Showing 30001 words to 33000 words out of 47874 words

Chapter 11 - Mijin Marainiya Book Complete Hausa Novels by Fadila Lamido .pdf

Advertisement

16 Mar 2025

4159

da safe zai tafi gidan hajiya.
ummi tana ganin shi tace ina zakaje da sasafen nan bayan yau babu aiki.
ummi zanje gidan hajiya ne, in duba safna.
zonan ka zauna babu inda zakaje.
ummi bata fah da lafiya ne.

eh naji zoka zauna bayan jalal ya sauna ummi tace wai me yake damun safna?

jalal yace nima ban sani ba.
ummi ta sake cewa toh waye yace wa alhaji safna tana da ciki?
gaban jalal ya fadi da saurin sa yace ummi ban sani ba.
ummi ta sake cewa jalal ina fatan dai babu abinda ya shiga tsakanin ka da safna?
shiro yayi kan shi akasa, gaban shi kuwa sai faman faduwa yake dan gaskiya yana matukar
jin kunyar ummi sa, kartaga yaki jin magarta.
cikin fada ummi tace dan ubanka bada kai nake magana ba.
sai alokacin jalal yace ummi babu komai kasa ka rasawa yayi dai dai lokacin alhaji ya fito.

alhaji yana fitowa yace jalal kana nufin cikin da safna take dauke dashi ba na ka bane??
jalal mikewa yayi yace nawa ne daddy.
mikewa ummi tayi tace wlh alhaji karya yake zai dai rufa mata asiri ne , amman bata taba
kwana dakin sa ba.

alhaji ya juya yace haka ne jalal, ka fada min gaskiya?

jalal ji yayi kamar ya tsaga kasa ya shige ayau zai kar yata mahaifiyar shi kuma in yayi
shiru beyiwa safna adalci ba.
alhaji ya sake cewa jalal dakai nake magana, dama baka taba kwana daki daya da safna
ba??
dukar da kai yayi hawaye na zuba afuskar shi yace mun taba daddy sau biyu
[8:40PM, 12/13/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜



Story
&
Written
Fadeela lamido
Mmn Yazeed📊

82-85



Ummi kalon jalal tayi cike da mamaki batace komai ba illa dafe kanta da tayi ta koma ta zauna
jabar.
alhaji kuwa ajiyan zuciya yayi tare dayin hamdala azuciyar shi, kallon jalal yayi yaga duk yabi
ya rikice sai kace mara gaskiya alhaji yace ni abinda nake son na sani shine yaya akayi safna
tabar dakinka bayan tun randa aka daura aure aka kaita dakin ka?

jalal ya bude baki zaiyi magana ummi tai sauri tace alhaji yariyar ce,
alhaji be bari ummi ta karashe maganar taba yace ba dake nake ba ki rufemin baki, jalal ina
sauraran ka?


cikin en ina jalal yace ai tun ranar tabar dakin.
alhaji yace saboda me?
jalal juyawa yayi ya kalli ummi yasa ke dukar dakai.
alhaji ma kallon ummi yayi yace toh toh na fahimta jeka abinka.


da sauri jalal ya shige dakin sa dan dama ya kosa ya bar wajen.

yana shiga daki alhaji ya farawa ummi fada zaliha al,amarin ki ya fara bani tsoro dama nalura
da take taken ki baki son auren jalal da safna, yanzun saboda Allah zaliha abinda kikayi kin
kwauta kenan, akaiwa yaro amarya kije ki raboshi da ita dan dai ki lalata masu farin cikin su, toh
gashinan Allah yanuna miki iya karki dan yanzun nusaiba takira ni take gayamin safna ciki gare
ta, ni abinda yake daure min kai wai me yariyar ta mike da har kike neman ki raba su?

shiru ummi tayi tana dafe dakai idon ta a rufe.

alhaji yace toh bari kiji karki kara gigen raba musu aure dan idan har auren su ya mutu kema
naki zai mutu, mahaukaciyar banza mahaukaciyar hofi.

da sauri ummi ta bude idon ta da sukayi ja takalli alhaji tunda take alhaji betaba fada mata
bakar magana kamar nayau ba.

