Showing 12001 words to 15000 words out of 38754 words

Chapter 5 - UWAR GOYO COMPLETE BOOK Hausa Novels .txt

Nil   

19 Feb 2025

3510

fanne kawai
take cikin rashin fahimta sanne ta sake bude baki
zatai magana dashiya ta rufe mata bakin nifa ban
gane me kike nufiba babankine ya rasu?
Uhhjm dashiya kenan idan babanane ya rasu ai
abin zai zomin da sauqi tunda nasan duk mai rai
mamacine
To meye ya sakaki shiga cikin wannan halin ni
wlh kin sani a duhu
Fanne taja ajiyar zuciya sannan tace daxun
abbakar ya shigo yana shihowa na taresa da
zancen tafiya hajji kawai sai ya miqomin wannan
takardan kuma yace waiya sakeni kunji qarya
jama, a allah e mana tsari daga biyema son
zuciya amin
Dashiya tasa hannu ta amsi takardar dA tace
abbakar dinne ya bata tana dubawa
Dashiya tace da gaske kike abbakar dinne ya baki
gamida cewa ya sakeki dashiya tace da ita
lokacin data kammala karantawan
Wlh kuwa shine ya bani dubamin ki gani saki uku
yaimin ko?
Don na sanshi da rashin imani tare da mugunta
ga kuma baqar zuciya
Dashiya ta girgiza kai gamida jan yar guntuwar
tsaki tace kai jahilci mugun ciwo. To wannan
takardar bata komai bace illa illah ta shaidar biya
miki kujeran makkah da abakar yayi fanne tace
wattttttttttttt
Uwar goyo
Chapter7
TACE WAT dan allah dashiya kibarmin wasa ke
komai saikin shigo da wasa cikinsa ki nemo mana
hanyar da zamubi domin samun mafita ya
maidani dakina tun kafin maqiya su faramin daria
don daman da yawa yan anguwannan bason
zamana da shi sukeba ke hardama yan uwansa
dondai na zame masa qarfen qafane kawai yasa
suke sauraramin
Dashi tace na rantse miki da allah abbakar ba
sakinki yaiba kinji rantsuwar dan musulmi kenan
makkah ya biya miki
Kaman daukewar ruwan sama tai cak da kukan
kuma sai aka koma murna harda bama dashiya
goron albishirin
Tace kai abbakar anyi mai baqar zuciya yana
ganina inata shige da fice a ban daki kuma
yaqice dani komai kai gaskia na yarda jahilci yafi
hauka ciwo yanxu da nayi karatu aida duk haka
bata faruba allahma ya taimaka babu wanda yaji
ballentana aomin daria dashiya tace aiko baki
tsiraba don sai ana taro ko biki qawaye sun taru
zan baje musu tabar gazan da kikai tace haba
hajia qawalli don allah kar muyi haka dake
wannanfa ba qaramin yarfi bane kiyi haquri
banson abinda zaisa mutuncina ya zube a idon
jama, a
Dashiya tace to naji amman da sharadi saikinban
wannan atamfar da abbakar ya dinka miki
kwanaki da sauri ta juyo tana kallonta azahirin
gaskia tanason atamfar sosai don duk cikin
kayanta tafisonta kuma sbd tsadar atamfar saida
suka kai ruwa rana kafin abakar yasai mata
Kuma bata dade da dinka kayanba don sawa uku
kawai tai musu amman babu yaddah ta iya dole
ta bata domin samun kwanciyar hankali don da
yawa a cikin qawayen nata sun dauka tanada ilmi
tayna miqama dashiya atamfar ta tashi tai gaba
inda tya barta da kuncin zuci na rabuwa da
atamfar tata sai takejinma dabatama fada mata
tabar gazan data afka ba
Watan tafin alhazai ya kama don wasu harsun
fara tafiyama hakan yasa su fanne aka sona shiri
taje taima babanta da yayyinta sallama amman
ta sananr dasu cewa itace ta biyama kanta ba
abbakar ba babanta yai mata addu, a gamida
nasihohi sosai sannan yace mata don allah ta
rage fadan da take da jama. A dimin kuwa
