Showing 33001 words to 36000 words out of 123594 words

Chapter 12 - ALKIBLA COMPLETE BOOK By Safiyya Abdullahi Huguma .txt

22 Feb 2025

11862

hankali,ta maida karatunta sama kuma gaba da komai,saidai kuma duk da baka idan qaddarar bawa bata qare masa ba,tofa la shakka babu tsumi kuma babu dabara saita riskeshi.




*_ABDUL_YASAR_*




Matashin saurayi mai shekaru a qalla talatin,mai matsakaicin kyau kuma ma'aikacin banki dake aiki jahar kanon mu ta dabo,dan kaduna kuma,a fuskarsa yana da suffar kamala da hankali,wanda ya shigo rayuwar zahran a daren wata alhamis,qarfe takwas na dare sanda take kan dawowa daga gidan dinki bayan takai dinkin atamfarta sharada kan titin yahaya gusau,wanda a yanzu kusan da wahala ta shafe watanni biyu batayi sabon dinki ba,hajjanta ta tsaya mata,haka ma abban gwammaja.




Tun asali bata fiya son fitar dare ba,kada ma ace wannan unguwar zatazo,domin titin indai dare yayi akan samu qarancin zirga zirgar ababen hawa musamman na haya,saboda manyan gine gine dake cike a unguwar yawanci saidai motocin gida dake wucewa É—ai É—aiku.




Abinda ma yasa ta yanke taje din,ganin anyi gyaran titin na yahaya gusau din,hakan bazai bata matsalar dawowa gida ba,tunda tazarar dake tsakanin unguwarsu da unguwar bamai yawa bace,zata dawo da wuri.




Saidai kuma tunda ta fito titin adaidaitan data wuce basufi a qarga ba,su dinma akwai mutane ciki,haka ta soma takawa a hankali don rage tsayin tafiyar,gabanta na dan faduwa kasancewar titin akwai fitilun titi,amma basu da maraba da tirken awaki,tunda ba'a kunnasu bare su bada hasken da ake buqata,sai hasken gine gine jifa jifa dake bakin titin,da kuma hasken ababen hawan dake wulgawa.




Sai yanzu take jin hushin kanta me yasanya bata taho da dan rakiya ba cikin yaran gidansu?,tana tsaka da wannan tunanin wayarta ta dauki qara alamun kirane ya shigo,ta dago qwayar tana duba me kiran nata.




Hafsat ce,saita saki murmushi najin dadin ganin kiran 'yar uwartata
"Aini nayi fushi wallahi,babu abinda zakice dani" hafsan ta fada zahra na daga wayar
"Wayyo Allah na,me kuma nayi?"
"Au baki ma sani ba?,to bari na gaya miki,kinga na farko tunda mukayi aure zuwanki gidajenmu baifi a qirga ba,kowa qorafi yakeyi,na biyu kuma bani da lafiya,kowa yazo ya dubani,wasu sun kirani amma keda ya haidar baku zo ba banga kiranku ba,to wai don Allah meye marabarki da ya aliyyun ma?"
"Na yarda na miki laifi,amma ki daina hadani da wannan dagen....sannan kimin uzuri,rashin zuwa na gidanku wallahi hafsat makaranta ce,kuma kin sani,sannan lalurarki ni dana dawo babu wanda ya gayamin baki da lafiya"
"Eh ai saboda ansan ma ba zuwa zakiyi ba" murmushi tayi mai sauti
"Kiyi haquri....haba hansatuwa,aiba haka tsakaninmu,in sha Allah gobe ko jibi zaki ganni,kuma wannan karon bazan koma ba saina jewa kowa na kashe mitarku,ke ina tunanin ma da qyar idan ba strike za'a tafi ba wani satin,kinga idan hakan ta faru kwana daya daya zanwa kowa"
"Heee....na dai jiki kawai,a samu kizo dinma"
"Waima meya sameki?" Zahran ta fada tana qunshe dariya cikin salon tsokana saita dora da
"Kodai an gamu ne?"
"An gamu dake ba....idan kinzo kya gani"......




Tana tsaka da wannan maganar idanunta sukayi arba dasu,matasa ne su uku tsaye a gabanta sun tare hanyarta,saita sauke wayar da sauri daga kunnenta ba tare data samu sukunin yin sallama da hafsat ba
"Bani wayata!" Daya daga cikinsu ya fada cikin gadara yana miqa mata hannu,kai ka rantse da Allah wayar tasa ce,mamaki da tsoro ya sanyata tsaiwa tana kallonsu,daya daga cikinsu ya daka mata tsawa yana daga rigarsa ya zaro wuqa daga qugunsa
"Zaki miqo ko sai na farke miki ciki anan!" Kalaman da suka sake kadata kenan,ta miqa hannu zata basu wayar,dai dai sanda hasken mota ya dallaresu,ba tare da sun tsaya bi takan wayar ba suka ranta ana kare.




