Showing 18001 words to 21000 words out of 47874 words

Chapter 7 - Mijin Marainiya Book Complete Hausa Novels by Fadila Lamido .pdf

16 Mar 2025

4068

suka
shaida daurin auran harda baffa wanda alhaji yaje ya taho dashi yaso yaki zuwa amman alhaji
yace yayi danshi, dan haka ana daura auran alhaji yaba da mota aka mai dashi gida, jalal kuwa
da ka ganshi kasan yana cikin farin ciki. acikin gida kuwa safna ce da wasu kawayen ta su biyu bata san waya gaya musuba sai dai
kawai ganin su tayi,tana ganin su kuwa suka shiga fira tuni ta manta da bacin ran dake damunta
anty tashigo ta ajewa safna wasu kaya tace maza kisaka kije waje jalal na kiranki zaku gaisa da
abokan sa.
tun safe safna bata fitoba sai yanzun tana fito falo su hajiya ne da mutanen ta cike afalo suka
saka guda, safna kuka tasaka musu yau gata atsakiyan dagin miji bata da kowa, dagin miji sune
gatan ta wannan abu kawai in tatuna yana sata cikin baccin rai sai a yanzun wani kalma na
goggo yake fado mata ki zauna anan bari naje na dawo haka banzayen kakan ninki suka ma
uwarki har ta mutu bata kara sakasu a ido ba, goggo tana nufen mahaifiyar tama haka abarta,
ko shiyasa bata taba gani wani dan uwan mahaifyar taba kara rushiwa tayi da kuka hajiya tace
fatima kawo ta nan, hajiya fatima ta kawota har gaban hajiya kwatar da ita tayi ajikinta taita
mata nasiha.

bayan ta dan natsu hajiya tace tashi kije ki gaida ummin ko, sai ki wuce gurin su jalal din.

sun shiga ita da kawayenta ta gaida su suka amsa ba yabo ba fallasa.

sun doshi gurin rinsu jalal, jalal ya hango su tun daga nesa da sauri ya daga waya yace anty

dan Allah ki leko ki mayar da safna gida tasaka hijjabi.
dariya tayi tace haba jalal kabarta mana yau daya dai


kafin yakara wani magana sun iso wajen dan haka ya daure fuska suka gaida su cikin sakin
fuska suka amsa dayan daga cikin abokan ne wadda suke kira amir ya farawa safna tsiya
amaryar mu kirike shi da kyau duk abinda yake so abashi dan kinsan shagwabebbe ne ko
cokali be iya rikewa ba. jalal yace toh malam ya isheka haka kuma.
amir yace be isaba safna kinajina nina san halin jalal tare mukayi karatu jalal bashi da matsala
amman yanada fushi idan antaba shi, ya kalli jalal yayi murmushi sannan yace safna abu
nagaba jalal nada tsananin kishi .
da sauri jalal ya kalli amir yace wai amir lfyr ka kalau kuwa, ke ku wuce gida.
amir yace yazaka koresu ka barsu mana ai ban gama ba, hirace ta barke takanin safyya
kawar safna da amir amir , jalal zuwa yayi yakama hannu safna yashiga da ita har cikin gida.

da daddare mutane suka fara watsewa bakin hajiya kowa duk sun wuce gidan ta ,sai hajiya
da anty nusaiba kawai suka rage barayin ummi kuwa daga ita sai kawarta madina safna kuwa
na dakin su da ita sai kairat, kairat tace anty safna kikace da bikin ki zamuyi shagali amman
yanzun sai naga ba,ayi komai ba, natabayi yaya yace wai kece baki so ayi. Safna tace haka yace miki wayau yayi miki shine baya so,kairat tace ai dama yaya yacika
wayau haka ma da yace in kukayi aure zai tafi dani yanzun kuma yace wai wasa yake min,
kuma wlh bazan yarda ba saina biku yaya zaku tafi kubar ni ni kadai agida
safna tace ai bama inda zamu bakiga gidan ya kone bane.
suna cikin haka jalal yashigo dakin yace safna kizo hajiya nakiran ki tamike suka fito tare
ahanyar su ne jalal ya ce safna koda an tambaye ki Ina kike son zama kafin musami wani gidan
kice abarki adakina.
dauri safna ta fara kuka wlh yaya bazan iyaba .
yace daurewa zakiyi safna ,ko kin fi son hajiya ta wuce dake, ni indai hajiya ta wuce dake
bazan iya barciba wlh me zanyi agidan nan, to sai dai nima na biko.

gani tayi kamar ba,a cikin hakalin shi yake ba, matsowa yayi yariketa safna ki taimakeni karki
bari atafi dake.
safna ko azuciyar ta tafi son tabi hajiya dan gidan nan kwata kwata baya yi mata dadi jita
take kamar a kaya take.


