Showing 6001 words to 9000 words out of 38754 words
don Ko cimar da take
acan batayi Anan bata samun kudin kashewa
dukda dai yana bata Amman ba koda yausheba
Amman da a dakin mijinta take duk yaddah za, ai
kullun saita samu kudin adashi don koda Bai
bataba to saita Zara a cikin na cefane cikin ikon
Allah hannun fanne ya wake sarai suka koma
sabon gida a ranan da zasu koma ta dinga
yabama matan yayyaen Nata baqaqen
maganganu babu Wanda ya tanka Mata don
idanda Sabo sun saba a yammacin ranan da zata
koman ba Wanda taima sallama haka Suma babu
Wanda yai Mata rakiya sukace yafi non fari don
daman barinta gidan suke buqata
Fanne ta koma gidan abbakar ne da waNi buri a
Ranta Wanda Tai alqawarin lallai saita cimma
wannan burin nata sannan zata samu kwanciyar
hankali
Sun koma basufi da sati biyiba ta farama
abbakardin qorafi akan lallaifa saiya siya musu
gida sun koma su huta da biye biyen gidan haya
da farko Qin biye Mata yayi Amman kullun cikin
mitA take akan lallai saifa yasai musu gida sun
koma
Don akwai raNan da da safe bayan ya gama
karyawa Zai tafi kasuwa ta tsareshi aqofa ta tare
qofar gamida fadin wlh ba zakafitaba abbakar
tunda dai kaqi saurarata akan buqatata nason ka
siya Mana gida saidai Yaga abin Nata bamai
sauqi Bane nan ya soma Mata nasiha gamida
fadin
Wlh fanne Banda kudin da Zan siya gida koda
kuwa qaramine kinsan shagon da nake Kula dashi
a kasuwamafa ba shagona Bane kayan wanine
nake tsarewa don haka Ina zanje na samo kudin
da zanje na siya Mana gida yanxu?
Wanda yai nisa baijin Kira maganganun da yai
Mata duk ba Wanda ya ahigeta Ita gani take
kamar bason siyan gidan yakeba inba hakaba don
kuwa bajintar da yake musu ko wani Mai kudin
baiyi a gidans Gani take kaman zaman gidan
hayanne bai isheshiba shiyasa baison siya
musugidan tace lallaima abbakar Gani kake kamar
Banda hankali inba hakaba tayaya za, ai kacemin
baka da kudin siyen gida bacin Ina ganin irin
maqudan kudin da kake shigowa dasu gida duk
sanda zaka tafi sari haka kuma Ai kace Kana jefa
adashe acan kasuwar gashi kuma kacemin mai
gidanka na baka alawance duk qarshen wata Ina
kudin suke tafia?
Abbakar kasan Allah na baka Nanda sati guda
kasai Mana gida mu koma in kuwa ba hakaba
wlh tallahi ruwama sai an tauna maka kaji na
rantse don haka idan kunne yaji gangan jiki ya
tsira
Uwar goyo
Chapter4
Tace wlh na baka nanda sati guda ka siya mana
gida mu koma in kuwa ba hakaba wlh ruwama
sai an tauna maka da yake yasan halin matar
tasa sai baice mata komai ba har sati guda taxo
ta wuce dadai taga alamun baida niyyyar yin
abinda take buqatar saita bullo da wata hanya
duk sanda ya dawo gida da zaran taga ya cire
rigar dake jikinsa zata lallaba ta zare kudin dake
ciki ta raba biyu ta aje masa rabi ta dauke rabi
idan yaxo yaga an dibar masa kudi yana
tambayarta zata haushi da fada tana fadin wai ya
maidata barauniya ta inda take shiga batanan
fitaba dukda yasan itadince amman saiya basar
kawai abu dai yaqici yaqi cinyewa har takaiga
kudin da yake zuwa sarin kaya dasu inhar zai
shigo da kudinnan gida tofa dole saita diba hakan
yasa ya daina shigowa da manyan kudi gidan duk