Tana tsaye a nan sannu a hankali motar ta qaraso,babban mutum ne a ciki,don ya kusa haifarta
"Garin yaya suka tareki?,maza ki wuce kibar wajen nan"
"To baba na gode" ta fada a tsorace tana yin gaba,saidai ko taku goma batayi ba taji magana a bayanta.




Tana waiwayawa sukayi arba dashi
"Karki tsorata,muje na rakaki,ina daga can baya na hangi meya faru" matashin ya fada,saita danji nutsuwa,don haka tabi bayanshi har suka sake gangarowa bakin titi sosai
"Al'ummarmu ta lalace ta zama wata irin al'umma,tarbiyya tayi qaranci,daba sata fashi da makami,garkuwa da mutane fyade da sauran munanan ayyuka,gaba daya su suka cika al'ummarmu suke mana barazanar rushewarta,gaba daya matsalar an rasa makamarta,saidai abu daya ne,duk wannan matsalar tushenta da asalinta gidan aure ne" kai ta gyada cike da gamsuwa,kalamansa sun dace da mutum mai hankali irinsa,wannan dalili ya sanya taji tsoron da takeji ya sake raguwa,hankalinta ya dan kwanta,daidai lokacin da wata adaidaita ta nufosu babu kowa a ciki ya tsaidata,sannan ya waiwaya yana tambayar zahran ina ta nufa tace mishi gadon qaya,shi kuma ya shaidawa mai napep din.




Sai data shiga sannan yace
"Abokina nima bari na zauna gefanka,tunda duka hanyace,idan ka sauketa ka qarasa dani tal'udu"
"To ba damuwa master,shigo mana" ya fada yana dan gyara masa gefansa.




Tunda suka shiga kusan zancan yadda arewa kullum ke tabarbarewa yakeyi,wanda wannan yana daya daga cikin abinda ke ciwa zahra tuwo a qwarya,wanda takejin inama ita marubuciya ce?,inama ace zata iya rubutu,tabbas da alqalaminta zai sauka ne tsakiyar arewa,kuma kan 'yan arewa,yadda muka share baki muna bacci har yaqi ya cimmana har saman gadajen baccinmu,yadda shugabanninmu da wakilanmu suka zama lusarai,'yan son kai da son zuciya,suka zama kamar aladu marasa kishin kansu ma bare na jama'ar da suke wakilta,indai zasu cika aljihunansu da kudi,indai ba zasu talauta ba,yadda muma muka zama masu matacciyar zuciya,muka saida mutunci qima daraja martaba da kwarjini irin na arewa da 'ya'yanta,kuma har gobe baccin muke ci gaba dayi,mun kasa tunanin kanmu,anata tsere mana ana mana fintikau,an raina mu bayan mun wuce raini,munfi qarfin raini da dukkan wani qasqanci,muna kashe junanmu,muna talauta kanmu,muna dakushe tattalin arziqin yankinmu,bayan mune ZUCIYAR NIGERIA din ma gaba daya,wannan shine babban tunanin zahra akoda yaushe.




"Wanne layi zaki shiga?" Taji ya tambaya,saita nunawa mai napep din har suka qarasa qofar gidansu sannan ta sauka,tana niyyar biyan mai abun hawan yace
"A'ah hajjaju ki barshi,inason in samu ladan"
"Na gode" ta fada kawai ta fada gida,don har yanzu tsoron data shiga dazu bai saketa ba,batasan sanda suka bar qofar gidan ba.




Sanda ta shiga gida ta gayawa hajja sallallami ta saka
"To alhmdlh da ubangiji ya tsare,shi yasa fa ba'a son fitar daren nan,shi kuma daya kawoki har nan Allah ya saka masa da alkhairi.....oh ni fatima,wannan lalacewar tarbiyya ubangiji yayi mana magani,shekara kusan saba'in a duniya amma baka daina ganin abubuwa iri iri ba" dariya zahra tayi
"Wa zaice kin shekara saba'in din hajja?,don dai kawai kinqi aure ne,kin dage sai a lahira idan kin hadu da tsoho alu"
"Kyaci gidanku idan na miqe na sameki,saina gwada miki tsohon qashi" zahran na dariya ta wuce dakinta,cikin ranta tana godewa Allah daya kubutar da ita,sai kuma ta tuna da mutumin da suka sauketa yanzun qofar gida,lallai yana da tunani mai kyau
"Allah ka gyara mana yankinmu dama qasarmu baki daya" ta furta a sarari tana cire daurin dankwalinta zuwa kayanta ma gaba daya ta fada bandaki don ta watsa ruwa ko zata ji dadin jikinta,kafin kuma ga fita ta nemi abincin dare,don tasan tuni gaje ta gama.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 13
*OUM DUFAIL!!*
_GIDAN ADO ƘAWA DA KECE RAINI_💄💅�


_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau'in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki gaba daya ZAHIRINKI DA BAÆŠININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_


*kayayyakinmu sune kamar haka*



FACE AND BODY SCRUB=2500(300ml)
Face and body mango butter=3k (250ml)
Face cream= 1800
Corretor oil/vitamin C oil=2k
Fairness skin lotion= 2500
Hot chocolate skin lotion 2500
Serum (for Nuckles )2k
Nuckles cream (stubborn)3500
Mix fruits Arabian black =soap 1800
Mix fruit glycerine soap =1900
Beetroot=1900
Coconut, milk,egg..face soap=1200
Lavender mix fruit soap =1800
Body wash =1500
cleanser=1600
Hair spray =700
Hair oil =1500
Hair relaxer =700
Hair butter 1700
Shampoo =1500
Breast=oil 2k powder 2k
Strech marks cream= 2k
Beetroot pink lips =700
Baby care soap glycerine=1k
Baby care butter =1500
Shea butter baby soap =700
Tsumin tula =2200
Tsumin zinariya =1200
Sliming tea =1500
Amarya set =25k
Liquid Arabian black soap =1900
Cleansing water =1500




*Ku dubamu a handle namu na Facebook da Instagram*
Ummu Dufail


*ko ta number wayarmu kamar haka*


07067943479


*_muna turawa kowacce jaha dake fadin nigeria da yardar Allah_*


*_INGANCI DA RAHUSA SHINE TAKENMU_*������
_____________________________






Kusan ta mance da abdulyasar gaba daya,don a qalla an kusa sati da wani yammaci akace ana sallama da ita,tayi mamaki sosai don a yanzu tasan bata da appointment da wani kan zaizo nemanta,har ta aika yaron tace masa yaje yace bata nan hajja ta tsaidashi,tace
"kace masa tana zuwa" fuska tadan bata tana duban hajja
"Nifa wallahi hajja ban san waye ba,da kin barshi kawai ya tafi"
"A'ah,ai baza'ayi haka ba,idan kuma shine mijin auren fa kika koreshi?" Saita dan buga qafa kadan tana turo baki,sannan ta miqe ta nufi daki.




Ganin doguwar riga ce a jikinta mai dogon hannu,kuma budadde ne dinkin babu ta inda ya kama jikinta saita sanya qaramin mayafi tayi rolling dashi sannan ta fito.




Yana jikin katangar gidan a jingine tayi sallama,da murmushi a fuskarsa ya dago yana amsawa,sai a sannan ta gane waye,saita dan sake masa fuska kadan suka gaisawa.




"Hala baki gane waye ba" dan qaramin murmushi tayi
"Na gane mana,sunanka ne kawai ban sani ba"
"Nima haka,ai anmin rowar suna,har muka rabu banji sunan malamar ba,shi yasa yanzu nayo tattaki nazo naji daga bakinta....nidai sunana abdulyasar......" Daga nan yayi mata bayanin kansa,itama bataqi ba ta gaya mishi sunanta,sannan ya gabatar mata da abinda ya kawoshi,ya kuma dora da cewa
"Ni da gaske nazo,kuma da gaske nake,ina fatan babu wani a gabana,kuma babu wanda ya rigani?" Murmushi kawai tayi ba tare data bashi amsa ba,dai dai sanda motar haidar ta danno layin,ta kuma qaraso gaban gidan,yayi horn mai gadi ya bude masa ya shige,da alama yau ya dawo yazo hutune kamar yadda yakanyi kusan duk qarshen wata.




Tasan halin ya haidar din duk da bata ga alamun ya ganta ba,amma gudun faruwar wani abu yasa tayi masa sallama ta shige gida,bayan ya nace ya amshi lambarta.




