sasanta Amman saidaya
bata dubu biyar abindai nasu Kaman ya lafa sai
kuma ta tsiro da wani sabon Salo wai indai har
Zai kwanta da Ita to yasin saiya biya kunji
shegiya sai kace karuwa. Da
Wannan baqin Halin irin na fanne ansha kaisu
police station
Sunje cargi office yafi a qirga don da zaran ta
tabo marasa haquri sai sace sai anje police
station wani banzan haline da fannen da zaran
sun fara cacan baki da Kai Ko fada to duk abinda
Ke kusa da Ita Ko meye saita sauka tace zata
maka makakoda kuwa menene
Akwai lokacin da fada ya hadasu da wata Mata
wacce suke haya tare gulman Matar akai da
kuma akabi diddigi sai aka Gano daga wajen
fanne gulman ta fito Matar da aka daurama
gulman kuwa tace Aiko ba zata taba yardaba
daqar abbakar yashawo kan lamarin Ashe Ita
fanne abin nanan a ranta Wai sbd Matar tayi
Mata tatas a cikin Jama. A kuma abbakar ya
tsareta akan karta Tofa komai hakan yasa ta
kasa daukar mataki Ashe abin na raNta saidata
Bari anyi Kwana biyu sannan taje ta samu Matar
a kicing kuma a daidai lokacinda take kici kicin
daura sanwan dare
Daman fanne da rikici ta shiga kichin din Tana
shiga sai cema Matar tayi Ke kuma meye na
hararata budar bakin Matar sai tace a yaushe na
harareki din? Daman abinda takeso kenan Matar
ta maida Mata da martini kafin kace me sun
kicime da fada fanne batai wata wata ba ta
rarumo tabaryar dake kusa da Ita ta makama
Matar a kafada zata qarane sai kuma akai rashin
sa. A kafin ta qara Kai Mata tabaryan itama
Matar ta rarumo tabaryar da take daka dashu
saiji kake gauuuuu a hannun fanne Aiko fanne ta
kurma wata mahaukaciyar qara Wanda ya janyo
hankalin Jama
Ar dake tsakar gidan har suka fahimci akwai
matsala a cikin kichin nanfa sukai kansu domin
su raba fadan kafin kace me har Jama, a sun cika
qofar kichin din Kai harda makwabta abbakar na
tsaka da kasuwancinsa yaro yaxo ya samesa
gamida fada masa abinda Ke faruwa nan ya Rufe
shagon Nasa ya taho a gigice saidai kafin ya
qaraso Ashe har mijin matar yakai rahoto a police
din Yan sanda suka hadoshi da yan sanda biyu
mace daya namiji daya domin awuce da fannen
police station don har wajen tafia da itanma
saidatama yar sandan rashin kunya Ita kuma ta
mammaka Mata kulki a kafada kafin abbakar ya
qaraso har an tasa qeyarta Ji yai Kaman ya Barta
Tai Yan kwanaki a hannunsu koda zatadan dawo
cikin hayyacin Nata Amman Ina bazai iyaba gashi
bawai wasu kudine a hannunsaba kasancewar da
damuunane market baya ja
Jiki ba kuzari ya Kama hanya ya nufi station din
babu ko kunya tadinga zaiyano abinda ya faru
saidai dagajin yanayin magananar zakasan duk
qaryane Ga hannunta harya kumbura da qar ya
samu a ranan aka Bashi belinta bisa sharadi
saiyakai wannan Matar asibity an Mata maganin
ciwukan da fannen taji Mata yace ba damuwa
bayan an kammala komai suka dawo gida itama
fannen abbakar ya Kira Mai dauri aka daure Mata
hannun Nata saidai tasha wuya don saidatai
nadamar biyema Matar ammanfa Matar ta zagu
ta uwa ta uba babu irin zagin da Matar
batashaba
Nan ne Mai gida yacema abbakar lallai saisunn
tashi masa a gida don Nan gaba matarsa zata
iya kisan Kai ba irin roke da magiyan da abbakar
Bai ma Mai gidanba Amman yaqi yarda yace Kai
ayau dinnanma zaku tashi inkuwa kaqi yanxu na
Kira hukuma da sauri abbakar ya miqe gamida
cewa Kai haquri ranka shidade badai gida baneba
zamu tashi ba saitakaiga hukuma sun shiga
cikiba nanfa abbakar ya tashi cikin sanyin jiki ya
shiga dakinsa abin duniya duk ya damesa yanxu
Ina zanje na samo kudin haya Kai gaskia na gaji
wlh na gaji da irin wannan hijiran da muke a
kullun sai kace tururuwA nanfa ya rasa abinyi
