Showing 42001 words to 45000 words out of 47874 words
Chapter 15 - Mijin Marainiya Book Complete Hausa Novels by Fadila Lamido .pdf
halin da kike ciki da ace sanda nazo gaisuwar iya na
dauke ki da haka be faru ba, ninayi tunanin hanne zata hada da nata tarike, sai nake ga kamar
idan idan aka dauke ki zata ce annuna mata banban ci , bansan cewa bakin hali gareta ba. safna kara rugume hajiya tayi dan ita duk wani abu da yashafi iya gir mamashi take kuma ai
tun haduwan ta da hajiya na farko bata nuna mata tsana ba, kuma bata taba nuna mata
babbaci tsakanin ta da jalal da yake jikan ta ba, dan haka hajiya da 'ya'yata sun gama mata
komai tun da sun sota alokacin da basu san waye ita ba, dan haka ta dago ta fara sharewa
hajiya hawaye da hijjabin ta.
ummi ko tana cen gefe uwa kazar da aka tsamo ta daga cikin ruwa.
anty nusaiba ce ta katse musu shirun ni dama tunda naga safna sai da naji ta a raina, take naji
son ta ya kamani ashema 'yata ce.
alhaji yace ai irin abin da nake gayawa zaliha kenan yazun gashi inda abu ya koma, yanzon
me zakice wa yarki safna.
Ummi kuka kawai take ta kasa cewa komai, ana haka jarirain suka soma kuka anty nusaiba
tace safna tashi muje kiyi wanka kiba yaran nan nono, kamar jira take ta mike ta shige dakin
hajiya.
bayan anty ta gama gasa mata jiki suka fito ta sanya kaya ta haye gadon hajiya ta kwata anty
tace safna ba kwanciya zakiyi ba kibari yaran sudan ji dumin jikin ki mana.
anty nifa nagaji bacci nakeji.
ban ga ne kin gaji ba me kike nufi ko kallon yaran nan bakiyi ba fah .
anty ni bana so akai ma ummi ta rike ai su bazata ce basu da dangi ba.
anty kallon safna tayi tace karki haka safna yaran nan basu suka miki laifi ba, zadai kidau
hakkin sune kawai, ai irin haka jalal bazaiji dadi ba.
ai ni dama banson yaji dadi duk wani abu da ya shafe ummi ban son shi me sonshi ma bana
son gani wani sabon kuka ta saka tace anty dan Allah ku sa shi ya sakeni wlh bana son shi ko
ganin shi bana sonyi.
anty tace inalillahi wa,inna ilaihir raju,un kar ya kike safna kina son jalal, kar ki yadda laifin
ummin sa ya shafe shi dan baya goyan bayan ta
suna cikin haka hajiya fatima tashigo da yaran ta daura macen jikin safna tace bata nono
tasha sai kuka takeyi.
safna kallon yariyar tayi take taji son ta ya kama ta amman tana bakin cikin kallon wani abu
da shafi ummi dan haka ta fara kuka, hjy fatima tace safna bata mana.
sukuyar dakai tayi ta rufe ido, anty tace ai tace bazata basu nonon taba.
hajiya fatima ta bude baki zatayi magana su kaga jalal ya shigo bece komai ba illa mika hannu
da yayi hjy fatima ta saka mai na mijin ya sake cewa bani dayar batayi musu ba ta daukota
ajikin safna tamika mai juyawa yayi ya fita.
yana fitowa ya samu ummi makure taci kuka har ta gaji ya tsuguna ya mikawa ummi yaran
yace ummi gasu safna tace bazata basu nonon taba.
cikin tashin hankali ummi ta mike, dakin ta nufa ta samu safna ta kifa kai tana kuka ajeye
yaran tayi abayan safna ta tsuguna tarike kafar safna tace safna dan girman Allah kiyi hakuyi
kiyafe min, nasan na tafka babban kuskure nayi nadaman abin da na ai kata safna ina cikin
wani hali, dan Allah ki tausa yama yaran nan, haka ummi taita magana safna batace ta komai
ba ga yaran sai faman kuka suke, gani tayi safna bazatayi magana ba ta mike ta fita zuwacen
sai gasu da alhaji .
alhaji na shigowa ya zauna akan wata kujera dake gefe yace safna wannan hukuncin da kika
dauka yayi tsauri da yawa ni bance karki nuna fushin ki ba, amman inason fushin ya tsaya akan
zaliha ka dai, ya sake cewa safna indai kin daukeni uba agare ki toh na umarceki da ki dauki
yaran nan kibasu nono. cikin sauri tasa hannu ta dauke mace dan ita ke kuka na miji har yagaji yayi bacci, daddy na
kallon safna sai ciki cikin rike yarinyar take, yajuya yace zaliha tashi mutafi gida.
