Showing 48001 words to 51000 words out of 123594 words
Chapter 17 - ALKIBLA COMPLETE BOOK By Safiyya Abdullahi Huguma .txt
cewa komai har sai da abba babba ya maimaita tambayarshi,cikin muryar kuka tace
"Eh haka ne abba.....amma wallahi wallahi abba,na rantse da wanda raina yake hannunsa abba ba wani mummunan abu bane ya kaini,munje ne yin karatu nida sauran qawaye na saboda test da muke dasu da yawa a satin....ko sanda ya haidar ya ganni amsar abinci ya fito dani...."
"Ya isa haka,yarinya aita gama magana....idan dukkaninku baku yarda da ita ba,bakuma yarda da abinda tace din ba ni na yarda da hakan,dukkanku na fiku sanin wacece zahra'u....bama ita kadai ba,addu'ar da nake na dare ba rana ina da tabbacin ubangiji bazai wofantar da ita ba,babu wani cikin zuri'ata da xai aikata alfasha da iznin ubangiji"hajja tayi maganar da alamun ranta ya fara baci,ajiyar zuciya abba babba ya sauke,duk da dama zuciyarsu bata taba basu zahra'un zata aikata wata alfasha ba,amma yanayin yadda take magana ya isa ya shaida maka gaskiyar abinda take fada din,hakanan kuma bayanin nata ya sake sanya musu nutsuwa a ransu,saidai dukka ba zasu nuna haka tashin farko ba,dole ne su tauna tsakuwa don aya taji tsoro,don haka abba yusuf ya soma fada sosai kan zuwan da tayi,wanda yace sam bata da wata hujja ta zuwa din,tunda ba tarbiyyar gidan bace,hakanan duk wanda ya ganta akwai kallon da zai mata da kuma yadda zai fassara ta,haka ya dinga fada sosai,saboda kusan duka ya fisu zafi,yayin da kanta ke qasa hawaye wasu nabin wasu.
Itama ummin nata nata kan yana qasa,bata zargin diyarta ko daya,saidai tana da tarin fargaba,tana tsoron zamani,tana tsoron qawaye,tana tsoron gurbacewar muhalli,tana sane da cewa a yanzun tarbiyya ta zama wani abu mai tsananin tsada wanda sai wajen wane da wane ake samunta,tsadar tata taki jallin da hirar wanda ya rabauta da samunta ake,farautar masu ita ake,tsada suke da kuma wuyar samu,tattalinta kuma abune mai hatsarin gaske,wanda idan ka tsira da ita ba tare da wani yayi nasarar fauce maka ita ba to abun ayi maka sambarka ne,tana fargabar yadda diyarta ta kafa tarihin soma karatun gaba da secondry cikin gidan ya zamana ta kafa wani tarihin na daban,tarihin da bata fata ko burin samuwarsa,a kullum kwanan duniya dama takan kwana da tashi cikin fargaba,koda yaushe burinta shine diyarta ya zamana tana gidan nata mijin kamar yadda aka tsara ko kuma aka gina gidan akan hakan,wannan zai fiye mata kwanciyar hankali fiye da ace tana can tana karatu,tunda jarrabawa ta soma samun diyartata bata taba samun nutsuwa ko sukuni na sakan ba,idanunta basa barci,zuciyarta bata hutawa,bakinta baya gajiya da yi mata addu'a ako da yaushe,a kullum takan wayi gari cike da buri da kuma fatan Allah ya fiddo mata da miji na gari,koda kuwa zai zama silar datsewar karatunta,a yanzu kam a wannan bigiren....tana jin ya kamata ta motsa,tana jin ya kamata ta magantu,tana jin ya kamata tayi wani abu da zai sama mata nutsuwa ko yaya ne.
