Showing 63001 words to 66000 words out of 114799 words

Chapter 22 - Dr Khaleel Book Complete Document by Khalisat Haidar .docx

10 Mar 2025

8436

mugun faduwa, Abba ya jefa masa takardan ya dauka da sauri don ko kadan shi bae lura ma da rubutun ba ranan da Ashnaah ta basa, sake takardan yyi ya fadi kasa da wani irin shock, Abbansa da tuni ransa yyi mugun baci yace "lallai ka cika mahaukaci khaleel, kar ka raina mana wayo a nn, ka ga mun yi kama da yara ko marasu sanin ciwon kai, be careful fa" mikewa yyi a fusace yana kallon abokansa yace "plss ku tashi mu tafi, Allah ya ba mu alkhairi Alhaji" rikice masu Khaleel yyi ya dinga rantse rantse shi ba shi ya rubuta takarda ba, ya xamar masu kmr wani xautattce, Abban Ashnaah yyi murmushi yace "to ko da saki daya dan ku yyu ma 'ya ta banga dalilin da xan bari ta koma gidansa ba sae dae muje duk inda xa mu, ku dan ban lkcinku ku saurari abinda yasa nayi wnn furucin ba cin fuska ba" komawa Abban Khaleel yyi ya xauna, Abba ya shiga masu bayani a nutse ynda aka yi Khaleel ya auri Ashnaah snn ya kara masu da duk bayanin da Ashnaah tayi masa daxu, Abban Khaleel ya mike yana murmushi yace "ae hkn dai dai ne, kuma Alhmdllh da ta ga takardan, Allah kuma yyi mata sakayya" sallama yyi masa snn suka fice da abokansa da duk suma xancen bae masu ddi ba suka bar Khaleel nn xaune, da kyar ya isa gida a motarsa yana ganin double double, umminsa dake falo ta mike a rude yanayin da ta gan dan nata, ya xube nn gabanta ta duka da sauri tace "ya aka yi kuma? baku je bne?" daura kansa yyi a kafadarta ya shiga hawaye, rungumesa tayi a rude tace "ka gaya min ya ku ka yi son" kasa cewa komae yyi, hkn yasa ta dago sa suka nufi sama ta shiga bedroom dinta da shi ta sa ya kwanta ta xauna gefensa, ba a dau lkci ba bacci ya daukesa tayi shiru tana kallonsa, tasan jiya kwata kwata bae runtsa ba don a dakinta ya kwana, komawa falo tayi a sanyaye ta ci gaba da abinda take, can wajen azahar Khaleel ya tashi, sae da ummi ta tilasta masa ya ci abinci ya sha tea snn yyi sllh. Tana xaune gefensa bayan ya idar tace "ka gaya min ynda aka yi son" a sanyaye murya can kasa yace "mum its a set up, I knw it is, da writtin dina aka yi rubutun no body will blive I wasn't d one dat wrote it...." Kasa ci gaba yyi ta dalilin tokarewa da muryarsa yyi, lkci daya idonsa ya kada ssae, yana girgixa kai yace "I dont think xan iya rayuwa ba ita Ummi na ku taimake ni plss" hawaye ya gangaro idonsa, hawaye ne ya cika idon Ummi a hnkli tace "wa kke tunanin xae maka hka," shiru Khaleel yyi kmr me naxari snn ya mike tsaye da sauri yace "Ameesha! Ita kadae ta iya kalan rubutu na," makullin mota ya dauka da sauri ya fice daga dakin Ummi ta bi sa da sauri har kasa tana kiransa amma tuni ya shige mota ya figi motar yana danna horn aka bude masa gate ya fice a guje.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

71.....