Suna shiga falan alhaji ,suka ga kowa kowa ya hallara har ummi da kanin alhaji bayan sun
zauna aka fara yi musu nasiha kanin alhaji baba salisu yace to jalal hajiya nason ta tafi da safna
gidanta kafin agama gyara ma gidan ka dan haka nace bari muje ta bakinka tukuna dan yanzun
kai kake da iko da ita, meye ra,ayin ka? shiru yayi kansa kasa.

Safna ko tunani take azuciyar ta wato jalal shi yakasa magana ita kuma zai sata tayi rashin
kunya.

Jalal beyi magana ba saida baba salisu yakara maimaita tambayan shi.
sai da jalal ya juya gurin hajiya sannan yace toh hajiya harda ni zaki tafi ko?
duk falon dariya suka saka banda safna da ummi dan ummi kara tamke fuska tayi.
baba salisu yace ja,iri ai dani zakayi magana bada hajiya ba.
Jalal bece komai ba sai faman sosa kai yakai yake.
baba salisu yace indai na kula da kyau, jalal be yadda atafi mai da mata ba.
anty nusaiba tace toh hajiya kibar mai matarsa kawai tunda baso yake ba, da sauri ummi tace
nima dai abinda nagani kenan.
hajiya tace a,a nima ba matsawa nayiba kusha zaman Ku, in ma dakinka zaka kaita bisimillah.

hajiya ta sosa mai inda yake mai kaikayi dan haka ya farawa anty nusaiba alama da ido ,
banza tayi dashi kamar bata gani ba.
baba salisu ya kula dan haka yace jalal kamar kwai magana abakin ka, nusauba me jalal
yake gaya miki.
dariya tayi tace yaya nima ban fahimce shiba.
yace toh kuje waje kuyi magana duk abinda yake so ya fada kar yaji kunya ai matar sa ce.
anty tace jalal kayi hakuri mana kasan fa mamar ka bazata yarda dahaka ba.
anty nidai kawai ku kaita dakina ina da dalilina inhar kuka tafi baku kaita dakina ba nasan
ganin safna ma sai ya gagareni ummi zata iya hanani shiga dakin su safna.

suna komawa anty tace yaya shifa wai so yake ta koma dakinsa.
baba salisu da alhaji suka hada baki to dan wannan shine ka kasa fada kai da matar ka,
nusaiba kai mishi matar sa daki kizo mutafi.
ummi mikewa ta tasaka kuka agidan nan, za,yi wannan kwama calar wlh wlh bata isa ta hada
gado da jalal ba
[7:43PM, 12/5/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜



Story
&
written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📊


54-57

Han kalin kowa koma wa yayi gurin ummi safna kuwa hawaye ne ke zuba a idanun ta kamar an
bude faffu hajiya tace me kike nufi da wannan kalmar taki?

hajiya nidai gaskiya ban yadda da wan shawarar ba kawai ya bari sai sun samo gida amman
wannan ai bai dace ba.

hajiya tace to muna sauraran ki sai ki gaya mana yadda ya dace tun da kin fimu hankali.
bude baki tayi zata yi magana alhaji ya dakatar da ita yanzu nan dan baki da kunya magana
zakiyi , mikiwa tayi tabar wajen .

hajiya ta juya tace ke nusaiba rakata dakin jalal

daga dakin alhaji aka wuce da ita dakin jalal ban da kuka babu abin da safna take, abakin
gado ta zaunar da ita, rabon da ta shiga dakin jalal tun farkon zuwan ta gidan .