qasace xataje mai dumbin jama. A hade dayare
daban daban
A tanan da zasu tashi abakar ne ya rakata filin
jirgi lokacin da zasu tashin ba qaramin kukan
rabuwa da yarta momi taiba don tundata haifeta
yaune ranan farko da zasu rabu nadan wani
lokaci don hakanema yasa ta dauketa ta kaita
can wani gidan qawarta tace acan zata zauna har
saita dawo babu yaddah abakar baiba akan ta
kaita can vidansu wajen matan yayyenta ko kuma
wajen ummarsa domin kuwa baiga wani dalili
nakai yarinya can wani waje inda babu yan
uwanta na jiniba amman me fanne tai tsalle ta
dire tace ita batasan wannan ba abinda yasa taqu
amincewa shine bataso takaita can gidansu
wajen matan yayyenta daman sunada yara
qanana acan suyita gobje mata ya don nasan
bamai hanasu sannan tsanar umman abakar da
yan uwansa da tai yasa tace ba zatakai yarta can
ba don gani take kaman basason zamanta da
abakar din hakan yasa bata cika shiga
harkarsuba suma basa shiga nata
Amman ta tabbata yar tata zata samu kulawa
daidai gwargwado a wajrn qawarta hajia
hansatudon sun dade a tare akwaiqawance mai
qarfi a tsakaninsu
A ranan da jirginsu fanne ya tashi ranan taga abin
mamaki tun acikin jirgi ta dinga kauyanci tace
tab lallaine da ake cewa wanda ke zaune baiyi
kallo ba gaski masu kudi sunajin dadinsu ai wlh
nima kota halin qaqa sai nayi kudinnan kodan na
hucema kaina takaici
Cikin ikon allah akai aikin hajji aka gama sauran
dawo da ma aikatan aikin hajjin qasashensu to
fanne dai saidai muce allah e amsa ibadun nata
domin kuwa batasan komai na game da aikin
hajji ba ita yar abi yarima asha kidane ba
qaramin tsaraba taima yarta momie ba dan kusan
kudinta duk a sayayyar yar ya kusa qarewa
sannan taima qawayenta da yayansu suma
tsaraba mahaifinta da yayyanta da matansu
gamida yayansu amman abbakar kuwa ko hular
alhaji asallami dan banza bata siya masa ba
shida yan uwansa babu abinda ta siya musu a
matsayin tsaraba mahaifiyar abakar din kuwa ko
kallabi bata kawo mata ba dakinsu daya acan ita
da dashiya hakan tasa duk abinda zasuyi acan
din a tare sukeyi bayan sun dawo da kwana uku
ne ta fara bubbude tsarayba kai jama, a wanda
baida kunya yaji dadinsa a gaban idon abbakar
din ta gama rarraba tsaraban data kawo amman
ko ruwan zamzam bata bashiba wannan abu
damai yai kama ai koda ace bashine ya biya
mata kujeran hajjin nan ba kamata yai ace shi
zata fara yoma tsaraba don yafi kusanci da ita
amman ina saidai abin bai damu abbakar dinba
ko kadan sbd tuntun yasan bata daukeshi a bakin
komai ba ita kuma a nata wautar wai tasha
tsoronta yakeji shiyasa duk abinda tace masa
tana buqata yake mata kuma ta saki qafa tana
tsula tsiyarta a yanxu fanne ta gama tabbatar da
abbakar bazai iya sakintaba to inma ya saketan
aiba gidansa bane shine zai tattara yan
komatsensa yabar mata gidan sannan a duk
sanda yace zai qaro mata kishi wlh a ranan sai
anyi qaramin yaqi tunda ba gidansa bane kai
koma a wani gidan zai ajeta ba zata taba bari
abakar ya qaro aureba mutu ka raba ita dashi
domin kuwa ai itace tasha whlr zama dashi tun
baida komai sai yanxu da ya samu mai maiqo
shine wai wata zata shigo tace wlh na rantse
saina muzantawa duk wata mace datai gigin
shigowa gidannan kai bama itaba hardashima
abakar din saiya gane shayi ruwane ba, a