A waje Khaleel yyi parkin bae ko kalli masu gadin da ke gaishesa ba ya nufi cikin gidan da sauri, bae samu kowa a falo ba ya nufi sama fuskar nan tasa bbu alamar rahama ya bude kofar Ameesha, xaune ya sameta gaban madubinta idon nn nata yyi jajir da ganinta kasan ta ci kuka, ya nufeta ya fixgota lkci daya ya watsa mata wasu tagwayen mari masu lfya yana huci yace "ke kika rubuta takardan saki ki ka ajiye dakina don fateema ta gani ko, ki fada min me nayi maki a rayuwa kika min hka, duk halaccin da na maki na aure ki duk da ba son ki nake ba da wnn kaxamin aikin xa ki biya ni is dis my reward? I knw uwar ki ce ta sa ki 3dayz bck da ta xo, confess dat kar in hallakaki" cikin tsawa ys karashe mgnr lkci daya ya kuma watsa mata wani marin ya hade ta da bango yana huci idonsa yyi ja ssae, cikin kuka ssae muryarta baya fitowa ssae take cewa ban gane me kke nufi ba Khaleel, hw dare yhu xaka dinga duka na me nayi maka, bata rufe baki ba ya shaketa, ba karamin wahala ta sha ba ranan don dukan fitan hnkli ya mata, duk ya xama kmr wani mahaukaci, ya fice daga gidan. Ashnaah na xaune dakinsu ta jingina da gado Ashfah ma na xaune sae hiran film din da ake a tv take mata, ko kadan Ashnaah bata san me yar uwartata ke cewa ba, tayi xurfi cikin tunanin da take Ashfah ta dafa kafadarta jin ta kirata ya fi sau uku bata san tana yi, a dan tsorace Ashnaah ta dawo daga tunanin da take ta ce "me kika ce" Ashfah tace "Haba sister, wae tunanin meye hka kike, ain't yhu happy kin dawo cikinmu ynxu, wats ur prblm plss tel me" Ashnaah ta kirkiro murmushi tace "nothin sister just thinkn of my past" Ashfah tace "forget dat plss its nt worth rememberin, ko baki yi farin cikin dawowa cikin mu bne" Ashnaah tayi murmushi tace "am happy sister" Ashfah tace "to bana son in kara ganin kin yi shiru hka pls" Ashnaah ta gyada mata kai kawae, dai dai nn wayar Ashnaah ya shiga vibrate, Ashfah ta miko Mata ta karba a sanyaye tana kallon screen din, usman ta gani ta mika ma Ashfah tace "ki ce ina wanka bana cikin mode din mgna" Ashfah ta karba tayi ynda tace mata snn suka yi sallama suka ajiye wayar, Ashnaah ta dubi Ashfah tace "har an kawo kayan nawa ne?" Ashfah tace "wae masu gadin basu Bari ba wae mai gidan baya nn" Ashnaah bata ce komae ba, Ashfah tace "wae Abba yace mu je ki gaida inna anjima" kai kawae Ashnaah ta gyada mata, aka bude kofar dakin momy ta shigo tana kallonsu tace "abincin waye har ynxu a kitchen," Ashfah tace "na Ashnaah ne wae bata jin yunwa" momy ta hade rae tana kallonta tace "wae wani abu na damun ki ne, ina fa sane da safe baki yi wani kwakwakkwaran kari ba," mikewa Ashnaah tayi tana kirkiran murmushi tace "kallo mu ke ne momy ynxu xan je in dauka" ta gefen momynta ta bi ta fita, momy ta bita da kallo snn ta juya tana kallon Ashfah tace "wae me tace maki ke damunta" Ashfah tace "ynxun nn na gama tambayarta tace wae kawae past take tunawa" momy bata ce komae ba ta juya ta fita. Ashnaah ta sauko downstairs ta nufi kitchen don daukar abincinta da ya kusa awa hudu a ajiye don har an kusa gama na dare, bin ta da kallo Abbanta yyi, ta fito daga kitchen din rike da abincinta xa ta koma sama ys kirata, a sanyaye ta karaso falon ta duka ta amsa tana kallonsa, ya ajiye remote din hannunsa yana kallonta yace "kina da damuwa ne Fateema" ta girgixa masa kai tace "A'a Abba daga bacci na tashi" Abba yace "ok, gobe sae ki shirya driver ya Kai ki sch, kun kusa fara jarabawa ko?" Ta gyada masa kai tace "eh sae next wk xa mu fara wae, amma ynxu sae upper wk" yace "to shknn ki dage da karatu kin ga an wuce ki ssae u have to work hard to meet up" ta gyada masa kai tace "in sha Allah Abba" mikewa tayi ta dauki plate din abincinta ta nufi sama. Khaleel na komawa gida ya shige bedroom dinsa ya saka key ya shiga neman layin Najeeb, bugu daya ya daga, a raunane Khaleel ya shiga cewa "I need yhu plss ka xo ynxu Najeeb" bae jira cewarsa ba ya kashe wayar ya dafe kansa dake juya masa. "Ae ni bbu abinda xan ci gaba da ce maki da ya wuce Allah ubangiji ya kara maki, banxa kawae da bata yo halina ba, me gare Khaleel da har kika nace masa? Ya nemi kashe mana ke, ae sae naga uban da ya tsaya ma Khaleel a garin nn, xae san ya taba min ya ta, sae inda karfin ya kare wllh" cewar mahaifiyar Ameesha ga Ameesha dake kwance bbu abinda take furtawa sae wayyo Allahna, Alhaji mukhtar da ke xaune

