Showing 96001 words to 99000 words out of 114799 words

Chapter 33 - Dr Khaleel Book Complete Document by Khalisat Haidar .docx

10 Mar 2025

8418

baria debar maki dae" murmushi ta kuma yi bata ce komae ba don sae taji kankanan ya bata sha'awa, dad ya dauki wani plate ya shiga deban mata kankanan snn ya sa mata toothpick ya mika mata, akunyace ta karba tare da yi masa gdya, yace "tashi ki koma kujera toh" kin tashi tayi ta shiga cin fruit din nn inda take, sae ta ji ina ma Abbanta ne hka, tunanin hka ya sa kwalla ya taru a idonta.

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

103.....

A hnkli Ashnaah ta daga kai a sanyaye tana kallon Khaleel da ke tsaye har lkcn, suna hada ido ya dauke kansa, Dad kam ci gaba yyi da shan fruit dinsa, Khaleel ya juya ya koma sama da ganinsa kasan jikinsa yyi sanyi, a hnkli tayi ta shan water melon din har ta kusa shanyewa bata ji ya isheta ba, dad yace "yaushe ku ka xo?" Ta daga kai tana kallonsa tace "daxu da yamma" yace "shine xa ku koma ynxu?" Shiru Ashnaah tayi bata ce komae ba, dad yace "ku bari sae da safe ku tafi" kai kawae ta gyada masa, ya dauki wayarsa ya kira driver yace ya shigo falo ya samesa, ko minti biyar ba ayi ba drivern ya shigo dad ya ciro dubu biyu ya mika masa yace "kankana masu kyau xa ka siyo mata" kunya ya kama Ashnaah don ko kadan bata lura da har ta shanye kankanan gabanta gaba daya ba, da sauri tace "A'a Abba ni na koshi" Dad yace "bari dae ya karo maki ki kara" bata kuma cewa komae ba, dad ya canxa tasha xuwa news ya maida hnklinsa. Bayan minti sha biyu drivern ya dawo rike da ledan water melon, ya ajiye ma Dad kan center table, ya mika masa canjin dubu daya yace "na ga dayawa oga" dad yace "to rike canjin kai ma sae ka siya ka sha" gdya yyi ya fita daga falon, dad ya mike da kansa ya nufi kitchen ya dauko wuka da plate ya dawo ya dauki kankanan daya ya yanka snn yyi slicin dinsa kan plate din ya dauki toothpick ta saka ya mika ma Ashnaah da ke ta kallonsa, a kunyace ta ce "lahh Abba ni ya isheni fa" Dad yace "A'a ki dae kara" karba tayi tayi masa gdya kuma, har kusan Karfe goma da rabi Ashnaah na xaune falon da dad, ta dae ji ta fara jin bacci ta mike tana kallon dad tace "Abba bacci nake ji" yace "to tafi kiyi kwanciyar ki," ledan sauran kankanan ya mika mata yace "ga shi ki tafiya da sauran, Wanda aka yanka kuma ki saka a fridge" gdya tayi masa ta karba snn ta dauki plates din da tasha fruit din da nasa da wukan ta kai kitchen, tsaf ta wankesu ta ajiye snn ta fito ta kuma yi masa sae da safe ta nufi sama ina ma Abbanta ne hka da ta more rayuwa, dakin Ummi Ashnaah ta nufa, ta tarda Ummi xaune suna kallo da rukayya, Ummi tayi mata murmushi tace "sae ynxu" Ashnaah tayi murmushin ita ma, ta ajiye ledan hannunta xa ta xauna kasa Ummi tace ta dawo kan gado, ta xauna gefen gadon, Ummi tace "yana can dakinsa in kina jin bacci ki tafi ki kwanta kar ki takura kanki" Ashnaah ta sunkuyar da kanta tace "to ga fruit