Showing 84001 words to 87000 words out of 123594 words
Chapter 29 - ALKIBLA COMPLETE BOOK By Safiyya Abdullahi Huguma .txt
daya,sai sannan ta tuna yace mata ta rubuta list na abinda take buqata amma batayi hakan ba,saboda batason abinda zai ja ta dade bata koma gida ba,kodon jarabawarta data tabbatar duk abinda akw ciki ba zasu wuce two weeks basu fara ba,inda kuma ta rubuta din wala'alla ta hada harda shi,amma yanzun idan sun dawo dole ta rubuta abinda ba'a rasa ba,dole qanwar naqi ta dauki mayafi ta yafa.
Saman dining ta sameshi da waya a hannunsa yana dannawa,yana jin takunta ya dago kai,ga mamakinsa ba inda idanunsa ya sauka sai a qirjinta,yayi maza ya dauke kai yana jan tsaki can qasan ransa,mugun haushin kansa ya kamashi,meya kaishi ma daga kai koda fuskarta zai kalla bare wani sashe na jikinta,inda Allah ya taimakeshi bata kula da hakan ba harta qarasa,taja kujera ta zauna,ta gaidashi ya amsa yana ci gaba da danne danne a wayarsa,bata ma sani ba shi ko yayi breakfast din ko beyi ba,ta hada ruwan zafi ta fara kurba a hankali,tana jinta duk a takure saboda zamanshi a wajen.
Tayi rabin ruwan zafin taji ɓul daga qasanta
"Innalillahi" ta fada cikin faduwar gaba,da alama period dinta ne yaxo,ita kadai ta dinga wara idanu tana tunanin ya zatayi,bata gama wannan tunanin ba ta tsinci muryarsa yana cewa
"Ki sauri ki gama ki sameni a mota"
"Toh" ta amsa a sanyaye,yayin da shi kuma yayi ficewarsa.
Haka taci gaba da raba idanu da tunanin me zatayi,tana jin kuma yadda jinin ke flowing a jikinta,har zuwa sanda ya aiko mai gadi ya tsaya daga qofar falo yace mata ta fito inji oga,saidai tashin ya gagara,don ta tabbatar ba jikinta kawai ba,har kujerar da take xaune a kai ta baci.
Zabura ta kusa yi sanda ta tsinci muryarsa daga bayanta,ta waiwaya a hankali ta dubeshi,qwayar idanun nashi ne masu nauyi samanta yana dubanta
"Karki batamin lokaci fa...." Abinda kawai ta iya ji kenan daga bakinsa,bata da wata sauran dabara kuma,don haka ta miqe kai tsaye kawai ta tsaya cak ba tare data iya ce masa komai ba.
A hankali idanunsa ya sauka a inda ta tashin,ya fahimta sarai,don ta danyi staining wajen,saiya dauke idon nasa kawai ya juya ya fice.
Ta tabbata ya ga abinda takeson nuna masan,don haka ta nufi dakinta a hankali,ta wuce bandakinta,ta gyara kanta ta sake wanka gaba daya.
Tana tsaye waje daya a tsakar dakin tana tunanin me zata saka ta tare?,ko dankwalinta zatayi amfani taji an turo qofar dakin,duk sai ta duburbuce,ta rasa inda zata boye kanta.
Shi dinma dai kamar dazun,inda idanunsa suka sauka daxu yanzu ma haka
"Ya salam" ya fada yana aje mata ledar gamida juyawa yabar dakin,annan wanne irin jarraba ce yakeson dorawa kanshi?,wani mugun haushin kansa ya kamashi,yaja wani dogon tsaki kamar zai tsinke harshensa,ya shiga motar yana rufe murfin da qarfi kamar ita tayi masa,sumarshi yaje shafawa da hannu daya yana furzar da iska daga bakinsa,can cikin zuciyarsa kuma yana jawa kansa warning,tare da son gayawa kansa da zuciyarsa hakan bazai sake maimaituwa ba.
Sai daya fita taja ledar ta som duba abinda ke ciki,pad ce da pants masu yawa,wanda tasan sundi qarfin buqatarta na dan lokaci,sai ta cira wanda zatayi amfani dashi,ta dora ledar saman akwatinta sannan ta bareta ta saka,tayi mamakin yadda akayi size na pant din yayi mata dai dai.