take shawara ta fado masa yace Mata gida kawai
Zan maidake har izuwa randa Zan sama Mana
wani gidan haka kuwa akai Ita kanta ta gaji da
wannan yawo na gidan haya da suke Aman me
maimakon ta tausayama mijin Nata ta gyara
halayen Nata marasa kyau Ina Ai saima wuta da
take hura masa akan lallai ya samo musu gidan
da zasu koma domin su huta da wannan
galantoyin da suke akanTiti. Kullun
Kuma su huta da takaicin duniya
Acan gidan nasuma data koma nanma ba a
hutaba don kullun sai an jita da matan yayyinta
duk kuwa da Jinyan dake hannunta sai kuma akai
sa. A matan daidai da itane basa qyaleta lamarin
ya fara birkita mahaifin Nata idan ya zauna yana
tunani saiya dunga jinjinama abbakar yace lallai
abbakar ya cika mai haquri don tunda sukai aure
Bai taba kawo qarartaba haka kuma nasan Dole
duk yaddah za, ai saita bata masa Rai lallai
abbakar ya cika Mai haqurin gaske
Rashin kunyar fanne ba akan matan yayanta ya
tsayaba harta yayyan Nata zuba musu rashin
kunya take
Musamman idan Tana fada da matansu da zarar
anga itace bata da gaskia Tofa ba daman ace
Mata itace batada gaskia don yanxu zatai tsalle
ta dire tace goyon bayan matansu suke kawai
don anga marainiyace Ita mahaifiyarta ta rasu to
komadai menene babu Wanda ya isa ya taka
Mata birki tunda ai gidan ubantane ,, ko abinci
suka girka suka kawo Mata bata sai tace Wai
sunsa Mata magani habaici Kala Kala nayau
Saban na gobe daban suma sun soma gajia da
halin Nata yasa daya daga cikin yayyun Nata
wanda yake abokin abbakar dinne ya samesa har
shagonsa domin ya tuntubeshi game da maganan
neman gidan da yace yana nema da ya samesane
yake fada masa gaskia cewa har yanxu yana
nema kuma dukda rashin kudi yasa yake Dan Jira
kafin komai ya warware kumama daman so yake
tunda hannun fannen Vai warkeba ta zauna Anan
har sai hannun Nata ya warke sarai sannan
abokin Nasa yayan fannen yai shiru yana
Tunani don shida kansa ya fahimci abbakar ya
fara hajia da zama da fanne a ransa yace lallai
dole asan yaddah za, ai don ganin fanne ta koma
dakinta idan kuwa ba hakan to sunaji suna Gani
zasu rasa aurensu don Ko Jia daqar yashawo kan
matarsa Amman da dabircewa Tai akan Ita
gidansu zata tafi don ba zata iya juran halayyar
fanneva abbakar Dunne ya katseshi da fadin to
yanxu ya kake ganin za. Ai Kenan yayan Nata
yace kawai hada kudi zamuyi mu ganganda a
samo Muku gidan haya don zaman fannen a
wannan gidan ba alkhairi Bane abbakar yai
murmushi gamida cewa tona gode hakan kuwa
akai ba tare da bata lokaciba suka samu gida
mutun dayane a gidan daga shi sai matarsa don
Ko Yaya Basu dashi Amman me abbakar yace Ai
lallai sai fanne ta watstsake sannan zata tare a
gidan da suka koman nanfa murna ta koma ciki
don har sun fara murna wato qaya zata bar musu
gida sai kuma gashi mijinta ya bullo da wani Salo
na saita wake don Gani suke Kaman wani lokacin
zata dauka mai tsawo a haka taci gaba da zama
saidai baban Nata Yaga alamun za, a bata Goma
daya bata gyaruba hakan yasa ya miqe tsaye
wajen nema Mata magani don hannun Nata
kullun ba sauqi don harya fara wani ruwa Mai
wari don ko wucewa kaxoyi ta kusa da ita to
sauka toshe hancinka Amman da yake Allah
majiqan bawansane da baban Nata ya duqufa
davyin Mata addu. Oi akan ciwon safe da ran da
dare ba fashi cikin ikon Allah ba, ai satiba ciwon
ya soma warkewa ruwan da yake ya qafe nanfa
fanne ta soma murnan komawa gidan mijinta don
ita kanta ta soma qosawa databar musu gidan
tace me za, ai da wani gidan da bana mijina ta
tafijin dadin gidan mijinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login