Showing 6001 words to 9000 words out of 123594 words

Chapter 3 - ALKIBLA COMPLETE BOOK By Safiyya Abdullahi Huguma .txt

22 Feb 2025

11845

tsakiyar kujerun,ya miqe dogayen qafafunsa ya kuma hardesu waje daya yana kadasu a hankali,kallon farko da zakayi masa zaka fahimci wani irin kwarjini shimfide saman fuskarsa,wanda ke cakude da rashin fara'a da kuma daurewar fuska,wanda ko a yanzun da yake zaune shi kadai cikin falon wayarshi qirar iphone 12 na tsakiyar tafukan hannayenshi dake saman cinyoyinsa yana amfani da ita fuskarshi a hade take,da alama gwanin iya tsare gida ne qwarai,gefansa kwanukan abinci ne a jere,bata sani ba ci zaiyi ko kuma baida niyyar ci ya ajesu ne kuma baxai magantu yace azo a dauke ba.




Kallo daya tayi masa ta tabe baki,duk da bata samu nasarar ganin fuskarsa ba sai sumarshi dake gyare,ita bamai yawa ba ba kuma saisaye ba,saidai tafi kama da saisayen irin sama saman nan,tayi wani spring kamar zubin indomie,baqa sidik tana sheqi,da alama ana bata kulawa yadda ya kamata,don ba qaramin qara masa kyau da kwarjini takeyi ba,ta kuma dace da kalar kwantacciyar skin dinshi da hausawa ke cewa wankan tarwada,ga duk wanda ya dubeta yasan ya samu cikakken hutu dajin dadi,duk da kalar aikinsa bawai na hutawa bane waje daya,saboda aikine na hidimtawa qasa,da bada kariya da tsaro wa dukiyar al'umma da rayukansu.




SaÉ—af saÉ—af take tafiya saboda bata da buqatar ya ganta,dab da zata gotashi ya daga kanshi,saida gabanta yayi mummunar faduwa,kallo daya tak ya mata ya maida kanshi ga wayarshi,kamar baisan Allah yayi wanzuwar wata halitta ba,tilas ta fasa qudurinta na wuceshi da tayi niyya,ta dawo da baya
"Ina yini yaa haidar" kamar bai jita ba,hakan ya bala'in ɓata ranta,ta tsani wannam halayyar tasa fiye da kowacce,ita idan zai shekara zaune a waje baiyi magana ba ba damuwarta bane,amma don me mutum zai gaidashi ya watsar.




Ganin bai amsa ba ya sanyata miqewa donta wuce abinta,sai a sannan ya magantu
"Lafiya.....zoki zubamin" ya fada ba tare da É—ago daga duban wayarshi ba yana mata nuni da fulasan gefansa.




Kamar tayi tsako don takaici amma tasan bata isa ba,wato saboda tsabar izza yana jiran wanda zai zuba mishi ne,akan ya zuba da kansa ya gwammaci yayita jira har sai mai zuba masan yazo,laifin bana kowa bane saina zahra,ita ta batashi,don tana fara zuba abincin ta tabbatar girkin ma nata ne,ita ta dafa mishi.




Tana wannan tunanin zucin naman data debo a serving spoon daya ya subuce ya koma cikin miyar,take ta fantsamo man dake saman miyar,ya kuma samu kyakkyawan masauki saman farar shirt din dake jikinsa.




Da sauri ya daga kai daga danna wayar da yakeyi,ya dubi jikinsa sannan ya maida idanunsa saman fuskarta,zallar bacin rai ta hanga qarara,ta soma motsa baki da niyyar yi masa bayani saidai ya rigata magantuwa
"U r very stupid....baki da hankali ne?...."
"Ashsha.....inna wuro garin ƙaƙa?" Muryar hajja ta ratso falon,duk rashin tsoronta amma sai da taji kamar anyi mata rahama,kafin ta bata amsa ta iso
"Tashi maza ki samo omo da dan toli fefa a goge mishi" tsaki ya saki kawai yana miqewa,ba tare da yace da kowa komai ba ya soma takawa yana nufar qofar fita
"Ka tsaya a goge maka mana zaki(haka takan kirashi dashi ita da wasu mutanen,sakamakon sunan mijinta da yaci,bata iya kiran sunanshi)"
"No,barshi kawai"
"Abincin fa?" Ta fada sanda yake gab da ficewa
"Ku amfaneshi"ya amsa a taqaice yana qarasa ficewa.




