Showing 87001 words to 90000 words out of 123594 words
Chapter 30 - ALKIBLA COMPLETE BOOK By Safiyya Abdullahi Huguma .txt
Kai ta gyada,sotake kawai ya bata waje ta fita,amma a maimakon haka ma sai taji yana saka lock na jikin qofar yana rufe qofar,saita bude idanunta da sauri,sai kuma ta sake kauda kai,cikin rawar murya tace
"Pls....zanje wajenta....jira take" baiko bi ta kanta ba yayi gaba abinsa,ya bude ma'ajiyar kayansa ya dauko wanda ya dace da ra'ayinsa,ya dawo gaban mudubin yaci gaba da shiryawa,tilas taci gaba da tsaiwa tana jiran tsammani,saidai kuma ta bashi bayane tana duban qofa,hakan ya bashi damar qare mata kallo,lokaci lokaci,yana dubanta yana shiryawa.
Batasan ya gama ba duk da qamshin turarensa mai laushi daya addabeta,har sai data ji yana bude qofar sannan ta ware idanunta a hankali,sannan ta tako ta nufi qofar,dab da shi ta tsaya ganin shima yana tsaye bai fita ba,cikin husky voice dinshi yace
"Ko yaya iyayenka suka yanke maka hukunci,duk boren da zakayi kada ka yarda ka nunama duniya....aikata hakan kamar kana gayawa duniya ne how valueless they are",sai ya fara takawa yana ficewa daga dakin.
Magana yayi mata me harshen damo,saidai ta fahimceshi sarai,don haka tabi bayansa itama tana gyara yanayin fuskarta.
Ta taras suna gaisawa da nasreen din,daga yanda suke gaisawa kawai ya isa ka gane tana ganin girmansa sosai,cikin 'yar dariya kasancewarta mai yawan barkwanci tace
"Ai cewa dear nayi yazo muje dubiya....Allah yasa qaruwa muka samu" dan murmushin gefan baki kawai yayi,saidai ya maida dubansa ga zahra,sannan yace
"Wata qila,gatanan kya tambayeta" saiya miqe yana ficewa daga falon.
Dan tabota nasreen tayi
"Kai qawata daga zuwa kiransa yanzu fisabilillahi shine aka shanyani?" Murmushi tayi
"Ayimin afuwa...." Tun kafin ta qarasa tace
"Anyi miki....tun kafin boss yayi aure munsha yin gulmarsa nida dear...mun gode Allah ma da gidansa ke shiguwa,saboda irinsu ko.....basu iya qonewa a love ba,ki gansu a waje kamar gaske,amma a gida...uhmmm" dariya sosai ta baiwa zahra,lallai batasan ya haidar ba da bata fadi haka ba,batajin irinsu so na shagaltar dasu haka,amma saita share zancen kawai suka shiga wata firar.
Tunda ya isa farfajiyar gidan yaga tare suke da major ya sake tamke girarsa sosai,duk da cewa akwai saif a wajen
"Yallabai....irin wannan shanyamu haka?" Major ya fada yana washe baki,wani kallo haidar ya masa sanda yake bawa jafar hannu suna gaisawa,sai da yazo kansa sannan ya amsa mishi
"Da kasan kana da abubuwan yi da yawa ma da baka zo ba,incase nan gaba kaga irin haka ka dinga tafiyarka kawai" saif dai na danne dannen waya yana boye dariyarsa,shi yasan qarshen alewa qasa,don major ya dage ne kawai saiya biyosu,amma yasan haidar din bazaiyi maraba da zuwanshi ba,jin amsar daya bashin sai yayi shiru baice komai ba.
Daga nan inda suke tsaye haidar din ya qwalawa mai gadi kira,ya bashi umarnin bude guest room sannan suka dunguma zuwa ciki.
Zuwan dama ya shafi ayyukansu ne,tattaunawa zasuyi ta musamman,don haka kai tsaye haidar ya shiga abinda ya tarasu,don shi sam bai farinciki da zuwan major,shima daya lura da hakan suna gama maganar data tarasun ya musu sallama,yace yana da wani uzuri,akwai inda zashi.