suna fita falon alhaji yace nusaiba je ki nuna mata yadda zatayi, alhaji sallama yayi wa hajiya
suna fita suka samu jalal awaje ya hada kai da gwuiwa
[9:03PM, 12/23/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜
Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeedí ½í³
1017-1019
Alhaji yace jalal tashi muje gida, jalal beyi musuba ya tashi ya shiga mota ko acikin mota babu
me ma wani magana har suka isa gida, ummi taso suyi magana da alhaji amman yace ta bari
sai gobe, haka ta shiga daki badan ran ta yaso ba.
alhaji ko rike hannun jalal yayi suka shiga daki bayan sun zauna alhaji yace jalal ka kwatar da
hankalin ka insha Allahu komai zai wuce.
cikin sauri yace daddy naji fah abin da safna take fada wai bata sona har tana cewa wai ace
min na sake ta.
alhaji yace ya isa jalal kayi hakuri bacin rai ne ya sata fadan haka, kama ta uzuri yariyar tana
da hankali,lallashin ta zakayi zata sakko.
washe gari jalal yana shir yawa ya nufi gidan hajiya yana zuwa ya samu hajiya da anty
nusaiba suna hira bayan ya gaida su hajiya tace dama yanzon muka gama mgn akan sunan da
za,a sama yaran nace sai asa sunan iyayen ka.
jalal yace a,a hajiya abarsu da sunan su ummi ma bata so asa sunan ta.
hajiya tace ai jiya muyi mgn da ita tace asa ma macen saudatu.
hajiya dan allah ki dai na biyewa ummi kuma ni nafison abar su da sunan su, be sake cewa
komai ba ya shige dakin ya sami safna zaune tana cin tuwo hada fuska tayi nema guri yayi ya
zauna kusa da ita.
shiru tayi bata ce komai ba, jalal yace safna ba gai suwa.
gani yayi bata da niyar magana yace toh ni bari na gaida ki inakwana ?
ban za tayi dashi ya sake cewa safna fushi kike dani to me na miki?
daga kan ta tayi tace kawai ganin ka ne banaso, sabo da tun da na samu lbrn mahaifiya ta naji
na tsani dangin ta, mahaifiya ta tayi rayuwar bakin ciki na rashin iyayen ta har ta koma ga Allah
bata gansu ba wannan ya nuna min basa kaunar ta da suna kaunar ta basu manta da ita atiti ba
dan haka bana son wani abu ya hadani da dangin ta bana sonsu bana kaunar su. shiru jalal yayi ya dukar da kai zuwa cen yace safna kinga duk cikin wannan abun ummi ce me
laifi tunda ita ce ta bata musu rai har suka manta sun taho da ita.
ciki kuka safna tace bawani bacin rai da zaisa ka mance da danka yan zon Kai zaka dauki dan
ka ka,ajeshi atiti kace mai bari kaje kadawo, su mahaukata ne?
jalal yace naga alaman baki da hankali mikewa yayi zaifita safna ta bude baki tace kaine dai
baka da hankali.
juyo wa yayi ya dawo yace abin har yakai haka?
eh yama wuce haka tun da kafito ta tsotson ummi.
jalal ji yayi kamar ta caka mishi allura azuciyar shi , yace safna kar ki manta fa ummi mahaifiya
tace.
safna bude baki tayi tace jalal ai uwa batafi uwa ba.
tun da suke da safna bata taba kiran shi da sunan shi ba sai yau, kara kule wa yayi yace toh
nagane abin naki rashin mutunci ne
toh kisan magar da zata rika fitowa daga bakin ki dan bazan dauki wula kancin ki ba inkuma
kina ganin wasa ne kikara fadan wata magana kiga ni wlh mugun duka zan miki.
daidai lokacin su hajiya dake falo suka soma jin hayaniyar su aguje suka shigo daidai lokacin
da safna take cewa sai dai mudake juna, jalal kuwa yayi kanta gadan gadan anty ce ta riko shi
iya karfin ta amma sai kwacewa yakeyi hajiya ce ta shiga tsakiyan su ta girgiza jalal tana fadin
abduljalal dubeni nan me yayi zafi hake, kai da nake yabon ka. yace hajiya wannan yar karamar yariyar zata duga fadamin mgnr da taga dama ni sa,anta ne?
hajiya tace a,a kayi hakuri fita muje, juyawa yayi ya fita yana huci anty tabi bayan shi.
