Showing 84001 words to 87000 words out of 114799 words
Chapter 29 - Dr Khaleel Book Complete Document by Khalisat Haidar .docx
masa, wato ashe ya ma san tana da ciki knn, Shiru tayi tana naxarin magungunan da ya bata ranan har yana cewa kar ta kuma shan ko wani magani xa a bata a gida, kuka ta fashe da tace "wllh baka da imani, ka hada ni da iyayena kawae ka raba ni da su don son xuciyar ka, to bana son cikin xubar wa xanyi" kuka kawae take kmr ranta xae fita ta katse kiran, Khaleel da idanunsa suka kada suka yi ja ya dafe kansa da ke Sara masa xuciyarsa nai masa kuna. Kiranta ya kuma yi, Ashnaah da ke kuka har lkcin ta kasa kin daga kiran nasa duk da ta so yin hkn, ta dauka tayi shiru, a sanyaye yace "kiyi hkuri fateema xan cire maki cikin na maki alkawari tunda ba kya so, ynxu plss ki gaya min inda ki ke" taki cewa komae na wani dan lkci snn a hnkli ta gaya masa inda take, cikin mintunan da ba su wuce sha takwas ba Khaleel ya iso gun da ta gaya masa take, yana gama parkin ya fito ya nufi inda ya hangota da sauri ya durkusa gabanta ya kamo hannunta da damuwa yace "am vry srry wife, I caused all dis" kuka ta sakar masa, duk ya rikice yana lallashinta, ganin taki yin shiru yasa dago ta ya rungume abarsa, ta tsaida kukan da take da sauri ta kwace kanta ganin a titi suke, kama hannunta yyi tana ganin jiri har suka isa motarsa snn ya bude mata front seat ta shiga, ya xaga ya shiga shi ma ya tada motar suka bar wajen, ssae ta ba Khaleel tausayi ganin ynda ta da da ramewa da ganinta ka ga mai laulayi, ga kuma kukan da ta ci, kwantar mata da kujerar motar yyi ta kwanta, nn da nn bacci ya dauketa, gidansa ya nufa da ita, yana gama parkin ya fito ya dauki abarsa ya shiga ciki da ita, ta bude ido da sauri tace "meye hka" bedroom dinsa ya shiga da ita, ya cire bedsheet din kan gadon snn ya kwantar da ita.
94.....
Mikewa xaune tayi da sauri ta wani daure fuska don haushinsa kawae take ji, a sanyaye yace "srry na ga kina bacci ne" ta dauke kanta kawae har lkcn fuskarta a daure, mikewa yyi jiki ba kwari ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, hawaye ne ya shiga bin kuncinta duk she is confuse fushinta xata nuna masa ko jawo mijinta xata yi jiki. Jinginar da kanta tayi jikin gadon tana tunanin rayuwarta tun daga ranan da ta fara haduwa da Khaleel, wasu hawaye masu xafi suka shiga sakko mata, tana nn a hka har bayan minti talatin ta ji an kira sllhn Azahar, mikewa tayi a hnkli don xuwa tayi alwala taji jiri ya debeta ta dafa bango da sauri kan ta kai kasa ta koma kan gadon ta xauna, kasa mikewa tayi har aka idar da sllh Khaleel ya shigo dakin, ba karamin tausayi ya bata ba yanayin da ya shigo, ya karaso gabanta ya duka ya ajiye mata ledan abincin hannunsa da plate yace "ga abinci na siyo maki ki sakko ki ci" kallonsa kawae take ya bude abincin ta ga dafa duka ne da naman kaxa, nn da nn cikinta ya hautsine aroma din abincin na bugar ta, mikewa ta shiga