Showing 9001 words to 12000 words out of 38754 words

Chapter 4 - UWAR GOYO COMPLETE BOOK Hausa Novels .txt

Nil   

19 Feb 2025

3939

haihu taxo ta tare anan amman kafin ta
tafin saidata bata shawarar ta saidai rabin
zannuwan da aka kawo mata don an kawo mata
da yawa kai hardama na jariran in yaso babanta
saiya sai musu wani sannan ta tafi gamida ce
mata nanda kwana biyu zata dawo ta dubata da
babyn nata
Ba tare data nemi shawarar abakar dinba ta kira
dillaliya sukai ciniki ta biya don daman tana burin
taga tasai kayan daki masu tsada irin wanda take
gani a gidan qawayenta sai gashi tsuntsu a sama
gasasshe itadai komai tasa a gaba allah na bata
sa, a shiyasa wani lokutan take cema abbakar
itadin ai mai qashin alziqice
Ba, a dau tsawon lokaciba fanne ta gyara dakinta
gunin ban sha, awa hardasa saitin kujeru dataga
kudin sunyi sauranema tabama dashiyasu tace ta
sayo mata sarqar gwal mai kyau
A satin da fanne ta kammala gyaran dakinta a
satinne bre dinta ya tashin mata ya kumbura yai
sumtum ga a zaba yaddah taga rana haka take
ganin dare ga yarinya ta fara damunta da rigima
abin ya taru yai mata yawa
Ganin hakane yasa tacema abakar ya dawo gida
da kwana don koba komai ya taimaka mata da
rainon yarinyar nanfa abakar ya dawo yaci gaba
da dawainiya dasu shi zaima yarinyar wanka yai
musu girki ya hadama fannen ruwan wanka itama
bayan ya tafasa yakai mata bayi idan kayan da
suka cire yayi datti ya wanke musu kana ganinsa
zakasan yana cikin tashin hankali itama duk ta
sauya tayi wani iri duk wanda ya ganta a wannan
yanayin saiya tausaya mata sbd azabar ciwo
allah sarki mutum ba, a bakin komai yakeba duk
halin fanne nada yanxu babu su to inama bakin
yake da har zatai masifan tanata kanta ganin
haka yasa abakar ya tashi tsaye wajen nema
mata magani bashi wannan qauyen bashi wancan
qaiyen kuma kullun saiya kaita taga likita
Saida akai wata uku fanne tana wannan ciwon
bre din sannan allah ya kawo sauqi wani
makwabcinsu ya kwantanta musu wani mai
magani a wani qauye yace indai sukaje da iznin
allah zata warke basuyi wata wata abakar yadau
mota suka nufi garin a lokacin da suka isa
sundan tarar da layi ba tare da bata lokaciba
layin yaxo kansu har suka kaiga ganin mai bada
maganin bayan mai maganin ya duba bre din
natane yaga duk yaddah yake yace da ita kedawa
kikaxonan tace nida mai gidanane yace to cemai
ya shigo ba tare da bata lokaciba suka shigo
yana duke da zainab a hannunsa mai magani
yace naga matalan dake tattare da bre din matar
taka kuma in allah ya yarda zata samu sauqi
saida kuma idan zaka barta anan harta warke
sumul abakar yace to malam amman ya za, ai da
zainab yarta wacce ko kwari bataiba mai maganin
yace karka damu da wannan akwai tsoffin dake
kula da jarirai a ciki
Sannan suka tsadance abbakar yasa hannu aljiu
ya biya kudin maganin a take mai maganin ya
janyo wata jarka mai cike da baqin mai yace ta
bude brez din nata sannan ya shafeshi gaba daya
da wannan baqin man ya kwalama wata tsohuwa
kira daga ciki ta qaraso yace dauki wannan
yarinyar da uwarta ki kaita dakin da ake aje
majinyata sannan kici gaba da kula dasu sannan
abakar ya miqe yaima fanne sallama a take taji
hawaye na gangarowa daga idanunta tace
