Showing 18001 words to 21000 words out of 38754 words

Chapter 7 - UWAR GOYO COMPLETE BOOK Hausa Novels .txt

Nil   

19 Feb 2025

3922

ganin wannan abun ba tasa hannu ta
dafe daidai inda zuciyarta take jin zuciyar tata
take kaman zata futo da sauri da sauri
numfashinta ke fita gani take idan da za, a gwada
jininta ayau to sai nata yahau kai idan ana hawan
ruwama to sai tayi a yau don an bata mata rai
sosai
Wato daman abinda abbakar ke aikatawa kenan
shiyasa yakeqin kulata? Saisu debi tsawon
kwanaki ko sati bai gayyaceta zuwa
shimfidarsaba wani lokutanma sukankai wata
basuyi huldaba bata damuba a lokacin sbd
batasan abinda yake aikatawaba ita ta dauka ra,
ayine baidashi akan hakan shiyasama batabin
diddigin abinda ke hanashi rashin neman nata
kuma dadin dadawa abin bai damunta don bataga
amfaninsaba haka kawai mutum na cikin
hutawarsa a damesa bayan ba biyansa akeba
gashi kuma aita masa sukuwa akan ruwan
cikinsa sau kace wani doki duk kuma a kyauta
baza, a bama mutum ko sisiba ina amman ai ita
dadiron nasa biyanta kudi yake
Hajia fanne bata kushe tana tunanin abinda ta
gani a shagon alfijir super store ba saiji tai ana
kiraye kirayen sallan asuba da farko da taji tasha
ko kunnentane ke mata kizo dan abbakar bai taba
zuwa wanu waje ya kwanaba inhar ba sarin kaya
ya tafi ba tai gaggawan shiga falonta donta duba
agogo kuma ta tabbatar da abinda kunnuwan
nata kejin mata din ai kuwa hakane data duba
agofon qarfe hutu ne ba asuba harda yan mintoci
To ina abakar ya shiga har yanxu bai dawo
gidava kodai wani salon iskancinne ya sake
fitomin dashi kallai wuyansa yayi kwari kuma ya
sake bunqasa laifinsa a wurina tunda har yasan
ya kwana a gidan karuwa abinda bai taba
aikatawaba kenan daman ance ka tsoraci
mutumin da baya magana idan har ya tashi
kunsa maka baqinciki to saika rasa inda zakasa
kanka wato na kwana cikin baqinciki da tashin
hankali amman shi yanacan wajen dadirinsa ko a
jikinsa ko yau ni fanne na hadu da gamona wato
abbakar bai damu da damuwatava zuwa yanxy na
gama sanin cewa banida wata tasiri a cikin
zuciyarsa tabdijam lallai yau akwai rugiman da
bana fatan allah ya sauwaqeta inanan ina jiransa
zaizo ya sameni har gida koda kuwa ace shekara
zaiyi a wajrn nata ta gamacin burin wukaqanta
abbakar kuma ta nuna masa ita ba tsaransa bace
da zai mata wannan cin zarafinba
Tana kwance tana tunanin inda zata fara zuwa
neman abakar idan gari ya qarasa wayewa a
haka har bacci yai awon gaba da ita ta dade tana
barci batasanma gari ya wayeba sai zuba
minshari kawai take kasancewar ta kwana batai
barciba kuma ma daman ba sabonta bane rashin
barci
Bugun qofar gidan nasu da akene ya tasheta daga
nannauyan barcin da take tana murtsike idanu da
sauri ta nufi qofar gidan domin taga ko wanene
ke buga mata qofar gida haka kaman za, a cire
mata qofar gidan sai kace wacce ake bi bashi
tanada yaqinin abbakar ne hakan yasa da
azamarta ta nufi kiching gamida dauko muciya da
wuqa sannan ta koma zauren amman ina
zuciyarta bata amince da muciyarba don zata iya