Abba ya siya min" Ummi tace "to kin gode" mikewa Ashnaah tayi ma Ummi sae da safe xata fita daga dakin Ummi tace "to kin bar fruit din" Ashnaah tace "A'a na sha da yawa Ummi, na koshi" Ummi tace "to dauka ki kai ma Khaleel" bbu musu Ashnaah ta dauki fruit din snn ta kuma yi mata sae da safe ta fita ta nufi dakin Khaleel, a hnkli ta tura kofar dakin ta same shi durkushe kusa da fridge dinsa, gabanta yyi mugun faduwa ganin abinda ke hannunsa yana dubawa, tasan baxae wuce expire date yake dubawa ba, yana ganin ta ya mayar da sauri ya fiddo ruwa, ta dauke kanta ta ajiye ledan hannunta ta nufi kan gado, ya bi ta da kallo yace "yhu re back wife" kai kawae ta gyada masa ta kwanta gefen gadon ta juya masa baya kmr bata son mgna rufe fridge din yyi ya dawo kusa da ita ya xauna yace "jikin ne wife?" Girgixa masa kai tayi da kyar tace "bacci xan yi" yace "OK wife, amma bari ki fara shan drugs dinki" girgixa masa kai tayi da sauri tace "amae xan yi" bata jira cewarsa ba ta juya masa baya, mikewa yyi ya dauko blanket ya rufa mata, ta lumshe ido kmr me bacci, gefen gadon ya xauna ta daya side din yana danna wayarsa, har kusan sha daya Ashnaah bata yi bacci ba amma bata bari ya gane ba, mikewa ta ga yyi yana kallonta, ta rufe idonta gaba daya kmr me baccin gske, fridge ta ga ya nufa ya bude ya fiddo kwalban daxu yana kallonsa rabon sa da shan giya tun ran da ya sha a birthday, ganinsa yasa yaji kmr ya shekara goma rabonsa da sha, Ashnaah taji kmr tayi masa mgna amma ta kasa sae taji hawayen takaici na sakko mata, budewa taga yyi ya koma bakin gado ya xauna ya kai bakinsa ya shiga sha, ko second talatin ba ayi da kai shi bakinsa ba ta ga ya cire da sauri, juyawa tayi tana kallonsa don yasan ma ba bacci take ba, ya ajiye kwalban hannunsa kasa gefensa ya rike kansa, mikewa taga yyi da hanxari ya nufi bathroom ta bi sa da kallo, amae ta ji ya shiga yi, ko motsawa daga inda take bata yi ba, amae ssae yyi a bayin, daga karshe ya fito da kyar bae bari sun hada ido ba ya nufi can gefen gado ya kwanta ba tare da ya kalli kwalban da ya ajiye kasa ba don ko ganinsa ma bae son yi, nn da nn bacci ya daukesa. Ashnaah tayi murmushi ta mike ta dauki kwalban taga har ya kusa rabi, bayi ta shiga da shi ta toshe hanci don ko warin bata son ji, ta tuttular da giyan snn ta dawo dakin ta bude fridge ta fita da sauran ma gaba daya duk sae da ta tuttulesu a bayi hancinta a toshe snn ta wanke bayin da kyar don duk tayi weak, wanka tayi da ruwan dumi ta fito da kwalaban ta ajiye su dakin tayi kwanciyarta da xanin jikinta, nn da nn bacci ya dauketa ita ma, can cikin dare ta farka ta dalilin aman da ta dinga ji, ta mike xaune da kyar ta jingina jikin gadon xuciyarta na tashi, juyawa tayi tana kallon Khaleel taga baccinsa yake, mikewa tayi ganin aman na neman taho mata ta nufi bathroom da sauri, ta durkushe ta shiga kwararo aman, hkn ya farkar da Khaleel ya mike xaune da kyar ya rike kansa da ke juya masa.

104.....