Kafin ta qarasa sassansu wayarta dake hannunta tayi tsuwwa,hindatu ce ke kiranta,saita dakata da tafiyar ta tsaya amsa wayar
"Ya akayi ne qawa?"
"Lafiya wallahi.....ya gida yasu daddy?"
"Lafiya lau,duka na barosu a gida bama tare"
"Ina kika tafi kuma?" Zahran ta tuhumeta tana dan tsuke gira
"Ba wani waje bane me nisa,lagos ne,ana bikin wata qawata....so akwai wani event da za'ayi a nan din" gyara tsaiwa tayi
"Amma fisabilillahi hindu biki a kasa yinsa a garinsu amarya har sai an dauki wani event din an kaishi wani gari me nisa haka?"
"Wanne nisa tafiyar jirgi?,yan mintuna marasa yawa anje"
"A ina kuka sauka kenan?"
"Guest house mana,muna da wanda muka sani ne?" Dogon tsaki zahran taja
"Kunnen qashinki shi zai sa mu raba gari dake hindu,tunda bakya yarda da abinda nake gaya miki" dariya ta saki
"Ko kin raba gari dani ni bazan raba dake ba.....karki damu,idan akwai wani abu ba dai dai ba daddy ko mommy xasu yi magana,ni kiranki nayi ma na gaya miki....gobe fa za'a je strike din nan,kuma sai baba ta gani sunce" bata rai zahra tayi
"Wato a duniya shi dalibin nigeria bazai taba gama karatu ta dadin rai farinciki ko walwala ba?.....ai shikenan,sun yiwa kansu,muma mayi azuminmu a dadi,Allah yasa sai an sallace za'a koma" dariya hindatu ta saki
"Wallahi nima haka nace,kinsan hali dai,idan ina azumi ba kanta,bana ganewa kwata kwata" saita kauda wannan zancan ta dauko na farko
"Yanzu yaushe xaki dawo?"
"Gobe in sha Allah...."
"Kin tabbata?"
"Da gaske nake....jibi ma zanzo har gida ki tabbatar da kanki,saka ranki a inuwa" daga haka zahran ta katse wayar,Allah ya sani tana qaunar hindatun,kuma tana da halaye masu kyau na kirki da son jama'a,amma rayuwarta ita a wajenta da iyayenta ba komai bane saboda tsabar wayewa,dukkansu bata zarginsu da aikata alfasha da maza,amma saidai yanayin yadda suke gudanar da rayuwarsu wayewarsu tayi yawa,irin wayewar da dole zata iya janyo maka zargi ga idanun al'umma,kuma yana daga cikin cikar kamalar mutum ya guji dukkan wani abu da zai jefa zarginsa a zuciyar al'umma,da wannan tunanin ta isa sassan hajjan,saita tadda haidar dofane a hannun kujera yana latsa waya,jikinsa wata fara qal din shirt ce ta maza mai V neck short sleeve,sai wandon kaki dake jikinsa,da wani farin qal din booth da yakai masa har qauri,hajja na zaune daga gefansa,da alama wata maganar takeyi dashi,shi kuma yana sauraronta,yayi wani irin kwarjini musamman yau daya bar iya wandon ma kawai a jikinsa,hakanan fatarsa tayi fresh tamkar babu abinda ke damunsa,saidai kuma fuskarnan tana nan kamar kowanne lokaci babu rahama ko digon dariya tattare da ita,sai gashinsa daketa glowing wanda ya qara masa kyau da cikar mazantaka.




Kansa ya daga ya jefeta da wani irin kallo,murya a dake yace
"Ke....zonan" da baya ta dawo ta zauna jikin hajja kamar zata shige cikinta,ya cira kai da lumsassun idanunsa dake cike da kwarjini yace yana duban hajja
"Ya akayi ta fita da wannan shigar?,waye kuma a waje data tsaya dashi?" Duban zahra hajja tayi sannan ta dubeshi
"Me ya samu shigar tata?,sannan idan saurayi yayi sallama da budurwa dama binsu ake a tsaya tare dasu ko kuwa?" Sai daya lumshe idanunsaya budesu sannan yace
"Amma hajja kinfi kowa sanin tsarina a kansu tun sauran na gidan nan ko game da saka qananun mayafai ko?,sannan haka sama taka ba'asan mutum ba yazo ya kirata ta kada wadannan zoqala zoqalan qafafun nata ta fita?".




Wayyo....ji zahra tayi kamar ya kwada mata mari,tunda take ba wanda ya taba aibanta surarta saishi,tasha ji a bakin maza daban daban yadda suke koda halittarta duk da ita ba burgeta hakan yake ba,ba kuma damuwa tayi dasu ba,shine yau shi don wulaqanci zai jefeta da wannan kalmar?.




Hajja kam baki ta kama sannan ta saki tana ruqo hannun zahran
"Karka sake gayawa jikata haka,a ciki ni banga abun laifi ba,indai ba daga bracck aka bata kama rai ba zaka zo ka juyeshi a nan ahto" qaramar ajiyar zuciya ya sauke
"Ke tashi ki bamu waje" ya fada cikin sigar bada umarni,saita miqe da hanzari,ta murguda baki bayan ta juya musu baya cikin ranta tana mita.