kkrin yi da sauri ya lura da hkn ya mike yace "me ya faru, amae kike ji" toshe bakinta tayi ta sakko daga kan gadon tayi baya xata fadi ya kamota da sauri ta durkushe kasan dakin ya bi ta har lkcn yana rike da ita ta shiga kwarara masa aman a jiki, ssae ta bashi tausayi ganin bbu komae cikinta, gashi she is too young ace tana da ciki ynxu, yana rike da ita yana mata sannu a sanyaye har ta gama ta fada jikinsa tana mayar da numfashi ya rungumeta, sun fi minti biyar a hka snn ya dago kanta a hnkli yana kallon idonta da yyi ja yace "Sannu wife" sunkuyar da kanta tayi kawae, mikewa yyi ya dauketa suka nufi bathroom, da kansa ya gyara mata jikinta bayan ya cire mata kaya, snn shima ya gyara nasa jikin ya daukota suka fito ya kwantar da ita kan gado ya lulluba ta da bargo snn ya shiga gyara dakin, ko da ya gama har tayi bacci ya xauna gefen gadon a hnkli yana kallon kyakkyawan fuskarta wani mugun shaukin sonta na fixgarsa, yasan he can't do without Fateema, daura hannunsa yyi a hnkli kan goshinta ya ji xafi ssae, ya mike ya fita xuwa kitchen ya hado Milo kawae ba madara ya dawo dakin snn ya shiga tashinta a hnkli, bude ido tayi tana kallonsa, ya dago ta yace "ki daure ki sha tea plss sae in ba ki magani, jikin ki yyi xafi" girgixa masa kai tayi da kyar tace "Amae xan yi" rungume ta yyi yace "A'a baxa ki yi ba ruwan tea ne kawae, ki rufe idon ki ki shanye ynxun nn" girgixa masa kai tayi alamar baxa ta sha ba don ta kasa mgnr ma gaba daya, ya dauko tean ya dago kanta, ta sakar masa kuka tana girgixa kai, da kyar ya lallabata tayi sip uku don bbu xafi, yyi yyi da ita amma ta ki karawa, rungumeta yyi ya shiga shafa bayanta a hnkli ganin amae take son yi, har sae da ya ga ya fada mata snn ya kwantar da ita yace yana xuwa, makullin motarsa ya dauka ya fita ya nufi pharmacy ya siyo magunguna da allurori ya dawo ya sameta tana bacci, yana cikin hada alluran wayarsa da ya ajiye gefen gadon yyi ring, ya dauko wayar yana kallon screen din ya ga Dad dinsa ne me kiran, gabansa ya fadi don har ya manta rabon da ya kirasa, 'karan wayar ya tada Ashnaah ta shiga juye juye don wani ciwo da taji cikinta ne ko mararta ne ta kasa tantance wanne ne ke mata ciwon, mikewa Khaleel yyi ya daga kiran, gabansa na ci gaba da faduwa yyi sallama a hnkli, "Maxa maxa ka xo ynxun nn ka same ni a gida duk inda kke" abinda ya ji dad dinsa ya ce knn ya katse kiran a take, Khaleel ya ajiye wayar a sanyaye ya juya yana kallon Ashnaah ya karasa kusa da ita da sauri ya dagota yace "me ya faru" ta fashe da kuka tace "wayyo Allahna ciwo yake min" da damuwa yace "ina?" Taki cewa komae sae kuka take tana yarfe hannu, allurorin da ya gama hadawa ya dauko don yi mata, da kyar ya samu yyi mata don ta basa wahala ssae, ya rungumeta yana lallashinta ta gaji da kukan tayi shiru don kanta daga karshe bacci ya dauketa.
18 mins · Khaleesat Haiydar...
Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar
95.....
