Showing 102001 words to 105000 words out of 123594 words
Chapter 35 - ALKIBLA COMPLETE BOOK By Safiyya Abdullahi Huguma .txt
na qarshe da sauran moments nasu.
Batasan me yasa a kwanakin take yawan duba wayarta ba,koda yaushe tana kan cheaking sms da watsapp massages fiye da yadda ta saba,batasan dalili ba,sai randa zuciyarta tayi mata wata tambaya,wanda a take ta girgiza kai alamar a'ah
"Kina tsammanin samun kira da gareshi ne?" Wannan itace tambayar data yiwa kanta,wanda ko sau daya bata taba yarda da hakan ba.
Jarabawar wannan karon suna samun intervals sosai,don haka duk sanda taga akwai interval mai yawa saita tafi gida,tafiya gidan yakan sa mata nutsuwa,kuma yakan sanya taji kamar tadan rage nisan dake tsakaninta da wani abu wanda ada yake nesa da ita.
Sannu a hankali ta tabbatarwa da kanta damuwa ce,damuwa ce ta rashin ganinsa ko rashin jin muryarsa na tsahon tagwayen sati,har ana neman shiga sati na uku,hatta a gida hajja ta fara qorafin shuru haidar,bai kira ba,koda an kira ba'a samunsa,to Allah yasa dai lafiya,addu'ar data sanya gaban zahran mugun faduwa,saboda tuna maganar daya gaya mata
_"zanyi tafiya me nisa.....waje me hadari,zan iya dawowa....zan iya salwanta a can.....ki yafemin idan na saba miki a tarayyarmu"_,kawai sai taji kuka ya subuce mata,ta danneshi har sai data kai daki sannan ta sakeshi.
Kuka tayi sosai wanda ta kasa yarda da dalilin kukan nata da zuciyarta keta bata,saidai ko ba komai ta danji nauyin dake qirjinta ya ragu,ranar sama sama tayi karatun jarrabawar da zata zana a jibi,washegari ta hada kayanta ta koma makaranta,wanda jarabawar kawaidai tasan saidai Allah ya tsallakar da ita,amma ita kanta bata gama tantance abinda take rubutawar haka yake ba,ko akwai kusakurai da gyararraki ba.
Hajja kuwa bin zahra tayi da kallo tun sanda taga tayi daki da sauri sanda take jajjabin kwanakin da haidar din ya shafe babu shi babu labarinsa,murmushi ta saki,duk da tana cikin fargaba,saita daga hannunta sama tana cewa
"Allah na gode maka,Allah na gode maka,ko yau na mutu ubangiji ka cikamin dukka burina,Allah ka qara hada kan zuria'ata da iyalina,Allah ka qarawa annabi muhammad S A W wasila da fadila" daga haka ta sauke hannun nata,zuciyarta na mata dadi,ba shakka komai yayi dai dai yadda takeso,tasan cewa da zarar ya dawo komai zai kammala dai daita.
Ranar da suka kammala jarrabawarsu suka samu hutu na wasu kwanaki ba masu yawa ba,saboda zasu dawo ne suyi maza su dora sabuwar semester ta qarshe,tana kwance a dakinsu kamar ba wadda ke shirin tahowa gida ba,tana kallon su hindatu sunata shiri.
Tun sanda ta dawo daga abuja ta lura da wani abu,dabi'un su hindatun su canza gaba daya,abubuwa da yawa sun daina yinsu yanayin shigarsu ya canza sosai,wanda hakan ya bata mamaki,saidai bata taba tambayarsu ba.