Sai da yaga shigewarta sannan ya dubi hajja dai
"Hajja....yarinyar nan,haka kawai kuka kaita universty,ke baki ganin sauyin dabi'u tattare da ita?" Hannu ta daga masa
"Haidar....haidar...me yasa haka ne?,ni babu wani abu da zahrata ta sauya dashi,kada na sake jin wani abu makamancin haka daga bakinka" wayarsa ya mayar aljihun unifoarm din sojojin dake jikinsa,sannan ya miqe a nutse
"Ina kuma zaka muna magana?" Cikin i don't care manner yace
"Akwai kaya da nakeso a fito dasu kafin na shiga ciki,don bazan samu fitowa da wuri ba....idan na fito ma tattauna" daga haka ya soma takawa da wata irin tafiya mai cike da qasaita da nuna qarfi da ginuwar gangar jiki yabar falon.




Sai a sannan zahra dake labe ta fito da hanzari muryarta na rawa kamar zata sake kuka tace
"Kinji ko hajja....kinji sharrin da yakeson yimin,ni ba'ace komai a kanshi ba saboda zaman bariki ba saini don ina makaranta"
"Kinga dagani....na gaji da wannan iskancin naku keda zaki,yara kamar mayu?,kamar masu ganin hanjin juna?,to wallahi idan bakuyi wasa ba aure zan saka iyayenku su daura muku naga qaryar iskanci" wani irin tsalle zahra dake zaune a jikin hajja ga buga kamar wadda aka dorawa kunama a jiki,ita kanta hajjan saida tayi sak cikin tsoron tana duban zahra dake fadin
"A'uzu billahi minash shaidanir rajim,hajja....wacce irin masifa kike ambata da yammacin juma'ar nan?" Ta fada idanunta duka a waje,tafin hannu kawai hajja ta saka tana rufe bakinta dashi tana fadin
"La'ilaha ilallahu,muhammadurrasulullahi,sallallahu alaihi wa sallam inna wuro?,kamar wadda tace miki tsohuwarki ta mutu?,wannan zancen ne masifa?,anya zahra?" Ganin yadda bacin ranta ya bayyana yasa ta sassauta nata,ta qarasa wajen hajjan ta zauna tana narke murya
"Kiyi haquri hajja,ba haka nake nufi ba,don Allah ki haquri,amma.in sha Allah na daina shiga huruminsa,dama ni ba shiga nake ba,shine haka nan ba gaira ba dalili ya matsantamin"
"Kema ai bajin magana kike ba,ko don kinga ina baki kariya?"kamar zatayi kuka tace
"kiyi haquri dai don Allah abar zancan,na daina in sha Allahu" shuru tayi kamar ba zatayi magana ba,sai kuma ta sake ajiyar zuciya
"Ai shikenan....Allah ya kyauta" jin haka don kada ta sake jan wata maganar saita miqe kawai tayi dakinta,a ranta tana juya zancan
"Itama.hajjan nan wani lokacin wlh tuburarriya ce,haka kawai da yammacin ranar juma'a,dai dai sanda ake amsa addu'a ki fadi wannan mummunan kalamin kisa 'yan amin su amsa?" Ita daya ta qaraci mitarta cikin daki harta haqura.




Da magariba zata gurin me gadi amsowa hajja goro da me gadi yace tazo ta amsa taga qofar gidan nasu cike da jama'a,kusan hakan ba sabon abu bane wajensu,duk randa aliyyu ya sauka a garin gidansun baya rabo da mutane,duk da cewa ko baya nan din ba'a rasa mabuqata jifa jifa masu neman taimako,amma kuma cikarsu bata kaiwa yadda take a yanzun.




A yanzun ma rabon kayan abincin azumi da alama yasa akeyi,don ga kwalayen kayan abinci nan kala kala da qananun buhun shinkafa,tabe baki tayi sanda taji wani yana zabga addu'a da koda layin duk da baya wajen,don baya zama a inda ake rabon,saidai ya wakilta ma'aikatan gidan
"Uban tausayi uban talakawan unguwar nan dama gundumar nan gaba daya,zuciyarka fara tas take hakama ayyukanka,ubangiji yasa kafi haka,ya qara arziqi da daukaka"
"Green snake....under green grass kenan" ta fada qasa qasa tana sake tabe baki,tana tsaye tana kallon yadda suke layi suna karba cikin farinciki,don mai gadin shima yana can,sai daya hangota sannan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login