Mikewa yyi jikinsa a mace ganin har lkcn aman bae tsaya mata ba ya nufi bathroom din, dukawa yyi ya dafata ta turasa da sauri alamar ya kyaleta, komawa gefe yyi yana kallonta har ta gama ta mike ta wanke bakinta da mouth freshner ta fice ta bar masa aman a gurin. Gyara gurin ya shiga yi har ya gama snn ya hada ruwan wanka ko xae ji karfi a jikinsa, bakinsa ya soma wankewa snn yyi wanka ya fito daure da towel a waist dinsa, xaune ya sameta ta jingina jikin gado, suna hada ido ta dauke kanta da sauri don tun da suke bae taba fitowa hka daga wanka gabanta ba, kwanciya tayi ta shige cikin bargo ta rufe har kanta, ya gama sa sleepn robe dinsa yana kallon empty kwalaban da ta ajiye masa gefen fridge, dauke kai yyi da sauri don ko ganinsu bae son yi, agogo ya kalla yaga biyu saura, ya kashe wutan dakin ya kwanta yana kallonta, a hnkli ya birgina inda take ya cire bargon jikinta gaba daya, ta shiga turasa alamar ya rabu da ita, ya rungumeta a hnkli yace "Haba bbyna, am so srry plss" kuka ta sakar masa ya shiga lallashinta ta gaji don kanta tayi shiru, a sanyaye yace "wllh bana kara shan any Alcoholic drink wife, kin ma ga ya fitar min a kai ynxu, da na sha xan yi amae" shiru tayi bata ce masa komae ba, shi ma bae kuma cewa komae ba duk jikinsa yyi sanyi, a hnkli ta xame jikinta daga nashi ta juya masa baya.

Washegari karfe goma suka gama shirin komawa gida, falo Ashnaah ta samu dad xaune ta durkusa ta gaishesa snn tace xa su tafi, dad yace "da wuri hka xa ku tafi" tayi murmushi bata ce komae ba, ya mike yace "to ina xuwa" sama ya nufa dae dae stairs suka hadu da Khaleel da ke sakkowa, Khaleel bae bari sun hada ido ba ya basa hanya da sauri, a sanyaye ya karasa sakkowa downstairs yana kallon Ashnaah yace "mu tafi" tace "Abba yace in jira shi" bae ce mata komae ba ya fita falon don yasan ko ya tsaya yi masa sallama ma ba tanka sa xae yi ba tunda bae amsa gaisuwarsa daxu ba, Dad ya sakko rike da kudi ya mika ma Ashnaah yace "to gashi ki siya duk abinda kike so" kasa kin amsa tayi ta karba a kunyace tayi masa gdya ta mike yyi mata Allah ya kiyaye hanya snn ta fita don sun yi sallama da Ummi, xaune ta tarda Khaleel cikin mota yana jiranta, tana shiga motar ya tada mai gadi ya bude masa gate ya fita. Karfe sha daya saura suka isa gida, Khaleel ya juya yana kallon Ashnaah yace "ki shiga ciki wife, xan je siyo maki magunguna kafin su kare daga nn sae in siyo abinci, me kike son ci?" Ashnaah ta girgixa masa kai tace "ba komae, xan sha kunun da Ummi tayi min" kudin hannunta ta mika masa tace "ga shi Abba ya bani" yyi murmushi yace "to kin gode wife" tace "to ka karba mana" ya girgixa kai yace "ae ke ya ba ma wife ki rike kayan ki kawae" bata rae tayi har lkcn tana mika masa, yyi murmushi yace "to ki shiga sae na dawo ki ban" ba musu ta bude motar ta fita ya bi ta da kallo har ta shiga gidan, snn ya juya ya fice da motar, kwanciya Ashnaah tayi kan kujera a falo, wayarta taji yana vibrate ta bude jakar ta ciro da sauri ta ga Ashfah ce ke kiranta, daga kiran tayi Ashfah tace "sister ba ki turo address din ba kuma, ya jikin?" Ashnaah tace "lah gashi ban tambayesa ba kuma baya nn, Bari in tambayi mai gadi," da sauri ta fita ta tambayi mai gadi address din layin ya bata snn ta gaya ma yar uwartata, Ashfah tace to ga ta nn xuwa. Cikin minti ashirin Ashfah ta iso gidan, Ashnaah ta ji ddin ganinta ssae ta rungumeta tana tambayarta momynta fa, Ashfah ta ajiye ledan abincin hannunta tace "ta ce a gaishe ki" a sanyaye Ashnaah tace "Abba ya dawo?" Girgixa kai Ashfah tayi, Ashnaah tace "to inna fa" Ashfah tace "tana nn" shiru Ashnaah tayi bata ce komae ba, can ta mike tana kallon yar uwartata tace "mu tafi sama" mikewa Ashfah tayi ta bi bayanta ta kai ta dakin da take. Hira suka dinga yi har kusan karfe daya suka yi sllh, Ashnaah da kasala da tashin xuciya ya isheta tace ma yar uwarta bari ta dan kwanta don ta gaji, tana kwanciya nn da nn bacci ya dauketa. Ashfah bata xauna ba ta shiga gyara ko ina na gidan, tana kitchen tana wanke dan kwanukan da ta gani Khaleel da Najeeb suka shigo gidan, kin fitowa tayi daga kitchen din har ya suka shigo falon da mmki Khaleel ke kallon ko ina na falon, bbu abinda ke tashi sae kamshi Mae ddi, ya kalli kofar kitchen jin karan ruwa ya nufi kitchen din da sauri, daga bakin kofa ya tsaya yana kallonta da mmki ganin ynda tayi kwalliya, ko kadan bae lura ba Ashnaah ba ce don mugun kamar da suke, Ashfah taki juyowa jin bae ce komae ba ta ci gaba da wanke wankenta, karasowa cikin kitchen din yyi yana murmushi yace "waww wife duk ke kika yi wnn aikin," da sauri Ashfah ta juya ganin ya nufota xae rungumeta tace "ba ita bace" cak ya tsaya yana kallonta, ta dauke kanta tana ci gaba da dauraye plates din hannunta tace "ina yini" Khaleel ya koma baya da sauri ya fara kame kame "ohh srry sister, lfya lau, sannu da aiki, yaushe kika xo"

