Showing 45001 words to 48000 words out of 123594 words
Chapter 16 - ALKIBLA COMPLETE BOOK By Safiyya Abdullahi Huguma .txt
a dabarance yana qoqarin ku dinga hulda ta hada jiki romance da kissess amma kuma ko sau daya bai taba tunanin kiyi aure ba,ke koda ya taba tunanin hakan ko furtawa toba shakka na yaudara ne,daga sannan kuma kin samu babbar matsala,a haka da kike yawo dashi janna,cikin irin wannan shigar da wannan rayuwar kike tunanin zaya daukeki yakai gidansa a matsayin matar aure?,me zaya killace?,me zai burgeshi har yakai ga aikata hakan?,bakayi haka bama da sautayi a wannan zamanin ya kuka qarke dashi bare ace kinyi?,ni na isheki manuniya da ishara,kafin kice hisham ya yaudareki ya kamata ki fara cewa kin yaudari kanki,idan maganata ta miki zafi jannah kiyi haquri"sosai taga yadda jikinta yayi masifar sanyi,saita kasa cewa komai,sai dogon nazari da tunani data fada,bama ita kadai ba har hindatu dake kwance.
********** ******** ********
*_ƘADDARA....ta riga fata_*
Cikin sati sunyi CA sa yawa kamar yadda ta zata tun wancan satin,to satin gaba ma kusan akwai sauran tarin karatuttuka,hakan ya sanya kowacce ta sake haqura da zuwa gida weekend,saidai kuma sun shirya zuwa daya daga cikin masaukan baqi hotel don su huta a can a cewarsu.
Sanda suke shirya tafiyar zahra na zaune tana jinsu bata tanka ba,tadai yanke idan sun tafin gida zata wuce ko kwana guda ne ta rage ta dawo.
Saida suka gama hayaniyar yadda zasu gudanar da ranakun qarshen makon sannan suka soma raguwa sannan hindatu ta iso kusa da zahra ta zauna
"Amini....ko sau daya baki taba karar binmu bafa" kallonta tayi
"Ko sha'awa wajen banayi,me zai kaini nikam,kuma ina mamakin yadda kuka maida wajen kamar ba'a bakin komai ba zuwanshi" dariya sosai hindatu tayi
"Kinga,mufa mutanenmu ne suka yiwa wajen mummunan fassara,amma a qa'ida wajene da iyali ma suke iya zuwa su kama daki suyi dukka iya kwanakin da sukeso,su huta daga hayaniyar gida data jama'a,ni kusan duk qarshen wata bazan manta ba kafin nakai haka,sannan abubuwa basu yiwa daddy yawa ba muna zuwa muyi kwana biyu haka ko uku,ba wani abu bane me muni,saidai idan mutum dama da mummunar niyyarsa yaje,don Allah kizo muje wannan karon,sau daya dai tak" kai zahran ta girgiza
"Naji bayananki,amma am sorry bazan iya zuwa ba hindatu saikun dawo" ranta ta bata da alamun bataji dadi ba
"Shikenan....tunda baki yarda dani ba,komai kika fadamin ina qoqarin yi dabi,bana tsallakewa shawararki saboda nina aminta dake....na gode,dama sunatamin dariyar cewa ni kadai na damu dake,yau na gasgata hakan" saita sauka daga gefan gadon ta koma nata tana hada kayan da zasu je dasu.
Ganin yadda harta gama hada kayan bata kalleta ba dakin shuru yasa taji duk babu dadi,ba kaifi hindatun tana daukar duka shawarin zahran da qoqarin ganin tayi abinda zahran keso,da gaske taji haushinta kenan sosai,har ta isa bakin qofa zata fita zahran ta kira sunanta
"Haushi kikaji kenan?" Kafada ta daga
"Saboda me?,bayan baki yarda dani ba?,akanme zan takuraki kiyi abinda baki niyya ba" kaita kada tana murmushi
"Zanje....shikenan ko?" Cikin murna ta dawo
"Na gode sosai....ina mai tabbatar miki zakiji dadin tafiyar da zamuyi,gobe da kanki zaki ce muje" murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 17
*KIJI TSORON ALLAH ������,karki taba kayan da ba naki ba ba kuma mallakinki bane*
Ƙarfe hudu na yammacin ranar suka dunguma su shidda cikin motar gidansu hindatun suka tafi.