Sai da suka gama fadan sannan sukayi mata jan kunne da gargadi mai qarfi,saida suka gama gaba daya sa'annan umminta da tunda aka fara batace komai ba tayi magana
"Hajja.....yaya(haka suke kiran abba babba tun tale tale,dukka matan qannen nasa
"Na'am halima muna saurarenki"
"Yaya dukkan fada da qoqarin da kukeyi akan zahra'u duk da cewa diyarku ce.....amma ya zama dole ga duk wanda ya gani ya yaba muku...idanma har akwai abinda yafi yabo din kun cancanci samunsa,a yau sau daya tak ina neman wata alfarma....alfarma guda daya da nake fata da kuma burin xan sameta daga gareku" shuru ya dan ratsa kafin abba babban ya bude baki yace
Fadeta halima....in sha Allah ba zata gagara ba"yayi furucin tare da yaqinin haka yake cikin zuciyar mahaifiyarsa hajja,domin halima takai mace,duk inda mutum mai tsananin kawaici kan diyoyin cikinsa da sanin ya kamata yakai takai,suna da tabbacin tunda har yau ta iya buda baki tayi magana to ba shakka lamarin ba qarami bane a zuciyarta.
"Inason a dakatar da zuwan inna wuro makaranta....ma'ana a dakatar da karatunta" sosai zancan ya daki zahra,don bata taba kawowa umminta da bakinta zata nema hakan ba,fitar furucin daga bakin ummin nata ba qaramin razani da gigita ya sanyata ba,domin tana qaunar karatunta a yanzu,qaunar da a baya batayi masa ba,ta damu dashi damuwar da abaya batayi masa ba
"Ba wanda zai dakatar da ita daga karatunta bayan bamu tabbatar da laifinta a kanta ba"
"Don Allah hajja na roqeki to kimin alfarma ta biyu....taci gaba da karatunta,amma da sharadin zata koma bakin karatun nata ne da igiyar aurenta a kanta....." Dif dakin yayi tamkae anyi ruwa an dauke,ga zahra kuwa rudanin data shiga yanzu ya zarta na baya
"Don Allah hajja....kiyimin wannan alfarmar" muryar ummin tata ta sake ratsa shurun.
Dukka wata laka ta jikin hajjan tamkar an zareta,wani irin nauyi da tausayin halimatun ya shigeta sanda take zaune gabanta tana roqon ayi mata alfarma kan diyar cikinta,ayi mata alfarma kan diyar data haifa da kanta,diyat da duk duniya tafi kowa iko da isa da ita,tabbas! Halimatu mutum ce,cikakkiyar mace mai cikakken kunya da kuma tarin kawaici,kawaicin da bata jin baya ga halimatu sai khadijatu mahaifiyar haidar ce kawai za'a samu da irinta tattare dasu,bata taba ba!,koda wasa bata taba nema ko maida hukuncin hajja baya ba a kan zahran,kulkum abinda hajja ta aiwatar ko ta zartar dai dai ne akan zahran,halimatun bata da wani zabi ko nuni dangane da duk wani lamari da ya shafi rayuwarta,lallai a yau din ya kamata....ya cancanta ayi mata itama abinda takeso!,saidai kuma hakan na nufin yiwuwar rugurgujewar ko samun tasgaro ga karatun zahra'un tata,karatun da take da tabbacin a yanzun shine komai na zahra'un,kai.....bata tunanin wannan ra'ayi ko hukuncin halimatu ne,tafi zato da zargin aliyyu shine ya shirya komai ta bakin ummin,ya kuma ja bakinsa yayi shuru,bayan taja kunnensa,ta kuma jaddada da masa buqatarta,lallai itama zata nuna nata qarfin qwanjin,zata nuna nata ikon,kai lokacima yayi da zata cika mafarkin data dauki shekara da shekaru tanayi,lokaci yayi da zata cika burinta,lokaci yayi da baraka guda daya data rage zata dinketa tsaf!,koda hakan na nufin rikici da tashin hankali daga kowanne gefen.
Cikin wani irin amo da salo daya tabbatarwa da duk wanda ke dakin da gaske hajja ke magana,da gaske hukunci take zartawa mai zubin KAIFI DAYA!,MAGANA DAYA!,cikin salo na umarni kai tsaye tace
"Kin wuce ki nema alfarma akan diyarki halimatu,baki ma taba nema ba sai yau,kuma zaki samu da izinin Allah,zahra ba zata koma makaranta ba saida igiyar aurenta akanta....zahra zata koma makaranta cikin satin nan a matsayin matar aure....a matsayin matar Aliyyu,rana ita yau nakeson inga zahra'u a matsayin matar aliyyu!" Takai qarshen zancan tana sauke idanunta kan abba babba,wanda hakan ke nufin cewa tana da buqatar ya zartar da umarnin data bayar kenan.