shi kuwa yana gama maganar sa yayi waje, ko sallama be mata ba.

ummi tana son ta zubar da hawaye amman ta kasa ashe kuka ma rahama ne, jitayi duniyar
na juya mata tun daga nan bata kara sani me ya faruba.

jalal ne ya fito ya same ummi cikin ma woyacin hali kinkiman ta yayi ya nufi motar sa da it a.

bayan sun isa asibiti aka mata yan gwaje gwaje suka tabbatar wa jalal jininta ne ya hau sosai
sun so sukwatar da ita amman taki yadda, dan haka suka bata magun guna suka koma gida.

jalal dakan sa ya bata magani tasha sai da yaga tayi barci ya koma dakin sa.

ya koma daki da tunani kala kala azuciyar shi yana son yaje ya duba jikin safna kuma baya
son yabar ummi.

har dare jalal be fita ba sai zarya yake dakin ummi, zuwa cen yaji da wowan alhaji dan haka

ya shirya ya fito da nufin tafiya gidan hajiya.

dakin ummi ya fara shiga ya same ta zaune ta fito wanka neman guri yayi ya zauna yace
sannu ummi ya jiki?
Waigo wa ummi tayi tace tashi ka fita kabani guri dan iska kawai, na barwa safna tunda ka
zabeta akai na ,kai dadi mata har ace ina cikin gidan nan kuka maidani baho.

tsugunawa yayi ummi dan Allah karkiyi min haka kiyi hakuri ummi gani nayi mata tace.
au zakaci gaba damin rashin kunyar ne, ai gara kanuna min ka girma, saida nagama cin
kashin ka da fitarin ka, ni bazan ma baki ba amman karka kara zawa inda nake niko ganin ka
bana sonyi.

da sauri jalal ya mike yace ni ummi baki son ganina, me nayi miki da zafi haka, kuka ne ya
kwace masa, amma duk da haka be bar maganar ba, sake cewa yayi ummi anya kuwa ke kika
haifeni?

ummi tace au mamaki kake yi ai dan ma bagida na bane da koran ka zanyi.
jalal ya fara share hawaye yace toh ummi nagode da saurin sa yabar dakin.

dakin sa ya koma dan bazai iya fitaba yana shiga ya sake kuka kamar karamin yaro.


safna kuwa tun bata damu da rashin zuwan jalal ba, har ta fara tunanin meye ya hana shi
zuwa.gani tayi har dare yayi ta zauna tayi tagumi, gurin karfe 8:30 mijin anty nusaiba yazo
daukan ta.
safna tace anty tafiya zakiyi?
anty tace au da kin dauka kwana zanyi toh ko na kwana ne?

cikin shirin kuka tace a,a ba haka nake nufi ba, yaya ne yaki zuwa har yanzun.
murmushi anty tayi tace safna ai na dauka baki son jalal yazo kusa dake ne, tun da kina son
ganin shi bari na kira shi, anty takira wayar jalal tajita kashe dan haka ta musu sallama ta wuce.

safna mikewa tayi ta shige dakin Hajiya kuka ta fara ta dauki wayar ta tagwada kiran jalal har
yanzun wayar shi kashe take, kukanta karuwa yayi ita fa gaskiya in bataji muryar sa ba zata iya
barci ba

hajiya ce ta shigo ta samu safna sai faman kuka take tace ke lfyr ki kuwa?
mikewa tayi ta nufi gadon hajiya tana fadin ba yaya bane yaki zuwa.
hajiya tace ikon Allah yaran zamani babu kunya, yanzo nan duk kukan jalal din ne.
kwanciya tayi ta juya baya tayi shiru.
hajiya ta dauka bacci tayi dan haka itama ta kwanta, gurin 10:45 hajiya ta farka ta fara juwo
kukan safna kasa kasa, daukan wayar ta tayi ta kira alhaji, alhaji yana dauka yace lfy kuwa
hajiya

hajiya tace lfy lau ina abduljalal ne yau bamu ganshi ba, nusaiba takira shi wayar shi kashi.
toh inaga yayi barci ne gobe zai zo da safe.
ai ni safna ta hanani barci sai faman kuka take bataga mijin taba.
alhaji dariya yayi yace bari na tado shi tunda ta hana ki bacci gara kowa ya tashi
[7:59PM, 12/14/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜

Story
&
Writeen
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📊

_*DEDICATE*_
*_dis page to_*
_Faty afreen_

*Gaisuwa agareki*
*💋Big girl💄*
*marubuciyar NUFIN ALLAH*

*KUNA RAINA*
*Sa,adatu lamido*
*Anty rabi lamido*
*Sa,adatu abdullahi*
_(ummita)_
*Rukayya sani gini*
😘😘😘


86-88


Sauko wa yayi ya nufi dakin jalal ya tura kofa yajita kulle dan haka ya shiga bugawa.
jalal dake kwance sai faman juyi yake agado ya bude baki a hankali yace waye?

muryar daddy yaji yana fadi nine, sakowa yayi cikin sauri ya bude kofar alhaji ya shigo ya kalli
fuskar jalal yace me ya same ka?
shiru yayi yasa kan sa akasa.
girgiza kai alhaji yayi sannan yace kai da mamar ka ne ko?
jalal be amsa ba kuma be daga kai ba.
alhaji ya sake cewa me tace maka?

ba komai daddy kwai dai nasan tana fushi dani ne.
toh dan wannan kake tada hankalin ka, kabar ta zata sako , kaji ko, me ya hana ka zuwa ka
duba jikin safna?
daddy naga ummi bata da lafiya ne, kar na fita kuma jikin ta ya tashi.

kai ka dai na biyewa ummin nan taka wanne irin ciwo take lafiyar ta kalau dama abin da take
so kenan.
jalal yace wlh daddy bata da lfy jininta ya hau sai da nakai ta asibiti dazun.
shiru alhaji yayi zuwa cen alhaji ya matsa bakin gadon jalal ya zauna yace matar ka keson
magana dakai, warshi ya danna ya mikawa jalal sannan yace inka gama ka kawo min daki ,
dakin ummi ya nufa, yagan ta kwance tana bacci dan haka ya wuce dakin sa.

shikuwa jalal bayan yasa wayar akunne sa murya hajiya yaji tana fadin an tado shiko?
jalal yace hajjaju ya gari, har yanzu bakiyi bacci ba, yanzun fah 11:14.
ina ni ina barci safna tasani gaba sai kuka take.
kuka kuma, me aka mata?
hajiya tace wai dan rashin kunya tun dazun take kuka wai baka zoba.

duk da halin da yake ciki sai da yayi dariya, sannan yace Ina take?
hajiya na mikawa safna wayar ta tashi ta fita.
safna na karbar wayar ta saka mishi kukan sha gwaba, jalal ya rasa yaya zaiyi mata inama
suna kusa da juna.
a halin yace safna ya isa haka, kiyi shiru, kara sautin kukan ta tayi .
jalal ji yayi yana yin jikin shi ya fara cen zawa babu abin da yake so ayanzu ila ya ganshi
kusa da safna.
daker ya bude baki cikin kashe murya yace safna kina tayar min da hankali fah, dan Allah kiyi
shiro gobe zan zo.
cikin kuka tace ni yan zon nake so.
jalal yace safna bakiga dare bane yanzun, kibari gobe da wuri zan fito.

toh naji karfe nawa za kazo, jalal yayi murmushi yace ke zaki fada

tace karka wuce 9:00 am.
toh ba damuwa insha Allahu zan zo haka din, yaya jikin ki?
wlh yaya ni babu wani saukin da naji karuwa ma yake yi, yanzun ma fah ko ruwa bana son
gani miyar nan ma dana ke sha yanzon bana son ta, kasan me nake son ci yanzun?