ÆŠaya daga cikin tsadaddu kuma qawatattun hotel sukayi masauki,suka kama daki guda babba wanda zai ishesu a wadace,itakam tana zaune daga gefe tana kallonsu yadda suka sake tamkar suna cikin gida ko cikin makaranta,ita kam har cikin ranta bata jin wani walwala ko karsashi ko kuma wani jin dadin zuwa wajen,sai take ji acikin zuciyarta duka wani irin babu dadi,sai takejin kamar ta aikata wani mummunan abu mara kyau,haka kawai takejin babu dadi har qasan ranta,har sai da farida ta ankara da haka
"Ki sake mana haba zahra,mu kadai ne fa a dakin,babu wanda yake shigo mana ko ya isa ya shigo" murmushi kawai ta musu,sai tabi lafiyar lafiyayyen gadon dake dakin tayi kwanciyarta akai,don kafin su fito tasha karatu sosai,tana son ta huta kafin ta sake dora wani,don ta taho da dukka litattafanta,har suna tsokanarta cewa ba hutawa zataje yi ba kenan,tunda ba zata bar qwaqwalwarta ta huta ba.
Suna ta hayaniya da walwalarsu har zuwa sanda akayi knocking qofar aka kawo musu abincin dare,kowa ya fara diban nasa duk da cewa akwai sauran lokaci kafin ma ayi sallar magariba din,hindatu ce ta dubi zahran
"Zahra....ga abinci,ki sauko kowa nacin nasa" kaita kada tana hamma
"Kai a'ah,sai an idar da sallah" daga haka ta sake gyara kwanciyarta,tun tana jin hirarrakinsu sama sama har ta fara daina jiyosu,babu jimawa kuwa bacci mai nauyi ya debeta.
Sanda ta farka hindatu ce kawai tayi saura a dakin,tana niyyar saukowa daga gadon tana duba agogo,qarfe bakwai da ashirin na dare,inda Allah ya taimaketa tana hutun sallah
"Duka ina suka shiga?" Ta jefawa hindatun tambayar wadda ke tsaye gaban madubi tana gyara sumarta da mayukan gyaran kai
"Duk sun fice,amma sun kusa dawowa"
"Fita kuma?,nan duka bai ishesu yawo ba?" Ta sake tambayar hindatun
"Nan kusa da inda muke nefa,aka bude wani sabon wajen cin abinci daxun,to na wani abokin farida ne,shine ya gayyacesu" baki kawai ta tabe,ba shakka duk inda wayewa tayi yawa matsala ce,su a wajensun wannan normal ne,ba wani abu bane,amma a asalin tarbiyyar malam bahaushe wannan din mummunar illa ce,saita miqe ta shiga toilet ta canza pad ta kuma daura alwala ta dawo ta zauna bakin gadon tana karanto azkar dinta na maraice da bata samu damar karantowa ba,tana yi tana duban hindatu daketa shiri da alama fita zatayi,batace mata komai ba har sai data ga ta daga waya tayi magana na 'yan mintuna ta aje,ta dauki mayafinta tana yafawa
"Ina kuma zaki kema?" Waiwaya tayi tana duban zahran
"Waya zamuje siya nida mudassir a glass show,minti talatin ta isa munje mun dawo" sosai zahran ta hade fuska
"Yanzu kina ganin kamata ce ki fita da saurayi takwas saura na dare siyan waya?,cikin motarsa daga ke saishi?"
"Babu komai qawata kada ki damu,ko a gida dana sanarwa mommy muke tafiya" maganar ta ratsata,batasan illar boko xallah ba sai yanxu,gaba daya duk wani abu daya kamata a kalleshi amatsayin abun qyama suba hakan bane a wajensu saboda rashin tasirin ilimin addini,saita miqe ta isa inda hindatun ke tsaye.