Mikewa Khaleel yyi bayan ya lullube ta ya koma can gefen gado ya xauna ya dafe kansa yana tunanin kiran da Dad dinsa yyi masa na gaggawa, juyawa yyi yana kallon Ashnaah, can ya Mike yana kallon agogo ya ga uku da rabi ya dauki car key dinsa ya fice daga dakin don xuwa amsa kiran dad din nasa don ya san baxata tashi ba a lkcn, ana kiran sllhn La'asar ya isa gidan, sae da ya fara shiga masallaci yyi sllhn snn ya shiga gida, Ummi na kitchen da rukayya suna girki, ya shiga kitchen din ya gaida umminsa, ta amsa masa ba tare da ta kallesa ba, jikinsa yyi sanyi jin irin amsawar da Ummi tayi masa, yana kallon rukayya yace "Abba fa?" Rukayya tace "yana falonsa" a sanyaye Khaleel ya nufi falon dad dinsa a Sama yyi sallama ya shiga, xaune ya sami dad din nasa da amininsa sae kawunsa, ya nemi kasa daga gefen kawunsa ya xauna ya gaishe su kansa a kasa, Kawunsa kadae ne ya amsa, Dad dinsa ya mike yana masa mugun kallo yace "me na gaya maka kwanaki Khaleel" shiru Khaleel yyi bae ce komae ba, ya daka masa tsawa yace "are yhu daft?" Khaleel ya dago a hnkli yana kallonsa still bae ce komae ba, Dad yyi murmushin takaici yace "har ni xaka dinga ja ma ana biyo wa har gida ana ci ma mutunci ko Khaleel," sunkuyar da kai Khaleel yyi kawae, Kawunsa yace "wae yarinyar nn ita kadae ce mace a duniya Ibrahim, yau ko da ace baka saketa ba baxa ka iya rabuwa da ita ba ko dan tijaran da mahaifanta ke ma ubanka?" Dad yace "to bari ka ji khaleel wllh daga yau ka kara nuna kasan yarinyar nn ba ni ba kai har abada, maxa maxa ka sallameta ta koma inda ta fito idan ba hka ba ka ga bacin raina, na haneka da kara interact da ita bbu kai ba ita, na raba ka da yar matsiyatan nn daga yau ta je can ta karata, kuma duk inda xa mu shiga ka amsa cikin da ke jikinta na ka ne bn yafe maka ba, tashi ka ban waje malam" Khaleel da tun fara mgnr Dad dinsa xufa ke karyo masa ya dago kai da kyar yana kallon dad din nasa da idanuwansa da suka kada, Alhaji mukhtar ya daka masa tsawa yace "uban me kke jira mister man, c'mon get lost" hawaye ne suka shiga sakko masa da kyar yana girgixa kai yace "Dad ni bn saketa ba wllh matata ce har ynxu, kayi hkuri dad I can't deny her pregnancy" bae rufe baki ba dad ya sauke masa mari, tunda yake a iya saninsa Dad dinsa bae taba marin sa ba sae ranan, Khaleel ya kasa dago kansa cikin tsawa dad yace "har ni xaka bude baki kana gaya ma wnn mgnr? to wllh Khaleel I mean my wordz idan har baka rabu da yar marasu mutuncin nn ba bbu ni bbu kai, shari'a fa ubanta yace xae yi da mu," Khaleel ya dafe kansa har lkcn yana hawaye yace "kayi hkuri Dad idan nace xan guje ta ban san halin da xata shiga ba, kuma ni ina son matata, forgive me dad" kallonsa duk suka tsaya yi da mmki, dad yyi murmushin takaici yace "hka kace koh?" Khaleel bae ce komae ba har lkcn yana rike da kansa, dad yace "gud, bani dukka makullan gidajena dake hannunka da documents dina," Khaleel ya gyada kai da kyar yace "toh" snn ya mike ya fice daga falon duk suka bi sa da kallo da mugun mmki, gida Khaleel ya koma, har lkcin Ashnaah bata tashi ba ya dauki duk kaddaran dad dinsa dake hannunsa a