karyewa kamin ta morema dukan nasa dashi don
haka ta juya can bayan gidan nasu taje ai kuwa
tai karo da wani faskaren itace nanfa tayo awon
gaba dashi cikin sauri ta sake dawowa qofar
gidan tana budewa bata tsaya duba wanene a
wajenba takai masa wawan duka da iccen
faskaren sauran kiris fannen ta gicciyema
makwabcin nasu gefen jafada da iccen don ita a
tunaninta tayi zaton wai ko abbakar ne ya dawo
daga yawon iskancin nasa da sauri mutumin ya
kauce don kuwa idan har ya bari wannen
faskaren ya samu mazauni a jikinsa
musammanma kansa don ya lura hajia fannen
nan take harin sama to sai buxunsa don dukan
data kawo bana wasa bane wannan dukan da
hajia fanne ta kawo masa ya dada bashi mamaki
kuma ya qara tabbatar da maganganun da jama,
a keyi akanta marasa kyau
Kai lallai kam abakar na fama da kuncin xuciya
mutum mai haquri da kamala amman allah ya
jarrabeshi da matsiyaciyar mata dashi ya dauka
duka qaryane akan abinda ake yamadidi dashi
akanta a cikin anguwa dukda yanajin ana cewa
masifaffiyace baiyi xaton lamarin nata yakai
hakaba domin ko magana bata hadata dashi da
itaba tunda allah ya kawoshi anguwan ballentana
aje ga batu na rashin jituwa suna mutunci sosai
da abbakar don bashi daga cikin masuma
abbakar din mummunan fahimta da yayi tunanin
komawa gidan nasa ba tare daya fadama fannen
abindaya kawoshiba wajen nata don iya jutewa
zai iya jure duk wani abu da zata gaya masa idan
kuwa har takaisu ga sa, insa to shine mara
gaskia tunda shine ya tako har kofar gidan nata
amman kuma daya tuna irin alkhairan da abbakar
din ke masa da kuma alkhairansa garesa ga
kuma haqqin makwabtaka sai yaga rashin
dacewar yin hakan ga kuma halin wahala da
abbakar ke ciki tun daren jiya har izuwa yanxu
sakamakon hatsarun motar da sukai wanda ake
ganinma da wuya idan zaiyi rai ya zama dole ya
daure ya fada mata domin taje taga irin halin da
yake ciki koda kuwa ace zata sakashi a cikin
turmi ta kirbashi to ya fita haqqinta ko a wajen
allah
Kai malam lfy kaxo kana bugamin gida da
sassafe kaman wanda kakebi bashi? Ko kuwa
dakai muka hada kudu mukasai gidan? Sannan ka
zubamin ido kana kallona tun daxu ka kasa cewa
komai sai kace wani maye wandayai shekara
baici namaba to ka bude kunnuwanka dakyau kaji
inhar kai mayene kaxo ka lashe kurwata toni
fanne nafi qarfinka
Kurwata kur take namana da daci nafi karfin
karamin maye kamarka don haka ka koma gida
ka sake shiri don yau babu sa, a a gareka inason
ka sani idan kanacin kasa ka kiyayi ta shuri
dominni murucin kan dutsece van fitoba sai daba
shirya kuma ni jeji ce babu mai iya min kyaure sai
mahaukacin kafinta gahon ari sai fanna ramin
kura sai yayanta daga yau nidakai mu zuba shege
ka fasa tunda fanne ta soma masifar bata dasa
ataba saida taxo iya nan shi kuwa mutumin shiru
yai yana sauraron maganganun da take yaba
masan cikin tsawa da tsiwa da kuma gatsali
dukda cewa yaji zafin maganganun nata saiya
danne zuciyarsa gamida cewa ina kwana hajia ?
cikin girmamawa daban kwanaba ka ganni ?