shikenan y tafi ya barni a garin da bansan
kowaba wannan kngurmin dajinda ko mafarkin
zuwansa bata tabayiba wani katon daki mai
kama da zaure wannan tsohuwar takai fanne an
shimfide dakin da tabarmi ga majinyatanan mata
a ciki kowacce ra riqe kai sbd azabar ciwon dake
addabarsu itama fannen jiki a sanyaue ta nemi
waje ta zauna da rana aka kawo musu koko ko
sigari babu a ciki kofi daidaya gashi kaman ruwa
kallo daya taima kokon ta kauda kai da darema
aka kawo musu tuwo miyar kuka babu ko manja
fara fatal da ita nanma bataciba gashi cikin dare
ciwon nonon nata ya tasar mata nanfa ta tashi ta
dinga zagaye dakin tamkar mai safa da marwa
A darebn ranan batai barciba washe gari aka
kawo musu koko tace ta qoshi bayan mai bada
magani ya kimtsane yace kowa yaxo daya bayan
daya domin amsar magani sannan yacema fanne
taje tahau wani gado ta kwanta akai bayan ya
gama duba sauran matanne ya umurci da akawo
masa wuta da wasu qarafunan nanfa hankalin
fanne ya tashi tsoro ya soma kamata yace karki
damu sakiya zan miki kumama ga wani magani
nan zakisha kafin a fara zai rage miki radadin
zafin da zakiji hakan kuwa akai cikin ikon allah
yai mata sakiyan sannan ya umurci daya daga
cikin tsoffin dake wajen dasu maida ita dakin
nasu aikuwa suna kaita barci mai nauyi ya
dauketa har abakar yaxo dubata bata tashiba
ananne ake ahaida masa da matarsa bata iyacin
abincin da suke don haka saiya dinga taho mata
da abinci yace ba damuwa dukda nisan da
garinnan kedashi haka abbakar ke jigilar kaima
fanne abinci safe da yammah allah sarki abbakar
mutumin kirki satinsu daya a wurin mai magani
fanne ta samu sauqi nonuwan nata suka warke
sarai sannan suka tattaro suka dawo gida
Haqiqa fanne ya cancanci da tabama abbakar
lambar yabo don ya cika masoyi na gaskia don
ba duk namiji bane zai iyama mai hali irin na
fanne wannan dawainiyar ba kuma dukda bajin
dadin zama da ita yakeba wlh in wani namijinne
ko sannu bazai mataba ballentana har takaiga ya
nema mata magani
Shi kuwa abakar da zuciya daya yake mata komai
ba tare da duba duk wasu wulaqanci da tai masa
a baya ba
Fanne sauqi ya samu sosai itama yar tata da
take kira da momy ta murje kasancewar nono na
isarta yanxu ba kamar daba fanne nason yar
kaman ranta sam batason abinda zai taba mata
ita hatta kuda adan dole yake taba yarinyar
danba yaddah zatayine kullun yar cikin kwaliya
take kuma a goye in kaga fanne ta sauke yar to
barci tai yarinyar da fanne tai kama komai nasu
iri dayane sam batai kama da babantaba
Abbakarma nason yar don idan yana gida yana
daukarta sosai amman sond yake mata baikai na
momcyn nata ba lol su fanne an zama uwA
A kwana a tashi momy ta isa yaye sai dan
banzan rashinjin tsiya ga kuka idan ta fara kuka
ayi ayi ta tai shiru taqiyi wani zubinma sai cikin
dare take tashi tahau kuka suyi rarrashin
duniyannan taqiyin shiru fanne tace wai ba lfy ne
da itaba don haka kullun suna kan hanya zuwa
ganin likita
Wani rashin jinma saida yar ta iya tafia wohoho
komai ta samu zubarwa take ta balla wannan ta
watsar da wanccan ta rikito wannan wani abin
takaicin kuma fanne na zaune yar zataita barna
amman taqi hanata wai bataso ta hanata don kar
tai kuka lol saidai kuma bata barin yar tana
