Showing 15001 words to 18000 words out of 38754 words
mutum ya nemi ilmi na arabi dana
boko domin shi ilmi kinshiqine na rayuwar dan
adam mutumin da yake rayuwa babu ilmi shida
jaki duk daya suke gaskia ne
Admin yace/living without walking is dying
wethout nowing/
Don zai iyayin abubuwa marasa kyau amman a
wajensa yaga ai masu kyau ne mutum mara ilmi
komai nasa kai tsaye yake ba tare da tunaniba
hakanan ya dinga samun sabani da mutanen da
yake zaune dasu kenan sbd rayuwarsu ba zata
zamo iri daya ba momie a yanxune kikeda damar
yin karatu sbd ke yarinyace kwakwalwarki bata
da wani damuwa a cikinta wanda zai hanatta
daukar abu cikin sauri a cikinta zaki dinga daukar
karatu matuqRar kin maida hankali ina jiye miki
danasani marar amfani anan gaba haka abbakar
ke zaunar da momy wasu lokutan yaita mata irin
wadannan nasihan wasu ta fahimci abinda yake
nufi wasu ku ta kasa fahimta duk kuwa da
kwakwalwarta nadaukar abinda mahaifin nata ke
fada mata domin ta zaiyanema fannen amman
saitacemata karta sake ta dauki abinda yake fada
mata domin kuwa ba sonta yakeba shiyasa
yakeson dode mata kwakwalwa da shirmensa ya
maidata mara yanci
Cikin ikon allah arziqin abbakar sai qara bunqasa
yake hakan yasa dashiya ta hurema fanne
kunnecakan lallai ta takura mata yasai mata
mota itama ta shigo gari ai kuwa ba tare da bata
lokaciba ta tunkari abbakar da zancen siyan mota
baiyi niyar siya mata motarba amman takura da
naci kawai saidayasa yasai mata sbw dal ba
qaramin wahala yashaba kafin ya samu ta iya
motar don shine ke koya mata harya samu ta iya
amman ba sosaiba tundata iya kuma fanne tabar
zaman gida akoda yaushe tana gidan qawaye
kasuwanci sai soma habbaka yake yanxu abbakar
dubai da chaina yake zuwa sarin kaya kuma idan
ya dawo gida naija sari yake badasu su hajia
fanne an zama masu fada aji ganini kudin da
abbakar ya qara qawar fanne ta fara nemansa ta
harkar banza domin taci kudinsa ta ware dashiya
kenan dayaqi amincewane ta nemi suyi aure
nanma yaqi yarda lokacinda ba kudin bata nemi
suyi auren bane sai yanxu ganin tayi tayi ta shiga
malamai amman ba sa, a yasa ta sallama masa
mahaifiyar abakar dinma taso ya qara aure koda
zai qara samun haihuwa amman sai ce mata yai
tai haquri idan lokaci yayi zaiyi da yake uwar tasa
mai hangen nesace yasa bata takura masaba taci
gaba da yi masa addu, a
Tajia tsigala wato fanne kenan na cikin katafaren
shagon alfijir ita da yar tata idan baku mantaba
sai siyayyar take mata. Bayan ta bude jaka zata
biya kudin siyayyar da taima yar yata kenan
momin tace laaaaa mama ga baba shima yazo
siyan kaya
Hajia fanne takai dubanta inda momy ke nuna
mata wani irin jirine ya dibeta wanda har saidaya
kusa kadata abinda ta ganin saidayasa
idanuwanta suka daina gani nadan wasu sakanni
dishi dishi take ganinsu sannan zuciyarta tahau
harbawa da sauri da sauri gashi duk jikinta ya
mutu daqar taje iya daga hannayenta duk wannan
abu ya sametane sakamakon ganin mijinta da tai
abbakar kenan dauke da wata yar matashiyar
yarinya a kafadarsa gefensa kuwa wata tsaleliyar
matashiyar matace wacce a qallah ba zata wuce
shekaru24 a duniyaba tana duba wani takalmi