Yana fita saif ya qyalqyale da dariya yana kallon yadda haidar din ya hada girar sama da qasa
"Mai master....wannan wai duka kishin ne haka?,lallai fatima ta ciri tuta...wannan so ba qarami bane" dashi da saif din duka sunsan magana yake gaya masa a fakaice,saiya masa wani irin kallo ya bude baki
"Sosai,ko laifi ne hakan?....akan me ma zaku daukomin wannan kwarton ku shigomin dashi gidana....kai J,haka ka hadoshi da matarka a mota daya kuka taho?" Ya jefawa jafar tambayar,bai amsa mishi ba shima illa danne dariyarsa da yakeyi,sai haidar din ya jijjiga kai
"Next time zan gaya mata,duk sanda zaka dauki wani qato a motarka to saika sama mata abun hawa,koka bata motar tayi driving ku kuje ku hau ta haya....kai kuma" ya nuna saif
"Ka kiyayi haduwarmu wallahi" saiya miqe yana ficewa don sawa a amso musu drinks.
Sun dan jima don basu tafi da wuri ba,sai daya sallamesu sannan ya koma cikin gidan.
Cikin sauri take kammale falon da kwashe kwanukan zuwa cikin kitchen,don bataso yazo ya risketa,nauyi yake sanyata ji haka kawai duk sanda suka hada wajen zama.
Kallo daya ya mata ya dauke kai ganin yadda ta zumbula uban hijabi
"Ki shirya jibi zamu wuce gida" ya fada sanda take qoqarin wucewa kitchen,daidai sannan wayarsa ta dauki ruri ya soma qoqarin cirota daga aljihu.
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin dadin zancan komawarsu,tayi kewar 'yan gidansu gaba daya,musamman yasira dake ranta,wadda sukayi sallama randa zasu koma haihuwa ko yau ko gobe,tana ta zuba idanu amma shuru bataji ance ta sauka ba,wayarta kuma ya rasa me matsalarta yau kwana uku taqi daukan layi,so take duka saita koma ta bayar a duba mata.
Sunan hajja daya gani saman wayar yasa ya samu waje ya zauna sannan ya daga wayar,a aladabce yayi sallama kana ya soma gaidata,saida suka gama gaisawa sannan tace
"Kai daga baka aron diyar mutane sai ka yiwa mutane dif?,an gaya maka haihuwar yasira yau kwana uku ba'a samunta a waya amma banji daga gareku ba,halama baka shaida mata ba.....to ka dawomin da jikata maza maza ayi taron suna da ita" ya soma gajiya da rigimar tsohuwar,yana ji cewa zai fara nuna mata shima dan yaune ko zata dinga shafa masa lafiya,don haka cikin dakakkiyar muryarsa yace
"Zamu dawo,amma ba yanzu ba"
"Me kace?,to baka isa ba,ai dama aro na baka,na taimaka wa wannam shegen baqin ran naka,wala'alla idan kanajin motsin dan adam kusa dakai ka rageshi"
"Nidai dawowa ba yanzu ba,matatace....kuma qarqashin ikona take" daga haka ya yanke wayar,saboda iya tsiya ma saiya kashe wayar gaba daya,yadda ko zata sake kira ba zata sameshi ba.
Yana sane yayi mata haka,kuma a niyyarsa a wasance ne,amma sai yaji zancan daya gaya matan ya zauna har cikin zuciyarsa,saiya tsinci kansa da yin mita shi daya
"Wai aro....kaman wani yaro" ya furta qasa qasa a fili,wannan karon shima sai yayi wasa da hankalin tsohuwar,zata ga dan zamani kuwa,da haka ya miqe ya dauki duk abinda yake buqata a falon ya wuce.
Har zai shige dakinsa saiya tuna hajjan ta gaya masa ba'a samun wayarta,don haka ya sauya akalarsa zuwa dakin nata.