Bari kaji na gaya maka ni banason gaisuwarka ta
munafukai abindaya kawoka kawai nakeson ka
gayamin idan kuma halin naka na dan akuya daka
sabayima matan anguwannan kaxo kaimin to sai
kai da babban murya domin duk wannan nuku
nukun da kake babu inda zai kaika sannan inason
ka sani koda nidin yar iskace kamarka bazan
yarda dakai a matsayin kwartonaba ka dubeni
dakyau sama da qasa niba irin matan da kake
zuwa wajensu kana yaudara bane kai amman anji
kunya ba, aji dadin haliba dubeka tsofai tsofai
dakai amman ka rasa abinda zaka dinga
aikatawa sai bin matan mutane idanma iskancin
kakeso to ka tafi gidan karuwai mana tunda gasu
can a gari kaman jamfa ajos bawai ka dingabin
gidajen jama a kana lalata da matansuba
Haqiqa ayau da ace mijina yana gida da saika
raina kanka kuma daga kaina da ka daina zuwa
yin kwartonci gidan mutane kenan dukda bayanan
idan ya dawo saina sanar dashi abinda ke faruwa
don haka saika zauna cikin shiri na zuwa kotu
don ba yarda zanyiba ka batamin suna ina zaman
zamana ba mutane suna ganin mutuncina a cikin
anguwa
Fannen ta bude vaki zata qara magana kenab
mutumin ya dakatar da ita da hannu cikin fushi
ke dakata don allaha marar kunya wacce tarbiya
bai ishetaba ki sani niba abokin yinki bane kuma
wlh kinji na rantse kinci darajar mijinki vadon ina
kallonsa da daraja da qimaba a idonaba da na
rantse da wanda raina ke hannunsa daga kaina
kin dainama wani rashin kunya amman da yake
ko a lahira wani yanacin albarkacin wani yasa
zan kyaleki amman kici gaba da yima mutane
rashin albarka da sannu zaki hadu da daidai ke
kuma sharrin da kikaimin na barki da allah shine
kadai zaimin sakayyah abindaya kawoni wurinki
zuwa nai na sanar dake mijinki yayi hatsari tun
jiya da daddare kuma yayi mummunan rauni
wanda mutane da dama sun tausaya masa sbd
rayuwarsa tana cikin dayan biyu mutuwa ko
rayuwa allah ne yasa kwanansa na gaba shiyasa
har yanxu yake numfashi a halin da ake yanxu
yana general hospital na garinnan yana kawowa
nan a zancen nasa ya juya da nufin yabar wajen
tunda ya gama abinda ya kawoshi domin
tsayuwar da take a kusa da fanne hatsarine don
zuciya ba qashine da itaba kaman daga sama
yaji fannen cikin daga murya tace ahayye nanaye
allah na gode maka inama ace abbakar mutuwa
yayi yau da sai nayi qaramin fati sbd murna da
farin ciki shegu muna fukai ai halinku daya kai
dashi shiyasa taku taxo daya kai dashi banda
neman mata babu abinda kuka sani to gashinan
allah allah ya kamashi sauran kai ina mai
tabbatar maka da idan baka nutsu kayi hankaliba
a wajen kwartonci mijin wata zaiyi ajalinka
Wohoh wato dattijon ji yai kaman fannen ta dibo
ruwan garwashi ta watsa masa a jiki amman me
Mu hadu a next chapter donjin yaddah zata kaya
Naku har kullun
Uwar. Goyo.