~Dr Khaleel~ By Khaleesat Haiydar

105.....

Ba tare da Ashfah ta juyo ba tace "Yauwa ngd" juyawa Khaleel yyi ya fita daga kitchen din da sauri ya koma falo, xaune ya tarda Najeeb ya kunna Tv yana canxa tasha hnkli kwance uwa falonsa, Najeeb ya daga kai yana kallonsa yace "kace jikin Madam yyi kyau knn tun da har ta fara aiki" kai kawae Khaleel ya gyada masa ya dauki ledan da ya shigo da ya nufi sama, Ashnaah ta fito daga bathroom knn ya shigo dakin, da ganinta kasan amae tayi, bata ko kallesa ba tayi kwanciyarta kan gado ya karaso ya xauna gefenta a hnkli yace "sannu wife" bata tanka sa ba sae ma juya masa baya da tayi, yace "ashe twin sis ta xo, tot ke ce a kitchen sae ta ce min ba ke bace" nn ma dae Ashnaah bata ce masa komae ba, shiru yyi bae kuma cewa komae ba, ta juya ta hade rae tana kallonsa tace "daga ce min ynxun nn xaka dawo shine xa kayi tafiyarka ka barni ni kadae a gida koh" ta karashe mgnr kmr xata yi kuka, Khaleel yace "ohhw am srry bbyna, Najeeb ne ya bata min lkci, but ae twin sis ta xo ta taya min ke xama toh" harara ta galla masa tace "ba ynxun nn ta shigo ba" yyi murmushi ya jawota jikinsa ya lumshe ido a hnkli yace "am so srry wife" lamo tayi bata ce komae ba.