tabonibana nayi masifa inaga an shigo sabgata
Abinda kuwa bata saniba shine kullun sai jama, a
sun bashi shawarar qara aure ko wataqila allah
zaisa ya dace da mace ta kwarai a cikinsu harda
mahaifin fannen don yana sane da irin zaman da
suke amman abakar din yai biris da zancen
donshi gani yake kaman bazai iya ruqe mata
biyiba inma zai iya din baijin zasu iya samun
zaman lfy ita da fanne a gidan hayama ba, a
zauna lfy da utaba inaga kuma ace wannan
kishiyartace ai kullun an dinga tashin hankali a
gidan kenan masu ita magan na cewa zaman lfy
yafu zama dan sarki da ace kullun yana cikin
tashin hankali shida matansa kwara ya zauna da
daya inhar zai kasance cikin kwanciyar hankali
ballentanama ya tabbata fanne ba zata bari ya
qaro aure ba in kuwa kaga hak to saidai ian basa
tare ko kuma idan ya saketa abinda baya fatan
ya faru kenan don inhar ya saketa to bai cika
alqawarun daya daukarma kansaba
Inhar kaga sun rabu da fanne to saidai idan
dayansune baya raye amman har abada bazai
taba sakintaba saidai idan ita da kantane ta gaji
tace ya sauwaqe mata to sai yai mata abinda
take buqatan
Hajia fanne kenan tundata dawo daga hajji ta
zama cikakkiyar hajiya kuma naira suka qara
budema mai gidan nata tofa tun daga nan ta qara
bunqasa iya shegenta bata ganin kowa da gashi
hatta mijin nata gashi ta fara shafe shafen man
bilicin tayi wani fari kamar fatalwa sannan idan
zatai kitso sai an mata qari da atacment dukda
hakan ba kyau yake mata ba amman har yanga
take dashi
Ana cikin hakane abbakar ya kammala musu daya
bangaren na gidan nasu gamida canja musu fenti
gidan ba qaramin kyau yaiba flat ukune don haka
abbakar ya koma daya itama ta tashi ta koma
daya daga cikin sababbin tace tsohon zat
maidashi wajen sauke qawayenta
Dashiya uwar yan hadi tun da taga abakar yayi
flat uku ya koma daya fannema ta koma daya
don haka ta dinga zuga fanne akan ta tashi tsaye
inba hakaba kuwa sakiyar da ba ruwa zai mata
don tun da taga yayi flat uku to aure zai qaro
akullun fanne saina baki shawara akan mijinki
amman sai kiqi yarda wlh namiji bashi da tabbas
duk dadinki da namiji wataran sai yayi miki
kishiya muddun kika zauna kara zube ba tare da
kin nemi taimako daga wajen malamai da
bokayeba zauna garin kallon ruwa kwado yai miki
qafa idan kikai wasa kinaji kina gani matar zata
shigo ta dinga miki abinda taga dama idan kuma
kika takura ya baki rasit dinki takardar sallama
daga gidan kinga kin tashi a tutar babu kenan
tunda dake akasha wuya saida dadi yaxo sannan
wata zata zata shigo kenan tun wuri ki sake
tunani ki nutsu sannan kisan inda ke miki ciwo
yanxu lokacinkine kuma kinada damar yin komai
kar kiyi sake damarki ta kubce miki don daman
bature yace dama sau daya take zuwa
Hajia ki saki kudi kiga aiki da cikawa yanzu na
kaiki wurin wani boka mai suna lukum aikinsa
kaman yankan wuqa yake
Don na rantse miki saikin juya abbakar kaman
waina a tanda
Duk wani taurin kai da yake miki idan kin
tambayeshi kudi saiya dainaahi ke in tabbatar
miki inhar magani yaci kara idan kika aje kikace
karya qetara bai isa ya qetareba hatta harkan
kasuwancinsa kece zaki koma bashi umurnin
yaddah zai tafiyar da komai amman inkika tsaya
a haka to dan hakin da kika raina ina mai
tabbatarmiki da shi zaizo yana zokale miki ido