A gurguje ta shirya sannan ta fito,tun kafin ta qaraso ya hade ranshi sosai,ya kuma dauke kansa daga direction dinta harta qaraso ta bude gidan gaba ta shiga.
Tafiyar kurame dai sukayi kamar kullum,har suka isa ginin da kallo daya tayi masa ya gaya mata asibiti ne,private asibiti,daga yanayin tsarinsa da gininsa kadai ya isa ya gaya maka kudin da ake lasa na marasa lafiya,saidai kulawar da suke baiwa mara lpy ya cancanci kudin da suke karba.
Da alama nan yake zuwa idan yana garin,duk da cewa akwai na sojoji,saidai wala'alla kayan aikinsu da ma'aikatan ne basuyi masa ba.
Tare suka shiga ganin likitan,yana tsaye ta gama bayani ya rubuta mata magani,da kansa ya tsaya a pharmacy na asibitin ya amshi maganin.
Ita kam komai yayi mamaki yake bata,tamkar ba ya haidar din data sani ba,bata taba kawowa ranta akwai ranar da zatazo ta samu koda kallon mutunci sau daya ba bare akai ga kula da lafiyarta.
Bayan sun baro asibitin saiya tsaya a wani babban kanti yayi musu siyayya bisa radin kansa,ya zaba abubuwan da yake tunanin zata iya buqata sannan ya dawo suka tafi.
*_washegari_*
Tun qarfe shida na safe ta kasa komawa bacci saboda yunwa da takeji,wani lokaci ulcer dinta tana yi mata haka,sai ta sanyata jin yunwa kamar hauka,uwa uba kuma zaman banza data gaji dashi,wanda daga kwanciya sai danne danne a waya,gaba daya zaman ya gama gundirarta,babu wani abu na debe kewa.
Parlour din shuru babu kowa,saita wuce kitchen din kai tsaye,wanda wannan shine shigarta ta biyu tunda tazo gidan,sai a sannan ta qare masa kallo,babu abinda babu a ciki,babun ce kawai babu,hakanan komai atsare yake,da alama kuma tun tafiyarsu hajja ba'ayi girki a ciki ba.
Da iya cikinta kawai tayi niyyar dafa abinda zata ci wanda bazai ja mata lokaci ba,amma saita tuna gida,daga umminta har hajja basa gaba yin girki iya cikinsu,dole sai sunyi da al'ummar annabi,da kuma wanda rabonsa ya tsaga zaici,data duba store da fridge din kuma saita tadda akwai duk wani kayan buqata na amfanin girki,zata iya dafa kowanne abinci,don haka ta diba duk abinda tasan zata buqata ta fara sarrafawa.
Gas din waje hudu ne dashi,saita kunna biyu yadda komai zaifi mata sauri ta dora,ganin bata da sauran abinda zatayi saita fara tattare kitchen din,duk da bawai datti yayi ba,amma akwai qura na rashin shiga kwana biyun,data gama taga har yanzu abunda ta dora baikai mata ta sauke ba,saita miqa falon.
Tas ta gyareshi,ta kuma gyara guraren da baiyi mata ba,dama wani aikin sai diya mace,nan da nan sai gashi ya sake tarwai kamar an qara masa kyau,zuwa sannan ta koma kitchen taga abunda ta dora yayin,saita dora da aikinta daga inda ta tsaya.
A gaggauce ya fito daga dakin yana sake kallon agogon da yake daurawa a hannunsa,cike da mamakin yadda lokaci ya kufce masa haka yanata aikin bacci,sam baisan lokaci yaja haka ba,sai daya soma jiyo qamshin girki a hancinsa,wanda da farko ya zaci a mafarki ne,sai daya farka yaji cikin gidan ne,bai kawo zata shiga kitchen ba,don haka ya barwa ransa daga maqota ne,abinda ya sanyashi gaggawar kuwa daya tuna babu abinda zataci cikin gidan,jiyan dama nasreen ce ta kawo musu shi.