Sae girgixa kafa yake shi ma fuskar nn tasa a daure ya mike ya dauki wayarsa ya fice daga dakin. Najeeb yyi shiru yana kallon Khaleel bayan ya gama jin bayaninsa, Khaleel ya dafe kansa har lkcn yana hawaye a sanyaye yace "plss don't b surprise frnd, wllh ni kaina nasan na kamu da son fateema da dde wa, help me plss give me a solution to dis prblm I beg yhu" dafa sa Najeeb yyi a hnkli yace "its OK frnd, ka bani address din su Fateeman, I

will c wat to do" nan Khaleel ya basa Address dinsu Ashnaah, Najeeb ya kwafe a wayarsa snn yace "amma me yasa xaka xarga Ameesha har ka doketa, idan ba ita bace ba fa" Khaleel yace "don't tell me dat, ita kadae ta iya rubutu kmr nawa, snn bayan ita bbu mai shigar min daki, to wae ma mu nawa ne a gidan da xaka ce kar in xargeta, ko kwana biyar fa ba ayi da xuwan uwarta gidan ba abun nn ya faru, to wa ya sa ta idan ba ita ba" Najeeb ya mike yana kallon abokin nasa yace "kar ka damu frnd ka kwantar da hnklinka, gobe xan tafi can gidansu fateeman."