Bugu hajja ta kaiwa zahra wadda ke tsaye tana yiwa qeyarsa gwalo gamida murguÉ—e murguÉ—en rawa
"Ja'irah,hala kina sane ko?" Dariya ta saki tana zama gurbin daya tashi,wanda ke fidda qamshin turarensa ta soma sake bude kwanukan tana baiwa hajja amsa
"Inda ina sane ai da sai abun yafi haka.....arashi aka samu,kuma hakan yamin dai dai"
"Zahra....zahra....kinga ki fita daga idona akan yayanku,kamar ba jininku daya ba"
"To hajja ko kinfi sonsa yanzu a kaina ne?,babu inda nake sakewa fa sai nan,haka kawai sai nan dinma yazo ya zauna ya hanamu sakewa,idan na koma wajen ummi canma yana nan,da nayi wani abu itama ta hauni da fada itama,don ya girmemu kawai saiya damemu" daga haka ta jawo fulasan tahau zubin abinci Abinta tabar hajja da kallon ikon Allah"




"Allah ya shirya" hajjan tace tana sauke ajiyar zuciya kawai,bata amsa mata ba taci gaba da zurin abincinta.




Salma ce tayi sallama cikin falon tana tsaka da cin abincin,sanye da atamfa dinkin A shape,sai dan kwalinta data zarga a kanta,hannunta riqe da qaramar wayarta me keyboard itel,wanda akafi kira da rakani kashi,kusan dukka gidan zahra ce me waya torching,ita dinma sai da aka hau rimin gafiya kafin a samu lamuncewar oga kwata kwata haidar ya barta da wayar,a hakanma bisa goyon bayan hajja,saboda abban gwammaja ne ya kawo mata,ita kuma tace sam ba za'a watsa masa qasa a idanu ba,tunda wayar bawai wata babba bace can,sannan uwa uba an hanata walwala an dauketa an kaita makarantar kwana aiko ba'a hanata riqe waya ba a duk sanda tazo hutu,tunda hutun ai baya wuce wata guda kacal,uwa uba kuma ma rashin riqe wayar yafi riqeta yawa,hakan yasa dole aka barta da abarta.




"Lalalaaaa......lallai zahra.....wannan ba kwanukan da naga yaa xahra nata fadin tashin hadawa yaa haidar abinci bane?" Sai data kai lomar qarshe na hannunta sannan ta daga kai ta dubeta
"Sune mana....kema idan xakici bismillah,zoki zuba iya zubunki" kamar wadda ta danawa wuta a jiki salma ta janye gefe da sauri tana kada hannu gami da fidda ido
"Lalala,bada ni ba saa lallen karya,inason lafiyata wallahi,haka kawai ina lallaba jikina kisa amin shaidar da xanje kabari da ita,kedai da kika shirya tarar aradu daka"
"Ba zakuci bama,kema wanda kikaci shi kadaine rabonki,tunda kika hanashi ci kema baki ci,yarinya ta zauna ta bata lokacinta saboda yaro amma a qarshe kuta yiwa aikin,to baku isa ba,ko ruwan lipto yace ku dafa masa sai kunyi qorafi,kada ma ke inna wuro kiji labari" cewar hajja,tana kaiwa qarshe ta soma qwalawa gaje kira,zahra ta mele baki
"Ko iya haka ma alhmdlh" dai dai lokacin gaje ta qaraso,hajja ta sanyata ta debe kwanukan tana ci gaba da mita,xahra ta miqe tana kakkabe jikinta
"DaÉ—ina dake hajja baki iya samun magana daya ba.....muje sister ki bani labarin daxu"
"Zakici ƙaniyarki,zaki dawo ki sameni,nasan da wanda zan hadaki" ta fuskanci sarai me take nufi,amma tasan ba iyawa zatayi ba,don idanma ta hadata dashin ƙarshe sai tafi kowa mita da jin ciwon hukuncin da za'a matan.