kixo kina kukan da baida amfani tunda kinbar gini
tun ran zane
Ai duk matan da kikaga suna yaddah sukaso a
gidajen mijinsu kuma su juya yaddah sukeso to
saida sukabi ta wannan hanyar ke bakyajin ana
fadin matambayi baya bata ba ne kuma qawata
wlh ba zaki tabbatar da abinda nake fada miki ba
sai nan gaba lokacin da zakiga kina juya mijinki
kaman yaddah kike juya tashoshin talabijin ki
murza naira a hannunki ki kerema sa, aninki wlh
qawata ni masoyiyarkice maison ganin kin
dauwama a cikin jin dadi kuma banso damarki ta
kubce mikine shiyasa kikaga ina baki wannan
shawarar a wannan lokacin fanne ta fara amanna
da abinda dashiya tazo mata dashi don a zahirin
gaskia itama tanason taga ta zama mace mai
fada aji acikin gidanta shiyasama batama abakar
din da sassauci idan abu ya hadasu don gani take
kaman hakan shi zaisa ya dingajin tsoronta
dukda sai ankai ruwa rana yake mata wasu
buqatun nata sannan takecin nasara wani
zubinma yaqi yaddah amman dole tabi hanyar da
dashiya zata daurata kodan ta magance matsalar
tata. Tai murmushi hmmmm abbakar ka kusa
shihowa hannu don saina juyaka yaddah nakeso
kuma zan iya kashe koma nawane don ganin
biyan buqatuna don daman masu iya magana ai
sunce saida kudi ake samun biyan buqatuuuuu
Sannu a hankali har dashiya ta koyama fanne bin
malaman tsubbu kuma ta fara ganin amfanin
abun domin a yanxu duk abinda ta tambayi
abakar din ba musu yake bata
Sai yanxu fanne ta qara tabbatar da maganan
dashiya ashe gaskia ne data sani aida tuntuni da
take fada take xijewa data amince komai da yaxo
mata da sauqi ganin nasarorin da take samu
wajen abbakar yasa fannen ta qara qaimi wajen
bin malamn tsubbu don ba qaramin kashe musu
kudi takeba kuma duk abinda sukace tai da sauri
takeyi ba tare da bata lokaciba don kawai samun
nasaranta
A yanxu kusan duk abinda ta samu a wajen
abakar a malamai yake qarewa shiyasama har
yanxu din ta kasayin abin kanta akace rashin
sani yafi dare duhu da fanne tasan duk asirin da
takema abbakar bai kamashi data daina jiqa
malamai da kudinta domin kuwa duk abinda taga
yana mata hakan ya samune ta hanyar budin da
allah yai masa don daman akace idan allah ya
buda maka saika gode masa harkar kasuwancin
tasace data qara bunqasa yasa shima yace bari
ya qara kyautatama iyalansa domin suma sunada
haqqi a cikin dukiyar mahaifiyarsa yan uwansa
dama wanda yake tare dasu kowa na samun
alkhairai a wajen abakar hakan yasa jama, a
kowa keson abakar din
Ba qaramin baqin ciki fanne kejiba idan abbakar
yai kyauta a gabanta kai koda kuwa yan
uwansane ita bataqi ace daga ita sai yartace
zasu dinga cin dukiyarba duk kuwa sanda yaima
wani kyauta a gabanta sai taji kaman tasa hannu
akai taita rafka ihu gashi ba daman tabi wanda
akaima kyautar ta kwace tace matsiyata kawai
lokacin da basu da komai waye yaxo ya taimaka
musu sai yanxune da allah ya buda masa sannan
za, azo a dinga manne mashi tace allah ita gani
take ma kaman abbakar bada guminsa yake
samun kudinnanba wlh domin bushashar da yake
dasu saika rantse kace shine yafi kowa tausayi a
duk duniya wasu lokutan idan anxo neman
taimako wajen abbakar din sai fanne tace bainan
ya tafi kasuwa idan kuma yan uwansane sai tace
musu yana barci kuma bai bada umarnin idan