Da wani irin sauri aliyyu ya dago da kanshi,wanda tunda aka fara dambarwar wayarsa ke hannunsa yana sarrafata cikin qwarewa,kanzil baice ba sai a yanzu da yaji fitar furuci mai nauyi daga bakin hajjan,furucin da ko cikin duniyar mafarki bai taba hakaito kwatankwacinsa ba,sai yaji sam hukuncin ma bai samu zama a kwanyarsa ba,lafazin nata kamar wani wasa ne ko raha a kunnuwansa,haka yaci gaba da gayawa zuciyarsa,saboda haka saiya sake rusunar da kansa yana ci gaba da danne dannen wayarsa abinsa,saidai kuma wannan karon sam zuciyarsa taqi yarda ta bashi hadin kai yaci gaba da abinda yakeyi din,gaba daya ta karkata ga sauraron abinda ke gudana a falon.
Ta fannin zahra kuwa numfashinta ne yayi qaura daga gangar jikinta na wucin gadi,tana son kiran sunan hajja ta kasa,tana son roqon hajja alfarma amma ta kasa,tana son tace a'ah amma dukka ta gaza aikata hakan,har zuwa sanda hajja tace
"Kai ka bata zaki....kuma kaine zaka gyara....dolenka" furucinta na biyu daya sanyashi shiga taitayinsa,ya kuma sake alamta masa hajjan fa da gaske take,abinda take fada da gaske takeyi,saiya aje wayarsa gefansa,karon farko shima da yace
"Me na bata hajja?,me nayi ni din?"
"Duukkan abinda ke faruwa anan kaika bazashi har ya kawomu ga zama a nan...."
"Bashi bane hajja.....kada ki masa hukunci ba bisa laifinsa ba,haidar bai gaya min komai ba,kuma ya bani mamaki daya boyemin...tunda ba don kunnuwana sun jiye min ba haka zai rufeni?,bayan shine mutum daya tilo cikin matasan gidan nan da yake da dabi'ar tsawatarwa da tsaiwa tsayin daka kan halayyar qannensa,don me zai watsar akan zahra'u?.....na roqeki hajja ki soke qudurinki.....kiyi haquri,amma zan iya cewa ba'a kyautata masa ba matuqar akace shine wanda zai aureta"
"Halimatu.....indai na isa a gidan nan,indai nina tsugunna na haifeku(ta fada tana nuna su abba yusuf)to rana ita yau inna wuro zata zama mata ga zaki....ku riqe wannan"
"Hajjaaaaa!" Zahra da wannan karon ta samu nasarar fisgo kalaman bakinta ta furta cikin wani irin rauni,hawaye na sauka saman kuncinta
"Don Allah hajja.....don Allah kiyimin kowanne irin hukunci amma banda wannan....wannan din ba gata bane hajja......shine hukunci mafi tsanani da tsauri da zaki yankema rayuwata a karo na farko!" Ta qarasa maganar kuka na qace mata,tsam ummin ta miqe a nutse ta fita daga falon ba tare data tsaya sake jin komai ko sake cewa komai ba,mutum na biyu da ya sake miqewa zai rufawa ummin baya haidar ne,don shi maganar hajjan jinta yake kaman tatsuniyar gizo da qoqi,don baiga dalili ko abinda zai saka wannan kwamacalar yiwuwa ba,kawai saboda ana son hukunta yarinya sai an jingina da tashi rayuwar?