wasu bubuwa da zaiyi inhar na kudine to a shago
yakeyi ganin sauyin da yaine tace oho wato tanan
ya bullo lallai zai gane to tun daga ranan da
zarar ya dawo tun kafin ya zauna zata charge
aljihunan dake jikinsa sama da qasa ko nawa ta
gani a jikinsa saita zare abin na bama abbakar
mamaki ya rasa shin wai me fanne take da
maqudan kudin da take zara daga wajensane
shidai yaga ba sana, a takeba abinda bai saniba
kuwa wani adashi ta shiga na zubi kullun kai har
a cikin kudin cefanema ragetake inhar ya bata
kudin cefane raba kudin take uku tayi cefanen da
kashi daya sauran kuma ta tura a adashi
Wasa wasa saiga fanne ta samu kudin da zai iya
sawa tasai fili hakan yasa ta yanke shawarar
zuwa wajen babanta domin ya siyamata filin da
abbakar din tai niyyar va mawa ya siya mata sai
kum tace ina wlh bazan bashiba don har yanxu
ban gama yarda dashiba dagananne kuma tace
kodai yayyaina zan bamawa su siyamin can kuma
tace kai ina suma ta kansu suke ina basu miyar
gidansu zasu gyara su barni da kumfar baki
dagananne kuma dai ta yankr shawarar kawai ta
kaima daddyn nata don ta tabbata daddynta
baxai taba cin mata kudintaba a ranan da taje
wajen daddyn nata ko iznin abbakat din bata
nemaba ta tafi inda tana zuwa kuwa tai sa, an
samunsa yau yana gida bai fitaba vayan sun
gaisane yake cewa ahh yau su fAnne ne a gida
ince dai lfy tace lfy lau baba daman wata yar
mAgana nakeson muyi yace ina jinki nanta koro
masa zance gamida bude jaka ta zaro kudin ta
damqa masa yai shiru na wasu yan mintina
sannan yacecshi abbakar dinne yace ki kawomin
domin na saya miki fili? Tace a.a baba kawaidai
dacewar hakan na gani domin kuwa namiji bashi
da tabbas zai iya cinyemin kudin daga baya muxo
mu dinga rigima
Abban nata yai murmushi gamida cewa fanne
kenan wlh dukda ba tare nake da abbakar ba
amman na tabbata ba zai cinye miki kudinkiba
shine wandayafi cancanta daki tunkara da
wannan maganan gamida shawara don abbakar
mutum ne na gari nasan bazaiqi ci gabankiba
kuma hakanne ya qara tabatarmin da mijin naki
ba mugu bane don nasan duk wadannan kudin
daga jikinsa kika samesu kasancewar nasan
kedin dai ba sana, a kikeba
Don haka inaso ki koma gidanki daki nemi
shawarar mijinki kuma ina umartarki dakibi
abinda yace koda kuwa ya saba ga ke yaddah
kikesonne
BATAJIN dadin furucin abban nataba dukda kuwa
gaskia ya fada mata sai take ganin kaman
abbakar dinne yafi so amman ya ta iya dole tai
abinda yace din don tasan halin abban nata sarai
Tace to shikenab abba amman don allah kabar
kudin a wajenka inyaso idan na koma gida sai
nace kana nemansa idn yaxo saika bashi kudin ya
siyamin idan ka bashi kudin da hannunka zaifi
riqesu dakyau donni banso na bashine yaxo ya
salwantarmin dasu bayan saida nasha whl kafin
na samu
Yai murmushi gamida cewa to shikenan fanne jeki
karma kice masa ina nemNsa din zansa aimin
kiransa tace to na gode abba nandai ya qara
mata da nasihohi sannan ta tashi tai gaba don ko
matan yayyan nata bata shiga gidan domin su
gaisa ba ta koma gida abinta
Washe gari yasa akai masa kiran abakr din bayan
sun gaisane yake shaida masa abinda ke faruwa
murna abbakar din ya tayata sosai da mata fatan