bannata mata kayan data siya da kudinta koda
kuwa kukan jini zatai
Amman abu indai abakar ne ya kawoshi tofa
zatabar yar ta barnata koda kuwa menen sannan
ba daman yai magana da zarar yai magana to
yinin ranan babu kwanciyAr hankali wai bayason
yarta bazai barta ta sakata a gidan ubantaba to
in batai barna a gidansuba ina zataje tayi hakan
na nufin abindaya kawo yafi yar tasa daraja
kenan a yinin wannan ranan ta dinga mita kenan
hakan yasa koda yana zaune yar ta fara barna
baice mata komai don shirun nasa yafi ace fanne
ta dinga yaba masa baqaqen maganganu
To yarinyadai haka ta taso cikin sangarta komai
tayi marar kyau a wajen uwar tata mai kyau ne
sam batason ganin bacin ran yar tata abbakar na
qoqari wajen bama yarinyar tarbiya ta kwarai
saidai me yanayine fanne na warwarewa don da
yarinyar tayi abu marakyau yana fara yin mata
fada zatace ina sam batasan wannanba gaskia
kuma ya daina takurama yarta duka duka nawa
take kumama yaushe aka haifeta harda zai fara
takura mata to wallahi inaso ka sani wanan
hanyar daka dauko bamai bullewa, bane don haka
tun wuri kwara ka dakata inkuma ba hakaba ta
murza yan yatsunta sukai qara lol
Mu hadu a nxt chapter jare donjin yaddah zata
kaya
Via. The. C.E.O @littafan hausa zallah
Duk wanda yaga anyi kicking dinsa out karya
zargi kowa ya zargi kansa don bamuce ai like din
wannan page dinba don kawai kaxo ka karanta
lbr kacwuceba anyine don idan akao post a dinga
comment don qarama admin qarfin qwiwa mu
kawai koment Mukeso idan mukai post ko meye
ku rubuta hakan zai tabbatar mana da lbrn yakai
gareku bafa roqon coment nakeba a, a if u like
coment if u like kar kayi I dnt care amman idan
nai kicking dinka waje karkaga laifina
Uwar goyo
Chapter7
Sauda tari a gaban yarinyar fanne zataita ma
abakar rashin mutunci hakan yasa yarinyar ta
taso cikin rashin tsoronsa don koda tana abu
yanacewa ke daina zatace ba za, a dainaba din
rashin mutunci kala kala babu wanda fanne
bataima abakar akan yar tasu hakan yasa abakar
din ya tattarasu daga ita har yar tata ya watsar
a kwandon shara don sau tari yar zata dinga
barna a gabansa amman ya kauda kai yai kaman
baimasan allah yayi mutum a wajenba
Hakan yasa momie ta tashi cikin gata da rashin
tarbiya ga rashin jin tsiya da rashin tsoro kullun a
anguwan sai anyi fada da fanne duk sbd rashinjin
tsiya akwaita da tsokana kuma yaran anguwa ba
kyaleta sukeba tana sokanansu suke kamata su
daka ita kuma fanne abinda bataso kenan aima
yar tata magana mara dadima aima yar sai inda
qarfinta ya qare inaga kuma an dakar mata ita
haba ai tuni zakuga ta zari gyale ta nufi gdan
iyayen yaron daya daki momin idan taga iyayen
nasa ta qare musu masifa da Zagi ta uwa ta uba
idan kuma tai arba da yaron ta kamashi tai masa
dukan tsiya a gaban uwar tasa babu yaddah ta
iya sannan ta zuyo shidai abakar ido yasa musi
gamida yin musu addu, a kullun bai gajia da
neman musi shiriya a wajen uban giji domin kuwa
shiriya a hannunsa take
A anguwar tasu akwai wani yaro taqadiri da duk
yaran anguwan tsoronsa suke idan yaro ya
tsokanesa to a duk inda suka hadu saiyamai
dukan tsiya fadarsa bata mutuwA
Wata ranan laraba da la, asar sule na cikin