Hindatun ce ta qaraso ta taba zahran dake kwance rub da ciki,saita daga kai tana duban hindatu,hijabi ne dan madaidaici a jikinta wanda ta dorashi saman abayarta,wadda ta rufe jikinta ruf
"Tunanin me kike mrs haidar?" Murmushi ta saki,ta tashi ta zauna tana duban hindatun,fuskarta qunshe da murmushi
"Ina mamakin me ya canza qawayena haka tashi guda" murmushin itama hindatun tayi,ta zauna gefan zahra
"Tasirantuwa mukayi da qawar qwarai,hakan shiya canza mu,sannan kuma mukayi aiki da hankali da tunanin da Allah ya bamu,muka ga cewa,babu wata rayuwa ta wayewa face wadda addininmu ya tsara,hakanan kome zakayi kayi abinda zai kauda mummunan tunani a kanka,mukayi karatun cewa samarin yanzu sam basu da ALQIBLA....ko kuma ince ALKIBLARSU mafi yawansu bame kyau bace,ba miqaqqiyar ALKIBLA bace,kowanne yana amfani da yanin shigarmu yana mana hukucin cewa mu din lalatattu ne,duk wanda zai durfafemu zai durfafemu ne da mummunan niyya.....,suna tunanin cewa mu din mazinata ne,mun saba kowacce harka data saba addini da al'adarmu,mukaga meye ribar rayuwar diya mace?,ki killace kanki,ki tsare mutuncinki dana iyayenki,kikai qimarki gidan miji,qima kuma bawai ta budurci kawai ba,harda ta kyakkyawar shaida da kyakkyawan tarihi,abun yabo,abun alfahari da zaki barwa 'ya'yanki da jikokinkin ba,rayuwarki kawai ta zame mana abun misali,yanayin rayuwarki bazai hana a kiraki wayayya ba,saidai komai naki bisa tsari ne,irin tsarin daya dace"murmushi sosai zahra keyi cikin jin dadi da Allah yasa ta zama silar gyaruwar halayyar wasu,ta kuma sake jin dadi qwarai data sake samun tabbacin babu wadda ta saida mutuncinta a cikinsu,sai tace
"Na godewa Allah da yamin baiwar da mutum hudu suka gyara tsarin rayuwarsu saboda ni,Allah yaci gaba da tabbatar damu akan shiriya"
"Amin zahra" hindatu ta fada tana ci gaba da shiryawa,jifa jifa suna taba hira da zahran da har yanzu take kwance
"Wai ba zaki koma gida bane naga babu alamun shiri tare dake?" Baki ta kwabe tana gyara kwanciyar tata,sam sam batajin wani doki ko murnar zuwa gidan
"Zanje,so nake rana tayi sanyi ne"
"Amma zahra....sai nakega kamar akwai abinda ke damunki kwanakin nan" murmushin qarfin hali tayi
"Me kika gani?" Sai data rufe akwatinta sannan ta dawo gefanta ta zauna
"Yanayinki ba kamar yadda na sanki ba,don ba haka mukeyi dake ba....like kamar akwai damuwa a ranki" qaramin tsaki taja
"Ba wani damuwa,kawai yana yine"
"Yanayin kewar soja ko?" Ta fada tana qunshe dariya,cikin qarfin hali da son qaryatawa tace
"Kamar da can na sanshi ne da yanzun zan damu kaina,karki sake wannan batun don bashi bane,stress ne kawai na exam" tabe baki hindatu tayi tana miqewa
"Tunda wannan shine karon farko da kika fara yin exam din,maji ma gani" ta fada tana dariya abunta,batason dogon magana sai kawai ta barta a hakan taci gaba da kwanciyarta.
******** *** *********
Cikin babban mayafinta data yane ilahirin jikinta ta shigo falon,cotton ne mai zanen adon furanni masu kyau,wanda kusan shine mayafin da hajjan tafi amfani dashi tuntuni har yanzu,saboda kaurinsa da suturta jiki,duk siyayyar da za'a mata na sutura tofa sai an nemo mata shi.
"Ashe ka iso,lale maraba" ta fada tana murmushi gami da samun wajen zama,murmushi shima abu sufyan yayi yana saukowa qasa ya gaida hajjan,tana tsaka da amsawa zahra tayi sallama dauke da jakarta
"A'ah.....kamar tare kuke" cewar hajja tana duban zahra,saita saki gajiyayyen murmushi ta samu kujera daya ta zauna
"Ni hajja yaushe rabona da naga ya abu sufyan ma,sai yau" murmushi yayi
"Ku dinne ai kukayi tsada,daga ke har xaki,ganinku nan gaba sai munyi da gasken gasken" murmushi tayi tana rufe bakinta da tafin hannunta
"A'ah bamu isa ba"
"Har kunyi yawa" datse zancan tayi ta hanyar soma gaidashi,don sam ita a kwanakin nan bata jin wani armashi wajen yin raha ko walwala,ita kadai tasan takurar da ranta da zuciyarta ke ciki,suna gama gaisawa ta miqe,taja jakarta zuwa ciki tana tambayar hajja abinci,don tun break din da tayi da safe na zallar ruwan tea bata sake cin komai ba
"Akwai raguwar na rana,don gaje bata nan,saita dawo zata dora na dare".