inda suke hirarsu gunin ban sha, awa ita dashi
hankalinsu kwance fanne ta qara qurama yarda
abbakar ke rungume da ita ido taga yar dashi tai
kama sak farinne kawai ta dauko na uwar tata da
yake shi abbakar din ba za, ace masa fari tas ba
saidai ace masa wankan tarwada amman matar
dake gefen tasa farace ta da ita kyakkyawa
Hirarsu suke cikin kwanciyar hankali don da
alamunma sun manta a inda suke sbd hirar zance
Fanne ta dingajin zuciyarta tana mata wani irin
tuquqi sannan sai tafarfasa take sauran kadan ta
fashe domin ta kumbura sosai ji take kamar zata
faso qirjinta ta fito ga kuma wani abu da yaxo ya
tokare mata maqogoro mai daci wanda ta kasa
hadiyewa yawun bakinta gaba daya ya qafe a
rayuwa ta tsani taga abbakar na hulda da wata
mace bayan ita fanne nada tsananin kishin da har
ya wuce gona da iri shiyasama bbata sake masa
fuska da zaran yaxo mata da maganan zai qara
aure
Sannan ta kashe kudi da yawa ga malamai da
bokaye akan su masa maganin da zaiya yaji bai
sha, awar qara aure tayi zaton aiki yaci kuma ta
rigada ta gama dashi ashe ba haka abin yakeba
daman ance munafuki bashi da kama a duniya
yanxu ashe abbakar munafurtarta yake neman
mata yake bata saniba? To ina gaskiyar tasa take
da a kullun idan ka tabashi zaice maka shi mai
gaskia ne?
Tun yammah tai dashi akan ya dauki momie
domin yaxo yai mata siyayyah a wannan kantin
amman yace mata baijin dadi kumama a gajiye
yake ba zai iyaba sai gobe har fushi tai amman
yaqi fir yace bazai iya zuwa yau ba
Da dare yayi abbakar ya fita sallar magrib
mommy ta dammi fanne akan su tafi kanti ko za,
a iya dacewa a samu irin kayan da takeso ba
yaddah ta iya dole ta dauko key din mota da
kyale tacema direba ya kaisu kantin alfijir ashe
akwai abinda zata gani wanda zai tayar mata da
hankali watoma abakar ashe karuwarsa zai kawo
siyayyah shiyasama yaqi yarda da abinda tace
tunda hakane wlh yau zan nuna masa nima
macece mai yanci wacce nafi qarfin namiji ya
wulaqantani wlh sai yayi danasani marar amfani
a cikin shagonnan saina kunyatashi tunda daman
ai hausawa sunce kunyar mara kunya asarace
Tana cikin zancen zucinne saiji tai momie na
fadin laaa momy abba zai tafi habawa tabajin
haka tuni taji wani qarfi yaxo mata nan take cikin
sauri ta isa inda su abbakar din suje tasha
gabansu ba tare da bata lokaciba ta dau hannu
ta wankama matar dake tare da abbakar din mari
kwarara har biyu ita kuma matar juyowa tai
domin ganin wanda yai mata wannan aika aikan
don marin ya shigeta sosai gashi kuma ba
zatonta hakan ya faru shiyasama ta shiga cikin
rudu a karo n ukune da ta daga hannu domin
kaima matar abbakar ya riqe hannun nata nanfa
ta shiga kokuwar kwacewa daga riqon da yai
mata don kuwa so take taima matar dukan tsiyar
da saita kwana a gadon asibiti kuma saita bata
wannan kyakkyawar fuskar wanda shine ke rudan
mijin nata da taga ba zata iya kwace hannun
nataba daga riqon da yai mata dinba don riqon
bana wasa bane sai kuma ta shiga surfa musu
zagi yan iska masiyata duk jama, an dake cikin
kantin kowa hankalinsa ya dawo kan fanne a
ranan abakar yasha zagi masifa kawai take tana
kumfar baki wasu dattijun matane su uku suka
shiga bata haquri tare da tausarta amman ina