Daga bakin qofar ya tsaya yayi knocking,ba'a jima ba aka bude qofar a hankali,fuskarta tarwai a hasken qwan dake corridor din,tayi rolling da wani pink mayafi saman doguwar rigar baccinta mai kauri da laushi data sauka har qasa,sosai mayafin ya haska fuskarta,qamshin turarenta na busowa tun daga cikin dakin da kuma wanda ke jikinta zuwa inda yake tsaye,saiya sauke boyayyar ajiyar zuciya,muryarsa tayi laushi qwarai qwayar idanunsa cikin nata yace
"Me ya sami wayarki?" Dan yamutsa fuska tayi wanda hakan ya qara mata kyau ba tare data sani ba
"Hakanan ta daina daukan layi"
"Me yasa baki gayamin ba?" Yayi mata tambayar dashi kansa yasan batayi ma'ana ba,qila hakanne ya sanyata yin shuru itama tana juya maganar,saiya waske da fadin
"Daukomin ita" juyawa tayi a nutse ta koma cikin dakin,yabi takunta da kallo.
Batayi koda minti guda ba ta qaraso da wayar,hannu biyun data sanya ta miqa masa yasa ya bita da kallo,garin hakan bai kula ba ya hada da hannunta,ta zame hannun nata da sauri sai wayar ta subuce zata fadi a qasa,cikin zafin nama ya tarota da hannu daya yana ambaton
"Bismillahi" dan ja baya tayi kadan,sai taga ya juya kawai yabar wajen ba tare da yace komai ba.
Maida qofar itama tayi ta rufe tana sauke numfashi,wanne irin taushi hannunsa keda shi haka?,take tambayar kanta,sai tasa yatsa ta dungure kanta da kanta tana fadin
"Shiga hankalinki".
_ZAFAFA BIYAR_🤙�🤙�🤙�🤙�🤙�
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 32
*M'S TREATS*
_BASU FITO BA SAI DA SUKA SHIRYA_
*_shin kuna da labarin m's treats?_*
*_idan baki dashi to su ake kira da KOMAI DA RUWANKA_*
*Domin kuwa sun hade dukkan wani abu da rayuwarku ke buqata*
*su gyara muku JIKINKU sannan kuma su gyara muku CIKINKU*
*_sun tanadar muku abubuwa kamar haka_*
*KAYAN QAMSHI DANA GYARAN FATA*
Smal halut
Sandal coconut
Janal banal
Arabian oud sandal bakhuor
Special kajiji
Sandal falake
Vip hawi
Sudanes sandal rose
Humra
White humra
Black humra
Kulakcca
Dilka soap
Whitening soap
*KAYAN SPICES*
Curry powder
Corriander powder
Tumeric powder
Mix spices
Ginger powder
Black pepper
White pepper
*SNACKS*
Samosa
Spring rolls
Meatpie
Cupcake
Birthday cake
Doughnut
*MAZA GWADA NEMANSU TA WADAN NAN LAMBOBIN WAYAR*
07061106161 *KO*
08099990056
*_ZAKU IYA ZUWA KU SAMESU A bayan northwest university layin gidan ruwan dish KANO NIGERIA_*
*_MUNA MUKU ALBISHIRI DA INGANCI DA KUMA RAHUSA_*
*hausawa sukace SAI AM GWADA AKAN SAN NA QWARAI*
_________________________________
Da kanta ta sanya hijabi ta miqawa maigadi nasu abincin,wanda ya amsa cikin farinciki yanata mata godiya,don ba kadan ba yaji dadin hakan,sannan ta dawo ta zauna tana cin nata abincin,lokaci zuwa lokaci tana kallon inda abun ya faru,tana tuna fuskarshi a sannan,sai ta dinga jin wani banbarakwai,don haka ta cuccusa ta miqa kwanon kitchen,sannan ta dawo ta kunna kallo bayan ta tabbatar yabar gidan.
Da daddare ma ita tayi girkinta mai lafiya,ta jere komai ta wuce daki,saidai har wajen goma na dare bataji shigowarsa ba,sai goma da rabi sa'annan taji dirin motarsa.
Tana kwance a daki tana iya jiyo motsinsa a falo,har zuwa sanda ya bude dakinsa ya shige,saita saki ajiyar zuciya ta tashi ta dauko maganinta tasha ta kwanta.
Ta zaci zatayi bacci ne da wuri,tunda batayi baccin rana ba,saidai kuma ina,haka ta yita juyi,har kusan sha biyu saura minti goma sannan ta samu bacci awon gaba da ita.