Kayan jikinta ta cire ta sauya wasu bayan ta shiga daki,saboda taji inna gaje bata nan,tana tunanin ta karba girkin daren tunda Allah ya dawo da ita,kafin nan umminta ta dawo,don ta fara leqa sassan nasu bata taras da ita ba,su ilham din ma suna islamiyya,duk da sun fara zama 'yammata,gidansu sam babu wasa da karatun addini,ita kanta da take boarding duk sanda tazo hutu akwai islamiyyar da take zuwa har a koma hutu,don haka babu wani karatu da yake hanasu karatun addini tun suna qananunsu har a aurar dasu,ko samarin gidan yanzu haka akwai makarantar dare ta maza manya da suke zuwa duk dare,har kwanan gobe.
Fitowarta kenan zata wuce kitchen din taji muryar abu sufyan yana cewa
"A matsayinsa bashi zaije wajen ba....shi xai tura,amma kishin qasarsa yana ya saka kanshi sahun masu shiga wajen,waje ne mai hatsari,wanda yawanci ko rashi aka samu sai randa suka dawo ake qididdige wadanda suka mutun a bada sanarwar mutuwarsun a hukumance.....amma kuma abun daure kan shine,shi din yana da 'yancin fita ai yayi wayarsa,ko ya sauka a masaukin daya zaba.....amma shurun yayi yawa,ace har yanzu babu wani motsi daga wajensa" kamar an buge mata gwiwoyinta haka taji,sai taji kamar ba zata iya qarasawa kitchen din ba,zata zube ne a wajen,daqyar a daddafe dai ta samu takai kitchen din,saita dafe kantar kitchen din ganin tana niyyar zubewa
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" abinda ta dinga maimaitawa kenan,sai taji hawaye na sauko mata,zuciyarta ta shiga gaya mata ya mutu,ya haidar ya mutu kawai.
Kifewa tayi saman kantar ta soma kuka sosai,kuka mara sauti,mai dauke da rashin madafa,batasan iya lokacin data shafe a haka ba,sai data tsinci muryar hajja na fadin
"Ke,lafiyarki kuwa?" Dago kanta tayi da fuskarta ke jiqe jage jage da hawaye ta dubi hajja,cikin muryar kuka
"Hajja....." Saita kasa.magana,ta juya da sauri ta fice a kitchen din,hajjan ta bita da kallo kawai.
Tun daga lokacin bata kuma fitowa a dakin ba bare ta tambaya wani abinci,har zuwa washegari data sake jin abinda ya daga mata hankali,tara su abba yusuf da hajja tayi cikin damuwa tanason su nemo wani labari daga bangaren haidar din,wata kusan biyu shuru?,wannan shi yasa ta qara rafkewa,saiga zazzabi mai zafi ya rafketa.
Ba wanda ya sani saida hajja taji shurun yayi yawa sannan ta leqota,hankali tashe hajjan ta kira mustapha ya kira mata abban tsakiya tun baikai ga fita da motarsa su kai zahran asibiti,koda akaxo tafiya ma kasa tashi tayi,Allah yasa sadiq yana gidan yazo hutu daga wajen aikinsa,shiya dauketa ya kaita bakin motar suka wuce asibitin.
Taimakon gaggawa suka bata,aka daura mata ruwa bayan allurai,ba jimawa bacci mai nauyi ya dauketa.
****** ***** ****** *****
Zaune take saman gadon asibitin,inda ta jingina bayanta da bango,ta kuma miqe qafafunta saman gadon,cup din tea ne a hannunta take kurba kadan kadan,tanayi tana yamutsa fuska,saboda anty aliya ce ta sanyata a gaba akan sai tasha din,tana ta fada gami da bambamin ta yaya zata samu lafiya taqi abinci sai magani da aketa dirka mata,bayan ga ulcer nan itama da takeson tayar mata.
Turo qofar dakin akayi gami da sallama,yaya sadiq ne a gaba dauke da kwanuka,sai hajja dake bayansa,daga bayan hajjan kuma abba yusuf ne.