abokansa a qofar gidansu makwabtansu fanne ne
saiga momi ta fito tana ganinsa tace aule
kunnuwa sannan ta fara masa daria shi kuma
yaron abinda ya tsana kenan a rayuwArsa kace
masa kunnuwa koka kalli kunnuwansa kana masa
daria habawa allah dawaka hadani inba da momi
ba nanfa tana cikin darianne bata ankaraba sai
ganinsa tai a gabanta ba tare da bata lokaciba
yahau kanta da duka saidayaga yayi mata lilis
sannan ya kyaleta yai tafiyarsa gamida barinma
anguwar dan yasan halin uwar tata momi ta
shiga gida cikin kuka fanne ta ganta hankali tashe
take tambayarta abindaya sameta cikin kuka take
fada mata cew kunnuwa ne tace kan ubannan me
kikai masa da har zai miki irin wannan dukan
harda fasa baki kodon yaga ya fiki qarfi lallai ya
taro ruwan bala, I baisan daya tabaki gwara yaje
ya rungumi transfomer ba tashi maza maza muje
gidan nasu
Nanfa fanne ta kama hanya harda tuntube riqe da
hannun momi saidai me da taje bata bata samu
suleba kuma uwar tasa itama akai rashin sa, a
taje anguwa nanfa fanne ta dinga sarfa ruwan
bala, I bakinta har kunfa yake saida tai mai isarta
sannan ta dawo gida ba, a sati da faruwan
abunbA
Momi da sule suka sake haduwa ita batama
gansaba ballentana ta tsokanesa ta bayanta ya
zagayo kafin ta ankar harya chakumota ya dinga
dukan bakin nata har saidaya fashe sannan ya
tsere gamida barin anguwan a lokacin da momi
ta isa gida ta shaidama fanne cikin bacin rai ta
suri tabarya idonta ya rufe don ko gabanta bata
gani sbd tsabar baqinciki ta isa gidansu salen a
bakin rijiya ta iske uwar tasa tana diban ruwa ba
tare da wani dogon bayaniba ta hau uwar tasa da
duka da tabarya tako ina saida taga ko moysi
bayayi sannan natsuwa yaxo mata
Tsorone da fargaba duka suka kamata don gani
take ke kamar matar ta mutu hakan yasa cikin
hanzari tabar gidan don kar azo a ganta abinda
bata saniba kuwa shine ashe tun shigowarta ashe
akwai yayar sulen dake can nesa dasu ganin za,
a kashe mahaifiyarsu yasa ta ruga can inda
mahaifinsu ke zama ta sanar dashi
Abbakar bai dade da dawowa daga kasuwaba sai
ganin yansanda sukai cike da mota ba tare da
wani bayaniba suka tasa qeyar fannen sukai gaba
da ita bayan sun tafi da itanne abbakar din kejin
abindaya faru girgixa kai yayi gamida mamakin
abinda fannen ta aikata kwana biyu yayi yana
sintirin zuwa station amman anqi barinsa yamaga
fanne a ransa yace wannan karon fanne ta dauko
ruwan da zai dafasu daqar da sidin goshi aka
bashi belinta wai donma ya dauki lauya kenan
don a tunaninsa akai lamarin koti a wannan karan
ba qaramin kudi abakar ya kasheba donshi yadau
nauyin jinyar matar da dannen takusa kashewa
don ata dalilin hakanne matar ta rasa rabin
kunnunta na gefe daya da manyan raunika wajen
fito da fannenma ba qananun kudi ya kasheba abi
ya taru yai masa yawa ga jinyar matar daya daka
ga kuma jinyar fanne don itama tundata fito
kasancewar ta daku fuskokinta duk sun kumbura
idanuwanta sukai jajir kana ganinta kasan ta
daku to tun daga ranan itama ta kama rashin lfy
hakan yasa yaci gaba da jinyar tasu su biyu
sauqi ya samu a wajen fanne saidai zuciyarta
cushe yake da baqinciki akan tozarcin da mijin
wannan matar yai mata taso ta daukaka qara
kotu domin abi mata haqqinta to saidai me