dakinsa, snn ya fito ya samu mai gadinsa ya basa cheque din dubu hamsin yace ya ja jari ya sallamesa don xae rufe gidan ne sanin gidan dad dinsa ne ba nasa ba, abubuwan da yasan xae bukata ya kwashe a dakinsa ya kai cikin mota, snn ya dawo dakin ya shiga tada Ashnaah a hnkli, bude ido tayi tana kallonsa, ya sakar mata murmushi yace "srry na tashe ki koh?" Dagota yyi ya dauki hijab dinta ya sa Mata snn suka fito ya kulle gidan, ita dae bin sa kawae take don jiri ne ke dibanta, mota ya bude mata ta shiga ya kulle snn ya xaga ya shiga motar ya fice daga gidan ya fito ya kulle gate din ta waje don har mai gadin ya wuce snn ya koma motan ya shiga ya tada ya nufi gidansu, bacci Ashnaah take daga xaunen da take cikin motar ko da ya isa kofar gidansu, hkn ya basa daman fita ya nufi cikin gidansu ya haura sama xuwa falon dad dinsa, ynda ya barsu hka ya same su, ya isa gaba
~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar 96..... A hnkli Khaleel ya
shiga tada Ashnaah a cikin mota bayan ya shiga hotel din yyi
masu bookn din daki ya fito, Ashnaah ta bude ido tana kallonsa,
da ganinta kasan bacci ne ssae a idonta, ya kamo hannunta yace
"Cum on wife mu je ki kwanta, I knw yhu need rest" da
taimakonsa ta fito daga motar ta shiga bin haraban hotel din
kawae da kallo, snn ta juya tana kallonsa, murmushi ya sakar
mata ya nufi entrance din shiga hotel din yana rike da hannunta
har lkcn, bin sa kawae take har suka shiga hotel din ya haura
sama da ita, room din da aka bashi suka nufa ya tura kofar dakin
suka shiga, hijab din jikinta ya cire mata ya shimfida kan neat
bedsheet din da ke kan gadon dakin snn yace ta kwanta tayi
baccinta, bbu musu ta kwanta shi kuma ya fita don shigo da
abubuwan da yasan xa su bukata, ko da ya dawo har ta koma
bacci, ya ajiye jakar hannunsa ya xauna gefen gadon a sanyaye ya
dafe kansa da yyi masa nauyi yana tunanin abun yi ynxu, yes
yana da 4.5 mlln a acc ynxu wat is he suppose to do, idan yace
xae siya gida there will b nothin left he knw, to da me xae kula da
ita da bbyn da ke cikinta idan ya siya gidan, yes sae ya nemi aiki
to meet up their needs nd demands idan ya siya gidan ynxu, kmr
wnda ya tuno abu ya girgixa kai a hnkli ya lumshe ido yace "No!
lookn 4 job is a kinda hell ynxu, dafe kansa ya kuma yi a
xuciyarsa yace "its better I rent an apartment, yes 5 to 6 hndrd
thousand I guess" shiru yyi yana tunanin shawaran da ya ba kansa
na karshe, ajiyar xuciya ya sauke ganin hkn kadae ne abun yi
ynxu, wayarsa dake gefensa ya shiga ring ya daga da sauri ya sa
cylnt don kar ya tada Ashnaah, ya ga Najeeb ne ke kiransa, da
kmr baxae daga ba don wani mugun haushinsa yake ji, sae kuma
ya daga yace "ya aka yi?" Daga daya bangaren Najeeb yace "kana
gida ne? Gani nn xuwa ynxu." Khaleel yace "bana gida ina Zaria,
Akwae matsala ne?" Najeeb yace "of course no dan bakar mgna,
kawae naga kwana biyu bamu hadu bne" Khaleel yace "ina Zaria
ynxu, sae na dawo." Najeeb yace "ok ka kirani idan ka dawo"
Khaleel yace "OK" snn ya katse kiran ya ajiye wayarsa tare da jan
tsaki, ko kadan baya bukatan taimakon kowa a ynxu dae. Mikewa