Dukkansu bakin gadon suka taho kai tsaye,anty aliya na gaida abba yusuf da hajja,ya sadiq kuma ya gaida anty aliyan,gaidasu tayi sannan sukayi mata sannu da jiki,abba yusuf da ya sadiq din basu jima ba su suka tafi suka bar hajjan,don dama ita din kusan kullum yini takeyi.
Dakin saiya zamana daga ita sai hajjan sai anty aliya,sawa tayi aliya ta kawo mata kujera gaban gadon,tana shirin zama tace
"Nidai jikin nan naki har yanzu banga irin sauqin da nakeso ba....anya zahra'u babu wani abun kuma?" Ta tambaya tana dubanta,shuru tayi mata,don batasan amsar da zata bata ba,duk amsar da xata bata din zata zama tamkar tonuwar asirinta ce,sirri ne da a yanzu bata buqatar kowa yasanshi.
Bata kai ga cewa komai din ba wayar hajja ta soma ringing,tayi kiciniyar daukowa ta kasa,saita miqawa aliya
"Ke fitomin da wayar nan,umaima ce don jaraba ta cusa min ita can ciki....ni idan banda dole ma me ya kaini ta'ammali da wannan aba" dariya sosai aliya tayi sannan ta karbi jakar ta ciro mata,idanuwanta ta fiddo waje
"Kai.....haidar ne" zancan da ya sanya zahra saurin dago da kanta,qirjinta yayi wani irin bugawa,saita tsurawa wayar da hajja tayi hanzarin karba,ita dinma kamar zata wafta ne daga hannun aliyan saboda tsabar sauri.
"Assalamu alaikum" hajja ta fara fada bayan ta saita kanta,shuru na wasu sakanni sannan ta qara magana
"Lafiya qalau alhmdlh.....kaiko zaki lafiya?,wanne irin shuru ne satittika masu yawa?" Shuru ta sakeyo kafin tace
"To alhmdlh....Alhmdlh" daga haka saita miqe ta nufi qofar fita wayar na a kunnenta,aliya tabi bayanta,sai zahra ta bisu da idanu,ji take kamar ta tsaida hajjan ta hanata fita,ta jingina kanta da bango tana maida numfashi sanda suka kammala ficewar.
Batasan mintina nawa tayi a hakan ba saijin dawowarsu hajja tayi,ta bude idanunta da sauri,tabi hajjan da kallo,ta tsammaci jin wani abu daga bakin hajjan,amma sai taga taja kujera tayi zamanta abinta kamar yadda ta tashi dazu,hada idanun da sukayi da zahran sai hajjan tace
"Lafiya?,ko jikinne?" Kai kawai ta girgixa mata,ta maida idanun nata ta sake lumshesu,ita kadai tasan yadda zuciyarta ke mata,kamar ta jawo hajja ta tambayeta me yace?,shi dinne da gaske?,saita sanya ran idan anty aliya ta shigo zata ji wani abu daga gareta,aqalla ko relief zata samu.
Saidai koda anty aliyan ma ta shigo shuru kakeji,bata ce da ita uffan ba itama,kamar ma ba haidar din da aketa dakon kiransa bane ya kira,saima suka shiga wata hirar ta daban,hakan ya sake quntata mata,ranta ya baci sosai,sai kawai ta zame ta kwanta ta rufe idanunta kamar me bacci,saidai duk abinda suke tana jinsu,shiga da fitar 'yan dubiya duka,hakanan taji batason magana da kowa.
A hankali ya kashe wayar ya zurata cikin aljihunsa,wani murmushi fuskarshi ke fitarwa,ya dauki cup din baqin tea adan mitsitsin kofi irin na buzaye,ya qara yawan shayin yaci gaba da kurba a hankali,idanunsa kuma nakan sojojin dake gabansu kadan suna training,wanda shi yafara horas dasu,ya dawo yadan huta ne ya kuma yi waya kamar yadda ya tsara.
"Amma.....bansan hikimarka na hana ayi mata maganarka ba,sannan kaidin baka kirata ba" cewar saif dake zaune a gefanshi,sanye da wando da booth na sojoji,sai shirt dake jikinsa,saman kansa hular malafa ce itama irin ta sojojin,sak shigar dake jikin zaki kenan,bambancin kawai shi farar shirt ce a jikinsa,hakanan hular na aje daga gefansa.