wanda take tunanin zai tsaya mata din har tao
nasara yace tai haquri don koda sunje kotu ita
za, a bama rashin gaskia tunda itace ta tashi taje
har gidansu laraban ta sameta badan tasoba y
haqura amman ta kudiri niyyah a ranta komin
daren dadewa saita rama cin mutuncin da akai
mata tun daga lokacin gaba ta kullu tsakanin
fanne dasu laraba ko magana bai hadasu daman
tun a station aka shiga tsakaninsu hakan yasa
yanxu sule bai taba momi hakanma itama tun
lokacin da yai mata mazgan farko ta soma jin
tsoronsa duk inda ta gansa a yanxu guduwa take
a tsakaninsu yanxu kowa jin haushin kowa yake
saidai kuma ba daman yin fada
Yanxu haka shekarun momi hudu amman fanne
bata sake daukan wani cikinba a tunaninta
tundata dade kafin ta haifeta kuma yanxu ta dade
bayan ta haifetan babu wani ciki sai take tunanin
kaman daman ita dayace allah ya rubuta zata
haifa hakan yasa ta janyota cikinta gamida bata
kulawa yaddah ya kamata tareda sangartar daita
ta bata freedom din yin duk abinda ranta yakeso
A duk fadin anguwan babu yaron dake samun
gatan da momy ke samu kullun cikin kwalliya
take ta saka wannan ta cire wancan kuma aka
sakata wata makaranta mai hade da islamiya ta
yayan masu dashi don a anguwan nasu ba ko
wane yaro bane ke makaranta allah sarki a
wannan shekarar ne allah ya sake budama
abakar mai gidansa ya kirasa sukai lissafin
abinda ke wajen abbakar din gida uku suka raba
mai gidan nasa yadau kashi daya yabama
abbakar din kashi biyi yace wannan mallakinkane
kaje na mallaka maka kaja jari daga yanxu ka
tashi daga qarqashina ka koma cin gashin kanka
hatta shagon da kake kula dashi shima na
mallaka maka wohoho ikon allah krnan daman
ance mahakurci mawadaci ba qaramin murna
abbakar yaiba harda hawayen farinciki mai gidan
nasa yace rabonkane abbakar kaje allah yasa
maka albarka a cikin kasnuwancin naka sannan
yace ameen ya tashi ya tafi
Yana tunkarar fanne da zancen uban gidansa ya
ware masa kudi masu tsoka domin jan jari saita
fara lallabansa akan yakaita makkah don duk a
cikin qawayenta itace kawai bataje hajjiba don
akwai wadanda duk shekara suke zuwa kumama
haji da umara zakaga mazajensu ke biya musu ka
duba qawata dashiya zuwanta uku gana hudu
tana shirin zuwa dukda batai aureba samarintane
ke boya mata baiyo mamakin jin kalaman rashin
hankali daga bakin fannenba kasancewar yasan
halinta sarai saidai shiru yai baice mata qala bala
ita kuma a wautarta tasha ai ya amincene hakan
yasa ta fara watsawa a gari da qawayenta cewa
itama wannan shekarar zata makka amman me
shiru kakeji shidai abbakar baice zai biya mataba
kuma baice bazai biyaba hakan yasa hankalin
fanne ya soma tashi don bazataso taji kunyaba
bayan ta gama shaidama qawayen nata zata
makkah wannan shekarar kuma zance ya sauya
salo don daman duk a cikinsu itace
maqasqanciya wai donma mijin nata na mata duk
abinda takeso kenan shiyasa har yanxu suke tace
tace ina ai dolenema abakar ya biya mata aikin
hajji taje don da taji kunyar duniya gwara taji na
lahira
Dadai abin ya dameta sai ta nufi wajen qawarta
dashiya domin nemo mafita don ta qare wajen
iya hada tuqqu kuma duk wani abu daya shigema
fannen duhu ita dashiyar itace ke shawo mata