"Hindatu,a koda yaushe inason ki dinga tuna cewa kina rayuwa ne a qasar hausa,ina son ki dinga tuna cewa qa'ida da kwaikwayo kan tafarkin addini shine gaba da komai,na miki uzurin rashin tashi kan irin nawa bigiren,wala'alla har a zuciyarki ba komai bane hakan,amma idan baki sani ba bari na gaya miki illar.....akwai babbar illa a wajen 'ya mace ko ince ganganci wajen shiga motar wani da namiji,nasha maimaita miki wannan maganar....abinda yasa na nace mata shine,shiga motar da namiji ki yadda ya tuqaki shine mafarin komai,shine sila da dalili na faruwar komai,komai zai iya faruwa,idan nace komai ciki harda rasa budurcinki gaba daya....." Idanu hindatun ta qwalalo
"Ki yarda dani qawa.....wallahi ban taba zina ba,ban taba bada kaina ba" murmushi zahra tayi ta dafa kafadarta
"Haba hindatu....ta yaya zan miki wannan mummunan qazafin,amma idan kin kubuta daga zargina sauran mutane fa,kin isa ki wanke kanki?,akwai abubuwan da zaka dinga aikatawa da zasu iya ja maka mummunan zargi da zato daga mutane,zargi mai wuyar wanke kai,irin wannan rayuwar,ku kunsan bakwa wani mummunan aikin,amma shaidar da mutane zasu muku itace ku bana gari bane,idan kin shiga motarsa komai bai faru ba zaki iya kubuta daga riqe miki hannu da zaiyi?,zaki iya kare kanki daga yunqurin miki kiss ko runguma?,idan yaso cutar dake kin isa ki bawa kanki kariya?,sannan kome ya miki baki da hujja,laifinki ne,ke kika kai kanki hindatu" sosai jikinta yayi sanyi,ta daga kai tana duban zahran
"Gaskiya kika gayamin qawata,na kuma fahimta maganarki,sannan na gode miki qwarai da gaske,ban dauki hakan a wata babbar tawaya ba sai da kika nusashsheni,in sha Allah irin hakan ba zata sake faruwa ba" ta qarashe maganar tana cire mayafinta,sannan ta dauki wayarta ta tura masa tex ta koma ta zauna.
Daya daga cikin halayen hindatun da suke burge zahra kenan,sauqin kai da kuma saurin daukan shawara.
Tana zama saiga sauran suna shigowa,kafin kace me sun sake hautsina dakin
"Kai....kai jama'a,ku bakwa gajiya dan Allah da hayaniya?" Inji zahra da suka hana kunnuwanta sakat,dariya suka saka gaba daya jannah tace
"Kamar yadda baki gajiya da karatu ba" saita saki murmushi kawai tana gyada kai,tasan me hali dai bazai fasa halinsa ba.
***** ***** ****** *****
Washegari a daki dukka suka yini a tare,saidai da yammaci lis suka shirya dukkansu domin zuwa siyayyan kayayyakin amfani da kuma kallon wani sabon hausa film da za'a haska a film house cinema dake ado bayero mall.
Fir tace ba zata bisu ba,hakanan idan suka jima basu dawo ba saidai suzo suga ta tafi,basu ji dadi ba,saboda sunce ba jimawa zasuyi ba,hakanan bai kyautu su barta ita kadai ba,amma tace sam itadai sai sun dawo,hasalima akwai sauran karatunta da bata qarashe ba,haka suka shirya suke fice a motar jannah.
Karatunta taci gaba dayi,lokaci lokaci tana kallon tv dake aiki,saidai ba'a jima ba taji zaman ya gundireta,shuru hakanan babu kowa ba motsin kowa,don haka ta aje littafin tana duba agogo,dab ake da kiran sallar magariba,koda ta fita bata da matsala,tunda tana fashin sallah,don haka ta dauki mayafin doguwar rigarta ta yane kanta,sannan ta zira plate din takalminta daya dace da kayan jikinta,ta buda dakin ta fito.