Saman carfet din dakin suka zauna,salma tadan dubi hafsat dake baccinta haiqan
"Shegiya kasa,bata da aiki sai bacci" ta fada tana zungurarta,idanu tadan bude kadan,ta gane salma
"Ki saurara min 'yar baqincikin baccin mutum" daga haka ta cusa kanta qasan filo tana gyara kwanciyarta su kuma suka shiga hirarsu
"Wai kinsan meke faruwa kuwa?"
"A'ah saikin fada" inji zahra
"Sabon kamu fa nayi" sosai zahra ta maida kallonta ga salma
"Kamar yaya?,sabon kamu bayan sulaiman din?" Farr tayi da idanunta
"Wallahi,kuma a yadda nake jinsa a raina zan iya hada matsayinsa dana sulaiman" idanu dukka zahra ta fiddo waje
"Keee salma.....kiji tsoron Allah,sulaiman din?" Kai ta gyada kai tsaye itama tana dubanta
"Shi dinfa,meye abun naji tsoron Allah a ciki?,igiyar aurensa ce a kaina koko yaya?,don kawai na zabawa raina shi a matsayin wanda raina ya amince na nuna duk lokacin da aka buqaci na nuna wanda na tsayar?" Kai zahra ke kadawa kawai dama da hagu cikin nuna zallar jimami
"Gaskiya nidai bazan iya ba,haba amana ai bata ce haka ba".




Dariya sosai salma ta saki har tana toshe baki kana daga bisani ta tsagaita tana duban zahra
"Amma inna wuro na yadda lallai boarding ta dakusar da duk wani wayo da basirar da muka sanki dashi,wai ce miki akayi su samarin yanzun tsoron Allahn sukeyi?,ko ce miki akayi idan don saurayin yanzu yana gaya miki da nuna miki daga ke babu wata.....idan bake ba sai rijiya,kece rayuwarsa da sauransu yana nufin hakanne da gaske har a badininsa?,bance miki fau fau ba'a samun wanda hakan bane.....amma sunyi qaranci qwarai,da yansu maqaryata ne,maha'inta ne,basu da *ALƘIBLA* qila kece ta bakwai kota goma a wajensu,hakan yasanya nima bazanyi saki na dafe ba,na laru dashi shi daya ina masa son gaskiya da dukkan zuciyata da gangar jikina ba.....na shafa rana guda naji wayam" ta qarasa maganar tana bugun cinyarta.




Shuru zahra tayi nadan wasu sakanni tana nazari a zuciyarta,sam maganar salma bata samu mazauni a zuciyarta ba,hasashene kawai irin nata da kuma son baiwa kai mafaka,banda haka ita shekararta nawa da nuraddeen bata taba ganin wani abu tattareshi dashi koda sau daya bane makamancin wanda salma ke hasashe?,a kullum soyayyarsu qara gaba take,kishinta yake kiyaye bacin ranta yake,don me zata yarda da zancan salma 'yar tamore
"Nikam bazan iya wannan kwamacalar ba" zahran ta amsa mata bayan takai qarshen nazarinta tana tanqwashe qafafunta waje daya,qaramar dariya salma tayi
"Eh....kekam taki zuciyar na daÉ—e da sanin cewa daban take,kinayin soyayya ne dakkan yaqini da amannarki,wanda a yanzun samun hakan yayi qaranci daga wajen mazan har matan" kusan hirar da suka dinga yi kenan a tsakaninsu,wanda har ya kusa kaisu ga musu.




Saidai basu ja da yawa ba dakin ya soma cika da 'yammata,hakan ya sauya akalar hira suka shiga hirar sabgogin da suka shafesu,kamar qawayensu na unguwar dana islamiyya wadanda aka kawowa kudi da wadanda aka sawa rana,jarrabawar qualifying da suke fuskantarta,candy da zasuyi nan gaba da kuma aurensu da sauran hirarraki da ba'a raba 'yammata dasu.




Duk da wannan hirar da ake amma hankalinta nakan wayarta lokaci lokaci,tana tsumayin nuraddeen kowanne lokaci,amma saidai har suka tasamma watsewa saboda lokacin É—ora girkin dare yayi a kowanne sashe,kasancewar kowaccensu duk da akwai masu aiki É—ai É—ai a kowanne sashe amma ba'a barsu sun zauna sun ta'allaqa komai a kansu ba,babu nuradden ba duriyarsa,don haka ta jawo wayarta ta miqe da ita tana tunanin zuwa wajen yaa zahra ta tura mata updated watsapp,don nata yayi expair.




Ci gaba da hayaniyarsu ta hira suke har suka zo zasu gifta ta ma'ajiyar motocin gidan.




Dukkaninsu sun hangeshi,duk da cewa bayanshi kawai suka hango amma babu wanda bai ganeshi ba cikinsu,saboda haka kowacce taja bakinta ta saisatashi gami da rage sautin muryarta.