Hajiya ta kamo hannu safna data manne da bango ta zaunar da ita bakin gado tace safna
kintaba jin laifin wani ya shafi wani, shi meye nashi, me lefi daban wanda ake hukun tawa
daban, karki kara safna dan Allah kisawa zuciyar ki salama.
safna kuka take sosai tace hajiya toh kice mishi ya sake ni.
cikin fada hajiya tace yazon dai kina nufin babu wanda zaigaya miki mgn kiji ko ?
girgiza kai tayi bahaka bane Hajiya ni cewa nayi ya dai na min magana.
haba safna ban da abinki ta yaya zakice ya daina miki mgn mijin kine fa dan Allah karna kuma
jin wannan mgnr abakin ki kuma kije ki bashi hakuri, safna ki daina gayawa jalal munanan mgn
akan ummin sa uwa uwa ce safna kuma hannun ka baya rubewa ka yanke kayar , safna yanzon
zaliha ta gane kuran ta ya kamata ki yafe mata, tana cikin wani hali ki taimaka mata ta samu ta
daidaita da iyayan ta, saboda ayanzon ke da baki da iyayen kin fita kwanciyar hankali dan kin
rabo dasu lfy , itako ga iyayen tana kallon su amman ba dama taje gurin su, sabo da suna fushi
da ita, toh dan Allah kiyi hakuri ki yafe mata, yanzon anriga an zama daya, ban da matsayin ta
na yar mahaifiyar ki, kuma ga jikokin ta nan agaban ki, dan Allah mu yafi juna kwata kwata
duniyar ma guda nawa take.
jikin safna yayi sanyi tace shikenan hajiya amma ni abin da yake bani haushi yaya za,ayi
mutun ya manta da dan sa.
hajiya tace bar wannan maganan safna kandara ce haka Allah ya so.
tace dama hakane sai mutun yayi abu da gangan yace wai kaddara ce.
hajiya tace safna bar wannan maganan tashi kije kibawa jalal hakuri dan naga yayi fushi sosai
.
suna fitowa suka samu anty nusaiba tana rarrashin jalal yana zaune idon shi ja wur kallon
safna yayi ya girgiza kai itama kallon shi tayi ta neme guri ta zauna tayi shiru.
anty nusaiba ciki ta shiga hajiya ma barin gurin tayi aka barsu su biyu, cikin sauri jalal ya mike
zai fita safna ta tashi ta riko rigar sa, kallonta yayi yaga tayi kasa dakai
bece mata komai ba, ahaka suka tsaya safna na rike da rigar jalal har tsayon minti 15 ba
wanda yace wa kowa komai
07014197556
[6:58AM, 12/27/2016] Fadeela lamido: í ½í²˜í ½í²í ½í²MIJIN MARAINIYAí ½í²í ½í²í ½í²˜
Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeedí ½í³
120-122
Gani yayi bata da niyar magana dan haka ya zame rigar shi yayi gaba.
safna naganin ya wuce ta fara kuka, sai da ta gaji da tsayowa ta wuce daki, ta shiga ta samu
jarirain sai kuka suke, cikin tausayawa ta dauke su ta sasu acinyar ta.
tana cikin haka taji muryan alhaji da ummi suna gaida hajiya, bayan yaran sun sha nono ta
kwantar dasu tamike dan gai da daddy sai da ta saka hajjabi sannan ta fito.
alhaji naganin ta ya washe baki , gwaiwan ta tasa akasa ta gaida shi ya amsa, ta juya barayin
ummi kanta akasa ta gaida ta, amsawa tayi cikin farin cikin .
safna mikewa tayi zata bar wajan alhaji ya dakatar da ita.
ahaji yace wata magana nake son muyi me mahimmanci hajiya kisa mana baki dan naga
safna har yanzon bata huce ba,
hajiya gyara zama tayi.
alhaji yace yazon daga gidan baffa muke nashiga ni kadai na mai bayani abin da ke faruwa
amman kwata kwata yaki saurara ta wai mun shirya karya ne nida zaliha daga karshe cewa yayi
indai da gaske ne , toh nakawo mai yarinyar.
alhaji na kaiwa nan yayi shiru
hajiya tace toh amman da naso abari ayi suna tukun, shiru suka yi na dan wani lokaci zawacen
hajiya tace, safna tashi ki shirya.
mikewa tayi cikin daure fuska ta shiga daki ,bata jimaba ta fito ,ummi ce tabita da kallo taga
bata fito da yaran ba, bata ce komai ba ta mike ta shiga ta kwaso yaran ta fito ganin inda safna
ta daure fuska yasa hajiya ta mike tana fadin bari na dauko gyale na, naraka ku.