A sama suke,saidai akwai qawatacciya kuma doguwar baranda ta bayan dakunan wadda zaka iya hangen farfajiyar hotel din idan ka tsaya ta jikinta,hakanan wanda yake qasa shima zai iya ganinka idan kaso,anan din ta tsaya,tana kallon yadda mutane ke kai kawo cikin hotel din kowa na sabgar gabansa,wanda yawanci duk wanda zai shigo ko ya fita cikin mota yake,da kadan da kadan take kallon wajen tana kuma karantar wasu abubuwa masu tarin yawa.
A qalla ta shafe kusan minti ashirin tsaye a haka har duhu yadan fara yi sannan taji tsaiwar ta soma isarta,saita janye idanunta da niyyar juyawa tabar wajen,saidai caraf idanun nata suka fada kansa.
Matashin saurayine fari sol,ma'abocin tsaho hakanan baida jiki,mai yalwar baqar sumar kai da kuma qasumba,sanyw da qananun kaya yana kuma tsaye jikin motarsa idanunsa fes bisa kanta,tsaki taja mai qarfi data lura da irin kallon qurilla da yake mata,ranta yana quna,tana fadi a ranta,wama yasan adadin lokacin da ya shafe yana kallonta bata sani ba.
Koda ta koma daki bandaki ta shiga ta sauya audugar jikinta,sannan ta dawo ta fesawa hannuwanta da jikinta turare ta koma kan karatunta,tanayi tana duba lokaci,saidai har yanzu babu su hindatun babu alamarsu,ranta ya soma baci,ta soma jin haushin kanta kan me yasa ta biyosu?,bayan gaba daya tsarin rayuwarsu ma ba daya bane?,yanzu meye amfanin zamanta a nan?,saita dauki wayarta ta soma kira.
Saidai duk wadda ta kira din tana shiga tana kuma ringing amma ba'a dagawa,babu kuma amsa,haka ta qaraci kiransu gaba dayansu babu wanda ya daga,zuwa sannan tara da rabi na dare agogo ke nuna mata,ga yunwa tana ji,duk da sun gaya mata taje tayi order din abinci a reception idan tana da buqata kowanne iri ne,to batason fita shi yasa bata karbo ba,ga wayar dakinsun daxu ta samu matsala bare ta kira daga daki a kawo mata,zuwa yanzu kuma yunwa takeji bata wasa ba,hakan yasa ya zame mata tilas ta fita ta karbo din kenan,saita sake tashi ta gyara yafenta ta kuma fito daga dakin.
Cikin tuqi mai cike da nutsuwa ya sako kai farfajiyar hotel din,hannunsa daya yana tuqin dashi,yayin da daya hannun yake amsa wayar cikin nuna girmamawa ga ubangidansa da gazo gani cikin hotel din,wanda ganawa ce ta sirri da zasuyi dashi gabanin taron qasa sa za'a gabatar na dukka ma'aikatan tsaro na qasa,kama daga sojojin sama dana qasa dana ruwa gaba daya,yanzun yana amsar direction ne na daki da inda zai ganshi,har ya qaraso wurin ajiyar motoci sannan ya ida wayar yana mai cewa
"Yes sir!" Sannan ya sauke wayar daga kunnenshi ya kasheta gaba daya,ya janyo aljihun motar ya zurata,sannan ya zauna na wasu mintuna yana karantar yanayin wajen a matsayinsa na qwararren jami'in tsaro,sai daya tabbatar komai na wajen yayi masa sannan ya bude murfin motar ya fito.
Duk wanda ya kalleshi saiya kuma,duk da cewa babu wata alama da zata nuna maka yanayin aikinsa,amma shigar da yayi da wasu shegun qananun kaya masu kyau da aji sun amsheshi,takawa yake zuwa reception cikin wata tafiya me cike da kuzari mazantaka da kuma karsashi,hannunsa daya riqe da key din motarsa,daya hannun kuma wata 'yar mitsitsiyar waya ce da yake iya rumtseta a tafin hannunsa guda daya.