batasanma sunayiba don idanunwanta sunrufe
sbd tsananin masifa daqar suka samu hajia fanne
tai shiru jikinta sai tsuma yake daya daga cikinsy
tace baiwar allah ba wannan matar ya kamata ki
dakaba a matsayinta na karuwar mijinki shi mijin
naki shine babban mai laifi akansa zaki dau
mataki kai kuma ka cika mata hannu tundacan
samu tayi shiru
Abbakar yacema matar kije ki shiga mota ki jirani
ina zuwa tanaji yace ds ita haka ta fice daga
cikin shagon cikin sauri sannan ya sake hannun
fannen yana saki da axama ta rufama matar baya
so take ta cin mata tun kafin su isa inda sukai
parking din motar matannanne suka biyo bayanta
tare da riqeta suna mata kalamai masu tausasa
zuciya ganin sun riqeta abbakar din shima ya fita
daga shagon yai wajen motar cikin azama yai
mata key suka bar wajen hajia fanne na fanin
abbakar yai wajen motar yai kukan kura ta
watsar da matan amman ina tayi rashincsa, a
domin kafin ta isa har sun bade wajen da kura da
gudu ta bisu kamanxsbn hauka amman ina sun
mata nisa a kan tit ta tsugunna ta daura hannu
akai tana rusa ihu direbantane ya qaraso gamida
fadin hajia yi haquri ki tashi mu tafi kar jama a
su taru kinga har wasu sun fara zuwa tambayar
abinda ke faruwa
Fanne ta tashi cikim jin haushin rashin samun
nasara ta shiga mota direba ya jasu suka nufi
gida
Haqiqa hajia fannne ta fusata matuqa wanda har
tama rasa irin hukuncin da zata yankema abakar
din idan ya dawo gida
To nima anan zan dakata domin barin hajia fanne
ta samu nutsuwar zuci mu hadu a book 2 donjin
yaddah ZATA KAYA
Crews. U nw wat?????
This is just de begining yanxu book din zai fara
ldan naga ruwan comment sai mu fara gobe
Naku har kullun
Uwar. Goyo Book2
Chapter9
Cikin moyar yadau shirur babu mai magana face
aheshsheqar kukan matarnan da fanne ta mara a
kantin alfijir tunda ta shiga motar take kukan
takaici wannan ai cin mutuncine tunda take a
rayuwa bata taba tozarta irin na yau ba idan ta
qara tunawa da munanan kalaman da hajia fanne
taita fada mata saita sake fashewa da kuka
Ayau tai nadamar kasancewarta da abbakar a
yaddah taga mutanen dake cikin kantin suka
gasgata kalaman da tai a kanta din don har wani
kallo suka dinga binta dashi wasu daga cikin
matan dake gefenta kuwa harda ce mata
Ammanfa kinji kunya dukda kyaun fuska dana
suran da allah ya horeki dashi amman ki kasa
gode masa sai kinyi karuwanci tirr da wannan
halayyah taki yarinya qarama dake kin bata
rauwarki kin shafama rayuwarki baqin fentin da
bazai taba gogewaba har izuwa kan yayanki da
jikokinki domin shi abin kunya ko mutum ya jefar
dashi sai yayi tattali ya sameshi ke kuwa baiwar
allah mai yada kika zabama kanki irin wannan
rayuwar mai yasa kika bari namiji ya yaudareki
ya hure miki kunne gami da bata miki rayuwarki
ki sani duk abinda namiji yai a rayuwarsa adone
ita kuma mace ya zame masa abin kunya da gori
a wajen jama, a ki tunafa duniya ba matabbata
bace ki tunafa duk iya tsawon rayuwan da mutum
zaiyi a duniya ne haqiqa kinyi babban kuskure da
kika biyema zuciyarki haqiqa son zuciya bacinta
ne kuma inhar kana biyema kyale kyalen rayuwa
to ba zaka taba ganin haske a rayuwarka ba yar