Chapter11
Dukda yaji abinda ta fada din amman sai bai juyo
ya tanka mata ba zuciyarsa cike fall da baqin
cikin abinda hajia fanne tai masa wannan ai cin
fuskane rayuwa kenan kuma komai aida
sanadinsa haqiqa matarnan taci darajar igiyar
auren dake kanta inda kuwa ba hakaba wlh da
saina nuna mata da ruwa ake shayi don kuwa
bazai yiwu taci masa fuska ta kwana lfy ba kuma
da daga kansa ta dainama mutane fitsara da
rashin kunya kai duniya ina zaki damu bawan
allahn nan ya sadaukar da rayuwarsa wajen
samo mata abinda take buqata amman dukda
haka bai tsira ba kullun cikin tafiye tafiye yake
don kawai ya samu asirinsa dana iyalansa ya
rufu allah ya horema abbakar abubuwan jin dadi
ga kuma ilmin arabi dana boko
Hajia fanne mutumin ya tafi ya barta a wajenne
ta kasa aiwatar da komai domin jin maganar tasa
tai
tamkar a mafarki wai abbakar yayi hatsari har
wai yaji ciwo sosai wannan ai qaryane kumama
zancen banzane waya sanima qila hadabaki sukai
mutumin da yake cikin qoshin lfy jia da dare cikin
nishadi ga kuma mace a gefensa shine za, a wani
zo mata da zancen yayi hatsari kai gaskia nayi
sakaci da nabar wannan munafukin mutumin ya
tafi aida ta kansa na fara nuna musu abinda
zanma abbakar din inyaso yajema abbakar din
dashi don ya tabbatar masa da akwai bala, in
dake jiransa a gida kai mai yasa banbi
mutuminnan a bayaba domin na gano gidan
dadiron abbakar din don na tabbata gidan nasu
yanxu zai koma domin ya sanar dashi yaddah
mukayi
Amman abakar ya daukeni sakarya marar hankali
jiya mu rabu dashi lfyrsa qalau yau kuma da
sassafe axo acemin yayu hatsari dagajin
maganarma ai kasan zuqi ta malle ce sannan
kuma daga yaddah mutumin ya nuna da farko
zaka gane bashi da gaskia zuwa yanxu na harbo
girgin abbakar so yake ya nunamin ya fini sanin
duniya karka damu ai na gano shirin naka ka
gama zagaye zagayen naka zakaxo ka sameni
inanan zaune daram a cikin gidan ba asibiti kake
zauneba allah yasa a kabari kake indai har zakaji
sauqi to rigima nanan tana jiranka a gida aida
naso sanar da dashiyama abindaya faru amman
na fasa ai wlh sai naga abinda ya turema buzu
nadi don wlh abbakar ka tono tsuliyar dodo wlh
daga wannan lokacin na daina saurara maka
komai tunda nafahimci kaiba dan mutunci bane
gaba gabama inaga har gida zaka dinga kawomin
karuwan tunda naga alamun idanuwanka sun
rigada sun rufe akan aikata masha, ar taka ni
inanan zaune ina banga macen da abbakar zau
kawomin a matsayin matar da zai auraba ashe
mugun yanacan yana muna furtata a waje haqiqa
ina ganin wautar matan dake fadin da kishiyar
gida kwara ta waje kalmarma ba dadinji aini da
mijina ya fita waje neman karuwa kwara ya
auromin mata uku a rana daya ya ajemu a gida
daya ina ganin shige da ficensu Abbakar ka
cuceni harka mutu kuma bazan manta da wannan
cuta dakaimin ba haka kuma baxan taba yafe
maka haqqina daka tauyeminba
Sarkin iya magana kawai waya sanima ko shima
ta irin wannan hanyar aka sameshi tunda ni
bansan ubansaba haka tunda mukai aure ban
taba ganin dangin uban nasa sunzo wajensaba ta
kyalkyalr da daria sannan ta nufi dakin barcinta
ba tare da bata lokaciba nannauyan barci yai
awon gaba da ita bata farkaba har akai sallar
azahar wanda daman ko sallar safiya bataiba
daman can fanne ba sallah takeba bayan an idar
da sallar azhar dinne ta miqe zaune gamida
murtsuke idanu hade dayin wata doguwar hamma
cikin nutsuwa ta ture qafafunta kasa tare da
miqewa ta nufi hanyar falonta daga cikin kujerun
dake falon nata ne ta samu daya ta zauna