jalal yace sai kin fada.
zugale nake so da mangoro gobe inzaka zo kataho min da shi.
jalal yace a,a safna ban miki alkawari ba ni bansan inda ake sai dawa ba , ki gayawa hajiya
ne.
toh mangoro fah?
Jalal yace ai yanzun ba lokacin ta bane, jalal gani yayi zata sake rikice mashi, yace toh ya isa

zan duba kwanta kiyi bacci, da haka sukayi sallama kallon agogo yayi yaga har 12:03 yasan
yan zon daddy yayi bacci ajiye wayar yayi ya kwanta ya rungumi filo tunani ya shiga yi wato
safna cikin nan bayan kwadayi har da surutu yasa ta

jalal be samu bacci ba sai da yayi sallah asuba ya kwan ta dan haka be tashi da wuri ba,
koda ya tashi ya duba agogo sha daya saura da sauri ya tashi yashir ya
ya fito sai da ya duba dakin ummi bata ciki dan haka ya wuce dakin daddy acen ya sami ummi
bayan ya gai da alhaji yace ummi ina kwana, kin amsawa tayi alhaji yayi kamar besan me suke
ba jalal yasa ke cewa ina kwana ummi, wayar ta tasa akune tafara magana, alhaji ya kalleta
yace jalal tashi mu tafi, mikewa yayi suna cikin tafiya alhaji yace jalal nagama gyarama gidan da
zaka zauna sai dai karami ne, ban sani ba ko zaka so hakan.
da saurin sa yace ina so daddy .
alhaji yace yauwa jalal shiyasa nake son ka kwata kwata baka dauki duniya da zafi ba, mamar
ka ko ban san ina ta samu wannan karyar ba, kaga wancen gidan ma daya kone sai da tayi
korafin yayi maka kadan, toh yan zon yaushe zaku tare dan anriga anzuba komai agidan.
daddy ni duk ranar da kace.
murmushi alhaji yayi yace nifa so nake ku tare ayau dan bana son kowa ya sani hanta
mahaifiyar ka kuwa.
kwana alhaji yayi yakai jalal gidan ya gani gidane karami mai kyan gaske me dauke da
dakuna biyu kowan ne da bayi aciki sai falo da kitchen jalal ya yaba tsarowan gidan sai yaga
kamar ma yafi wancen kyau girma kawai wancen zai nuna ma wannan, gadiya ya shiga yiwa
daddy. lokacin da suka nufi gidan hajiya daya saura dan haka ya samu safna ta cika tayi taf, alhaji
kawai ta gaida ta juya ta shige daki, alhaji ya kalli jalal yace duk wayar da kuka kwana kunayi
baku shirya ba.

jalal yana dariya yace daddy time ta bani nikuma bacci ya kwasheni ban tashi da wuri ba yana
fadan haka yamike yabi bayan ta , hajiya na fadin kardai ka zama mijin tace
yana shiga ta mike ta zata fita falo jalal ya tare ta nan da nan ta saki kara sakinta yayi da
sauri yana fadin baki da hankali ne bakiga daddy na falo ba, safna bata tsaya sauraran jalal ba
ta nufi falo kujerar dake kusa da ta alhaji taji ta zauna akasa, tana zama jalal ya fito yasan ta
zauna agurin ne dan kar yaje kusa da ita dan haka kujerar bayan ta yaje ya zauna.
yana zama yasa kafarsa abayan ta yana dan zungurin ta, dakewa tayi kamar bata jishi ba
zuwa cen ya fara mata waiwayi ta fara gan tsarewa tunda daddy yaga safna tana zabure zabure
yasan jalal ne amma sai ya dauke idon shi daga waje.
shikowa jalal so yake ya dame ta har ta gaji ta koma daki, zuwa cen yasa kafar sa ya daga
rigarta ta baya ya fara mata cekulkuli, zabura tayi tare da sakin kara ta matsa cen tana soshe
soshe.
daddy ya waigo yace safna lfy.?
daddy wani abu ya saka min ariga.
alhaji yace kaga jalal karka firgeta yariyar nan tashi daga gurin nan kadawo nan.
jalal mikewa yayi yakoma cen gefe kusa da hajiya.

alhaji yace safna ki shirya anjima nusaiba zata rakaki gidan ki.

dasauri tace daddy abari ba yanzun ba

07014197556âœ
[6:11AM, 12/16/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜


Story

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login