"Kai aliyyu....dakata" abba babba mahaifinsa ya dakatar dashi,saiya koma hannun kujerar daya tashi cikin girmamawa ya zauna
"Gani abba" ya fada wata irin murya mai kauri
"Dukkaninmu nan daka ganmu(ya fada yana nuna junansu da yatsa)albarkarta muke nema....dukkanmu aljannarmu tana qarqashin qafarta,sa'annan babu wani abu da zata nema nan gidan duniya mu kasa yi mata shi,koda fansar ranmu ne zamu bada,ina fatan ka fahimci abinda nakeson fada?" A wannan karon zuciyarsa sake gaya masa take abun babba ne,saidai har yanzu zuciyar 'yan mazan a dake take,har yanzu baiji wani darrr ba,don haka ya gyada masa kai kawai ya dora da fadin
"Eh abba...."
"Amma yaaaya.....hajja ina ganin kamar wannan hukuncin baiyi tsauri ba?,ya kamata a zauna a sake duba abinda zai yiwu ko?" Cewar abban tsakiya wanda kukan zahran bai masa dadi a ransa kamar yadda baiwa sauran
"Kai muftahu....." Hajja ta fada da salon son dakatar dashi,dai dai nan haidar ya miqe tsam abinsa ya fice daga falon.
Da wani irin sauri itama zahran ta miqe tayi dakinta saboda ji da tayi ta kasa zaman falon,kamar idan ta tashi tabar musu falon ta tserewa wannan mummunan hukunci na hajjan,amma data shiga dakin saita kasa zaune ta kasa tsaye,kamar wata zararriya haka ta dinga jin kwanyarta na yamutsawa,ta dinga leqensu abban tana so suyi subar falon,tana da tabbacin barazana ce kawai hajjan keyi amma zata janye,tasan cewa da taje ta kwantar da kai ta lallabata shikenan za'a wuce wajen,duk da tafi kowa sanin halin hajjan tunda tafi sauran zama da ita,sau tari tana da kafiya da zafi kan wasu abubuwan,wanda idan ta juye maka zaka tsammaci ba ita bace.
Kansa yake gayawa cewa babu wani abu da zai faru sansa yake dosar nahiyar da dakunansu suke,dukkan abinda hajjan ta fada barazana ce kawai saboda tana tunanin ya qetare abinda ta gaya masa,tana so ne ta kaÉ—ashi kawai saboda haka,saidai can can qasan ranshi ya kasa samun nutsuwar da yakeson samawa kansa,ya kasa gamsuwa da dukka kalaman kwantar da hankali da zuciyarsa ke jero masa,ya kasa daukar kowanne daga ciki,indai har kuwa hajja na nufin abinda ta fada da gaskene har cikin zuciyarta....to a karon farko wani mummunan al'amari zai iya faruwa wanda shi kansa bai sanshi ba,bai kuma san qarshensa ba.
Har ya saka key zai bude gefen nashi wayarsa ta dauki tsuwwa,tun kafin ya ciro ya saki tsaki,don sai yaji qarar wayar kamar wani qarin damuwa ce cikin kwanyarsa,ya zaro yana duba mai kiran,general hamza ne,babu uzuri matuqar kira daga wajen irinsu ne,don haka ya daga,ya gaidashi cikin girmamawa kamar yadda ya saba
"Abu biyu yasa nayi kiranka aliyyu.....na farko akwai wani gagarumin al'amari daya tunkaroka,wanda kyanta idan ka samu dama ka sameni saboda kaji kai tsaye daga bakina.....na biyu kuma batu ne na auratayya" saiya dan saki murmushi
"Ina farincikin shaida maka cewa ina saka ran nan gaba kadan xamu hada zuri'a,zamu hada jini da familynka....,duka dai idan ka samu dama kazo na ganka" kusan bai fahimci dukka maganganunsa ba,ya sani kuma a yanzun yadda yake jinsa ba fahimtar zaiyi ba,don haka kawai yace
"Sir...in sha Allah zan shigo gobe da safe" godiya general ya yiwa aliyyun kamar ba shine samansa ba,sannan ya katse wayar......