~Dr khaleel~ By khaleesat Haiydar 72..... Nan Najeeb yyi masa sallama ya fita, Khaleel ya fada kan gadonsa ya runtse ido, duk ji yyi duniyar tae masa xafi, Ashnaah da komae nata kadae ke masa yawo a ka, nn da nn ya ji kmr xaxxabi xae rufesa. Karfe shidda saura na yamma Abban Khaleel ya shigo gida ya nufi dakin Ummi fuskarsa a daure yana kallonta yace "ina ibraheem" da kmr baxa ta ce komae ba sae dae tace "me ya faru kuma" cikin tsawa yace "nace yana ina" bae rufe baki ba Khaleel ya shigo dakin kmr wani mara lfya a sanyaye yace "gani Abba" kallonsa Ummi ta tsaya yi ganin ynda ya wani rame lkci daya, Abba ya juya yana kallonsa a fusace yace "don uwar ka wae halan kana shan giya ne" shiru Khaleel yyi bae ce masa komai ba, Abba ya daka masa tsawa yace "ka fada min me yarinyar mutane tayi maka ka ne mi kasheta yau" fada ssae Abba ke yi kmr xae maresa shi dae Khaleel bae ce komae ba hka ma Ummi, Abba ya gaji don kansa ya juya ya fice a fusace, Khaleel ya daga kai ya kalli mum dinsa snn ya juya ya fice daga dakin. Yana shiga dakinsa da minti goma kiran dad din Ameesha ya shigo wayarsa, da kmr baxae daga ba sae kuma ya daga yyi masa sallama, ba tare da ya amsa ba yace "ka xo gida ka same ni" bae jira cewar Khaleel ba ya katse wayar, sae da aka yi sllhr magrib Khaleel ya samu umminsa yace xae fita snn ya kama hanyar gidansu Ameesha, xaune ya tadda iyayen nata a falo da yayyinta maxa, Abbanta kadae ne ya amsa gaisuwarsa, ya xauna kasa yana kallon Abban nata bae dae ce komae ba, Alhaji mukhtar yace "wato da abin da xa ka biya mu knn ko Khaleel, dats great" takarda da pen ya dauka ya jefa gaban Khaleel yace "bani takardan ta ynxu" daukar takardan Khaleel yyi da pen cikin minti daya ya gama rubutun da yake ya dauka ya risina ya mika masa, karba yyi yana duba content din takardan kmr hka, "Ni Muhd Khaleel na saki khadija saki daya" Alhaji mukhtar yyi murmushi ya dauki wani takardan yyi rubutu yyi sign snn ya mika ma Khaleel, khaleel ya karba ya shiga duba rubutun, sack letter ya gani, mikewa yyi ya cukuikuye takardan ya jefar nn tsakiyar falon yace "sae da safen ku" snn ya juya ya fice daga gidan, mum din Ameesha tace "duk inda xaka neman aiki baxa ka samu matsayin da ka rasa ynxu ba sha sha sha kawae mahaukaci me gare ka xaka walakanta yar mi" Khaleel na shiga motarsa ya hade kae da steering xuciyarsa na masa wani irin xugi, yes tunda ya rasa Ashnaah komae ma ya rasa, wasu hawaye ne suka shiga sakko masa, duk duniyar yaji tayi masa xafi ya rasa me xae yi ya ji ddi, y him?" Da kyar ya iya jan motar ya bar layin, har ya kama hnyar gida yyi tunanin xuwa layinsu Ashnaah ko Allah xae sa su hadu, yana shiga layinsu cikin ikon Allah ya gansu ita da Ashfah sun dawo daga gidan inna knn.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 73..... Parking Khaleel yyi daga gefe ya fito da sauri ya nufo su, kamshin turarensa kawae Ashnaah ta shaka ta juya da sauri tana ganinsa ta ruga a guje ta nufi gate dinsu da sauri, Da mugun mmki Ashfah ke bin Ashnaah da kallo har ta shige gate din kawae gani tayi ta kwasa a guje ba dalili, juyawa tayi da sauri don ganin me take ma gudu, suka yi ido hudu da Khaleel ita ma ba sae ta ruga a guje ba, bin ta yyi da sauri ya shiga kiranta yace "don Allah don Annabi ki tsaya sister," kasa ci gaba da gudun ta yi ta ja burki ta tsaya ba tare da ta juyo ba, karasowa yyi inda take da sauri ya marairaice mata yace "Plss kanwata, kice da fateema tayi hkuri ta saurareni ko na minti daya ne plss help me beg her" Ashfah ta rasa abun