Shi dinma bayan yayi wanka ya saka kayan baccinsa saiya haye gado,yanajin gajiya kadan kadan cikin jikinsa,don tunda ya fita bai zauna ba,bayan sun gama meeting da manyansu kuma ya nemi zama da Battalia da yake jagoranta suka tattauna,babba kuma muhimmin aiki ne yake tunkarosu kan tsaron qasarmu,wanda yakeji a jikinsa da wahala wannan karon bai aje girma ko muqaminsa ba ya shiga cikin aikin da kansa anyi dashi ba.
Neman bacci yayi ya rasa,saiya dinga kame kamen abinda zai debe masa kewa,irin wannan yanayin na rashin zuwan bacci baqo ne a rayuwarsa,ya saba a duk sanda yaji bacci,kawai daya kwanta zai daukeshi,sai gashi yau zancan yasha banban,saiya dauki system dinsa yahau duba saqonni,har zuwa sanda yaji baccin da gaske,ya kasheta yayi addu'o'insa ya kwanta.
Duk yadda yakai ga jin barcin sai yaji kwanciyar babu armashi,ya soma canza position daga dama zuwa hagu,yana tambayar kansa ya akayi jiya yayi barci lafiya lau?,yau kuma abun ya faskara?,saiya tuna abinda ya farun jiya,da sauri ya kauda tunanin,ya dinga maimaita hasbiyallahu la'ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim,sannu a hankali yaji yana samun dai daito,bai dade da yawa ba baccin ya sureshi shima.
*_ASUBA TA GARI ZAHRA DA HAIDAR DIN HAJJA_*_MAGA WA ZAICI WASAN?_😜😜
Washegari ma tayi breakfast din,ta kuma aje masa ta shige daki,saboda sam batason haduwarsu,kallon dra lura yana mata ne bataso,nauyi yake mata da yawa,tana tsoron tsirfarsa kada ya lauya mata wani laifin,koya kwaba mata magana,saidai a rashin saninta ranar tunda sassafe ya fita,meeting din dai suke ci gaba dayi har sai sun kamo bakin zaren,batasan bai nan ba sai data fito wajejen la'asar zata dora girkin dare sannan ta ganshi,sai fita tayi dashi ta baiwa maigadi ya bayar,na dare ma data gamanan ta jere masa,saidai shi duk da ya dawo a makare kuma a gajiye bai fasa ci ba,saboda taste din yana masa dadi sosai.
Sai da safe xata gyara gidan ta gani,tayi tsammanin yau din ma ya fita da wuri,don haka tea kawai ta hada,ta soya qwai guda biyu ta hada da bread taci,saita gyara gidan,ta hada kayanta data saka zata wanke,don haka ta sanya t.shirt me qaramin hannu ta daura plain zani,hakan datayi saiya tuna mata da makarantar boarding,saita saki murmushi,ta tsaya gaba mudubi ta dubi kanta,ta tuna lokacin da bata fiya son shigar ba,saboda zakaga kamar ta saka pushup bra ne kuma ba ita ta saka ba,idan ma tayi shigar saidai tana maqale da hijabi,saboda baiwar halitta da qirar jiki da Allah yayi mata,sai suyita tsokanarta,shi yasa take zama da hijabin.
Barin gaban madubin tayi ta tattara kayan ta fice dasu backyard na gidan,inda yake da famfo da wajen shanya ta zubesu ta fara wankewa,babu jimawa ta gama ta fara shanyansu daya bayan daya.
A nutse ya fito daga dakinsa yana rufe bakinsa saboda hammae data subuce masa,ya dubi kan dining yaga wayam babu komai,sai yasa hannu ya shafi cikinsa,don yunwa yakeji qwarai,gajiya ce ta hanashi fita yau da wuri yadda ya saba,ya yanke kawai ya kwanta yadan huta zuwa azahar ya fita din,ganin babu komai akan dining din saiya juya ya shige kitchen.
Can ma wayam,saiya taka a hankali ya bude qofar da zata sadaka da bayan gidan don ya samu fresh air kafin yayi tunanin abinda zaici.
Itace ta farko da idanunsa suka fara gani,tana ta shanyarta a nutse,gefe da gefen zaninta duka ya jiqe,hakan ya sanya yabi jikinta ya lafe,ya bayyana shatin santala santalan cinyoyinta,t.shirt din jikinta ta zauna mata itama ta fitar da duk wata sura tata.