Yana magana da daya daga cikin receptionist din sanda ta qarasa saukowa,a nutse itama ta tsaya saitin daya ma'aikacin wajen tana gaya masa abinda ya sauko da ita.
Cak ya tsaya da maganar da yakeyi,a hankali ya juya kanshi zuwa sashen da yakejin muryar na fitowa,daidai sanda itama qamshin turaren da take tsammanin ta sanshi,a kuma cikin gidansu ya soma shiga hancinta,har kuma yaja hankalinta zuwa ga kallon gefanta.
Ido hudu sukayi,cikin matuqar tsoro da razani taja baya tana kallon cikin idanunsa,yayin da shima ya kafeta da idanun yana mata wani kallo daya sanya taji kamar an maida qafafunta sama ne kanta kuma a qasa,tashin hankali da gigita suka bayyana tun daga zuciyarta zuwa saman fuskarta.
*_kuyi manage don Allah,yau nayi busy_*
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 19
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_
_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234Â 803Â 081Â 1300/+234Â 808Â 540Â 5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
_____________________________
*_BA ZATA!_*
_Baya da qura_
Tana tsaka da sallah sau biyu inna gaje na leqowa dakin da zummae ganin ta idar din?,a zuwa na uku ne ta sameta tana zaman tahiya,saita tsaya tana dakon zahran har zuwa sanda ta kammala ta kuma yi sallama.
"Uwar masu gida anason ganinki a falo" inna gajen ta fada tana duban zahra,saita saki addu'ar da takeyi tadan ja tsaki
"Anty uwani ko?,ni sam banison zuwanta gidan nan wallahi,haka kawai baka taka mata ba baka zubar mata ba ta saka maka idanu" kai inna gaje ta kada
"Ba ita bace,hajja ce....da alhaji babba" haka kawai taji wani faduwar gaba da batasan meye dalilinta ba,haka nan sai jikinta yayi sanyi
"Tom,ina zuwa" ta fada tana qarasa addu'o'inta ta shafa sannan ta miqe.
Tun kafin ta qaraso gabanta ke dukan uku uku saboda fuskokin data hanga cikin falon,abba babba abba yusuf,abban tsakiya haidar da kuma hajja,sai umminta daga gefe
"La haula wala quwwata illa billah" shine abinda take maimaitawa,take dukka qafafunta sukayi wani irin sanyi kamar ba zasu iya daukar gangar jikinta ba,hakan yasanya tafiyarta ta koma slow harta qaraso cikin falon.
Cikin girmamawa kamar kowanne lokaci ta gaidasu,suka amsa mata fuskar kowannne babu komai a samanta,ko kuma ace ba zaka karanto wani sauyin yanayi tattare da ita ba.
Shuru ne ya biyo baya na wasu sakanni,sa'annan abba babba ya soma magana
"Zahra'u..."
"Na'am abba" ta amsa cikin sanyi da raunin murya
"Mahaifiyarki tazomin da wani al'amari wanda yake da girma a wajenmu,bayan na saurari dukka bayananta da kuma hukunci da matakin da take buqatar a dauka.....nayi magana da aliyyu gashinan,na kuma ji duk abinda ya sani daga bakinsa,saina samu hajja na kuma tuntubeta game da lamarin....tayi mana bayanin komai itama,da kuma yadda kika gaya mata,saidai duk da haka mun nemi ta bamu damar yin magana dake,duk da cewa da farko taqi hakan,to a yanzu gamu gaki inna wuro,ina son ki dubi girman Allah ki gaya mana cewa shin da gaske a hotel haidar ya ganki?" Qas tayi da kanta,qwalla na taruwa cikin idanunta,kunyar kalmar takeji kamar qasa ta tsage ta shige,dana sani da nadama na sake cika zuciyarta,ta kasa