allah ya sanya alkhairi sannan yace baba ai kaine
yafi dacewa daka saya mata filin don kuwa
dagani har ita duk a qarqashinka muke kuma
qasa dakai babu yaddah baiba akan abbakar din
ya amshi kudin domin ya siya mata amman yaqi
badon yasoba ya qaleshi ya tafi gamida tausaya
masa don yaga tsananin damuwa a tare dashi ya
fahimci abbakar baijin dadin zama da fanne ko
kadan saidai ance ai mai daki shi yasan inda
yake masa yoyo
Fuloti guda ya siya mata a waNi anguwa da babu
cikowan jama, a
Sannan ya kira abbakar da fannen ya shaida
musu gamida damqama abbakar din takardun filin
a hannunsa kaman jira take su fita suna fita tai
wuf ta kwace takardun tace bannan ai nima
nasan yaddah ake tanada tajardu kawai salon
lokaci guda kawai acemin fiki ya bata gabaki
daya murmushi kawai yayi yace fanne kenan
Tun kafin su qaraso gida ta fara masa maganan
gini yace kinada kudine isassu a wajenki? Donfa
kinsan aikin gini akwaishi da cin kudifa
Wani kallon raini ta bishi dashi sannan tace kana
nufin nice zan bada kudin da za, ai ginin to bari
kaji inma zaka dage damtse gara ka zage domin
kuwa sisina bazaiyi ciwon kaiba akan kayan da
za, a siya na aikin gidan
Kaiko kunya bakaji namiji kakkarfa kamarka ace
macece zata siya mata gida to wlh inma zaka
zage damtse gara ka zage ai namayi mai wuyar
da har na siya maka fegi
Tsugunne bata qareba saida fanne, ta matsama
abbakar lamma akan lallaifa ya fara gini a filinnan
domin su koma don kuwa badon yasoba ya fara
gini a filin a kuma shekarar ne alllah ya azurtasu
da haihuwa a ranan da fanne ta fahimci tanada
ciki a ranan batai barciba sbd tsabar murna
Kasancewar abbakar din bamai hali bane yasa
ginin bai tafiya da sauri gashi fanne tace irin ginin
masu kudi takeson ai mata don musamman
tajashi sukaje wata anguwa ta nuna masa wani
gida tace irin ginin takeso ayi gashi yanayin ginin
zaici kudi hakan yasa sai ai sati ba, aje ginin
gidan ba kasancewar gashi bamai qarfiba fanne
ta matsa masa lamba akan sai irin ginin masu
kudi ga sayayyar kayan haihuwa ga hidiman gida
abin duk ya taru ya cakude masa amman da yake
abbakar din jarumine yasa ko a fuska ba zaka
fahimci da damuwa a ransaba
Har yanxu ba, a gama ginin gidanba gashi cikin
fanne ya shiga watan haihuwa nanfa hankali ya
tashi
Don ita so take ta haihu a gidansu na kansu ba, a
gidan hayaba hakan yasa ta hurama abbakar din
wuta akan lallaifa yasa a gama ginin gidannan da
wuri tun abin baya damunsa har yaxo ya fara
damunsa ta matsa matuqa hakan yasa ya fara
fita ginin da kansa don daman da yana sacandire
yayi aikin leburanci sai yabar yaron shagonsa
yaci gaba da kula da shagon tun safe zai fito
yaxo ya fara aikin randa yakeda kudi ya dibi
jama, a aje shima ya shiga cikinsu aita aikin
randa bashida kudi kuwa shi kadai yake zuwa
aita fama donma wai allah ya taimaka ya gama
siyan kayan ginin kenan tun safe zai fita bazai
dawoba sai dare idan ya dawo ya kasa barci sbd
wlh sannan asuban fari zai fice abd rashin imani
irin na fanne ko dumame bata masa hakanan
yakeci da sanyinsa wai donma kar yunwa tai
masa illa kenan hannunsa duk sun kunkunbura
sunyi ruwa sbd tsaBar wlh. Lol