uwa ke yarinyace shiyasa kika yarda da zaqin
bakin da namiji wanda kuma ba tabbas ne dashi
ba tunda dai ga idanuwanki sun gane miki
gaskiya ga matarsa ta sunnah harda yayansu
amman ya barsu ya tafi wajenki kuma karkisa a
ranki wajenki kadai yake zuwa mutumin da ya
yaudari matarsama bare ke da kuke dadiro tana
kawowa nan saita sake fashewa da kuka harda
buga kanta a jikin kujeran mota yar dake tare
dasu a cikin motar mai kimanin yar shekara biyu
tai shiru tana sauraron kukan mom din nata da
alamun batama fahimci me kukan mamar tata ke
nufi ba
Shi kuwa uban gayyah goga na fanne ya rasa
meke masa dadi a cikin ransa zuciyarsa sai
harbawa take da sauri da sauri kirjinsa yai masa
nauyi maqogoronsa ya qafe yanason yai ma
matar dake zaune a kusa dashi magana amman
ya kasa furta komai ji yake kaman ansa kwado
an bame bakin nasa kwakwalwarsa tadau zafi
tunanine sukai masa yawa so yake ya samo
hanyar da zaibi don warware wannan matsalar
data kunno masa kai amman ya kasa samu yaya
zaiyi da rayuwarsa waccce kalma zaiyi amfani da
ita wajen gamsar da fanne cewa abunda take
zargi ba haka bane
Ya juya a hankali yana kallon matar wacce har
yanxu kukan take tausayinta ya kamashi a
rayuwarsa sam ya tsani yaga mace tana kuka
tabbad yau ya dibo ruwan dafa kansa ubangijin
sammai da qassai ne kadai zai iya kwatansa a
hannun fanne kodai yaje wajen mahaifintane ya
sanar dashi gaskiyan lamarin kai haba kar kayi
haka addu, a kawai zakaitayi har allah ya doraka
a kanta abinda wata zuciyar ta sanar dashi kenan
zuwa yanxu ya kasa zure jin kukan da take
domin kukan na shiga har cikin kwakwalwarsa ya
juya gamida cewa don allah ruqayyah ki daina
wannan kukan da kike kar yaje yaja miki wata
illar sannan kukan naki na qara sani shiga cikin
rudani ba kuka bane maganin matsalarnan
tamuba ruky addu, a itace kawai magani domin
itace takobin mumini kaman jira take abbakar din
yai mata magana saita sake fashewa da kukan
tare da cewa
Na dade ina tunani tare da taraddadin da tsoron
zjuwan wannan ranan a cikin zuciyata na sani
babi wanda yasan abinda zai faru a gaba sai
allah amman hasashe ya fadamin irin haka zata
faru koma fiye da hakan nasha fada maka cewa
ka fito fili ka fadama matarka abinda ke gudana
a tsakaninmu tasan gaskiyan lamari tun kafin
abinda kake boye mata ya fito fili hakanan duk
tsawon darw sai gari ya waye to gashinan tun
ba, aje ko inaba magananr da nake fada maka ta
fara bayyana dukda cewa a lokacin da nake fada
maka din baka dau maganar tawa da
mahimmanciba a kullun sai nai maka nuni da
cewa wannan abin da kake aikatawa ba qaramin
kuskure bane kuma matsalace mai girma ka
dauko ma kanka saidai muyi fatan allah ya kawo
mana ita cikin sauqi na tabbata zaka fuskanci
bacin rai da bakinciki kunar zuci idan har matarka
ta gano abinda ka tona rami ka binne
Uwar Goyo
Chapter10
Abbakar din yace mata abunda zamuyi shine mu
natsu mu koma ga allah sannan mu nemi hanyar
da zamu bulloma lamarin ba kukane maganin
wannan abinba mai afkuwa ta rigada ta afku don
haka saidai muyi fatan wannan abu daya faru
damu shine mafi alkhairi a rayuwarmu
Ruky mumini baya taba zama a duniya ba tare da
allah ya jarrabeshiba ni a yanxu na damune da