Sanda ya fito falon,dai dai lokacin da zahran ke fitowa dauke da warmers guda biyu,tana ta sauri ta gama ta jera ta koma daki abinta,don batason ya ganta,tayi ne kawai don babu kyau mugunta,musamman ta yunwa.
Ido suka hada dashi,saita dauke qwayar idanunta da sauri gabanta na faduwa hakanan,sannan wani kyau taga ya mata a ido yanzun da yake sanye da wasu kaya,saita koma takawa a hankali tana wassafa yadda zata wuce ta gabanshi,saboda yana tsaye qyam ne,kuma dole ta giftashi,uwa uba ma kuma riga da skert din dake jikinta na roba ce mai rawa,ya zauna yabi kowanne lungu da tudu na jikinta,kanta ne kawai keda dankwali,shi kansa dan kwalin rabi ne,dukka sumarta ta baya da goshinta ana gani.
Sannu a hankali idanuwansa suka bar fuskarta data dan yi fayau saboda ciwon kwama biyun da tayi,sai suka zarce suka sauka a muhallin da tun daxun yake gargadarsu a kanshi,hannunsa ya damqe waje guda yana dauke idanun nasa daga kanta,saidai shi kansa baisan yadda akayi ba yaji qarar faduwar flask din hannunta a gabasa,gab da yatsunsa,saura kadan su sauka a qafarsas,sannan ta daki jikinsa ta zame zata kai qasa.
Cikin matuqar zafin nama ya tarota,gaggawar yin sarving dinta ta hanyar tarota yasa ya dora hannunsa saman qirjinta ba tare daya ankara ba,da sauri ya daga hannun nashi daga wajen,kamar yadda itama ta miqe da sauri ta tsaya da qafafunta,duka sai suka duqa kusan lokaci daya suna qoqarin daga flask din.
Allah yasa ya rufu sosai,babu abinda ya zuba sai dan abinda ba'a rasa ba ta gefen murfin,da sauri ta dauke ta nufi dining din qafafunta na rawa,ta dorasu akai,ta yagi tissue tana goge bakin nasu,da zimmar bata lokaci har yabar wajen,saidai duk yadda ta dinga laqai laqai din gamawa don ya tafi aikin banza tayi,don sai jinsa tayi ya hauro wajen,yaja kujera daya ya zauna abinsa,fuskarsa a dake kamar bada shi abun dazu din dazu ya faru ba.
Gaidashi tayi a gurguje tana bari wajen,saita fasa komawa kitchen ta dauki abincin,ta fada dakinta kai tsaye.
Gefan katifar ta zauna tana maida numfashi,har yanzu tana jin dumin hannunsa saman jikinta,sai takejin kamar bai dauke hannun ba,don haka ta koma rub da ciki ta kwanta tana rufe idanunta tana kuma sauke numfashi É—aya É—aya.
Hanyar data wuce yabi da kallo sai data wuce,shima saiya sauke numfashi me nauyi daga qirjinsa,baisan me yasa koda yaushe idan ta fito ko baiso saiya kalleta,kamar wanda ake jan idanunsa da magnet,abinda sam ba halayyarsa bace,hasalima yana daya daga cikin jinsan mutanen da suka tsani yawan kallo.
Qoqari yayi ya kauda tunanin gefe,ya janyo kwanukan abincin ya soma budewa,tuni qamshi ya sake game wajen,saiya soma zubawa,yana fatan Allah yasa É—anÉ—anon a dace da bakinsa,duk da yasan cewa ba baya bace ita,tunda kaf cikin yaran gidan ita kadai yake cin girkinta,itama albarkacin hajja take ci.
Sosai ya lodi abincin,duk da dama shi din ba baya bane wajen baiwa cikinsa haqqinsa,to amma ya dade rabon daya zauna yaci abinci mai yawa irin haka,sanda ya kammala ya duba agogonsa,yayi dai dai da lokacin da zai fita din,saboda meeting na gaggawa da aka kirasu,ya miqe yana gyara tie din wuyansa yana dan duban qofar falon,kamar ya shiga kamar ya fice,to amma idan ya shiga din me zaya ce da ita?,don haka saiya doshi qofa kawai ya fice,ya samu drivernsa yayi ready shi yake jira,ba bata lokaci suka fice daga gidan,dai dai sanda zahran ta saki ajiyar zuciya,ta miqe zaune sannan ta tashi a kasalance zuwa kitchen don ta dauki nata abincin.