A hankali yakai bayansa ya jingina da qofar daya bude din,yana goye hannayensa a qirjinsa,ba tare da yasan me yake aikatawa ba yaci gaba da binta da idanunsa duk inda ta motsa,wani irin abu me qarfi da baisan meye ba yana fusgarshi zuwa gareta.
Ƙarar faduwar bucket daga hannunta shi ya taimaka masa ya dawo zuwa hayyacinsa,da sauri ya taka a hankali da baya ya koma cikin kitchen din,yana sauke ajiyar zuciya tare da jin dadi da bata ganshi ba,cak ya tsaya tsakiyar kitchen din,yama rasa wanne tunani yake,yasa hannunsa ya ranqwashi tsakiyar kansa,cikin zuciyarsa yana gayawa kansa me yake damunsa?,me yake aikatawa haka?,dogon tsaki yaja ya taka zuwa inda gas yake ya kunna ya dauki tukunya ya zuba ruwa,saidai kafin yakai ga zuba kayan hadin tea din ya lura da flask din tea dake wajen,yakai hannu ya daga sai yaji akwai a ciki,don haka ya dauki cup ya zuba ya jingina bayansa yana kurba a hankali.
A hankali ya dinga ganin motsinta na daxu cikin idanunsa,ba tare daya ankara ba zuciyarsa ta soma zayyano masa irin abubuwan da yake buqata tare da mace,kowanne tana haska masa shi cikin idanunsa,yana kaucewa da qarfin tsiya tare da qaryata kanshi da kanshi,ya dinga jan tsaki shi daya yana kokawa da tunanin.
Da hanzarinta batare da tsammanin akwai wani a kitchen din ba ta shigo,saita zabura zata koma da baya,daidai sanda suka hada idanu,saita tsaya cak na wasu sakanni,sanda taga ya dauke idanunsa ta fara shigowa ciki don ta wuce,zuciyarta na wani irin bugawa da yaqi daidaita.
Sake daga idanunsa yayi karo na biyu yana kallonta ta qasan idanu,kallon da idan duba daya kayi masa ba zaka zaci ita yake kallo ba,saika dauka a lumshe idanunsa suke,dab da zata giftashi tace
"Ina kwana" ya amsa qasan maqoshinsa.
Ji take kamar zata harde ta fadi,jikinta yana gaya mata akwai idanu a kanta,kamar ta zuqo qofar ficewa daga falon ta fice gaba daya,saidai kash!,dab da zata fita taji muryarsa a dake yana cewa
"Zo nan" haka kawai ya tsinci kansa da fadin hakan ba tare daya shirya ba,sai yaji baiso ta fice ne kawai,kamar tace masa zata qarasa daki ta dauka hijabi,to amma batasan me zaya fassara hakan ba,don haka ta sake juyowa ta dawo zuwa inda yake,dukka idanunsa na kanta da salon kallon qasa qasa mai kama da me bacci
"Hadamin breakfast" ya furta yana sake kurbar tea din hannunsa,ta zaci fita zayayi ya bata waje,sai taga ya matsa gefe kawai abinsa yana ci gaba da shan tea dinsa,daga qarshe ma sai yaja kujera yayi zamansa cikin kitchen din,sannu sannu kansa tsaye yaci gaba da binta da kallo duk motsin da zatayi.
Gaba daya duk sai ta rude ta daburce,sabida wani irin tasiri da idanunsa ke mata cikin jikinta,jikinta duka rawa yake,gani take kaman ba ya zakinsu ba,tun da can idan ya tsareka da idanunsa saika gwammace ya dakeka akan kallonsa mai nauyi,wani irin kwarjini ne cikin idanunsa,batasan me yasa ya tsareta haka da kallo ba,don haka duk aikin da zatayi saita dinga yinsa kwan gaba kwan baya.
Ta bangaren haidar kuwa haka kawai ya samu kansa da nazarinta,tun daga halitta zuwa yanayin aiki,shi kansa baisan nazarin na meye ba,amma ya kasa dainawa ko hana kanshi,har zuwa lokacin data sanya hannu zata sauke prying pan,wanda sam ta manta da ya kamata tasa wani tsumma ko safar hannu ta kitchen dake rataye kafin ta sauke din,sai ta saka