damuwarki wannan kukan da kike basonsa
nakeba ada idan nace dake banason abu to kin
dainayinsa kenan har abada amman gashi a
yanxu kinason nunamun ban isa dakeba kuma
duk maganganun dana fada miki sun tashi a
banza kenan mai yasa ruky kikeson daukan
halayyar daban sanki dasu bA? Yayi furucinne a
daidai lokacin daya juyo yana kallonta hannu tasa
tana share hawayen dake fuskar tata sannan ta
tsagaita da kukan
Da alamar wannan karon ta yarda da kalaman
nasa don haka tausayinta ya sake samun
mazauni a cikin zuciyarta ryky macece mai
sauqin kai tare da bin duk wani abu daya gindaya
mata shi yasa a kullun yake sake jin sonta a cikin
zuciyarsa tare da kwadayin zama da ita da ace
ita ya fara aure to da babu abinda zaisa yai mata
kishiya domin ruky ta hada duk wani abu da
mace ta gari takedasu allah yayi mata baiwa
nakyau tare da kuma kyan hali ga kuma tarbiya
da iya zama da mutane gata da kyawawan dabiu
idan mutun ya zauna da ruky na kwana daya sai
yaso ace ya rayu da ita a waje daya sbd tanada
mu, amula mai kyau da mutane
Sam abbakar ya mace da tuki yake kuma akan
kwalta yake don zuciyarsa ta lula wajen tunanin
yaddah zai bulloma fanne cikin ruwan sanyi ba
tare dasun daga murya maqobta sun jiyosuba a
kullun yana ganar da fanne illar daga murya idan
har abu ya hadosu amman bata sauraranshi don
wani lokacin idan ta fara azalzalin bala, in nata
har sai makwabtan sun shigo bata haquri wani
lokutan ma gidan nasu cika yake da yara da
manya suna kallin fanne tana masa tijara idan
har hakan ta faru kunya ba qaramin lullubeshi
takeva don daqar yake samu yana fitowa waje
don kunya amman ita ko a jikinta ko allah wadai
da wasu mutanen anguwan nasu ke mata bai
damunta balle ta sake halinta sanin kowane
zaman aure ya kunshi jin dadi da kuma kishiyarta
akan samu rashin jituwa a wajen ma, aurata
wanda har saiya kaisu ga rabuwa ko zuwa wajen
magabata a sasantasu duk wannan abu yana
faruwane a cikin sirri
Qarar horn din da ake ta kwada masa shine ya
dawo da abbakar din daga duniyar tunanin da ya
shiga kuma a sannanne ya tuna da tukin mota
yake kuma akan kwalta yake a sanda ya gama
dawowa hayyacinsane ya lura da abinda ke shirin
faruwa
Innalillahi wainna ilaihi rajiun ya furta da qarfi sbd
ganin da yai ya nufi kan wata babban mota
gadan gadan saura kiris suyu taho mu gama
shine direban motar ya dannama abakar horn da
sauri abakar ya murza kan motar gefe guda
domin ya kaucema dureban motar rashin sani yafi
dare duhu kuma idan ajali na kiranka saika je
ruky dake zaune a gefensa ta rafka tagumi tana
tararrabin abinda zai biyo baya kaman daga
sama taji abakar na salati da qarfi don haka ta
dago idanuwanta don ganin abinda ke faruwa
salati ta shigayi tare da kabbara a daidai lokacin
da taga suna gab da mutuwa tsoro ya shiga
zuciyarta ta juya da sauri tana kallon inda yarta
ke zaune khadija ita batasanma meke faruwaba in
banda wasanta da take da yar bebinta ruky tasa
hannu zata dauko khadijan kena sai motar tasu
ta daki wani rami dake kan kwaltar tai tsalle
gamida hantsalawa ta fada cikin wani kwalbati
kusa da kwaltan sannan kuma ta kama da wuta
allah yasa akwai mutane a wajen lokacin da