Uwar. Goyo
Chapter5
Saida tai fanne bata girl saidai ta saabinda ranta
keso taci bayan a kawai kayan abin cin wai ita ba
zata iya gikil ba sbd cikin dake jikinsa
Don wasu lokutan ko abincin darema batayi
saidai idan shi abbakar dinne ya dawo daga
shago yake girka musu ko a jikinta akullun idan
abbakar ya zauna yana tunamin yaddah rayuwa
ke tafiya saiyaji kaman ya daura hannunsa akai
yaita rusa ihu a kullun bai gajiya wajen yin ma
fannen addu.ar allah ya shiryeta kuma ta gane
gaskia amman shiru kakeijkaman an shuka dusa
a ransa yace ko tsaGoron jahilcin dake kanta ne
yasa har yanxu take ganin ita komai tayi daidaine
don a iysaninsa da fanne bai taba ganin ta saka
uniform bama balle ai tunamin zata makaranta
toma
To inama ta zauna kullun tana yawon bin gidajen
qawaye ai gulma anan a toni fada a can abinda
ta iya kenan
Duk wannan uwar wahala da abbakar Kesh a
fanne bata gani ita ga nima take bai qoqari tun
da gashi har e zuwa yanxu ba.a kammala aikin
gidan nasuba gaba daya bata jinjina masa da rin
qoqari da yake saidai ma idan ya dawone a
gadarance zata ce masa an gama ginin gidan
kuwa wanizubi yacemata tukunna dai wani lokaci
kuma idan abin ya tsaya masa arai ko kulata
baiyi
Idan hakan ta faru kuwa a ranan mitane da
rigima ya tashi kenan harma damai gorin
rashizuciya don ita ganinta rashin zuciyarsane
yasa har yanxu ba.a gama aikinba
Wannan rashin imani na fanne ba qara min bama
abbakar mamaki ya keba don kanta kawai ta sani
ta maidashi kaman wani bawanta data siyo da
kudinta a kasuwa duk tsadar abu inhar ranta
naso koda kuwashi abbakar din baiso tofa saiya
siya mata shi Sam bata lura da halin matsin da t
yake ciki ita a kullum abinda ranta ya raya mata
take yi gaba daya bata da Lissafi ballentana
Aje ga batun abinda zai amfaneta
Uwar goyo
Chapter6
Ba ruwanta ita burinta a duniya bai wuce taji dadi
kuma ta kasance abin kwatance a wajen
qawayentaba
Shiyasa a koda yaushe zaka ganta a cikim
kwalliya da shiga ta alfarma kaya duk tsadarsa
indai har yayi mata tofa saita matsama abbakar
yasai mata
Gata da qawaye kuma duk qawayen nata masu
kudine kuma gogaggun yan barliki kana ganinsu
zakasan babu Allah a cikin zukatansu
Abbakar da kansa na mamakin inda fanne ke
samo wadannan gogaggun yan barikin
Duk sanda wata ta haihu a cikinsu ko za. Ai mata
hidima to sai fanne ta matsama abbakar ya bata
maqudan kudade don takai gudunmuwanta a cikin
qawayen nata akwai wata da abakar yafi tsana a
cikinsu kuma duk ta fisu zuwa gidan nasu
malamace a wani asibiti kuma yar hakimin wani
kauyece gaba daya halinta yaxo daya dana fanne
a wani gidan biki suka hadu har suka kulla
qawance
Duk wasu halaye da fanne ke nunama abbakar a
yanxu ita take sata bata daukar maganan kowa
saina wannan qawar tata saude kenan jama, a na
kiranta da dashiya sbd munanan halayentane
yasa bata dadewa a gidan miji aurentake mutuwa
don a yanxu haka aurenta na bakwai kenan tana
shirinyin na takwas bazawarace kuma duk
mazajen da take aura masu hannu da shuini ne
munanan halayentane kesa a gidan miji akeyo
waje da ita ita ke kawoma fanne samfarin atamfa
duk tsadarta idan ta kawoma fanne sai tace mata