Sanye yake da wata farar riga ƙal me gajeran hannu,wanda hakan ya baiwa murɗaɗɗen dantsensa damar bayyana,sai dogon wando shima fari gamida wani farin booth dake qafarsa,daga inda kake wucewa kana iya jiyo qamshin lallausan turarensa da iska ke kwasowa tana bazashi ko ina,ba kayan dazun bane a jikinsa,da alamu ma wanka yaje ya sake ya sauyasu saboda miyar data batashi,waya yake amsawa,kallo daya zaka masa kasan cewa yes!,aikin da yake yayi matuqar dacewa dashi,ko shafawa kayi kasan cewa shi din SOJA NE.




ƙasa ƙasa zahra taja tsaki cikin ranta
"Da wannan kayan yafi kamata ma ace jikinsa ya ɓaci dazu naga ta qaryar gayu da ƙyanƙyami" ta qarashe maganar tana fitar da tsakinta a sarari dai dai sanda ta hangi ya musty na qarasawa inda yake tsayen bayan ya baro wajen me gadi wanda da alama wani saqo ya bashi.




Suna gab da rabuwa kowa ta shige sashensu ba tare da sun ankara ba sukaji muryar ya musty na nufosu yana fadin
"Yaa haidar na magana fa 'yammata" dukkansu babu wadda cikinta bai murÉ—a mata ba,yusra da tafi kowa tsoro cikinsu cikin rawar murya tace
"Wa yake kira a cikinmu?"
"Dukanku" ya bata amsa yana qunshe dariyarsa,don basu ba,hatta su da suke maza ba kasafai kiran haidar ke musu daÉ—i ba.




Junansu suka kalla,yusra ta sake cewa cikin qas qas da murya don kada ya jisu
"Amma me kuma muka yi masa ya musty don Allah?"
"Idan kunzo kwaji" daga haka shima ya juya abinsa don kada yayi laifi.




"Kome zai mana ai bazai rabamu da numfashinmu ba ko?,kuzo muje" inji hafsat qanwarsa wadda suke uwa daya uba daya,zahra ko tabe baki tayi,duk da cewa ita dinma a tsorace take,haka suka nufeshi sum sum kamar waÉ—anda suka É—auko gawa.




Gaba daya su bakwai din suka zube gabanshi,yayin dashi kuma ke tsaye abinsa yana latsa waya kamar baisan An haliccesu wajen ba.




Saida suka tsammaci ya manta dasu a wajen,sannan ya buda baki kamar wani saraki ya jefo musu tambaya yana ci gaba da latsa wayarsa
"Wace inna wuro a cikinku?" Tambayar duk saita zo musu wani banbarakwai,tunda sunsan dai duk wanda ya kwana ya tashi cikin gidan ya san me sunan,hakan yasa suka kasa amsashi suka hau kallon kallo.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 04


*KIJI TSORON ALLAH������,KADA KI TABA KAYAN DABA NAKI BA,BA KUMA MALLAKINKI BANE*
___________________________


*Assalamu alaikum warahmatullah, shin kintaba amfani da turaren gashi a matsayinki na mace data amsa sunanta idan amsarki aa toga dama tasamu *awwaba scent* *tazomaku* *da turaren fesawa a gashi natural 100% organic *wanda akahada rose water da essential oils tripped action gashi yy kamshi yay kyali kuma moisturiser at *the same time ba anan abun yatsayaba duk wanda yy order zaahada masa da freshener kala hudu ta daki *ta bandaki ta Mopping da turaren wanka a kan kudi 3,000 kacal indai q cikin watan September dinnna ne daganan kuma zasukoma *normal price dinsu, hakanan turarukqn wuta da humra dinmu anyi masu ragi duk me bukata se nememu a 08034236800 ta what's app kokuma ya ziyarci shafinmu a instagram* *@turare_by_awwaba mungode*
_______________________________






Sake maimaita tambayar yayi a karo na biyu dai ba tare daya kallesu ba,sanin hali yasa suka fara yunqurin nunata kawai,saidai basu kai ga aikata hakan ba tsawarsa ta mamayesu wanda ta rudasu,ba shiri kuma suka nuna zahra dake tsakiyarsu.




A hankali ya dora birkitattun idanunsa dake cike da kwarjini irin na cikakkun maza a kanta na sakan daya kana ya janye yana cewa
"Itace ta dawo yau daga boarding ba?" Haushi tambayar tasa ta bata fiye data dazun,baqo ne shi,ko yau ya soma zuwa gidan nasu,tuni suka amsa masa da eh
"Good" ya fada yana kashe wayarsa ya zurata a aljihun wandonsa na baya,idanunsa dake ladabtar da mutum na bisa kanta.