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 18
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su ko’ina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_
_______________________________
Da wani irin zafi ya soma takawa inda take tsayen,tamkar ma ya manta da cewa gap din dake tsakaninsu ba wani me yawa bane,itama sai tayi yunqurin ja da baya,wanda hakan yasa yakai mata cafka da zafinsa,ya samu nasarar riqe singalalin hannunta,abinda ya sake rudata kenan ta sake daburcewa,tsoro ya kuma cikata,yayin daya bude baki cikin wata tsawa
"Me ya kawoki nan!" Ya fada da dakakkiyar murya mai qarfin amo da sauti,irin ta sojan daya saba karba da bada umarni a fagen daga.
Yadda dai daikun mutane suka juyo suna kallonsu ya ankarar dashi,saiya sake mata hannun nata da sauri,fuskarsa na gauraye da wani irin bacin rai,ya zare muqullim motar daya maida aljihunsa ya cilla mata,ya kuwa sauka saman qafafunta,duk da taji zafin amma ba shine a gabanta ba,tashin hankalin dake a gaba take hararowa,tasan cewa abinda zai biyo baha din ba dan qarami bane,ta kuma fahimta me yake nufi,don haka ga duqa ta dauki key din ta fara takawa tana ficewa daga wajen kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki.
Sai data fice sannan yabi bayanta ba tare daya tsaya amsar number dakin da yake nema din ba,tana gaba yana bayanta amma ba zaka zaci tare suke ba har ta isa bakin motar,daidai lokacin matashin da tun dazun yake dawafi cikin hotel din yana nemanta tare da burin sake ganinta ya hangeta,don haka da sauri sauri ya sauko a nufosu idanunshi a kansu,yana ganin sanda haidar ya fisge muqullin ya buda motar ta shiga baya ta zauna.
Sai daya tabbatar ta shiga sannan ya sanyawa motar lock,duk da ya dage dukkan gilasan motar bakan baisa yayi tunanin kunna mata ac koya rage wani glass din ba don iska ta shigo mata.
Yana zare key din yaji an dafe hannunsa,ya daga kai a nutse don ganin waye
"Me haka kake?,zaka kama yarinya ka rufe cikin mota saboda me?" Wani banzan kallo haidar din ya kafeshi dashi,cikin ransa yana tambayar kansa da kansa shi din waye?,sosai ransa ke tafasa baiso ya huce masa laifin da bashi ya aikata ba,amma kuma yanajin wani sabon bacin ran na taso masa dangane da rainin hankalin da yakeson zuwar masa dashi,shi waye nata da zai qalubalanceshi kan hakan?,ya santa ne?,shi ya kawota?,ko tare suka zo?.
Zare key din yayi ba tare daya sake bi ta kansa koya dubeshi ba,ya juya ya soma takawa zaibar wajen saurayin ya mara masa baya yana ci gaba da cewa
"Malam ka budeta nace tun kafin ka gano kuskurenka.....bakasan waye ni ba ko?" Ya fada cikin zafi dason nuna nashi qarfin qwanjin.
Wani irin juyowa haidar din yayi a zafafe har hana take masa rabin qafa da ingarman takalminsa
"Idan kaci gaba da bina kana min wannan ɓaɓatun sai na saka kayi nadama kai da banzan matsayinka,kuma zaka gane kuskuren aikatamin hakan kafin ni na gane nawa kuskuren,stay awa frm me tun ban rugurguza kwanyarka" tabbas ya hangi wani strong abu cikin idanunsa,ya kuma hangi yadda yake furta maganar bilhaqqi,ya kuma tabbatar ba'a banza yake magana kan yarinyar with confidence haka ba,amma a amtsayin da mahaifinsa keda shi a nigeria yafi qarfin wani da baisan ma ko waye ba ya gaya masa magana irin haka ya qyale ba,don haka zai jira yaga yadda za'ayi ya fita daga hotel din ya kulle 'yar mutane cikin mota
"Zan gani ta yadda zaka fita daga wannan ginin" ya furta sanda haidar ke komawa zuwa ciki,sai daya sake bi ta reception aka gaya masa dakin sannan ya wuce.
A nutse ya bude dakin da sallama a bakinsa,mutumin wanda a qalla ya kusa shekara hamsin da biyar ya amsa mishi,yana zaune saman kujera riqe da jarida