ta matsama abbakar ya siya mata don itamawai
ta dinga fasowa gari mutane su dinga bata
respect kullun itake zuwa yinma fanne awon ciki
don wani lokutanma anan takecin abinci duk
randa batazoba kuwa da zarar fanne ta kammala
girki zata zuba a kula ta umarci abakar akan ya
kaimata gidanta dake cikin asibiti
Abu dayane ta kasa rinjayan fanne akai shine bin
maza tayi tayi akan taja ra. Ayinta wajen harkan
bin
Amman firr taqi yarda don gani take kaman ba
zata samu fiye da abinda abakar ke mata ba
kumama bataso ana haka wani ya ganta yaje ya
shaidama babanta ta shiga uku don tasan halinsa
sarai babu yaddah dashiya ta iya dole ta qyaleta
amman gamida ce mata da kanta zataxo ta
amshi buqatar data nemeta dashi don namiji
baida tabbas kumama ai duk macen data maida
namiji uba to lallai saita mutu marainiya, inji
masu masu iya magana ba lol
Daqar dasidin goshi abbakar ya kammala bangare
daya na ginin gidan nasu wanda akai dakuna biyu
a ciki ko wannensu da bayinsa sannan da
bangaren kichin da sito ga makeken gate da yai
musu kaman sunada mota sannan yai fenti a
ranan da ya sanar da fanne cewa ai an gama har
anyi fenti ba qaramin dadi tajiba take ce masa
kaga gobe sai kawai mu koma don daman na gaji
da zaman gidan haya wlh
Koba komai ma samu kwanciyar hankali
Abbakar din yace a.a badai gobeba ki bari a
qarasa aikin gidan da kaina zan fada miki ranan
da zamu koma don akwai sauran yan aiyukan da
za. A qarisa amman fanne tace ina aiko ita
batasan wannanba ya za. Ai ita da gidanta
sannan ace wai sai wani yabata iznin tarewa a
ciki ba yaddah bai da itaba amman tai tsalle ta
dire gamida cewa ita batasan wannanba yakece
mata kingafa ko qofofi ba, a saka bafa na
winduna da qofofi a hakan kikeson ki koma ciki
tace wannan matsalarkace kaje kasan yaddah za,
ai a siyo qofofi a yau dinnan a saka gobe mu tare
ba qaramin fada sukaiba irinna wanda tunda
sukai aure basu taba yinsaba harsaidata kaisu
durkushewa a gaban mahaifin fannen fanne ce
takai qarar abakar din akan yaqi yarda dasu tare
a sbn gidansu gashi kuma ta kusa haihuwa don
ita tafiso ta haihu a gidansu bana hayaba
kasancewar tanason ai sunane na kece raini
wanda zai zama abin kwatanceca wajen
qawayenta wannan kai qara da fanne tai ba
qaramin qonama abakar zuciya yaiba yace wato
kenan shiba mutum bane da yai haquri na duk
tsawon lokacinnan da irin munanan halayyarta ba
tare da ya taba kai qararta koda sau dayaba sai
itace zata kawo qararsa akan wani abu da bashi
da tushe abinda bai taka kara ya karyaba ya
girgiza kai gamida cewa gaskia fanne sai gyaran
allah
A lokacin da abakar din ya iso gaban mahaifin
nata haquri baban nata yabama abbakar din
gamida cewa yai haquri su koma gidan tunda dai
hakan shine zai kawo zaman lfyrsu kuma idan
allah yasa kun koman koda ahankali a hankaline
sai kasai qofofin bai masa musuba yace shikenan
insha allahu zuwa jibi zan nemi motar da zata
kwashe mana kayan namu saimu koma abban
nata yace yauwa abbakar na gode allah yajiqan
mahaifinka kuma yasa ka gama da duniya lafya
yace amin sannan ya tashi ya tafi
A hanyarsa ta dawowane yake tunanin irin hali na
baban fanne gaba dayansa bamaison tashim