"Daga dawowarki yau shine kikeson maida mana qofar gida tasha?" Ya jefa mata tambayar da batasan amsarta ba,hakan yasa tayi shuru tana nazari,tare dason gane me yake nufi da hakan
"Am asking you!" Ya kuma fada cikin tsawar data dan razanata,wannan karon bai jira amsarta ba ya dora da
"Wato kaiko boarding da akayi baisa komai ya canza ba ko?,su samarin da sukazo suna son mana tumasanci qofar gida duka ina kika sansu kina kulle cikin makaranta?,koko malaman naki ne soma biyo sawunki?,duka duka shekarunki nawa?tun baki tafasa ba zaki qone?,to i wil deal with u,bazan dauki wannan iskancin ba tun baki riqa ba,ba zaki fi qarfinmu ba,ki gayawa kowanne shashasha duk randa ya sake zuwa qofar gida ya mana fada saina masa daurin da za'a kasa ganeshi,ba gidan 'yan iska bane nan,hope kin haddace abinda nace?" Tuni hawaye ya soma ambaliya saman fuskarta saboda tsabar bacin rai,hakanne yasa ta kasa amsa mishi,har sai daya maimaita mata cikin tsawa
"Kinji ko bakiji ba?"
"Naji" ta amsa cikin muryar kuka
"Ku bacemin a wajen sakarkaru kawai!" Ya kuma fada cikin tsawar.




Tuni suka miqe har suna rige rigen barin wajen,sai da suka tabbatar sun bar inda zai iya jinsu suka fara bawa zahra dake kuka haquri,kasa amsa musu da komai tayi,ta kuma kasa zuwa tura watsapp da zuwa sassan umminta don tayata dora girkin da mafi yawancin lokutta nata girkin dana hajja take hadawa,duk da itama hajjan idan tayi sha'awar wani abun tana dafa abinta,sai kawai ta juya ta koma sassan hajjan da sassarfa kuka Na sake qwace mata,maganganunsa na dawo mata.




Me yake nufi kenan?yana mata kallon 'yar iska ne koko meye?,bin maxa take a makarantar kenan har suke biyota gidan ubanta yake nufi?ko ita ta kirayesu tace suzo,bayan batama san kosu waye sukazo din ba,fatanta daya Allah kada yasanya da nuraddeen dinta akayi hakan.




Saman kujera ta zube a falon tana qoqarin tsaida qwallarta duk da taqi tsaiwa,daidai lokacin hajja ta fito daga dakinta tana riqe da carbi,da alama zikirinta data saba takeyi.




"Ke lafiya?,kukan me kike bayan qalau kuka fita?" Hajjan ta jero mata tambayar tana tsaiwa kan zahran tana rungume da hannunta fuskarta cike da damuwa da fargaba.




Kasa bata amsa tayi saboda yadda zuciyarta ke suya,sai data dauki wasu mintuna kana cikin sheshsheqar kuka ta gaya mata abinda ya faru,sannan ta dora da cewa
"Ki masa magana hajja,ki shiga tsakanina dashi"
"Ya isa,amma karna qara jin kince haka saboda yayanki ya miki fada,kawai maganganun daya fada dinne basu dace ba,tunda an jima ana wannan case din,kuma duk sanda irin haka ta tashi ina masa bayani,dole su dinga haquri wata macen haka Allah ya halicceta da farinjini,kome qoqarinta na ganin ta kaucewa samari bata isa ba musamman idan tana kan ganiyarta,yanzu dai ki tsaida kukan nan haka,zaizo ya sameni har inda nake".




Da qyar hajja ta sha kanta,duk da tsaida kukan amma saitayi kwanciyarta saman doguwar kujera tana ta hadiyar zuciya gamida tuna maganganun daya gasa mata,ta jima zaune anan har akayi sallar magariba sannan ta shiga dakinta ta daura alwala ga bada farali,bata cire hijabin jikinta ba ta miqe da niyyar taje ta tura watsapp din da bata samu damar turawa dazu ba.




"Ga abincin dare fa an gama,ki tsaya kici sannan ki fita"
"Yanzu zan dawo hajja,ba dadewa zanyi ba" ta amsa mata tana ficewa,don tana son taga nuraddeen koda online ne,shurun yayi yawa,bataso kuma ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login