anty nusaiba juyawa tayi tace safna sai da safe Zan kiraki awaya kema idan kina son wani
abu ki kirani kigaya min.
kasa amsawa tayi sai kuka take dan gaskiya dan zaman nan da sukayi da anty suyi matukar
shakuwa da juna tanan zaune tafara tunanin wannan wani irin aure ne dan dai bani da gatane
da inada gata baza akawo ni dakin jalal ba, da sai dai nazauna agidan iyaye na ,tana cikin
tunani taji an turo kofar ta zata jalal ne sai taga anty tana shigo da akwatuna harta gama shigo
dasu gaba daya sannan takuma yi mata sallama ta fita.

zuwa cen taji tashin motar su takara saka kuka.
shiko jalal bayan sun tafi yayi masu alhaji sai da safe ummi shiru tayi bata amsa ba.
bayan jalal ya wuce ummi ma ta wuce dakin ta ,alhaji ya bita da kallo ji yayi babu dadi suda
suka aurar da dan su kamata yayi suyi farin ciki , dan haka yabi bayan ta yana shiga ya fara
rarrashin ta sannan ya tambaye ta me yasa bata son auran safna da jalal.

ummi tace au sai yanzo ne zaka tambaye ni ,ai aikin gama yariga ya gama kuma, ba, anyi ba
,har kunsa masa ita adaki , to meye Kuma zaka zo kana tambaya ta.
alhaji dai da yaga ummi baza ta gane ba ya tashi yabar mata dakin.

alhaji na fita takira madina ta gaya mata halin da ake ciki.
madina tace gaskiya zaliha ke kike jawa kan ki nace miki kwatar da kai zakiyi karki bari kowa
yagane baki son auran , irin wannan ai sai ki tona kin ki.
ummi tace yaushe kuma aisun riga ma sun gane, ni ba wannna bama, madina bakiga inda
jalal ke rawar jiki ba, a yadda naga take taken sa ,yau bazai iya hakuri ba sai ya kusan ce ta, ni
kuma abin da natsana kenan .
madina tace ni wlh mamaki kike bani ke baki san yadda zakiyi ki hana yarinyar kwana adakin
ba cikin kissa da dubara, kuma karki kara nuna baki son yarinya shi kuma jalal kija shi ajiki
kamar da, indai kikai haka sai kiga kafin su tare auran ya kare.

bayan sun gama waya da madina ummi ta fito ta nufi dakin jalal

jalal kuwa yana manne jikin safna sai rarrashin ta yake, bayan tayi shiru yace to ki saki jikin ki
mana keda dakin ki, cire gyalen kisha iska, kara rike gyalan tayi , jalal yayi dariya yace kicire
gyalan mana ki kwanta ni ba abin da zan miki.
safna shiru tayi kamar bada ita yake magana ba, dan haka jalal ya rike gyalan yana kokarin
cire mata, suna cikin haka sukaji. anturo kofar jalal ya sake gyalen ya juwo da sauri sai da
gaban shi ya fadi ganin ummi adakin safna kowa mikewa tayi afirgice.
jalal yaje ya rike safna ajikin sa , sannan yace ummi lafiya kuwa?

jalal lfy lau, safna ni kika gani kika firgita haka sai kace kinga dodo, daga na fada gaskiya,
lallai dama jalal yace kina son sa sai yanzun na tabbatar da haka.
zuwa tayi har jikin jalal ta jawo safna jikin ta, tace ki kwatar da hankalin ki kinji yata, niba kin
ki nake ba, duk abinda jalal ke so dole nasoshi


jalal dadi yaji har ran sa ,sai murmushi yake.
ummi jan safna tayi zuwa kojerar dake gefe suka zauna ta kwatar da ita ajikin ta tana shafa
kanta, tace safna kinyi kyau sosai, sai dai nasan ba ,dan gyara kiba, da jalal zai yadda yadan
kara mana kwanaki da an gyara ki.
jalal ya kalli ummi yace wani irin gyara ne wannan?
tace gyaran jiki mana irin namu na mata, kai nasan bazaka fahimta ba kabani ita kwai koma
meye zaka gani.
au ummi gyaran ma har sai tabar dakin nan, to abar gyaran mana ko yanzu ma ai a gyare
take.
ummi dariya tayi tace jalal ko sati biyu ne kabani na dan gyara ma ita, kai dan baka da kunya
ma ina ma magana kana mayar min, ke safna rabu dashi tashi muje.
jalal bin bayan su yayi yana fadin ummi ni dai gaskiya bana son wani gyara.