Ashfah na gama gyara kitchen din ta fito falo da nufin xuwa ta ce ma yar uwarta xata tafi, kallo daya tayi ma Najeeb da ke xaune falon ta dauke kai lkci daya ta ganesa, yana kallonta yace "ya jikin Fateema" bbu yabo bbu fallasa Ashfah tace "tana sama" bata jira ta kuma jin me xae ce ba ta nufi saman da sauri, Najeeb ya bi ta da kallo da mmki ya mike tsaye da sauri yace "wait! wait" amma tuni ta haura sama, kwankwasa kofar dakin tayi tare da yin sallama, Khaleel ya mike tsaye tare da amsa mata sallaman, Ashnaah tace "ki shigo mana sister" Ashfah ta turo kofan ta shigo tace "sister bbu wani abun da xa ayi maki koh? Xan tafi ne" Ashnaah ta hade rae kmr me shirin kuka tace "xa ki tafi fa kika ce Ashfah, yaushe kika xo" Ashfah tace "kin ga fa ina da lecture xuwa anjima" Ashnaah tace "ashe dama ba kwana xa ki min ba" Ashfah ta xaro ido tace "kwana kuma, ki bari nxt tym sis, ina da class yau" Khaleel yace "Haba sister ki kwana mana sae ki tafi gobe mana" Ashfah ta sunkuyar da kai tace "ka ga fa ba muyi da momy xan kwana ba wllh" Ashnaah tace "dan ara min wayar ka in kirata ni in gaya mata" Khaleel ya mika mata ta karba ta kira momynsu, momy na dagawa ta marairaice kmr xata yi kuka tace "Momy don Allah ki ce Ashfah ta kwana gobe sae ta tafi kin ga wae fa ynxu xata wuce" momy tace "Kinga Abbanku bae san ta fita ba kuma gobe xae dawo ki bari next tym kin ji" Ashnaah ta fashe da kuka tace "momy ba dawowa xata kuma yi ba fa nasani" Momy ta dan yi shiru snn tace "toh shknn amma gobe da sassafe ta taho kar ya dawo ya ga bata nn" Ashnaah tayi murmushin jin ddi tana share hawayenta tace "to momy ngdd" ta katse wayar ta juya tana hararan Ashfah ta ja tsaki ta mike ta fice daga dakin don xuwa ta dauko cup din da xata Debi kunu ta sha a kitchen, Khaleel yyi murmushi yana kallon Ashfah da mood dinta ya canxa lkci daya, yace "kiyi hkuri sister, yau da gobe ae duk daya ne koh" murmushi ta kirkira bata ce komae ba, kasa ci gaba da kallonta yyi don sae yake ganinta kmr Ashnaah don kmrsu tayi yawa, juyawa yyi da sauri kmr wnda ya tuna abu ya dauki hijab din Ashnaah ya bi ta da shi yana kiranta, Ashnaah da har ta kai stairs ta juya tana kallonsa ya mika mata yace "Najeeb na falo" karba tayi ta sa ta fita, tsaye ta tarda Najeeb har lkcn ya kasa xama idonsa a kan stairs, yana ganinta ya nufe ta da sauri yace "pls fateema kice twin sistern ki ta saurareni taki saurarata" Ashnaah tayi dariya tace "wae Ashfah, ae bata kula samari nn da ka ganta" Najeeb ya marairaice mata yace "Haba fateema kar muyi hka da ke mana, help me plss" Ashnaah tace "wllh da gske nake Ashfah bata kula saurayi," da mmki Najeeb yace "to sbda me?" Ashnaah tace "sbda Abbanmu ya hana, karatu ya fi so" Najeeb ya kasa daina mata kallon mmki yace "to ke ya aka yi har kika kula Khaleel ku ka yi aure, ko ita kadae ya sa ma dokar bn da ke?" Ashnaah tayi shiru tana kallonsa lkci daya jikinta yyi sanyi hawaye ya shiga taruwa idonta a xuciyarta tace "sbda bna jin mgnrsa ni" bude baki tayi xata gaya masa abinda ke ranta suka ji muryar Khaleel a bayansu, "enuf of those silly questns Najeeb" juyawa Ashnaah tayi ta nufi kitchen da sauri, Khaleel ya karaso kusa da Najeeb yace "wnn wace irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login