sannan ta shiga kwalama mai aikin nata kira da
sauri jummai mai aikin nata ta qarasao ta duqa
can nesa da ita tana kwasar gaisuwa sannan tace
gani hajia
Ki shiga bandaki ki hadamin ruwan wanka to
hajia sannan ta tashi ta nufi ban dakin domin isar
da umurnin hajiyan bayan ta gamane taje ta
sanar da ita cikin yatsine ta tashi tana wani taku
tamkar wacce takejin tausayin kasar sannan ta
fada ban dakin tana shiga mai aikin nata ta shiga
dakin nata domun gyara mata cikin kankanin
lokaci ta kammala sannan ta dawo falo nanma
ba tare da bata lojaciba ta kammala da yake mai
aikin nata akwaita da hanzari
Tsaf hajia fanne ta shigo falonta cikin kwalliya
kaman mai shirin zuwa wata liyafa sannan
jummai ta dinga jera mata abinci kala kala a
gabanta tare kuma da dauko mata lemuka irin
wanda takeso ina mommy take ta tambayi
jummai a lokacin da take zuba mata farfesun
kayan ciki tace da ita tun dazun ta farka nai
mata wanka gamida bata abinci sannan ta fice
tun sannan ban sake ganintaba
Kije ki nemomin ita aduk inda take kuma bance
kije ki zaunaba kamar yaddah kika saba idan na
aikeki ni na rasa mai yasa baki da hanxari kaman
na mutane kina tafiya kamar wacce kwai ya fashe
mata a ciki ina ganin idan na aikeki kalle kalle
kike tsayawayi shiyasa bakya dawowa da wuri
daman ai hausawa sunce komai akaima jaki sai
yaci kara yar kauye kawai wacce garinsu ko
kwalta babu
Itadai jummai batace da ita komaiba tashi tai
cikin hanzari domin aikatar da umurnin data bata
cikin zuciyarta kuwa tanajin baqincikin
wulaqancin da fanne ke mata idan da sabo yaci
ace ta saba da irin wannan cin kashin da hajia
fanne ke mata
Hajia fanne ta dauko lomai wainar kwai zatakai
baki kenan sai tsinkayar muyar mahaifinta a
tsakar gidan nasu yanayin sallama a haqiqanin
gaskia fanne bataso wannan ziyarar da mahaifin
nata ya kawo mata ba domin kuwa ta sani baya
zuwa gidan nata saida dalili bata ko shakkar
abbakarne yaje ya baibayeshi da zaqin baki akan
abinda ya faru jiya da dare shine yanxu ya debo
qafa yaxo gidan nata domin danne mata yanci
kaman yaddah ya saba ita tana ganinma fita
harkar baban nata zatai inyaso ta barshi da
abbakar din tunda yafi sonsa akanta fanne na
matuqar jin yinwa don rabonta da abinci tun jia
da yammah gashi kuma yanxu baban nata zai
katse mata cin abincin nata tana cikin hakane sai
jiyosu jimmai tai ita da momy taje ta rungume
kakan nata oyoyo shima cikin murna ya kamata
tare da tambayar maman taki tananan kuwa?
Tace eh tananan yace ti je kice da ita naxo ta
sakeshi sannan ta ruga falon maman nata domin
ta sanar da ita zuwan baban nata
Mama kixo banan cikin gida yaxo haka suke kiran
mahaifin fannen dashi tace ina xuwa momy ki
kaishi falon da ake sauke baqi saida fanne ta
tabbatar da cikints ya cika sannan ta fara tunanin
abinda zai wakana tsakaninta da mahaifin nata
wanda ayau ji take zuciyarta ba zata amince da
abinda zaizo mata dashiba idan har ya goyi
bayan abbakar domin ta gaji da danne mata
haqqin da ake haka kawai a daki mutum kuma a
hanashi kuka wai mai yasa jama a basa
ganewane a kullun daukar abbakar suke mutumin
kirki wanda ba haka bane dan akuyane mai
lullube da fatar kura wannan abin kadai idan ta
tuna sai taji ta qara tsanar abbakar din babanta
ya jima a zaune yana jiran fitowan fannen amman
shiru kakeji wanda har saida ransa ya soma baci
akan wulaqancin da tai masa daman kuma a
hasale yaxo gidan donma momy tana debe masa
kewa da irin zantuntukanta na yara ne saida
fanne taga lokaci na kurewa har yanxu bata samu
mafitaba sannan ta tilastama kanta fitowan cikin