hankali bane gashi kuma kamilin mutum sai kuma
gashi allah ya azurtashi da tantiriyar yarinyar da
gaba daya bata tunanin allah zai iya daukan
ranta ko koda yaushe sheqe ayarta kawai take
tabbas allah yayi gaskia dayace ina fitar da
rayayye a cikin matacce sannan na fitar da
matacce a cikin rayayye
A ranan da su fanne suka tare a gidan sbd murna
har barci ta kasayi kwana tai tana zagaye gidan
taro tai sosai domin tayata murna da kuma
rakiya kusan duk qawayentane amman fanne ko
sallama bataima makwabciyaryaba wanda suke
zaune tare duk kuwa da quncin da taita turama
matar wai donma matar bamai son tashin hankali
bane kullun tana qofarta kai har saida takaiga
matar a qofar dakinta take girki sbd tsabar takura
mata da fanne tayi
Kwanansu goma da tarewa a sbn gidan nasu
allah ya azurtasu da diya mace ba qaramin
murna abbakar yaiba da samun kyautar da allah
yai musu ba qaramin hidima yaima mai jegon da
diyar tataba shima baban nata haka kai hatta yan
uwan nata suma ba, a barsu a bayaba kafin
sunane ya ari kudi yasai qofofi ya saka badon
komaiba sai don sanin halin matar tasa don zai
iya zama musu abin tashin hankali duk kuwa da
itace ta takura akan saisun dawo a hakan
Gidan kuwa kullun a cike yake da qawayenta su
dashiya sune akan gaba wajen aiwatar da
abubuwan da suka kamata don a gidanma yanxu
take kwana
Hatta kayan suna dashiyarce ta amshi kudi ta
shga kasuwa da kanta wai acewarta tafi abakar
din sanin kaya masu kyau da aminci itadai fanne
ido kawai take binsu dashi
Allah ya cika mata burinta nason samun haihuwa
saidai duk abin duniya ya dameta don kuwatun
washe garin ranan data haihu dashiya ta bata
kanwa tace ta shafe kan bre din nata dashi baYan
bayan wasu yan mintuna saita wanke sannan ta
fara bama yar tata nono tana aikata hakan yar
tata na kama bre din ya dare tun daga raNan ya
soma mata ciwo wai donma allah ya taimaka
guda dayane ba duka biyunba
A ranan suna an shagale qawayen mai jego sun
fiddah ita kunya don kaya sukai mata sosai ita
da babynta ta hannun damanta kuwa dashiya
makida da mawaqa ta dau nauyin daukowa
domin a chashe wuni ranan abakar baiyi a
unguwarba don bazai iya jurar ganin tabar gazar
da ake tafkawa a qofar gidanan nasaba sai kaga
mace da aurenta ta fito cikin jama, a tana kada
mazaunai babu kunya kojin tsoron allah lol
Ranan sunan raguna biyu abakar din ya yanka
mata kuma ya wadataya da abinci duk abinda
tace ya kawo saida ya kawo mata shiyasama
abinci suna ya wadatu saida kowa yaci ya bari
wasuma harda diba suna guzuri dashi masu
qaramin qarfi kenan sunandai sai san barka dukfa
wannan shagalin da ake ko loman abinci daya ba,
a dibama abakar ba hatta naman sunan da aka
soya ko yanka daya ba, a bashiba wakema ta
kansa ana hidiman biki da yake abakar din mai
haqurine sai ya maida komai ba komai bane allah
sarki admin kansa ya jinjina maka abakar
Taro ya tashi lfy ya rage daga fanne sai dashiya
da kuma tsohuwar dake kula damai jego don
daman abakar tun randa fannen ta haihu tace
masa yasan inda zaije ya dinga kwana don
dakuna yai musu qaranci saida komai ya lafa
sannan dashiya ta koma gidanta dondaman tunda
fannen ta