yyi ya fita don siyo mata abinda xata ci kafin ta tashi duk da
yasan ba abincin ma take ci ba, wani supermarket ya tafi ya siyo
kayan tea ya dawo snn ya siya abinci a eatry din dake cikin hotel
din ya haura sama, xaune ya sameta kasan dakin ta hade kai da
gwiwa, ya karaso ya durkusa gabanta a hnkli yace "me ya faru
wife" ta dago kai tana kallonsa da kyar tace "amae nake ji,"
dagota yyi yace "mu je kiyi toh" kmr xata yi kuka tace "ya ki
fitowa" xaunar da ita yyi gefen gado ya ce "idan kin ci abinci xae
fito, ga abinci nn na siyo maki ki ci kadan sae kiyi aman" haransa
tayi sae kuma ta saka kuka irin ta shagwaba, yyi shiru yana
kallonta lkci daya yyi murmushi ya rungumota a hnkli yana shafa
bayanta yace "to ya kike son in maki wife" lamo tayi a jikinsa bata
ce komae ba, ya dago kanta yana kallon cikin idonta yace "to xa
ki sha tea?" Ta make kafada alamar A'a, murmushi ya kuma yi
yace "to me xa ki ci?" Kmr xata yi kuka tace "ni amae nake ji"
mikewa yyi ya dauko ledan abincin da ya siyo ya dawo gabanta ta
mike da sauri ta bar wajen don ko ganin abincin bata son yi, can
karshen gadon ta koma ta xauna, ya ajiye abincin ya bi ta ya
xauna gefenta yace "toh xa ki sha kunu?" Juyawa tayi tana
kallonsa tayi shiru kmr me naxari snn ta gyada masa kai da sauri,
wayarsa ya dauka, ya shiga neman layin Zeenat, har ya mance
rabon da suyi waya, duk da da can ma ita ke kiransa ba shi ke
kiranta ba, bugu daya ta dauka, suka gaisa tace "ka mance da ni
ko doctor" Khaleel yace "A'a ban mance ki ba, ya mutanen
gidan?" Zeenat tace "duk suna lfya, ya su Fateema da khadija"
Khaleel yace "suna lfya, kina kd ne?" Tace "ehh ina nn" juyawa yyi
yana kallon Ashnaah da ta hade rae tana kallonsa, ya mike ya fice
daga dakin, sae bayan da ya fita yace "favour daya nake son kiyi
min Zeenat" tace "na me fa Dr" Khaleel yace "kunu xa ki dama
min plss idan bbu takura" da mmki Zeenat tace "kunu?" Yace
"yeah pls" tace "to shknn office xan kawo maka?" Khaleel yace
"No idan kin gama ki kirani kawae xan xo in amsa" tace "to shknn
xan yi ynxu" yace "am grateful, ki hada min da ruwan xafi a flask
plss" tace "OK bbu matsala" ya kuma yi mata gdya, snn ya katse
wayar ya dawo dakin, karasowa yyi kan gado ya xauna gefen
Ashnaah ganin ynda ta wani hade rae ta juya baya yace "me ya
faru wife?" Kmr jira take "ta fashe da kuka tace "ina ruwanka," ya
dan yi shiru snn yace "Allah ya ba ki hkuri wife" kmr ya kara
tunxurata ta kuma rushewa da kuka, yyi murmushi ya mike jin ana
kiraye kirayen sllhn magrib ya nufi bathroom, mikewa tayi da sauri
ta nufi inda ya ajiye wayarsa ta dauka ta shiga call log don ganin
da wnda ya gama waya, ajiye wayar tayi a sanyaye ganin Zeenat,
ta koma inda take ta xauna duk gaba daya sae ta nemi aman da
take ji ta rasa. Ko da ya fito
kallo daya yyi mata ya fita daga dakin
don xuwa masallaci, kasa tafiya masallacin yyi ya dawo dakin ya
sameta ta sakko kasa ta hade kai da gwiwa tana kuka, ya karaso
kusa da ita yana murmushi ya durkusa gabanta ya dagota a hnkli
yace "I only belong to yhu wife, no one else but yhu" xaunawa yyi
a hnkli ya jawota jikinsa yana murmushi.
~Dr Khaleel~