yana barci a dinga tashinsaba koda kuwa waye
yaxo a haka suke haquri suna komawa
Saidai idan jama, a sun hadu da abakar din a
waje su fada masa abinda ya faru abin ba
qaramin cimai rai yakeba amman ko sau daya bai
taba mata magaba ba
Hakan yasa yan uwan abakar din basu damu da
zuwa gidan nasaba sbd wulaqancin fanne kai
hatta yan uwanta wanda suka fito ciki daya uwa
daya uba daya saida sukace mata ba zasu sake
zuwa gidantaba sbd wulaqantasu da take idan
sukaxo ta dinga binsu da kalllon raini hatta
dakinta bata bari su shiga saidai da zaran sunxo
ta shimfida musu tabirma a waje duk kuwa
buqatar mutum bata bari ya ahigar mata ban
daki wai kar suyi mata qazanta bayan a kullun
mai aikinta saita wanke bayin nata tatas sau
biyar a kullun
Lol
Uwar. Goyo
Chapter8
Lokacin da abban fannen yaji tabargazan da take
zubawa abinta hatta yan uwantama bata bariba
sai ya kirata gamida mata nasihohi akan
abubuwan da take din ba masu kyau bane koda
ace zataima wasu bai kamata ace yan uwanta na
jinima haka zatai musu ba kaman salihar arziqi
tace to shikenan baba na gode ta taahi ta tafi a
hanyarta ta dawowane ta dinga surutai kaman
zautacciya tace zuwa yanxu na fara gane shima
abbana ya shga sahun mahassadana tunda gashi
tun yanxu yana fadin inban a hankaliba bazanyi
kyakkyawan qarsheba harda wani fadin nabi
abbakar a sannu inba hakaba kuwa haqurinsa ya
kusa qarewa to ya qarw mana sai mene an gaya
musu ni inajin tsoron hukuncin da zai yanke akan
nawane idan har haqurin nasa ya' qare ko kuma
rasa mijin aure zanyi idan harya sakeni din a
yanxu yanda kaina ya waye idan har ya sakeni
suna zatan garari zan shiga banda qaddara da
kuma haihuwa ba yaddah za, ai na zauna da
abakar a matsayin mijin aurena wani kucaki dashi
wanda baisan tattaliba duk abinda ya samu
kashewa yake in banda wasu yan dalilai aida tuni
na takura masa ya sakeni ya kwashe
kwarmatsensa yabarmin gida don nasan yana
barmin gida bashi da inda zai koma shima ai
yasan da hakanne shiyasa yake bina a sannu in
banda inda wani buri a zuciyata wanda dole saida
aurensa zan cikashiba da wlh a yau dinnan saina
rabu daahi inga ta hassadan baban nawa adai juri
zuwa rafi don watarana tulun fashewa zaiiyi duk
wannan nasiha da mahaifin fannen yai mata babu
wanda ta dauka a ciki aban dakin nasa inda taji
anan ta zubar dasu tun daga lokacin ta daina jin
tsoronshi sam batajin tsoron gamuwarta ga allah
tun sanda baban nata ya kirata gamida yi mata
fada akan wulaqancin da takema yan uwan nata
tace daga ranan ba ita basu kuma duk sanda
suka sake zuwa sai tayi musu zagin qare dangi
sai kuma akai sa, a suma tun tafiyarsu sukai
alqawarin indai gidane na fanne bamai qara zuwa
a cikinsu koda kuwa garin sukaxo saidai idan ita
taje ta samesu
A lokacin data dawo tatas taima abakar akan
yanakai qararta gurin babanta wannan ai
munafurcine so yake ya hadata da babanta in
yaso yai mata baki ta lalace inba hakaba mai
takeyi masa wanda har zai kaishe zuwa gayin
qararta wajen mahaifinta in kuma gajia yai da
zama da ita ya gaya mata ba saiya tsaya yana
mata kwane kwane ba
Ko yana tsammanin idan ya saketa ba zata samu
mijin aure bane adama da takeda masoya
ballentana yanxu da ta qara sanin duniya
idanuwanta suka bude wanda basu kaitabama
suna samun mai sonsu ballentana ita ita?