Sai daya daga cup din ya qarasa shanye shayin ciki ya dire kofin sannan ya bashi amsa
"Inaso ne a sanda xan koma soyayyata tayi mata yawan da ba zata iya boyeta ba,tayi É—okina fiye da kowanne mutum cikin ahalina...." Murmushi saif ya sake sannan yace
"Kana da yaqinin tana sonka kota fara sonka kenan?" Miqewa tsaye yayi ya maida hularsa saman kansa,ya dauki bindigar da sukayi amfani da ita,ya kira daya daga cikin sojin dake zirga zirga ya bashi yace yakai tint dinsa sannan ya maida dubansa ga saif
"Ba'a iya rayuwa da al'ummata nake soja kawai ba,har a soyayya ni din sojan ne,ban barta na taho nan ba,sai dana tabbatar na dana mata tarkon da bata isa ta tsallakeshi ba,na bar mata tabon da bazai taba goguwa ba........na yarda da kaina,na kuma yarda da qwarewata....".
Miqewa saif yayi yana murmushi yayi saluting nashi,sai shima ya saki murmushin ya juya yana takawa a hankali zuwan wajen sojojin daya baro.
******** ********
Tun daga ranar take kasa kunne ko zataji wani yayi zancan ya zakin amma bata ji ba,har hajja kuwa,saidai wani lokaci idan ya kira hajjan tana gane hakan,amma harsu gana wayar ta koma gida ba zatace da ita komai ba.
Sannu sannu saita fahimta bayan hajjan ma yana kiran manyan gidan,ranar data gane hakan kawai sai taji ranta ya baci sosai,a lokacin nurse tana zare mata ruwan da yayi saura
"Ya kamata ku sallameni hakan,na gaji da zaman asibitinku" murmushi nurse din ta saki
"Madam ko kina tausayin me gidane daya biya kudin asibitin?,shi yace a barki ki huta sosai koda an gama baki dukka magungunan" shuru tayi tana mamaki,wanne me gida kenan?,ta tambayi kanta,amma kuma tunda taji tace maigidanta lallai ba shakka ya haidar take nufi,idan hakane shin yasan bata da lafiya?,tambayar da bata da amsarta kenan.
Washegari ta takura akan lallai sai sun sallameta,hakanan suka rubuta mata sallamar tunda ta takura suka tattara suka koma gida.
Tun randa suka koma gidan tayi qoqarin basar da komai,tayi qoqari ta cire tunaninsa da damuwa dashi daga ranta,saboda ta fuskanci akwai wata a qasa tattare da hajjan,sai taci alwashin ba zata bari kuwa bari hajjan ta gano lagonta,amma abinda bata sani ba shine shin zata iya?.
_gobe ina da uzururruka,idan kunjini shuru kuyi afuwa,idan kuma dama ta samu zaku ganni da yardar mai duka,na gode_
39
Da yammacine liqis,tana zaune a falon hajjanta,gidan yau kusan shuru yake saboda dukka yaran gidan suna islamiyya,saura kuma kowa yana wajen sabgarsa ta yau da kullum,kamar sassan nasu yau su biyu ne daga ita sai hajjan.
Da yake anguwar tasu babu laifi basa rasa nepa,tv ce a kunne take aiki,saidai dukka hankalin zahra yana kan wayar hannunta,charting take,kuma tana jin dadin xaman sosai.
Wayar hajja dake gefanta taji ta dauki burari,ta waiwaya ta kalli wayar da yake tana dab da ita kan hannun kujerar da take kai,number ce babu suna,yanzun hajja ta tashi bata jima ba ta shiga toilet,saita miqa hannunta daya ta jawo wayar ta daga ta kara a kunnenta,yayin da daya hannun take ci gaba da danne dannenta dashi a tata wayar
"Hajjan bata kusa,amma idan ta iso xa'a gaya mata" shuru taji anyi,duk da cewa da alamu bawai rashin network bane,tunda ga hayaniya irin daga dan nesa da inda me wayar yakeyin wayar nan tana shigo mata tana ji,saita dan maida hankalinta kan kiran,ta daga wayar ta duba taga ana kan layi,ta sake maidawa kunnenta tana fadin
"Hello....ance hajjan bata kusa,idan ta fito za'a gaya mata" jin still dai an sake yin shuru sai ta daga wayar daga kunneta hadi da jan tsaki,ta kashe kiran,ta maida wayar gefanta ta aje taci gaba da chart dinta.
Tana