nutsuwa ta shiga falon sannan ta qarasa wajensa
har qasa ta duqa domin gaishe dashi bai kalli
inda takeba haka kuma baice da ita komaiba a
lokacin da take gaishe dashi din ya dade yanajin
maganganu a bakin yayyun fanne game da
wulaqantasu da take idan sunzo wajenta dukda
yasan zata aikata hakan amman bai taba tunanin
shima zata aikata masa hakanba wannan shirun
da taga mahaifin nata yayi da kuma yaddah taga
fuskar tasa a daure tamau ta fahimci ba wasa a
tare dashi hakan yasa zuciyarta ta fara dukan uku
uku tsoro duk ya mamayemata zuciya bakinta na
karkarwa kaman mai zazzabi ko kuma maijin
sanyi tace
Kayi haquri don aallah idan na, bata maka raine
wlh na shiga wanka kenan momy taxo tacemin
kaxo shiyasa kaga nadade da yake shi mutum ne
mai saurin fahimta da zaran ya kalli fuskarka ko
yanayin maganar taka da sauri ya fahimci
maganan nata duk qaryane daman kuma tun
daya shigo falon ya tambayi mome me takeyi
tace dashi abinci takeci fanne ta tsugunna ta
sunkuyar da kanta qasa tana kallon qasa saiji tai
baban nata ya fara balbaleta da fada ta inda yake
shiga batanan yake fita ba yadau tsawon lokaci
yana abu daya ba tare daya saurara ba sai da yai
mata wankin babban bargo akan wulaqantashi da
tayi sannan ya umurceta data koma daki ta
dauko mayafi domin su tafi wajen abakar a asibiti
in banda rashin hankali irin naki ace mijinki yayi
hatsari tun jiya amman ki kasa zuwa dubashi to
idan allah ya dauki ransa me zakice? Yanada
ransama baki damu dashiba inaga ya rasa
wannan mugun halin irin naki na rasa a inda kika
samoshi domin kuwa dagani harmahaifiyarki babu
mai irin wannan halin naki
Zaki tashi kije ki dauko mayafin naki mu tafi ko
saina bata miki rai?
Jiki ba kwari fannen ta tashi ta nufi dakin nata a
lokacin data dauko gyalenne kafin ta fito daga
dakin nata take cewa ashe da gaskene abbakar
yayi hatsari allah na gode maka maganinsa kenan
allah ne ya sakamin a bisa cutar dani da yake
tare da munafurtata
Allah ya qara idan mutum shi bashi da aiki sai
zalunci aishi allah ba azzalumin sarki bane yana
kuma kallonsa akan duk abinda yakeyi allah yasa
da karuwar tasa yai hatsarin inaga mutane masu
goya masa baya idan sukaga abinda ya faru zasu
yarda da shidin munafukine daganan kuma
mutuncinsa ya zube mutane su dinga kallonsa da
abinda yake aikatawan
Shi kuma babana da yaxo yAnata wanimin masifa
ce masa akai nice sanadin hatsarin nasa ko
meye ? Da zaizo ya dingamin tsawa dolene sai
naje na gaishe dashi koko nice ke bada lfyn
daman ai hausawa sunce a wajen kwadayi kuda
ke mutuwa to gashinan ta faru akan abbakar
tunda ya biyema son zuciyarsa kuma ta kaishi ta
baro da danasani wanda bazai masa amfaniba a
motar hajia fanne direba ya tukasu daqar
mahaifin nata ya shiga motar donda shi cewa yai
bazai shiga motarba saidai su shiga ta haya
domin ya gama tsinkema da lamarin fanne don
gani yakema idan ya shiga motarma akwai
wulaqancin da zata sakeyi masa don haka yace
shi baxai shigaba daqar direban ya shawo kansa
sannan ya yarda ya shiga motan suka tafi a cikin
motarma nasiha ya dingama fannen akan tabi
duniya a sannu sannan tai hankali tun kafun
dunya ta koya mata duk abubuwan da mahaifin
nata ke fada mata bajinsu takeba don da tanajin
abinda yake fada mata da tuntun ta zama kamila
Sun isa asibitin mahaifin fanne ne yai musu
jagora zuwa dakinda abakar din yake duk mutum
mai imani idan yaga halin da abakar ke ciki saiya
tausaya masa akan mummunan halin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login