hatsarin ya afku kuma dare baiyi sosaiba ai kuwa
cikin hanzari suka taimaka wajen cirosu daqar da
sidin goshi akai asibity dashu kayan dake jikin
ruky sun rine da jini kafin a isa asibity a dalilin
jinin dake fita daga jikinta abakar kuwa jinine ke
fita ta baki ta hanci yar tasu ko cikin ikon allah
ba abinda ya sameta sai dan buguwa da tai
ganin hakanne yasa ta fara kuka tana kiran
iyayen nata don ta firgita gashi kuma bataga
kowa a cikin iyayen nata ba
Hankalun fanne data koma gida ya kasa kwanciya
sai jima tai gaba daya duniyar tai mata zafi ta
rasa inda zatasa ranta taji sanyi don haka ta
kasa tsaye ta kasa zaune sai safa da marwa take
a falon nata sai kace wacce ta hadiyi tabarya da
taga ba zata iya zaman cikin falon nata bane sai
kuma ta fito tsakar gida hankalinta a tashe yake
ji take kaman qirjinta zaiyi bindiga ga kuma
haushin matannan da suka riqeta a alfijir wanda
ta dalilinsune abbakar ya samu daman guduwa
da karuwansa mai yasama ta yarda har suka
riqeta kai amman wadannan mutanen sun cuci
rayuwata kuma sunmin abinda baxan taba
mantawa dashiba a rayuwa shegu munafukai
wata qilama qawayentane allah ya tsine musu
albarka yan iska masu kwacen mazan mutane
kurama qofar shigowa tai babu ko kibtawa jira
kawai take taga shigowan abbakar din domin ta
cakumoshi ta shiga nada masa katon katon na
masifa da bala, I irin wanda tai taba gani
kojinsuba tunda yake a rayuwarsa lallai namiji
bashi da tabbas kuma badan goyo da zani bane
shiyasa tun farko bata bama abbakar din fuskaba
kuma bata amince dashiba ballentana bashi
sirrinta ayau tayima abbakar tanajin bala i domin
kuwa yayi mata abinda wani mai rai bai tabayin
mata shiba tabbas tayi sakaci sosai da har ta
bashi daman da yake fita har yake neman wasu
mata a waje
Da wani ido zai dawo gidan ya dubeta bayan ta
gama gano abinda yasa a rami ya binne lallai ta
yarda abbakar kyan dan macijine dashi mugu mai
halin dan akuya ni ya ajeni a gida bagidajiya
wacce bata da gata shi kuma ya fita waje sai
sheqe ayarsa yake da karuwansa ko babu ko
kunyar idon jama. Ar gari ballentana yaji tsoron
haduwarsa da allah haka zaka ganshi kaman
mutum ashe babban dabba ne shege wanda
bazai iya haquriba
Gaskia momie batai sa, an uba na gari ba domin
kuwa ya janyo mata abin gori a gari ne a kullun
maganan abbakar shine naji tsoron allah na daina
abinda nake toshi tsoron allahn ne yasashi aikata
wannan mummunan aikin? Ni kardai acena yana
tare da wannan cutar da ake fada wanda idan ta
kama mutun har mutuwa to indai hakane
Abbakar ka cuceni kuma kaci amanar mahaifana
tunda ai amanata suka baka allah ya isa
tsakanina dakai shikenan inaji ina gani zanbar
duniya tunda sauran kuruciyata abakar bazan
taba yafe makaba akan abinda kaimin don
saimun tsaya dakai a gaban ubangiji
Lallai ya zama wajibi naje gobe dashiya ta rakani
muje a gwada jinina wlh inhar ya tabbata inada
cutar qanjamau to saina kashe wannan shegiyar
matar datai sanadiyar cusamin cutar kuma shima
zai yabama aya zaqinta dani suke zancen
Idanun fanne suka dunga mata gixo waiga
abakar can da karuwarsa akan gado suna aikata
masha, arsu da sauri ta tuntse idanuwanta wai
ba xata juri