bayan sun shiga mota hajiya tace ina jalal ya kamata ace tafiyar nan dashi akayi ta.
alhaji yace kwarai kuwa bari na kira shi, daga wayar shi yayi ya kira jalal, yana dauka alhaji
yace jalal kayi maza ka same mu gidan baffa gamu ahanya harda safna.
jalal najin an abaci safna yaji ranshi ya baci dan haka yace daddy bani da lafiya ne kaina
namin ciwo.
alhaji yace ka daure dai kazo ina jiran ka, bayan ya kashe wayan yace safna halan kunyi
rigima da jalal ko?
shiru tayi bata ce ko maiba, sai hajiya dake zaune kusa da safna tace ai kowa dai yau anyi
tsiya sosai dan naga jalal ya tun zura
alhaji yace yauwa dan indai kaji jalal na fadin kansa na ciwo toh akwai bayani.
nan dai alhaji ya farawa safna nasiha har suka isa gidan.
bayan sun fito daga motar dukkan su suka shiga cikin gidan safna tun akofar gidan ta fara
kuka.
sun shiga da sallama wata dattijiyar mata ta fito daga daki cikin sauri safna tabi da kallo ,cikin
sauri ta karaso ta rike safna ta kalli fuskar ta sosai ta juyar da idonta kafar safna cikin kuka ta
fara kiran baffa tana mai magana cikin fillanci.
fitowa yayi arude ya nufi safna kafar ta ya kallah shima kuka ya fara yana fadin Allah da girma
yake tabas yar saudatu ce kafar su iri daya cikin sauri yace rahane sa mana tabarma.
bayan ta shinfida tabarma kowa ya zauna ummi ko sai rabe rabe takeyi.
Itako safna tunda baffa ya rike hannun ta be sake ba tana zaune kusa dashi, abayan sun gaisa
alhaji ya gabatar da mahaifiyar shi agurin baffa da matar sa rahane, baffa dadi yaji sosai sannan
ya shiga yi mata godiya akan abinda alhaji yake mai yabon alhaji yayi sosai daga bisani ya
shiga saka mishi albarka.
hajiya ma dadi taji sosai ganin inda baffa kesawa danta albarka dan haka tace toh baffan
yaudai gaka ga yar saudatu dan haka yanzon sai mu yafi juna dan Allah abar tuna baya dan
zaman duniya dan hakuri ne, kuma in mune yau ba mune gobe ba dan Allah ka yafewa zaliha .
sai alokacin baffa ya kula da ummi data makure agefe yace hajiya ina jin bakin ciki idan na
tuna rashin mutuncin da yar isakar yariyar cen tamin tasani atashin hankali da bakin ciki badan
ina da tsawon kwana ba toh da bakin cikin yariyar nan ya kasheni tun lokacin da aka daura
mata aure da alhaji babu wanda yasan gidan sai yayar ta rabi, dan haka da muka ta dade bata
zoba na yanke shawaran nadauki mahaifiyar ta da kanwarta muje mugano ta ita da danta har
gidan yayarta naje tamin kwatan cen gidan .
bayan mun sauka amota sai muka fara tafiya da kafa dan iya kudin mu kenan kona komawa
gida bamu dashi tafiya taki karewa har saudatu ta fara gaji danaga ta gaji sosai gata ba karama
ba bare adauke ta , sai muka zauna gindin wata bishiya saudatu na zama ta fara gengyadi
ganin yama na karatowa mamarta ta tashe ta amman sai tace bata huta ba dan haka muka
barta wajan mukace bari muje mudawo, cikin ikon Allah muka isa gidan tunda me gadin ya fada
mata ga baki sai gata rike da hannun jalal yana karami cikin bacin rai tace wai lfy kuwa.
har yau na kasa mance wannan kalmar haka na daure nace naga kusan wata shida baki zo
bane nace bari muduba ko fly, cikin sauri tace lfy ta kalau kuje gida inanan zuwa, mahaifiyar ta
na kokarin magana tace a,a mama dan Allah kuyi sauri kar kawaye na su fito su ganku zasumin
dariya har tana kiran me gadin wai ya bude mana kofa. haka muka baro gidan cikin bacin mahaifiyar ta ttun anan ta soma kuka haka muka zauna
mukayi ta kuka sai yamma likis muka tuna da saudatu saida mukayi tafiya me tsayi muka isa
wajen, wayam muka samu gurin babu kowa duk muka