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 33
Karo na qarshe da suka hada idanun saiya saki hannun nata,yaja mata kujera ya mata nuni da idanu kan ta zauna a kai,a sanyaye kuma a hankali ta zauna din,saiya juya ya tsugunna yana tsince barin da tayi,ya gyara komai,kawai sai tagq yaci gaba da girkin
"Ya rabb..." Ta fada tana lumshe idanunta cike da zallar mamakin ya haidar din,dama zai iya amsar mata girki saboda kawai ta qone?,sauqin kaine ko ganin dama?,saboda dai su sun riga da sunsan halinsa,mai fada da kaushin hali shine tambarinsa a wajensu,bata gushe ba tana binsa da kallon mamaki har sanda ya kammala,yana juyowa suka hada ido,karon farko data ji wani abu me kama da kunya ya kamata,saboda kamata da yayi tana kallonsa,sai ya basar kawai yana riqe da plate din ya miqa mata daya,sauran kuma yayi hanyar fita dasu.
A daske a wajen take bin farantin da kallo,ya hada komai perfectly,duk da dama ta kusa gama komai din,amma shima yayi qoqari sosai,ba yunwa take ji ba,amma sai taji tana sha'awar taste dinshi,don haka ta sanya hannu ta diba takai bakinta.
Komai yayi daidai,kamar ita ta zuba seasoning din,a hankali tana ci tana ci sai gashi taci da dan yawa,ta ajjiye plate din tana duba hannunta,bai tashi ba har yanzu saidai alamun quna,hakan yayi mata dadi,tasan kuma sirrin fatihar daya dinga karanta mata ce.
Da kanshi ya dinga gayawa kansa akwai matsala,yana jin tsoron faruwar wani abu,yana ga ya kamata ya maidata gida tun baiyi abun kunya ba,abun kunyar daya tabbatar da cewa hajja saita masa tareren kaf dangi da 'yan uwa.
Bai taba yarda da zantukan abokansa ba sai yanzu,wani lokaci idan suna irin wadan nan hirarrakin da suka danganci aure,yana dauka shirmensu ne kawai da kuma batawa kai lokaci,har suna ganin ko lafiya ce baida ita?,saboda sun riga da sun saba,dai daiku ne cikin wanda zai zama soja,ya kuma kai mataki da matsayin da haidar din ke kai ba tare da yana mu'amala da mata ba ko kuma shaye shayen abubuwan maye,sai gashi shi din Allah ya tsarkake shi,ya kubutar dashi,ko sigari baya sha bare akai ga barasa da sauransu,game da mata kuwa bai ma tsaiwa ya musu wani dogon kallo,ko yayi dogon nazari a kansu da zaya dami rayuwarsa,hakan ya kawo masa sauqin al'amuransa sosai,ya kuma sake kauda masa duk wani abu game dasu,duk da yasha tsallake tarkunansu,saidai suma suna kama kansu saboda sunsan halinsa,bashi da sauqi sam.
Yana gama cin abincin yayi wanka ya fice,bai dawo ba sai gab da magariba,ganin an kusa kira saiya daura alwala kawai,da niyyar idan ya dawo yayi wanka,sannan ya leqa yaga hannun nata,ya kuma nema musu abinda zasuci,saidai yayi mamaki da yazo tafiya sallah yaga kwanuka kan dining,harta samu qarfin halin yin girki kenan.
Tana dakin taji dawowarsa,saidai bata sa sha'awar fitowa don ta gama duk abinda tasan zai maidata falon,ana kiran sallah ta shiga wanka,ta fito ta shirya cikin hight waisted skert ta shirt mai gajeran hannu wadda ta dace da skert din,ya fidda qugunta sosai tare da plate tummy dinta,gashinta ta taje sosai wanda ta tsefeshi saboda tana period,yawanci haka takeyi,saita tsefe idan zatayi wankan tsarki ta wankeshi sannan a maida mata kitso idan tana ra'ayi.