Ta dora da fada masa
Kai bara na fada maka ni fanne nafi qarfin na
zamo matarka fin qarfi kawai akaimin a lokacin
aurenmu wanda baka wuce danxaikenabama nifa
matar manyace masu fada aji ko kuma masu
murza naira yaddah ransu keso ba irinka wanda
abu qanqani idan na nema a wajenka saika tsaya
kana jamin raiba duk wannan harigidon da kunfar
bakin da fanne keyi abbakar na kwance akan
gadonsa yana jinta ba tare da yace mata komai
ba harta gaji tai shiru domin idan da sabo yaci
ace ya saba shidai a iya zamansu da fanne bai
taba kai qararta wajen mahaifinta koda sau daya
ba koda wanine madai ya fada mata ya ganshi
wajen mahaifinta domin kai qararta to ya barshi
da allah ko kadan bazai bata miyon bakinsa
wajen fada ma fannen cewa ba shine yakai
qararta wajen mahaifintaba saidai baiji dadin
kalaman fataita faffada masaba don koba dadi ai
mijinta neshi
Shin yaushene fanne zata gane ta daina masa
abubuwan da tae masa ya dafe kai gamida cewa
shidai allah baisa yayi sa, an samun mace ta gari
ba haqiqa yasan allah ya jarrabeshi ta wannan
hanyar shiyasama a kullun yake addu, ar samun
cinye jarabawan da ake masa idan abokansa na
masa irin abubuwan da matayensu ke musu najin
dadi da karramawa sai ya dingajin inama shine
ke samun wannan garabasar ya dauki tsawon
shekaru yana da aure amman daidai da rana daya
bai tabajin dadinsaba gabadaya baisan menenen
dadin aure ba a yanxu tsoron halin matama yake
domin a tunaninsa duk irin halinsu dayane dana
fanne abbakar na mamakin rashin tarbiya irin na
fanne bayan yasan iyayenta sunyi iya bakin
kwarkwadonsu wajen bata tarbiya ita kadaice ta
fita zakka a cikin yan gidan nasu domin duk yan
gidan nasu babu wanda bai sauke qur, ani ba ga
ladabi da biyayyah ga duk wanda ya girmesu
Abinda yasa abakar ya qara tsanantar fanne sbd
rashin da, ar da take koyama mommy tare da irin
halinta da take koya mata har cikin ransa
yanason yarinyar domin kuwa jininsane kuma
akanta ya fara haihuwa koda ace nan gaba allah
zai qara bashi yaya itace gaba dasu amman sbd
halin uwarta da take daukowa yakejin tsanar yan
amman wani lokutan tausaya mata yake a bisa
halin data tsinci kanta na rashin samun uwar
goyo ta gari yaso ace fanne ta barshi ya bama
mommie tarbiya mai kyau sannan ya sata a
makaranta domin takoyo ilmi wanda shine
ginshiqin rayuwa daqar ya samu ya sata a
faramare nanma saida sukai qaramin yaqi domin
saidaya nuna mata bacin ransa amman da
kafewa taso tayi naqin son asa yarinyar a
makarantar babu yaddah ta iya dole ta barshi ya
sakatan amman duk sanda baya gari idan yaje
sarin kaya a legas ko kwatono to yar bata zuwa
makaranta kasancewar itama yar bada son ranta
aka sata makarantarba yasa uban ba tafia sarin
kaya zatacema uwar ba zatava fannen tace yi
zamanki yata damanni ba karatun nakeson kiyiba
salon kije aita dukarmin ke kamar jaka idan
mommie ta kawoma abbakar sakamakon
makarantar nata yakan bata lokaci wajen yin
mata fada akan ta dinga maida hankali ya kuma
nuna mata shi ilmi yanada amfani kuma ya zama
wajibi akan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login