cewa can dae tace "to bari in je in mata mgna" da sauri yace "yauwa kanwata ngd ssae ina jira plss" ta gyada masa kai ta nufi cikin gidansu, dakinsu ta samu Ashnaah kwance tana ta rusa kuka, ta karaso da mmki tana kallonta tace "meye abun kuka kuma sister, Kinga fa ni bana son hka, don me xa ki dinga daga min hnkli ne" Kmr ta kara tunxurata ta kuma fashewa da wani matsanancin kukan, Ashfah ta nemi gu ta xauna fuskarta dauke da damuwa tace "don Allah Ashnaah ki daina kukan nn wllh bana so yana damuna" da kyar ta lallasheta tayi shiru sae a snn ta tambayeta a sanyaye ko Khaleel ya tafi, Ashfah ta dan yi shiru snn tace "ehh ya tafi" komawa Ashnaah tayi ta kwanta tare da lumshe idonta kmr mai shirin bacci, Ashfah ta lulluba mata bargo tace "kiyi baccin ki kawae" Washegari da safe driver ya wuce da Ashnaah makaranta kmr ynda Abba yace, ko kadan Ashnaah bata gaya ma kawayenta abinda ke damunta ba kmr ynda suka bukaci sani, through out lectures din ranan shiru kke jin Ashnaah, lectures din ma ba fahimtarsu take ba kwata kwata, Karfe uku da rabi suka ga lectures Ashnaah ta dauki Jakarta ba tare da ta jira kawayen nata ba ta fito don jiran drivernta don tasan at anytime xae xo tunda ta fada masa lkcn tashin su, motar usman ta hango ta dauke kai da sauri amma har ya ganta, ya karaso inda take snn ya fito daga motar da damuwa yace "y ain't yhu pickn my cal Ashnaah" Ashnaah tace "to ina lecture din xan yi pick din cal dinka," shiru yyi yana kallonta, hkn yasa ta dan saki ranta tace "lecture muke ne wllh ka ga fitowa ta knn" yace "bbu damuwa, ya kike ya gida" tace "Alhmdllh" yace "ynxu xa a xo daukarki ko" ba tare da ta kallesa ba tace "ehh" ya dan yi shiru snn yace "kin ko gaya min lkcn da mijin ki ke fita da safe Ashnaah, koh kina ga...." Da sauri ta katse sa tace "ka ga ni fa we re no longer togeda, ya bani takardata tun shekaran jiya ina gidanmu" da mugun mmki Usman ke kallonta yace "waow re yhu serious dear shine baki gaya min ba, waww am so..." Da sauri Ashnaah tace "ka ga, sae mun yi waya ga driver can ya xo" bata jira cewarsa ba ta nufi gun motar gidansu da sauri don ba karamin farin cikin xuwan drivernsu tayi don ko kadan bata son jin mai usman ke shirin cewa. Karfe hudu da kusan rabi Ashfah ta sauka daga a dai daita sahun da ya ajiyeta dai dai bakin gate dinsu, da ganinta kasan daga makaranta take, Najeeb da ke jingine jikin motarsa can nesa da gidansu ya karaso da sauri ganinta, sallama yyi mata ta juya tana kallonsa, wani irin kallo tayi masa xata shiga gida ya sha gabanta da sauri yace "ki saurara pls fateema" Ashfah tayi tsaki tace "ni ba fateema bace malam ka bani hanya" xae yi mgna sae ga Ashnaah ta fito daga cikin motar da yyi parkin gefensu don drivern yace baxae shiga ciki ba momy ta aikesa kasuwa, juyawa Najeeb yyi yana kallon Ashnaah snn ya kuma juyawa ya kalli Ashfah da mugun mmki, kallo daya Ashnaah tayi masa ta dauke kai ta karasa xata shiga gida, Ashfah kam tuni har ta shige gida. Najeeb yace "wait plss fateema" juyawa tayi tana kallonsa, sae kuma ta tsaya don jin me xae ce, ya karaso inda take da sauri yace "dama ku yan biyu ne" juyawa Ashnaah tayi xata shige gida ganin tambayar bae da ma'ana, yyi saurin cewa "ki saurareni plss fateema" Ashnaah ta kuma juyawa tana kallonsa tace "ka ga idan ba ka da abun cewa ka rabu dani don bana son Abbana ya gani tsaye a nn" Najeeb yace "OK but mgnr na da tsayi, ko in bari da nyt" ta daga kafa tace "Allah ya kai mu" snn ta shige

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login