kan lamarin cikin sauri tana labarta mata zancen
sai dashiya tace haba qawata ai wannan zancen
naki shi yafi komai sauqi kawo kunnenki kiji tana
rada mata fuskarta ta fadada da murmushi
sannan ta fara aiwatar da abinda dashiyar ta
fada mata washe garin ranan abakar na dadowa
daga kasuwa ko zama baiyiba balle yasha ruwwa
ta tareshi da zancen abbakar yace a gaskia fanne
banida kiudin da zan biya miki kujeran makkah a
yamxu ki bari zuwa gaba mu gani saina biya miki
inhar kinada rabon zuwa habawa aiji fanne tai
kaman abakar din ya watsa mata garwashin wuta
nanfa ta shiga surfa masa ruwan bala, I da
masifa tare dayin masa gore gore irin na jahilan
mata wadanda basusan inda ke musu ciwoba
Shidai shiru yai mata ba tare da yace mata komai
ba don idan da sabo ya isa ace ya saba da
wannan halin na fanne
Tun daga wannan ranan zaman lfy ya kaura a
gidan gaba daya zaman gidan ya ishi abakar don
inhar yana gidan fanne ta shiga yaba masa
baqaqen maganganu kenan tare dace masa
lusarin namiji wanda bai biyama matarsa
buqatunta in banda qaddara da rabon haihuwa da
mai zatai dashi
Wai sanin kansane ita ba tsaran aurensa bace sa,
ar manyace ya dubeta da kyau batayi kama da
irinsu yaku bayoba wanda baida zuciya irinta
zaruman maza kawai
Kaini fanne naga taskon duniya tunda har aka
hadani aure da wannan lusarin allaah dai yasa
kar yata momi ta dauko irin halinka na rashin
zuciya
A kullun ranan duniya sai fanne ta samu baqaqen
maganganun da zata sossokama abbakar tunda
yake a duniya bai taba ganin macen data raina
mijinta irinsaba
Yakan bata lokaci ya zauna yin tunanin abinda
yasa fanne ta rainashi haka backin kuma bai
rageta da komai ba duk wani nauyinta daya
rataya a wuyansa yana bakin qoqarinsa wajen
ganin ya saukesu suturan da yake sawama baikai
tsadar wanda yakesa kudi yana siya mata ba
gashi duk abinda ta nema yana mata
Kullin da akwai salon rashin mutuncin da fanne ke
bulloma abbakar dashi kai harya gaji dai ya biya
mata kudin kujerar makkan don ko abinci bata
barinsa yaci haka kuma bata barinsa yao barci
gashi ta dinga masa gori akan gidan da suke
cikima ai mallakintane
Abakar yana ahigowa gida kamar dai yaddah ya
sabanne da masifa aka tarbeshi saidaya bari tayi
mai isarta tayi shiru sannan ya zaro wata farar
takarda daga aljihunsa ya miqa mata wacce
shaidace na ya biya mata kujearar makkah
Zuciyar fanne tai ras nan da nan gumi ya karyo
mata cikinta yahau kuqi ta bude baki zatai
magana amman ta kasa domin bakin nata sai
rawa yake tunda takeca duniya bata tabajin
abinda ya kadata a duniya irin wannan ba a take
a wajen ta zuge da gudawa saidata shiga ban
daki yafi sau uku sannan ta dawo indacabbakar
din ke tsaye saidai har izuwa lokacin ta kasa ce
dashi komai tana tsaye a wajen ne saiga qawarta
dashita ta shigo gidan daqar fanne tayi qoqarin
nemo kalaman data amsa gaisuwar tata dasu
sannan tace zomu shiga daki akwai magana
Suna shiga fanne tasama dashi kuka gamida
cewa shikenan nikam na shiga uku asirina ya
tonu na shiga uku na lalace nikam ina zan saka
kaina naji dadi wayyo rayuwa yau duniya taimin
daurin dalmon minti ko kuma ince duniya taimin
atishawar tsaki dashiya dai kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login