Kamar daga sama taji sallama a falonsu,saita aje comb din hannunta da take kwantar da gashin nata cikin sauri ta bude qofa ta nufi parlour din.
Dr nasreen ce a tsaye cikin ado kamar yadda take a dabi'ance,kowaccensu fuskarta qunshe da fara'a suka nufi juna cikin murna,don har zuciyarta zahra taji dadin zuwan dr nasreen din,ko banza ta debe mata kewa yau na wasu awanni.
Sai data cikata da kayan ciye ciye sannan ta dubeta cikin mamakin me yasa har yanzu bata zauna ba
"Zauna mana kinata tsaye haka?" Murmushi tayi ta girgiza kai
"Ai banga ta zama ba,dear tana waje fa a tsaye" ido zahra ta fitar
"Kai!,ya shigo mana,me yasa kuma zai tsaya a waje" kai ta girgiza tana qwalalo ido
"Ah wai....ai bazai shigo ba,yasan fa waye mai gidan nan,wannan boss din naki akwai ban tsoro,yasan halinsa sarai....,ki fara shaida masa dai yana da baqo ko?" Saita dan daburce,tana nufin ta shiga dakinsa kenan ta masa magana,tunda ta tabbatar yana dakin tunda ya dawo gidan,dakin da tunda tazo bata taba gigin shigarsa ba,batason tace wani abu da zata dago kome ke tsakaninsu,don haka cikin fara'ar yaqe tace
"Yanzu kuwa zan sanar mishi,ai ba'a bar masoyi a waje ba" tayi qarfin halin tsokanarta,sai ta sake fadada fara'arta tana cewa
"Kema kya fada,shi yasa na kasa zama ai".
Inda zai yiwu zata faki idanun nasreen ne taje ta sanyo hijabi,to amma yin hakan zai sanya ta saka mata ayar tambaya,dole qanwar naqi tayi qundunbala takuma yi shahadar quda ta durfafi dakin.
Fitowarsa daga wanka kenan daure da towel iya qugunsa,yana tsaye gaban mudubi yana sharce ruwan jikinsa,duk da cewa daga wanka ya fito kuma a tube yake amma ac ke kwarara cikin dakin,kamar baya jin yawan da tayi.
A hankali ta bude qofar dakin ta saka kai,ta daga idanunta a hankali tana wulgasu cikin dakin,saiko suka sauka a kansa yana taje kansa da wani cumb,idanunsa cikin madubin yana kallota,ko kadan bata tsammaci samunshi a yanayin data ganshi ba,yanayin qira da duk wata siffa ta jikinsa ta fito muraren,mai tsayayyen jiki da siffa dake nuna qarfi da mazantaka,da kuma alamun ya horu sosai kan aikinsa,kana ganinsa kasan yana daga qarfe.
Sosai idanunta suka nuna razana muraran,da hanzari ta juya a sukwane ta durfafi qofa,taku uku qwarara ya cimmata,ya sanya hannu ya cafkota tare da birkitota gaba daya,sai gata tayi kyakkyawan masauki cikin faffadan qirjinsa,damshin ruwan dake jikinsa ya ratsa fatar hannunta da wuyanta,tsigar jikinta ta zuba,saiya matseta yana fadin
"Nutsu mana,ina zaki koma a haka kamar wadda wani mugun abu ya biyo,ba baqi mukayi ba?" Ya fada a dake,kasa furta komai tayi sai jikinta dake rawa,saiya yasa hannu ya janyeta daga jikinsa yana ladabtar da ita da kaifaffan kallonshi.
A nutse yake qare mata kallo tun daga yatsun qafarta har zuwa kanta dake gyare cike da baqa qirin din suma,fuska a hade yake dubanta
"Uhummm....,me yasa ko yaushe kike firgita kanki?,tell me,meke baki tsoro a jikina?" Gam ta rintse idanunta,don har ga Allah ba zata iya kallonshi a yadda yake tsaye a gabanta ba,don ita a wajenta bashi da maraba da tsirara,gashi hanya takeso ta samu ta tsere,saiya kada yatsanshi saman fuskarta
"Niba dodo bane?....kinji ni?"