tsayawa tayi tace au biyomu kayi, jawo safna tayi tace jeka da ita, ai bansan tsumuwar taka
takai nan ba.
kunyar ummi ce ta kama jalal yace kai ummi me yayi zafi kuma toh shi kenan kuje, kafen ya
gama magana ummi tayi gaba, dan haka jalal ya rike mata hannu yakai ta har dakin ummi yace
ummi gata nan.
ya juya ya fita ummi ta juyowa tayi ta kalli safna tana murmushi tace jeki dakin ku, ki kwanta
kinji 'yata.

cikin dare jalal kasa bacci yayi sai juyi yake agado yaso ya kasan ce da matar sa tunani kala
kala ne azuciyar shi yana mamakin ummi, wani irin abu ne wannan da fah ta nuna bata son
akawo safna dakin sa, har tana ikirarin safna bata isa ta hada gado dashi ba, lallai akwai wata
akasa mikiwa yayi ya fara zagaye dakin to ummi me take nufe akwai abinda take shir yawa so
take taraba ni da safna, lallai kwai rigima sai dai ummi tace bani da kunya amman dau ko
matata zan yi.

fitowa yayi ya wuce dakin ummi ya nufi dakin su safna ya tura kofar ya jita kulle ya fara
bugawa ahankali muryar safna yaji tace waye, haka ya tabbatar mai ba bacci take ba, dan buga
kofar da yayi be isa ya tada me bacci ba, yace nine bude min kofa.

bayan ta bude kofar ya kama hannun ta yace zo muje.
cijewa ta fara yaya ummi fa zata yi fada.

tsawa ya daka mata babu ruwan ki kizo muje kawai.
kin zuwa tayi yaya kairat fa, ita kadai zan bari.
eh barta zo muje , haka jalal ya wuce da safna dakin shi.
ya daura ta agadon shi komawa yayi ya sawa kofar key
[11:33AM, 12/6/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜



Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn yazeed📊


58-60

Jalal dawowa yayi gurin safna ya zauna daga gefe ya kalli agogo karfe 01:11 yace safna ina
cikin wani haly , yanzun yaya zamuyi?

safna shiru tayi dan bata fahinci me yake nufe ba.
safna yaya ina magana kin yi min shiru.
yaya toh me zan ce maka nifa tsoro nake ji kar ummi ta ganni anan dan Allah ka barni na
koma .
safna bana son irin wannan maganar ki bari babu inda zaki , tashi kije kiyi alwala.
kallon jalal tayi taga ya daure fuska
dan haka ta mike jiki babu kwari ta shiga toilet
lokacin da ta fito hawaye ne afuskar ta tafara boyewa dan kar jalal ya gani, shi ma tashi yayi
ya shiga toilet be jima ba ya fito bayan sun ida sallah jalal ya bude daya daga cikin akwa tunan
ta ya dauko wata rigar bacci me kyau ya mika mata kin karba tayi yace bada ke nake magana
bane safna me yasa kike min haka, kinga fa dare kara yi yake. kalon rigar tayi ta ganta yar karama ko hannu bata dashi kuma bazata wuce cinyar taba dan
haka tace nifah sanyi nakeji.
murmushi yayi yace sanyin sosai kikeji ko kadan?

da saurin ta tace sosai.
jalal yace yauwa kin gama daidai kenan karba kisaka ni dama zafi nakeji kinga kenan zamuyi
daidai.
mika hannu tayi ta karba ta tsaya tarasa yaya zatayi tacire kaya gaban jalal.
jalal ya fahince ta yace safna kona rufe ido nane?
eh tace dashi ahan kali, jalal ya juya baya yarufe ido.
tana cikin saka rigar jalal yace na bude kin gama ?
a,a ban gama ba.
mikewa yayi yafara taho wa yana fadin toh ni gaskiya na gaji kina so ido na yayi ciwo ne?
dasauri ta dauki zanin da ta cire tana kokarin daurawa akan rigar.
jalal ya kama zanin ya aje shi gefe toh tun daga nan fah labarin ya cen za daga karshe ma
daukan ta yayi ya sata agado , safna kuwa tun tana daurewa taga abu nason yafi karfin ta tafar
yan koke koke.
Jalal yace safna kina son ummi ta jimu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login